Showing 81001 words to 84000 words out of 144591 words

Chapter 28 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2361

fushi bale yaji? Tabasss sai na tabbatarwa kowa akasin tunaninsa.....in sha Allah sai na nunawa SHAHEED idan bai san darajata da ciwona ba Ni na san kayana....'

"Ke bana son ki ringa irin kallon nan fa? Tunanin me kike yi???" Zahra'u ta katse Najeeba daga duniyar tunanin da ta afka

Murmushi kawai najeeba ta yi ta koma dakin bata ce mata komai ba

Zahra'u ta sauke ajiyar zuciya da addu'ar Allah ya sanyaya lamarin nan, Allah ya sa zaman kawai za'a musu fada ne ace ta komawarta dakinta , ita tana mamakin Anmy wani lokacin da idan Najeeba ta yi fushi take kyaleta a nan, wai sai tace ta bashi space ya gane darajarta, .....bata san hakan da take yi koyar da Najeeba abubuwa bane dan kuwa Najeeba bata san wasa ba...... Allah ya kyauta.



Bayan sallar la'asar..................


26
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




27





Bayan sallar la'asar Najeeba ta nufi falon Anmy

Bata wani yi shigar daga hankali ba, has??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????alima riga doguwa ce a kasan hijabinta irin rigar nan ta barebari budadiya, sai carbinta fari, Muhammad na biye da ita yana rike da gefen hijabinta yana yi mata firar shi cake yake so kuma ita yake so ta yi masa

A lokacin da suka shigo falon ta Wan dakata saboda ganin falon da baki

A hankali ta juyo inda Muhammad yake kasa kasa ta ce" cake? To, ka bari in dawo Sai mu yi in sha Allah"

Murmushi yayi, wanda mahaifinsa ya hango tun daga inda yake zaune , hakan ya sanyaya zuciyarsa har ya Wan sake zuba musu ido kafin ya dauke a nutse yana lumshe idannuwansa cike da jin du fushin da yake ciki da ita du idan ya ganta sai ya ji fushin na kawarwa harma bukatuwa irin ta sunna da kasancewa da abin kauna na darsuwa a zuciyarsa

Dubansa ya kai kan Anmy, ya sake duban bawan Allahn da aka kawo aka shinfidar a nan, ya kuma bi matarsa da ?a?ansu da kallo Yana jin tausayinsu na kama shi, uwa uba wace take zaune kamar bata da lafiyar kwakwaluwa saboda du a firgice take, tunda suka shigo ta so kifawa saboda kallon falon sai da mahaifiyarta ta zaunar da ita kusa da ita sannan ta sada kai jikinta na rawa

Karasowa Najeeba ta yi ta gaisar da mutanen falon a jimulce ta hanyar fadin" Barka da warha"

Daga haka ta karasa ta zauna a nesa kadan da Anmy, sannan yayi kamar gefen SULTAN, hakan ya sa a dole sai ya karkata idan dai ita zai kalla, wanda hakan bai yi masa ba, ya so ta zauna daf da mamanta shi kuma ya ringa kallonta a haka koda abin ya tsawatar mata ya samu sai kawai yayi daga inda yake.

Anmy ce ta ba Malami damar yin bayanin abinda yake tafe da bakin nan

A lokacin da malami ya koro da bayanin nan NAJEEBA ta dago ta kafe su da ido baki dayansu, hakanan Sultan bai san lokacin da ya kafe mutanen da kallo ba, har malami ya gama bayani ya nemi afuwa sannan ya mike ya bada waje ya dakata daga kofa yana jira a yi Kiransa

Shiru ne ya wanzu a wajen na lokaci mai yawa

SULTAN gaba daya tsigar jikinsa tashi take yi na balakin dake kuno masa zuciya, haka kuma wani irin fargaba ya darsu a cen cikin zuciyarsa da tsoron jin tabatuwar zancen, sai dai ya sani dole zai ji, hakan ya sa ya dubi bakin, a tausashe ya ce" A ina kuka san likitar? A ina kuka san bayanin cikin Gimbiya da ya bare?"

