Showing 105001 words to 108000 words out of 144591 words

Chapter 36 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2333

mutanena




36

TALLAH TALLAH TALLAH

*Sauki......duniyar sauki a gidan SAJIDA AND AMINA SHOP*

Mutanenmu, tun daga jamhuriyar Nijar har zuwa Najeriya albishirunku.......
Muna tafe da sauki mai baki/baka ikon mallakar duk wani abu da kake ganin ya fi karfin ka ko ya yi tsadar da a yanzu zaka girgiza kafin ka same shi ta hanya mai sauki , wato Zubin dashin da zaka iya har Allah ya sa ka mallaki abinka cikin ruwan sanyi da nutsuwar zuciya....
Muna da haja kamar haka:

Kaya na maza da mata, tun daga kan lesh, shada, atampa, yadi, hula, hijabai, harta pant da slip

Kayan daki

Kayan KICIN

Jakunkuna da takalma

Sarka da yan kune harda na gold.

Abin hawa kowani kala

Dukan abinda kake da bukata muna da damar sama maka shi cikin sauki da hanyar biya mai sauki in sha Allah

*A DASHIN Y'AR GATA, ZAKI IYA YIN NA KUDI WANDA ZA'A HADE MAKI DUKIYAR KI A MIKA MAKI CIKIN AMINCI*

Ba Shikenan ba

Muna da special grup mai sunna MURMUSHIN ZUCIYARKU wanda muke tura kayan siyarwa masu kyau da tabo zuciya a farkon gani.

Muna da grup wanda muke baje kolin kayan gyara tun daga kan fata har zuwa pp na mace ko namiji

Ku zo mu je tare......
KU ZO KU RAKA MU
KU NUNA MANA KAUNA
KU TAYA MU TASHI DA KARFIN IKON ALLAH......

*TAKU CE, SAJIDA NIJAR*

Domin karin bayani a tuntubemu ta layinmu kamar haka

*CEEO SAJIDA ELHAJ SA'IDU KULLEY*

+22793811618


*ADJOINTE AMINA MAIKUDI ABDULAHI*

+234 803 885 6944



Labari



Dukan msg dinsa ta karanta, haka kuma a lokacin da ta samu msg din tana cikin duba tarin misss cal din wayarta da kuma msg din yan uwanta da na iyayenta harda na Aida uwa uba nasa wa'inda suke dauke da kalaman da ta manta rabonta da jinsu daga bakinsa

A zabure ta dago saboda diro mata da Muhammad yayi yana fashewa da kuka hadi da Wora kansa a saman kirjinta

Ido ta zarro tana sakin dariya kasa kasa ta ce" Kai, baka jin kunya? Sojan ne da kuka irin na mata?, meye waye ya taba min Muhammad dina?"

Abdallah ya tabe baki yana dubansa ya ce" Sai an yi magana yace shi jarumi ne, jiya babu irin kukan da bai mana ba Anmy, kato da shi sai da momy tace zata Goya shi ko zai samu barci, ya fa yi niyar hawa bayanta ta goya shin na masa rantsuwar kamar a gaban yan ajin mu ya hau aka masa bombo sannan ya ki hawa, Ama haka ya sakata a gaba da ita da mama1, da mama2, da autar aboki da abar kauna andiya yana musu kuka su kuwa sunna ta rarashinsa katon banza"

Najeeba ta Wan nuno masa yatsa ta ce" an gaya maka kuka rashin jarumci ne?, kai yi kukan ka dadin abin ai iyayensa ya ma, kai fa me ka aikata?"

Muhammad ya dago da sauri ya ce" Mah, kin ganshi ? Fada yayi kamar kare na fada da bako, ya fashewa dan ajin mu goshi, ya yi fada da malamar mu dan ta tabani tana tambayar abinda aka min a gida nake kuka, da Sarkin bulala ya fara rarashinsa da yi masa fadan ba'a fasawa mutun kai ya cewa Sarkin bulala baya cikin mood din magana, ke dai fitsarar da ya zuba ba kadan bace Danma Abiey bai zauna da mu ba ai da sai ya zane yaron nan!"

