Showing 108001 words to 111000 words out of 144591 words

Chapter 37 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2346

siyarwa masu kyau da tabo zuciya a farkon gani.

Muna da grup wanda muke baje kolin kayan gyara tun daga kan fata har zuwa pp na mace ko namiji

Ku zo mu je tare......
KU ZO KU RAKA MU
KU NUNA MANA KAUNA
KU TAYA MU TASHI DA KARFIN IKON ALLAH......

*TAKU CE, SAJIDA NIJAR*

Domin karin bayani a tuntubemu ta layinmu kamar haka

*CEEO SAJIDA ELHAJ SA'IDU KULLEY*

+22793811618


*ADJOINTE AMINA MAIKUDI ABDULAHI*

+234 803 885 6944



Labari

A hankali ya ce" To Ama, me yasa kike tunanin cewa, zaki yi ta sabon Allah har haka ke kuma ki ga karshe mai kyau ? Kin san kuwa cewar kisa ne kike yi saboda na tabbata a cikin abinda kika salwantar Akoy wanda aka busawa rai, ko kuma du cikin taimako ne a tunaninki shi yasa har kika takani Ni SULTAN SHAHEED?"

Tsigar jikin du wani wanda yake wajen sai da ta tashi saboda yana maganar a hankali tana hauhawa har ya zo karshe cikin sauke maganar da zafin da ya sa du suka sada kai, sai shamaki dake furta Allah ya huci zuciyarka.

Bai yi kasa da gwuiwa ba ya ce" Ni zaki Raina, ki shiga rigar likitancin da kika karanta, ki yi min karya a kan iyalina sannan ki koma gefe kina kalona bayan kin san kin zubar min da cikin matata, an fada maki kowani Wan halak ake yiwa takakiya ne?????"

Nan ma hakuri suke ta bashi, wanda bai yi wani tasiri ba, yana duban ta da kyamar yannayinta ya ce" Ki yi gaggawar tuba a wajen ubangijinki sannan ki bi du Wanda kika san kin cutar, saboda Allah baya yafe laifin dake tsakanin bawa da bawansa........., idan kika yi haka watakil ki samu salama da matse rayukan da kika yi idan kin je wajen da baki da wata hanyar guduwa ko tsira sai kin amshi Sakamakon ki a hannayen ki"

Mahaifiyarta ta fashe da kuka tana girgiza kai, a raunane ta ce" Allah ya huci zuciyarkkkkkkkkkkkkkkkk


"Ki mana shiru, ki bari ya gama magana!" Sarkin bulala ya fada

Da sauri Anmy ta Dube shi da duba kakausan da ya sa ya sada kai kasa, sannan ta dubi mahaifiyar IZRANE tausayin matar na kama mata zuciya.......

Kwarai cikin haihuwa babu kalar wanda baya fitarwar, sai fatan Allah ya shirye mu ya shiryar mana da ?a?ana

A hankali Anmy ta furta" Ki daina kuka, ki daina kuka "

SULTAN da idannuwansa ke lumshe shi da kansa kukan mahaifiyar IZRANE ya taba masa zuciya, shine dalilin da ya sa ya kasa ci gaba da maganar ma