Mahaifiyar kurma kanta a kasa cike da girmamawa da tsoron magana ta ce" Bamu san likita ba Allah ya kara maka lafiya, bamu da wata ala?a da ita, yarinyar nan ta santa, itama a gidan uwar dakin ta ne ta santa harma abinda aya faru ya faru, ina tsoron ko maganar da ta jin ce ta sa har likitar ta kwada mata kwano a gefen fuska ? Ko kuwa Akoy abinda ya faru? Ta dai ce a shekaran Jiya ne yan daba suka tarda su suka Wan dake su, to likitar ce da ta dawo hayacinta ta nemi wayarta dan ta kirayi mahaifinta, da ta tambayi kurma ne tace bata gani ba sai kawai ta warci kwano ta rotsa mata, kuma uwa dakin nata da ta dawo daga anguwa Jiya da dare sai kawai ta Wora dukan kurma har ta biyota tace ta ce sai ta kashe ta......, ranka ya dade ban tabbata cewar maganar da kurma ta fada gaskiya bane, Ni dai ina rokon alfarmar a sa manya su saka baki su yafe mata , kudin aikin ma da ta yi mun yafe ba sai sun bamu ba"

A hankali ya lumshe idannuwansa, lokacin da take yi masa bayanan nan na fado masa a rai, takardun da ta bashi, da kuma irin yadda suka yi da Najeeba

ANMY ta girgiza kai ta kai dubanta kan Najeeba, a tausashe ta ce" Yaya aka yi kurma ta ji bayanan nan?, ko tana jin magana ba sosai bane?"

Inar kurma ta ce" Tana ji ranki ya dade, sai dai wani lokacin jin ya fi na wani lokacin, bale yanzu tunda ta zo din nan kamar jin ya karu sosai dan motsi kadan take zabura ta nuna ta ji mutun"

Anmy ta dubi kurma a nutse ta ce" Yarinya, kina ji na?"

Kurma ta dubi Anmy kafin ta gyada kai

Anmy ta ce" Wacece likita?, yaushe kika ji tana maganar ta zubar da cikin Gimbiya?"

Kurma ta bude baki sama sama ta ce" Likita, likita kawar Hajiya Turai ce, kawarta ce, nan suke haduwa , likita ta sha zubarwa yan mata ciki a gidan Hajiya Turai, Hajiya Turai ta kawota suka zama kawaye a gidanta, idan aka dauko ciki Hajiya Turai ake ba kudin sai likita ta zubar Shikenan an gama, to tace tana son mai wukar yanka, haka dai suke maganar, kullum sai Hajiya Turai tace sai sun tashi tsaye zasu samu mai wukar yanka, idan sunna maganar sai likita tace Ni munafuka ce ina ji , sai Hajiya Turai tace a'a bana ji mahaukaciya ce Ni, Ni kuma ina ji, ina jin su , ba ruwana ne bana fadawa kowa, sai ranar wata asabar likita ta zo da dare daga asibiti da rigar aiki tana ta murna ta yi jira Hajiya ta gama tsinewa Elhaji sannan tace mata yanzu ta zubar da cikin Gimbiya, Ni dai na tsorata na tsorata har na ji babu dadi saboda Gimbiya tana ba jakadi abinci tana rabawa su inata, Ama kuma ina tsoron Hajiya sai ban fadi ba, shine Jiya Hajiya ta biyo NI tace sai ta kasheni bayan likita ta kumburani dubi nan, kali nan dina"

Kurma ta so tashi ta je, da sauri inarta ta zaunar da ita tana girgiza mata kai cewar kar ta je

ANMY na kallonsu tausayi na cika zuciyarta

A hankali Anmy ta ce" A ina kuke rayuwa ne?"