Najeeba ta kame haba ta ce" Uncle bulalar ka cewa baka cikin mood? to uban me Aka yi maka da zaka ringa fada da mutane?"

Abdallah ya turo baki ya harde hannayensa, sai Muhammad ya ce" To Mah me zai hana mu rigima bayan an ce kin bata? Bakya nan? Kin gudu?"

Ta zaro ido tana dubansu , a hankali ta ce" In gudu in je ina Ni kuma?, gidan aba Dayabu na je fa, Bama wannan ba, kar in sake jin an yiwa baba rashin kunya ka ji ko ?, kai kuma haka kawai sai ka Hanna musu sukuni ka ringa musu kuka ko kunya baka ji Fisabililahi? Da ace ka hau bayan Momy Zahra ai da ka karya min yayata, kai kam wannan sangarta haka da me ta yi kama, dagani Ni ka wani dane min kafafu "

Ai kuwa suka kalli junna, Abdallah ya fashe da dariya yana cire rigarsa ya haye gadon nata shima hadi da miko hannunsa ya riko nata hannun, Muhammad kuwa dama sassautawa kawai yayi shima yayi kwonciyarsa yana rike da rigarta

Da mamaki ta ce" Kai me kuke nufi? Ai kun san na raba daki da ku ko?"

Abdallah kasa kasa ya ce" Babu inda zamu je Mah, tunda ana farkawa a ga Bakya nan mu kam a nan zamu ringa kwana tare da ke"

Ta kuwa dage zata zazaga musu masifa su zahra'u suka shigo, a dole ta kame bakinta ta yi dif saboda tun Dazu suke dauki ba dadi da ita, ta duka ta basu hakuri da rantsuwar ba tana nufin ba zasu iya kwatar mata yanci bane, ba ta tafi dan basu isa da ita bane, ta yi haka ne dan kawai a dauki abinda take ciki da mahimmanci, kuma ai sun ga inda ta je din, tana tare da A'isha fa, Ama mutanen nan firrr suka nuna fushin su suka fatataketa sosai , Anmy ce ma tace ta zo ta yi wanka ta cenza tufafi ta kwanta ta huta, sannan su ma ta shiga yi musu nasiha da rarashinsu baki daya, bale jibi zasu yi taron sunnan babyn ummu, kuma tana so ana gamawa da kwana biyu kowace ta koma dakin ta, ya isa hakanan, tunda Allah ya sa mazansu masu barinsu zuwa ganin gida ne kar su ja abinda zasu daina barin nasu.

A sanyaye Najeeba take kallon su, har zahra'u ta idasa cire hijabinta ta zauna tana daga kiran yarinyarta suka shiga magana sannan ta mikawa Najeeba dan tambaya take yi da mamy dinta in an ga mamy dinta

Fira suka yi sosai sannan ta ba ummulkhair dan ta gaishe da su baki daya

Sunna gama wayar ta ajiye tana duban Najeeba dake ta yi musu kalar tausayi

Ta girgiza kai ta ce" Munafukar banza, sai kace wace take tsoron uban wani, sai ta aikata iya shegenta ta zo tana yi maka kalar tausayi, ai yaya Dayabu ya bani sako yace idan kika ganshi ki gudu"

NAJEEBA dake kalar tausayi sai gata da fashewa da dariya ta ce" Zahra tsaya fa ki ji, kiransa nake yi, bayan ya san yace min jikin Anmy ba sauki, wai ya ki dagawa, Ni kuma na je, kuma har ga Allah ban so a gani ba, ke maciji fa, maciji wani katon mage ya damko ya durfafoni da shi, to yaya zan yi? Shi din ma fa da wannan mutumen ya saki magen nan sai da yayi tsalle ya zata macijin zai bashi ya rike , shi namiji bale Ni? Kawai mijin A'isha baya son gaskiya to daga ina zan ce nake? Abiey fa ya tsareni da tambaya in na yi karya yaya kuke so mu kwasheta?"