Abiey ya sake dubansu, a tausashe ya ce" A yi hakuri, Allah ya sanyaya ya kara bada hakuri, IZRANE, ki nemi afuwa a wajen GIMBIYA, sannan ki nemi du Wanda kika cutar da saninki ki nemi afuwar sa, mutuwa fa gaskiya ce, kwonciyar kabari gaskiya ne, tsayuwa gaban Allah gaskiya ne, kuma wuta da aljanna gaskiya ne, shin me yasa muke dagewa sai mun kai kanmu ga halaka a Y'ar rayuwar nan kayadadiya?, haba dan Allah, menene ribar da zamu samu wace ta fi wace take jiran mu? Wallahi bawa ba zai raina kansa ba sai cuta ta same shi, ko kuma tsufa ya salamo masa......, a irin lokacin nan da ake so ku mori lokacin ku ta hanyar da ta fi dacewa a'a, kun fi gane yin wasa da damar Ku?, ki dubi iyayenki, ki dubi yanayin da kike ciki, kin wulakantasu kin wulakanta kanki, anya a haka za'a samu yadda ake so kuwa? Duk da wani dadi da kake ganin ka samu ta hanyar kaucewa hanya wallahi daci ne ko a dandanon bakinka bale a zuciyarka....., da ace ke din matarsa ce ai na sai kin bi ta hanyar nan zaki zama matar tasa ba, shin sake da addu'a ne?, buri ne yayi yawa? Ko kuma tafiya da mashawartan da basu da tsoron Allah ne??????, mu kula fa, a yada muka zo a haka zamu koma, babu wata dukiyar da ta wahalar da mu wajen nema da zamu tafi da ita dan ta zame mana guzurin siyan piyawata a doguwar tafiyar da bamu san farkon ta ba bale karshenta!, babu wani Wan Adam din da zafin sonsa ya sa muka aikata mugwayen abubuwan da zai yi mana rakiya a ramin mu ko na second daya ba, arziki, mulki, ya'ya, mata, iyaye zamu bar komai a inda muka tarar mu shige kabarinmu mu kadai fa, shin a irin rigimar nan da bamu san kalarta ba ba zamu ringa yiwa kanmu hisabi muna nemawa kanmu sauki ta hanyar kula da kiyaye dokokin Allah ba???????????"

Ya ajiye maganarsa a hankali yana dubansu baki daya

A tausashe ya ce" Komai mai karewa ne, dadi ko akasinsa....., dan haka mu ringa yiwa kanmu adalci, wallahi Akoy tafiyar da babu abinda zai ceceka sai aiyukan alkhairai, kiyaye dokokin Allah, rike carbi, kai gaba daya idan ba'a yi da gaske aka kawar da kai daga datin duniyar ba za'a iya shiga uku, dan haka maza ki nemi afuwar su, baki dayansu kafin a yanke maki hukuncin da ya dace cikin duba da yannayi da sassauci ko dan zuciyar iyayenki ba dan ke ba!"

Sultan ya dubi Abiey, gana daya Abiey so yake yi a kashe maganar nan iya nan, bayan shi an cuceshi? Ta yaya ake so a kashe maganar nan a nan bayan yarinyar nan shi ta yi wasa da hankali ta hada masa husuma da matarsa harda su yin yaji? Da ace yarinyar nan basu zo da iyayenta ba da har yanzu yana nan yana tafe fuska cike shi an zubar masa da ciki da gangan?, yaya Abiey yake sanyo iyayenta a cikin maganar bayan ya ji da kunnayensa cewa yarinyar nan ciki take zubarwa na mutane ba a kan Beebahhhhhhhhhhh kadai ta fara ba? To wai wani irin hakuri ake so ta bashi shi ? Cabdijan

Idannuwansa ya kai kan Anmy, wace ta aiko masa da duban karma ya fara, saboda sarai ta ga yannayinsa, kuma a yadda ake cikin nan ai bata da bukatar wani izgilin

IZRANE murya na rawa ta ce" Dan Allah na.....dan Allah GIMBIYA ki yafe min, na tuba ba zan kuma ba"

Najeeba ta yi MURMUSHI tana kallon yadda Nadiya ke girgije girgije ta dubeta da sauri tana mata alamun ba zata yafe ba

A tausashe ta ce" Ni ai baki min komai ba, da ba'a yarda da ke Bama ai da ba za'a yarda cewar Ni zan aikata haka....., bayan wannan ai Ni zan iya cewa alhamdulilah tunda cikin bai bare ba yana nan"

A zabure izrane ta dubeta, hakama Nadiya

Nadiya ta ce" Kai, kenan cikin naki ne bai zube ba? Ni ai na zata wani ne"
Sai kuma ta yi tsitttt tana bin mutanen da suka dawo da dubansu kanta da kallo itama harda tunanin kallon fa? Za'a wani dubeta kamar itace ta fi kowa zunubi a dakin nan!=?? ( Ah to kawata Nadiya fada musu=??)