Inna ta sanar musu a inda suke, harma da bayanin ciwon mijinta

SULTAN da idannuwansa ke lumshe ya bude a hankali ya yi gyaran murya hadi da dan doka sandarsa

Malami ne ya shigo ya duka

A hankali Sultan ya ce" A kai su asibiti ta kirki, a duba su gaba daya, a yi du abinda ya dace da lafiyarsu "

Malami na amsawa kansa a kasa, Sultan ya dora da fadin" Idan an dora su kan maganin da ya dace, a basu mazauni mai kyau malakinsu, sannan a zuba musu abinci...., yaran su koma makaranta, mahaifiyarsu ta samu aikin da zai bata albashi mai tsoka wanda ba zata wahala ba da shekarunta"

Nan ma malami yayi ta godiya hakama su Inna

A hankali bayan ya gama sauraron maganar malami ya ce" idan ya samu sauki, a sake zuwa da shi, zamu bashi aikin da ya dace da shi "

Nan ma godiya suke yi kamar su fashe da kuka, kai ina hawayen ma take yi, har sai da Anmy ta budi baki a tausashe ta ce" ki daina kuka, ku ci gaba da addu'a, in sha Allah zamu dauki nauyin karatun su har su gama, kar ku damu da wa'inda suka bi ku, zamu muku tsakani da su"

Ina kam kuka take yi sosai, hakama mijinta, aka kama shi aka mayar da shi baro dan a je mota da shi

Malami dake duke yana sauraron SULTAN

A tausashe SULTAN ya ce" an tafi kaita wajen kilatar?"

Malami ya ce" A'a ranka ya dade, dama jira ake yi duhu ya shigo kafin a Kaita"

Sultan ya sada dubansa, a hankali ya ce" Ina kawo kararta, a rubuta a shigar da karar hakan, ina so ta amsa karan zubar da cikin giwatah da ta yi, ina so a yi mata hukuncin da ya dace da ita idan an gama binciken rai nawa ta salwantar...... innalilahi wa Inna ilaihi raj'une "


"Allah ya huci zuciyar ka, Allah ya sanyaya zuciyar ka, in sha Allah sai mun bi hakin jinin bayin Allah "

Daga haka ya mike ya fice

ANMY ta sake sauke ajiyar zuciya tana dubansa ta ce" ka ga abinda nake fada maka?, yaya za'a yi ka yarda da maganar bare a kan ta iyalinka?, me ka taba kamata da shi da za'a yi mata shari irin wannan ka yarda ba tare da ka bincika ba?, Wani lokacin mukan tauye na kusa da mu ne dan jin dadi ko kuwa dan zalunci????, nan na kawo likita ta duba gwajin da aka yi mata ta min bayani, ina kallonka baka nemi jin abinda likita tace ba saboda kai ka riga ka yarda da abinda dayar likitar tace da kai saboda ka gama kankara hakori a kanta cewar zaka kawota cikin iyalinka......, to likita tace hoton cikin da ta gani baby uku ne, koda wani ya zube tana kyautata zaton daya ne, kana nan kana fushi da abinda ka sani sarai ba haka bane, Allah ya kyauta"

Daga haka Anmy ta mike ta nufi dakin ta saboda ta basu waje koda zasu tattauna

NAJEEBA ta lumshe idanuwanta tana sake jin kaunar addinin Musulunci a cikin zuciyarta.....

Tabas an gigitata an firgitata, ta yi kuka ta yi kuka a cikin kukan ta fadawa Allah ta roke shi alkhairi ta roke shi sakaya......sai gashi cikin ruwan sanyi an zo an fadi maganar da take kyautata zaton a yanzu ya yarda da maganar wani baren fiye da tata.....?

Murmushi ta yi kawai ta mike da nufin tafiyarta, sai dai tun bata yi taku biyu ba ta ji Muryarsa a hankali ya furta" BEEBAH"

NAJEEBA ta dakata, saboda duk rintsi bata iya take Muryarsa ta tafi ba, hakan ya sa ta juyo ta zauna kanta a kasa tana sauraron sa

Kallonta yake yi yana son ganewa, da gaske ta yiwu Akoy cikin? Ta yiwu ukun ko biyu? Innalilahi da gaske Akoy shi?