Ummukulsum ta ringa dariya ta ce" Ke wai yaya kuka kare kuma da mai jiri? Yaya fa jiri ya ringa yi...."

Zahra'u na dariyar itama ta musu alamu da baki da su Muhammad, ai kuwa suka yi tsitttt suka mike sunna barin dakin har itama ta gamsu da sun yi barci ta mike ta bi su, suka hadu suka hau rubuce rubucen shirye shiryen sunan baby da mahaifinsa ya yi musu surprise ya saka sunan Mai wukar yanka.........., wanda da Anmy ta sanarwa Sarkin bulala Dazu da suka kawo su Najeeba ya ringa murna yace ai kuwa sai sun yi hawan Dawaki da wasa kala kala ranar sunan nan, wannan dalilin ya sa su kuwa suka yi doguwar list, ta bangaren abinci daban, ta bangaren abin sha daban, ta bangaren harkar tarbar baki daban, ta abinda zasu saka daban, karshe dai harta mawakiyar da za'a ba damar shigowa ta yi daban , domin Najeeba tace sai an yi ko da suka nuna kar yayansu yayi fada , sai tace babu abinda ya shafe shi da wannan, biki suke yi ai ba zaman makoki ba

_________________________________


Washe gari, tunda duku dukun duhun asubahi Abiey ya karaso fada tare da iyayen IZRANE

Ya kuwa shiga ya fita ya sama musu zama da Sultan wanda ya shige wajen Anmy, ya samu umarni daga Anmy din, dan haka a dole ya yarda cewar su zauna a falonsa na baki

Kusan karfe bakwai du suka halarta a cen, harda Anmy din da Najeeba wace ta so kin zuwa Ama Anmy ta nuna mata sai ta je, uwa uba harda Nadiya wace ta samu labarin zaman daga bakin wace ke gyaran falon bakin a lokacin da ta zo yi masa ina kwana, hakan ya sa ta zauna har sai da kowa ya sameta a wajen saboda son da take ta ji kuma me docter din zata ce an yi mata? Su kam sun ga ta kansu idan matar nan ta shigo gidan nan, domin ita bata san wainar da ake toyawa ba ai

A zaman harda mahaifiyar IZRANE, da kuma Docter MUHSEEN wanda ya samu kira daga Sultan da kansa ya kuma garzayo ya halarci taron cike da mamakin gannin IZRANE a wannan yanayin da take ciki da Hajiya Turai , Duda basu da yinwa, Ama sun fita a hayacinsu baki daya

Karfe takwassss ya samu karasowa Falon nasa, ya zamo kowa ya sada kansa har ya zauna a kujerarsa, Malami ya ajiye kundin litafin Shari'a sannan ya koma gefe ya zauna Kamar yadda su shamaki suka zazauna

Addu'a aka yi a nutse aka sha?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? fa, sannan aka shiga gabatar da abinda ya da aka yi zaman

Tunda IZRANE ta ji maganar nan cikinta ke wata irin juyawa, kirjinta na bugawa, zufa na neman wanke mata fuska, jininta kuwa ya dauki rawa, harma ta rasa zaune zata yi ko kwonciya tsabar yadda jikinta ya mutu ta rasa laka ko kadan

Mahaifinta a tsorace yake kallon ta, hakama mahaifiyarta hannaye ta dora saman kanta a tsorace jininta na daukan rawa tana dubanta har shamaki ya gama bayani, da hujjojin da aka samu, da irin yadda ta ?aryata Najeeba da irin yadda yanzu suna zaune gaskiya ta yi halinta, aka ba kurma damar shigowa ita da mahaifiyarta, suka shigo kuwa kurma ta maimaita abinda ta fada tana sake tabbatarwa cewar izrane ce da kuma Hajiya Turai ba karya sannan aka fitar da ita aka tafi mayar da su nasu gidan suma, kafin shamaki ya dubi IZRANE ya ce" A bayanan nan da aka yi, kina musawa cewar an maki kazafi ne ko kuwa kin dauki laifinki kin san kin aikata?"