Sultan ya kafe fuskar NAJEEBA da kallo a lokacin da ta sakarwa Nadiya MURMUSHI tana girgiza kanta

A tausashe sosai ya ce" Ba yarda da ita ya sa aka gaskata maganarta ba Beebah......., alfarmar rigarta ta shiga ya sa aka yarda, likitaki ce fa Beebah......"

Da sauri shamaki ya sada kansa, Malami ma ya sake sada kansa a tausashe ya ce" Allah ya huci zuciyar GIWAR uban gidana, Allah ya huci zuciyar maman uban gidana, Allah ya kara maki lafiya da sauki a zuciyarki, Allah ya sa a sassauta mana laifin mu"

Shamaki yayi MURMUSHI shima a sanyaye ya ce" Lokuta da dama, ana shiga rigar daraja a kawo cece ku ce a cikin fili, wannan ne ya same mu ba da son ranmu ba, Allah ya huci zuciyar uwargida mai baban daki a fadar DAMAGARAN"

Abiey ya zuba ido kamar zai kama sunnan najeeba ya auna mata ashariya, sai dai abin haushin yana yi Anmy zata fara tarewa kafin shi wanda aka tarewa fadan ya bashi kunya, shi yanzu ai ido zai saka ya ga ikon Allah

Anmy ta saki MURMUSHIN da ta kasa rikewa ta dauke kanta cike da isa irin ta jinin sarauta

SULTAN kuwa, idannuwansa a kanta suke, so yake yi ta kara yin magana, Ama cikin ikon Allah ta gimtse bakinta ta dauke dubanta a kan kowa, karshema sai ya ringa yin irin na Nadiya, wato ya kalli wannan ya kalli wannan ya ga harta mamanta ba zata saka baki ba kenan? Kai jama'a wai me yasa za'a dauki lamarinsa da zafi haka????????

Shirun da wajen ya dauka ya jima , kafin ya sauke ajiyar zuciya ya maida dubansa kan shamaki ya furta" A yi hukunci, bisa sassauci, idan suna da ja su daukaka kara"

Najeeba kasa kasa ta dubi anmy ta ce" ANMY fitsari nake ji"

ANMY ta dubeta itama kasa kasan nan ta ce" Tashi ki je bangaren mu ki yi, kuma ai fita zaku yi ko?"

NAJEEBA ta gyada kai, Anmy ta ce" To Shikenan, balaraba fa yau zata sauka , kuma kin san zuwan naki ne, dan haka ki kula kar ki gaji da yawa dan na san idan ta zo a yau zata fara yi maki gyara ba zata kyale ki ki huta ba"

NAJEEBA ta sake gyada kai sannan ta mike a nutse ta saki alkyabarta da kyau kafin ta juya a hankali ta furta " Na barku lafiya"

Sannan ta wuce ta nufi hanyar fita ka ta tsaye wanda hakan ya sa ya bita da kallo da tunanin wai ta hanyar nan ta shigo dama ba ta corridor ba????, Anmy kuwa ta sake yin MURMUSHI ta fuskance su har sai da ya maido dubansa yana lumshe idannuwansa ya afka tunanin yanzu me zai yi mata dan ta sauko? Dan yanzu Bama ta shari'ar yake ba shi kam

A tausashe shamaki ya ce" Laifukan da muke da tabbacin su mu sunne na yunkurin zubar da cikin GIMBIYA, wace ta sanar a gaban kowa cewar ta yafe maki, sai kuma na WA'INDA akace sune suka baki kudinsu da kansu dan ki zubar, wanda wannan din shima bamu san adadi ba, kuma bamu san ko a ciki an samu kisan mai dauke da juna biyun ba ko babu......"