A hankali ya ce" BEEBAH, ki kaleni mana, in sha Allah ba zan kyaleta ba, Ni zata yiwa karya a kan ki?"

Najeeba ta dago cike da takaici tana kallon sa, a hankali ta ce" Me zaka yi mata?, za'a gurfanar da ita ne in asirinta ya tonu a Kaita kurkuku ko a ci tarar ta ko?, to Ni dai kar a saka da nawa laifin, domin na riga na biya mata laifin da ta aikata...., kuma zan ci gaba da biya mata, dan kuwa yanzu haka Ni ban yarda da maganar yarinyar nan ba, kazafi zata yi mata ne kawai"

Kallon NAJEEBA yake har ta mike zata wuce

A nutse ya ce" Menene?, ba gashi gaskiya ta fito ba?????"

Najeeba ta juyo kirjinta na bugawa ta sauke kausasun idanuwanta a kansa ta ce" Gaskiya ta fito? Da yarinyar nan karama ta fada maka ka yarda da maganarta fiye da tawa? Gaskiya ta fito bayan ka gama yarda da maganar wace ta tsara maka maganar nan a kaina?, gaskiya ta fito a yanzu da ka gama zaunar da Ni kana jiran jin laifina dan ka nuna min iyakata? Me ake da ita gaskiyar da Ni bata min rana a wajen ka....? SHAHEED ka dauka karya ce, Ni ce nan makaryaciyar kuma da akace na zubar da ciki gaskiya aka fada........, na zub"

"Ya dace ki sassauta muryarki, ki daina wannan abin, sannan ki daina daga numfashinki saboda kar ki yiwa kanki ila sannan ki yiwa cikina" ya katse ta yana mikewa saboda irin yadda take jan numfashinta

Kallon fuskarsa take yi a lokacin da ya tsaya a gabanta, ya miko hannu zai taba hannayanta

Da sauri ta ja baya idanuwanta na cika da hawayen da ta barsu suka bale mata

Sultan ya sake fuskantar ta a hankali ya ce" PLZ mana, zo jikina"

Najeeba ta bi hannayensa da kallo da rawanin da ya cuje ta sauke a kan sajen fuskarsa............

Hawayenta na diga ta bude baki a hankali ta ce" Ba zan taba yin daraja a duniyar ka ba , ka dauki fada da gareni fiye da kima, saboda wannan kana wulakantani....., babu ruwan ka da me zan ji, ba damuwarka bane idan na firgita da yannayinka a kaina............, ya zamo ko a yanzu zaman da muke Nadiya ta fi Ni gaskiya idan abu ya tunkaro na bacin rai wanda ya haWani da ita........."

A hankali ta ja kukan da ya rike makogwaronta ta ce" SHAHEED bani da wata daraja da zan samu rarashi sai ka gama wulakantani....., bani da wata dama da zan fada a duba kai tsaye a yarda har sai an kai ruwa an kai mari, Sultan baka min adalci a cikin adalcin da kake rabawa duniya......"

A hankali ya furta" BEEBAH PLZ, karamin abin nan ne zai sa ki ringa fadin haka......, zo mu tafi bangarena...., ko ki zo mu je bangaren ki....idan ma fita kike so mu yi zo mu je......"

"Kana tunanin a yanzu....., Ni Najeeba zan iya kuma sha?ar wata iska tare da kai????"

Kirjinsa ya wani irin bugawa, ya kausasa idannuwansa yana kallon ta

Najeeba ta yi murmushi mai mugun ciwo kafin ta juya ta nufi coridor ta bude ta nufi bangaren ta a hankali ta bude tana shiga ta murda ky ta barshi a jiki

Ya dan jima yana kallon inda ta bi, a hankali ya dauki hanyar da takalmin fatar dake kaffafuwansa ya je ya kama kofar ya murda, jinta a rufe ya sa ya shige ta bangaren Nadiya, bai nemeta ba ya wuce bangarensa direct ya dauki ky din na Najeeba ya karasa ya tura ky din, sai dai sam ya ki shiga, wannan dalilin ya sa ya gane a jikin kofar ta bar ky din nata kenan?????

