Showing 60001 words to 63000 words out of 144591 words

Chapter 21 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2331

a yanke mata gashin kanta.........., Zahra'u"

Zahra'u ta kai dubanta da sauri inda umi ta gama daidaita wajen da zasu yanke din tana dag da yankewa, zahra'u ta ce" Kar ki yanke umi"

Umi ta dubeta, itama ta dubeta

Umi ta ce" dan me?"

Zahra'u ta ce" Yaya yace kar a yanke"

NAJEEBA ta dago tana dubanta ta ce" Me ya haWa yaya Dayabu da gashina kuma???"

Zahra'u ta girgiza kai ta ce" Mai martaba nake nufi"

NAJEEBA ta bi wayar dake hannunta da kallo, wace alamun kore koren dake haskawa yana daukewa kadan kadan ya tabbatar mata da yana sauraron wayar, dan haka ta karaso tana kallon zahra'u wace take hararanta da yi mata alamun kar ta saki tace komai Ama sai Najeeba ta yi dan murmushi a hankali ta ce" Dama Akoy wani da yake da iko da gashin kaina ne bayan Ni?, ai du tunanin mai tunanin yana da iko da makashiya gwara ya daina.....Akoy lokacin da fita da dan kwali ke jirana Ni Najeeba MUTALAB"

Da sauri zahra'u ta ajiye kiran tana dubanta ta ce" Kina da hankali kuwa? Ya dace ki ringa rike fushinki, kar ki manta waye shi, kar ki saki ki yi wasa da shi Najeeba, kina da hankali da kike son nuna masa zaki fita da dan kwali a kafada? Me kenan? Dama idan kika mutu daga ke sai dan kwali za'a kai ki???"

Ummulkhair ta dubeta tana jan tsaki ta ce" Inaga haka take nufi, domin du balakinki baki isa ki ce zaki bar gidan nan ba, kar ki ja mu ci kaniyarki a kan yayanmu"

Najeeba ta yi murmushi ta amshi almakashin zata yanke gashin

Da sauri Ummukulsum ta karSe tana dubanta ta ce" Kar ki yanke, duk wani abu da yake kawata idannuwan mijinki a jikin ki kyanta ki kyautata shi ba ki lalata ba, tabasss zaki hukunta SULTAN, Ama ba ta wannan sigar ba, yaya kike so ya ji ne da furucin bakinki??"

Rai bace Najeeba ta ce" Ni yaya ya saka na ji a duk lokacin da ya dauko hanyar wulakantani????, a lokutan da yake dane hakina dan jin dadinsa me kuka ce masa dan ku kare Ni?????, tabasssss na rantse sai na janyowa kaina yanci mai girman gaske, kuma zaku gani"

Du da ido suka bita a lokacin da ta fice a dakin bayan ta dauki filo dinta ta nufi dakin anmy sai harare harare take yi, gani take yi su dinma so suke su koma bayansa bayan shine mai laifi

Ajiyar zuciya zahra'u ta sauke ta ce" Bakwa gannin kamar Akoy abinda take shiryawa? Tsoro take bani"

Umi ta ce" Ba wani abinda take shiryawa kawai ranta ne yayi mugun bacewa sai ta saku a hankali zaku ga ta dawo dai-dai, kun san bata iya so ba"

Zahra'u ta sauke ajiyar zuciya ta juya ta nufi dakin tagwaye na bangaren anmy ta buga sannan ta shiga da salama ta sanar musu sakon mahaifinsu sannan ta dan dakata har suka fito ta raka su wajen Anmy suka yi mata salama da mahaifiyarsu ta yi musu addu'a sannan suka wuce Sangaren nasa ta coridor



A bangaren SHAHEED kuwa ya jima tsaye da wayar nan a hannunsa......., cen wajen goshinsa na neman rikita nutsuwar fuskarsa da gumi irin na shiga tashin hankalin nan........