Izrane harta kanta rawa yake yi ba wai jikinta ba, domin ta san cewa ko a haka aka barta an gama sakata uku bale ta tabbata sai an yi mata hukunci mai tsananin gaske, hakan ya sa ta ringa gyada kai dan ta san idan ta yarda ta Musa, wannan sarkin bulalar sai ya fasa mata ido yau, dama ana daf da sanyota sai da ya lafta mata guda wace ta kusan sakawa ta saki fitsari dan ta jima tana a Sosa kafin ta daina jin radadin bulalar a jikinta da kwakwalwarta.

Shamaki ya sake fadin" Kin yarda cewar, kin ba Gimbiya NAJEEBA maganin da ya saka ta yi bari a kwanan baya? Kuma kin yi mata kazafin cewa itace da kanta ta zubar?"

Izrane ta bude baki da kyar a jigace ta ce" Eh ranka shi da......."

Wani irin ihu Sarkin bulala yayi ya zaburo yana nunota da damatsan hannayensa taurara ya ce" Kin shiga uku, domin idan baki buya ba jininki fansa ne a jinin jikan Muhamadu dan SHAHEED jikan MUTALAB!, tabas sai mun hana maki zaman lafiya a garin DAMAGARAN!"

A tsorace ta rarafa kusan mahaifiyarta jikinta na rawa, mahaifiyar Tata ta mike tsam ta koma nesa da ita tana share hawayenta zuciyarta na matukar zafi da kunna

Da kyar shamaki ya sa ya koma ya tsaya a wajensa, fata yake a yi a gama a basu ita su koya mata hankali!

Shamaki ya sake duban inda ta koma ya yi mata umarnin dawowa wajenta sannan ya ce" kina Musa maganar cewa kina bada gudunmuwa wajen zubarwa da mata ciki ke da aminiyarki?"

Nan ma IZRANE ta girgiza kai, Hajiya Turai ta fitar da hucin dake tabbatar mata tasu ta kare kuma

Shamaki ya sake duban ta yanzu shima nasa ran ya Saci sosai ya ce" Me zaki fada dan kare kanki? "

IZRANE ta rasa me zata ce, ta jima tana hade hannaye tana saukewa kafin ta ce" Bani da wani dalili da ya wuce burina na in zama nima matar gidan nan......"

Kafin shamaki ya ankara Sarkin bulala ya sauke mata bulala a fuska wace ta lauya sosai ta daki lebunanta da fuskar sosai, nan da nan kuwa wajen ya haye sundum Bama kamar lebunan, rai bace ya ce" ki fadi komai banda jingina kanki da ASARKI!"

Abiey ya dubi SULTAN a tausashe ya ce" Allah ya huci zuciyar ka, a yi hakuri a dakatar da Sarkin bulala, Duda yarinya nada laifi mai girman gaske, a bi yadda ya dace dan hukuntata idan ma iyayenta da ita sun zabi a je kotu ina rokon alfarmar a mikata hannun yan sanda a yi bincike sosai sai a je kotun a bima wanda aka cuta hakinsa......., ina matukar tausayawa zuciyar iyayenta, ina matukar girmama hakuri a lokacin da zuciya ta Saci sosai, idan har ban shiga hurumin nan da karfi ba a duba maganata a sassauta, kar a manta duk Macen da ta je neman a zubar mata da ciki itace ta kai kanta, ban sani ba ko Akoy ire Iren WA'INDA ta zubarwa dan ra'ayinta irin na GIMBIYA?, Ama inaga a yanzu dukanta bashi da wani anfani, Allah ya huci zuciyar ka, Allah ya karra maka lafiya"


Shiru ne ya wanzu a wajen, domin kukan da take son yi ita da kanta ya gagareta, dan yadda take jin furkarta idan ta bude baki tsaf fuskar zata tsage ko ta fashe da jinni

A hankali ya kai dubansa inda Anmy take da NAJEEBA da kuma Nadiya dake zarro ido hadi da talafe haba dan gaba Waya ita ai an gigitata, to cikin dai ya bare din kenan sabo ne aka yi a yan kwanakin nan? Eh lalle ana wulakanci da rai a fadar nan, lalle ana nuna mata abinda ba shi ba a zahiri, to meye dan sun nuna mata gaba suke bayan ba haka bane? To wai ita ke zuwa ko shi ke zuwa inda take? Kai ikon Allah!