Ajiyar zuciya ya sauke ya girgiza kai, a nutse ya koma bangarensa ya shige bayi dan sake yin wani wankan

Wankansa har shiryawarsa sun daukar masa kusan awa biyu hakan ya sa da ya fito magariba ta kusa, sai dai a aunawar da yayi yana iya shiga bangarenta ya fito ya damu sallah


A nutse ya shige shi kadai bayan yan rakiyar sun raka shi

Ganin fitilu a kashe ya sa ya kunna ya nufi dakin ta kai tsaye

Ky din ya gani a jiki ya murda ya shiga , sai dai bata nan

Har zai juya ya fita ya juyo da sauri sakamakon yadda saman gadonta ke barbaje da kaya

Kirjinsa ne ya sake bugawa, a hankali ya karasa da tunanin me yake faruwa? Domin a duniya sai dai ya sanarwa mutane wacece najeebansa wajen tsafta da tatare waje, sam bata barin waje a haka , bale kayan du ninkaku ne kawai dai an barbaza su ne a saman gadon

Zai juya din dai idannuwansa suke fizgarsa da wata takarda dake saman kayan

A hankali ya ajiye sandar dake hannunsa, lokaci daya ya kai hannun nasa ya dauko takardar yana bin tsararren rubutunta da kallo kafin ya nutsu ya fara bi kirjinsa na wani irin yankewa ya fadi

A hankali ya shiga karantawa kamar haka" *.......





>?y?>?y?>?y?>?y?>?y?>?y?
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




28



*ASALAMU ALAIKUM.......DASHI KIKE DA BUKATA? NA DUKAN WANI ABIN BUKATA KAMA DAGA KAN KAYAN DAKI, TUFAFI, KAYAN KICIN, ABIN HAWA, JAKA FA TAKALMA, HAR ZUWA NA KUDI KI TUNTUBI WANNAN NUMBAR.........IN SHA ALLAH ZAKI SAMU BIYAN BUKATA A DUK INDA KIKE 08038856944 Adashen y'an gata sai a duniyar AMINA*







*SHAHEED, I TRD......ZUWA YANZU NA GAMA YARDA CEWAR BA ZAN TABA SAMUN MATSAYIN DA BARAN GIDAN NAN YA SAMU A WAJENKA BA, GASHI KUMA IYAYENMU BA ZASU TABA DUBANA DA MAGANAR NAN BA, ANMYNA KADAI TAKE GANE ME NAKE CIKI, SAI DAI ITAMA BA ZAN IYA FIITOWA IN CE DA ITA GA HALIN DA NAKE CIKI BA WANDA YAKE TSAKANIN NI DA KAI NE....., SHAHEED NA GAJI DA ZAMOWA KULUN WACE BATA DA GASKIYA A CIKIN AL'AMURRAN RAYUWARKA BA , BA ZAN TABA SAMUN ADALCI A ZAMAN AURE DA KAI BA...... SHAHEED IDAN KA MIN ADALCI KA SAKA SANARWAR SAKINA A TV KO A YANAR GIZO ZAN GANI, IDAN KUWA KA GA BA HAKA BA NAN DA WATANIN DA MUSULUNCI YA BADA IN MACE DA NAMIJI BASU HADU BA MATSAYIN MA'AURATA ZAN DAUKA CEWAR BANI DA AURE.....MAGANAR CIKI KUWA KAMA MANTA DA SHI DOMIN TUNDA NA DAUKI HUKUNCIN BARAR DA SHI A LOKACIN DA BAN BARAR DIN BA, DOLE ZAN SHA LADAN HUKUNCINA.....DAMA ME ZAN YI DA CIKI DA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login