Ajiye wayar yayi ya juya yana murmushi hadi da girgiza kansa, a cikin zuciyarsa ya ayyana ' Beebah kenan"

Yaran sun same shi a dakin karatunsa, sunna zuwa ya ajiye komai ya saka su a tsakiya sunna fira, fira irin ta ilimi, fira irin wace idan iyaye na yi da ?a?ansu suke sauraronsu sosai sunna jin yannayin furucin ya'yan ta haka suke samu su ringa gyara musu duk wani abin da suka ji ba tarbiyyar harshe bane , haka kuma ta haka zasu kara saka shakuwa a tsakaninsu da ?a?ansu......, har yaran suka yi barci da daidaya sannan ya mike da daidaya ya kai su dakin da yake kwana da su idan sun kawo masa ziyara, domin baya kwonciya da su a dakin da yake kwonci da iyayensu......., ya saka su a gefe da gefensa, a hankali yana kallonsu hadi da yi musu addu'a, zuciyarsa cike da kewar mahaifiyarsu, kewa mai tsananin gaske, wannan yannayi da yake ciki ya Hanna shi kula wayarsa bale har ya san msg din da Docter ta ajiye a whatsup dinsa.


Washe gari da sasafe Nadiya ta gaza hakurin irin haushin da ta kwana da shi na takaicin namiji , domin bayan dogon nazari da ta yi ta gama gane cewar ba fa wani laifin NAJEEBA, abinda yayi mata a Jiya kawai dan zai kara aure ne, wannan dalilin ya kuntata zuciyarta, ta gaza hakuri ta nemi layin Docter IZRANE tun kusan karfe goma na safe

A lokacin da ta yi kiranta, ita din ma a wani yannayin take ciki, saboda a Jiya Hajiya ta kawo mata ziyara da dare , ta sake dorata kan dakalin bera ta tafi ta barta da sake saken zuciya dan neman mafita........, sai ga kiran Nadiya wanda da ta ga kiran sai da ta ja tsaki a bayyane ta furta" Ji wata masifa , ita fa wannan sai nacin jaraba, meye kuma?"

Sai dai ta daga kiran tana kokarin aro fuskar munafurci Nadiya ta dakatar da ita

Tana huci ta ce" Docter kenan, ki ce zuwan da kike yi kina duba mu ifannuwanki a kan mijinmu??"

Docter ta mike tsaye da sauri ta ce" Ban gane ba Nadiya?"

Nadiya ta ce" Yaya za'a yi ki gane kina munafurci kina son mijinmu?, Ama docter ko kunya baki ji ba?, du irin yadda kike sakani a gaba da nunin ke ta Allah ce ashe munafuka ce? Shine zaki aurar min mijina????"

Docteur IZRANE ta zarro ido, domin wani irin dadi da ya saukar mata lokaci daya tana sake gyara tsayuwar ta Wan ta gane wai da gaske Sultan ne zai aureta ? ta ce" Nadiya waye yace miki zan auri mai martaba???"

"Ke dan Allah Ni bana son munafurci, kin san dai in ba haka bane baki isa har a ce haka din bane ko?" Nadiya ta fada cike da jin haushi

DOCTER IZRANE kamar zata rangada guda haka ta ji, nan da nan bakinta ya bude, du wani abu da ya dane mata kirji ya ringa sakinta ta ji wasai, ta ce" Tunda har ke kika iya yin munafurcin auren mijin Najeeba ba tare da kin ji kunyar haka ba, ai dan Ni na yi ba laifi na yi ba, koyi na yi da Babar munafukar mai zamba cikin aminci, ko an gaya maki cewa du duniya idannuwa ba a kanki suke ba munafuka mai auren mijin Aminiya? Ai ke kam kin gama jin kunya, miji kuwa ki daina cewa naku, namu ne ai Nadiya "

Wata irin zufa ke wanke fuskar Nadiya, jikinta kuwa har rawa yake yi, ai kuwa ta dage ta ringa zagin IZRANE, sai dai da yake IZRANE din ma ba kanwar lasa bace du abinda ta fada mata ita sai ta ninka mata, domin ta riga ta samu bakinta ya bude nadiyar ta taimaketa ta sanar mata abinda take son sani, ai ita yanzu duniyarta sabuwa dallll sai abinda hali ya bada zata yi.