A hankali ya daga yan yatsunsa saitin da Sarkin bulala yake ya yi masa alamun zaunawa

Sarkin bulala ya zauna yana furta" Umarninka shine abin bina ranka ya dade"

A hankali ya fuskanci Docter muhseen, cen kasa kasa ya furta" Docter, me zaka yi matsayin bayanin da zai sa in gane cewar na da yawunka ka hadani da mai kisa ba????"

DOCTER muhseen ya sada kai, bai taba jin kansa cikin tashin hankali irin wannan ba, subahanalah, shin har ina mace take iya zuwa dan samun bukatar ranta????

A sanyaye ya ce" Allah ya huci zuciyarka, ban taba sanin cewa wanda zai ceci rai zai iya kashe rai dan bukatar ransa ba sai yanzu, tabas wannan din ba likitar da nake yiwa kyakywan zato bace, saboda Ni da kaina itace likitar iyalina......, kai kawo da fitintinun da na fuskanta a kanta a kwanakin nan ya sa ma na dakatar da ita dan yanzu haka Ni ba ma'aikaciyata bace, saboda na bata hutun sai na yi bincike a kanta, Ama abin mamaki du binciken da na yi ban ga komai ba sai jira da na yi kawai har lokacin ya cika ta dawo dan na dauka cewar an samu rashin fahimtar juna ne, Ama a yanzu kam ai Bama zan iya mayar da ita asibitinmu ba, dan Bama bukatar likita irinta!"

Sultan ya dubi iyayen IZRANE, mahaifin izrane hawaye yake yi da idannuwansa, Sarkin garin MAGARYA kuwa ya tafka tagumi bawan Allah, uwa uba mahaifiyarta dake kuka kashirban........

Kansa ya dauke ya dubi inda take ya ce" Ke ce da kanki kika zabi aikin zamowa likita, harma kika yi rantsuwar kare lafiya bayan kin gama karatu, ko kuwa tilasta ki aka yi yin karatun?"

IZRANE ta langwabar da kai ta ce" A'a, Ni ce na zaba....."

Sultan ya dauke kansa daga kanta ya dubi inda NAJEEBA take, idanuwanta a lumshe tamkar wace take barci, a hankali ya ce".........

>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




37


Tallah TALLAH TALLAH

*Sauki......duniyar sauki a gidan SAJIDA AND AMINA SHOP*

Mutanenmu, tun daga jamhuriyar Nijar har zuwa Najeriya albishirunku.......
Muna tafe da sauki mai baki/baka ikon mallakar duk wani abu da kake ganin ya fi karfin ka ko ya yi tsadar da a yanzu zaka girgiza kafin ka same shi ta hanya mai sauki , wato Zubin dashin da zaka iya har Allah ya sa ka mallaki abinka cikin ruwan sanyi da nutsuwar zuciya....
Muna da haja kamar haka:

Kaya na maza da mata, tun daga kan lesh, shada, atampa, yadi, hula, hijabai, harta pant da slip

Kayan daki

Kayan KICIN

Jakunkuna da takalma

Sarka da yan kune harda na gold.

Abin hawa kowani kala

Dukan abinda kake da bukata muna da damar sama maka shi cikin sauki da hanyar biya mai sauki in sha Allah

*A DASHIN Y'AR GATA, ZAKI IYA YIN NA KUDI WANDA ZA'A HADE MAKI DUKIYAR KI A MIKA MAKI CIKIN AMINCI*

Ba Shikenan ba

Muna da special grup mai sunna MURMUSHIN ZUCIYARKU wanda muke tura kayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login