Ya juya takardar da yayi rubuce rubucen ya ci gaba da fadin" bisa adalci da sassauci da muke iya yi maki zamu tura takardar bayananki a yau yau baban birnin Nijar, wato Niamey, zuwa minist?re na lafiya, dauke da dukan bayanan abubuwan da muka dauka, da bukatar mu ta a soke takardar karatun da kika yi, wato ba zata kuma anfanarki a nan duniya ba, da kwakwaran kashedin ko da wasa aka tsinci kin yi aiki da sanin da kuka taba samu na aikin likita sai an yi Shari'a da ke an rufe ki, haka kuma baki da damar sake yin karatun da ya shafi fanin lafiya koda na Hausa ne bale na Turanci................, daga wannan kuma sai hukuncin fitar da miji a kwana kusa dan a aurar da ke ki je ki yi biyayar aure, idan baki fitar ba zamu fitar maki ne da kanmu domin a DAMAGARAN Bama bukatar tsagera irin ki !"

Ya dago a kausashe ya ce" idan hukuncin mu bai yiwa wani a cikinku ba, daga ke har iyayenki sai ku daukaka kara, muna jiran samaci a ko wani lokaci"

Mai garin MAGARYA ne ya yi gaggawar furta" Hukunci ya yi mana dari bisa dari, Allah ya saka da alkhairi ya rufa asiri"

Mahaifinta ma da yayi mamakin cewar basu turata kotu ba bayan du irin abinda aka fada ya ce" Hukunci yayi, an yi shi bisa adalci, in sha Allah zamu yi yadda akace, Allah ya karra maka lafiya ya huci zuciyarka"

Anmy ta sauke ajiyar zuciya jin hukuncin dan ba zata so ace an tsaurara abin fiye da haka na, Hajiya Turai din nan ce dai sun ki su fadi nata hukuncin , ba zata so itama a tsaurara ba, domin ta kula irin su Hajiya Turai duniya ce ke horar da su.

Mikewa Anmy ta yi ganin an sanar da hukuncin kuma sun karba ta musu salama ta nufi bangaren ta ta coridor dan ta huta,

Sai da ta tafi sannan shamaki ya dubi Sarkin bulala kasa kasa ya ce" Ga Hajiya, a Kaita inda za'a saka mata a kwakwalwarta cewa, idan ta kuma shiga hurumin GIWAR mai DAMAGARAN babu abinda zai Hanna karnukan gari shiga hurumin ta ba ta kowace siga, a ganar da ita da yaran da ba zai taba ranta ba Ama zai zame mata rubutu a saman dutse cewar Allah ke yin daraja ga wanda ya so, kuma shi ya umarci a girmama magabata, a kuma ganar da ita cewar babu ita babu ahalin su kurma ko a mafarki, idan haka ya tabbata zamu sake zama nata ita daya...... Bismillah a je da ita!"

Hajiya Turai ta zabura, a rikice ta ce" kalu Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, to ai du na gane kuma bilahilazi du na dauka, wayo, wayo, dan Allah kar a tafi da Ni, IZRANE kina kallo? Ranka ya dade kar a je ko'ina da Ni a barni in fita da kaina na rantse ko hanyar fada ba zan kuma bi ba bale in shiga abinda ba'a SAKANI ba, innalilahi dan Allah kar a tafi da Ni"

Sarkin bulala ya samu yana dan fita da ita ya yi mata wata tankadar da ta sa ta je ta zube kamar kunnun munafuka kafin ya karasa cikin hargagi ya sa ta tashi suka yi baya wajen dawakai yana ware bulalarsa.......( >?z? Wayo aminiyarmu Turai jiki du bltng)

Gamawa suka yi suka mike bayan an salami su IZRANE sai kuka take, domin gaba daya rayuwarta ta lalace dan son duniya da rashin godiyar Allah , karatun da ta je har wata ?asa ta yi, ya zama aikin banza dan bata yi anfani da shi ta hanyar da ta dace ba, ita kam ai ta gama wulakantar da kanta da rayuwarta docter ya amshi takardar ya fice shima, aka bar Nadiya da Sultan wace sai da aka gama komai kafin ta mike itama ta masa Salama ta nufi nata bangaren tana nufar dakin ta dan kuwa lalle lalle zata yi kiran Aunty ta sanar mata ashe cikin nan ba'a barar da shi din ba, sai ta ji shawarar da za'a yanke!


Sultan kuwa ajiyar zuciya yayi ta saukewa kafin ya mike a nutse ya je Wan sake SHIRYAWA ya fita domin yau zai fita, saboda ya huta din a jiya ya samu ya rintsa, a yanzu koda yace zai kwonta daga n ba lalle ya samu barcin ba, kawai gani yake yi kamar da gaske idan ba'a kama masa ba fushin Najeeba nisa zai yi, bayan a yanzu bashi da burin da ya wuce ya ga ta sauko dan ya nuna mata cewar du abinda take tunani ba haka bane......, da ace yana da damar sanar mata irin girman darajar da take da shi a duniyarsa fiye da kowace mace da zai yi tarayya da ita matsayin matar aure da ya sanar mata ta yadda koda mace dari yake da damar aura ba zata taba daga hankalinta a kan haka ba, kuma ko wani irin fada zai hada shi da ita ba zata taba shakun amanar zucin dake tsakaninsa da ita ba!


A Saloon din Najeeba


Tunda suka zo saloon suka sa masu tsaron kofar cewar du Wanda ya zo yau ba aiki, suka baje dukan wasu abubuwan gyaran da suka zo da su suka shiga gyara ka'in da na'in

Mai jego suka fara SHIRYAWA kayan gyara kamar haka:
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




38


Da farko hadi mai sunan hadin da ya dace ace duk wata wace ta haihu ta fara yi ne Najeeba ta hada mata, wato maganin sanyi, maganin da zai kashe du wani sanyin dake cikin mace, Duda haihuwa na tafiya da wasu cututtukan sanyin, sai dai ba duka take tafiya da su ba, ga daya daga cikin hadin sanyin da aka hada mata " Bagaruwa ta Hausa da lemon tsami, idan ka samu bagaruwarka ka tsaftaceta sai ka yanka lemun tsami biyu ka hade ka dafa su, idan ka ga ya dahu sosai sai ka tace ka juye ka saka a frij, da safe a sha kofi daya da yama kofi daya, hadin nan ba dole sai da lemun tsami na, idan kina fama da ulcer ki hada abinki na tare da kin saka lemun tsami ba,, wannan hadi yana matukar yin maganin sanyi, idan har kika yi shi in sha Allah zai raba ki da matsalar sanyi, wace in har mace na fama da ita to fa duk wani motsi na samun sukuni da abokin rayuwa zai gagareta, domin Babar matsalar da take sakawa du irin maganin gyaran da mace zata yi amfani da shi ya kasa amsarta matsalar sanyi ne da basir, biyun nan na sakawa mace ta kauracewa abokin rayuwarta, shi da kansa abokin rayuwar nata na iya kaurace mata idan ya zamo bashi da wani abin karuwa sai na wahala idan ya kai ziyara a wajen da ya dace ace duniya ce tasa daban ta shi kadai.


Bayan wannan suka shiga harhada kayan gyara na garari irin su kwakwa da gujiyar miya da karanfani da madarar Peak, da sauransu, gefe guda kuma Aida ta je gidan mota ta dauko katon sakonsu da suka yi oder na kayan gyara na garari daga duniya Hajiya sameera harun, wato Hajiyar Nijar mai takama da ikon Allah, idan ka riki sameera Nijar ka gama zuwa gidan gyara, gyara tun daga kofa har kuryar kurya, gyaran da zai saka du kurumcin mijinka budar baki ya kyarara ihu a lokacin da bai shirya ba, gyaran da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login