Ita da kanta ta kashe kiran jikinta na rawa ta kife jikin kujera ta fashe da kuka mai tsanani zuciyarta na daukan zafi........ innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, dama da Najeeba ta ga miji daya suka aura haka ta ji? Dama da Najeeba ke fadin ba komai bane sunna iya haWa mijin da kowace ma ai daidai shi ne tunda yana da damar yin hakan har take gannin gaskiyar kenan ashe ashe da ciwo a zuciya? Dama har haka ake ji in za'a maka abokiyar zama? Da farko bata dauki abin da zafi na, gani take yi fadan Najeeba ne, Ama tunda ta ji wacece ta kasa samun nutsuwar zuciya, dama a haka Najeeba ta ture ta jure suka cudanyar junna har take fin ta jin zafin kishi na yau da gobe? Domin lokuta da yawa kiri kiri take yin abin a dubeta a zuwan jin zafin kishi, sai dai ta ga Najeeba ta yi murmushi ta dauke kai, yaya ake tana iya kyalewa ba tare da ta nuna mata ba?......Duda shi ya nemi aurenta kuma a lokacin da aka yi bata san cewa ya riga da ya zama mijin najeebanta ba, Ama da wata ce anya zata iya irin wannan sakewar da ita ta yi ? zumuncinsu mai karfi ne, a lokacin ita kadai ce kawa, shakikiya, aminiyar Najeeba, sai kawai aka wayi gari suka hada miji......., yaya Najeeba take ji a zuciyarta? Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une............... Ganin zata mutu ita daya a daki ya sa ta yi gaggawar sakawa a sanar da fitarta, dan kuwa gidansu kadai take iya zuwa ta samu salama a irin halin da take ciki.

Wannan kenan.

A safiyar yau kuwa, tun karfe goman Najeeba ta sada kanta da dakin karatu

A lokacin Malami na cikin rubuce rubuce na duk wani shige da ficen da suka karba na tsarin wunin mai Martaba, domin shamaki zai amsa zuwa karfe goma sha daya ya nazarta, dan idan da na sokewa ya soke........ Sai kawai ya ga shigowar mai baban daki, da katon hijabinta, da nikaf din ta, harda Safa, domin da ace bata yi magana bayan ta shigo ba da ba zai gane cewar ba ita bace, zai dauka cewar cikin yan uwan ta ne da suka zo fadar .

Da sauri ya sauko daga kujerar ya duka kansa a kasa ya furta" Barka da safiya Gimbiya, Barka da fitowa uwar dakina , ai da an ce in zo da Ni zan zo in ji bukatar GIWAR uban dakina"

NAJEEBA ta yi murmushi ta zauna saman kujerar dake ajiye

Da sauri ya mike zai dauko wani abin zaman yana fadin" Kai subahanalah, wannan kujerar yara ce, ga wace mai Martaba yake zama ranki ya dade"

NAJEEBA ta Dube shi cikin murmushi ta ce"
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




20




NAJEEBA ta Dube shi cikin girmamawa da murmushi ta furta" Barka da warhaka abah Malami"

Malami ya furta" Barka kadai GIWAR uban dakina"

NAJEEBA ta Wan sake sada dubanta, saboda irin yadda yake duke a gabanta, kuma ta san ko me zata ce ba zai tashi ba, haka yake yi mata, ta yi ta yi baya dainawa, ya fada mata cewar daukaka ta Allah ce, Allah yayi ta sama da shi, a dole zai girmamata, kuma itama tana girmama shi fiye da zato, hakan ya fi komai faranta masa domin har maganar ake yi irin yadda idan datijan fada suka duka take yin kamar zata duka din itama, sai da kyar suka samu ta daina haka, Ama har ta gama magana da kai ita kuma kanta a kasa cike da jin nauyin irin duka matan da ka yi bayan zaka iya girman mahaifinta ma. Wadinan dalilan su suka sa a da baya take cewa ina ita ina sarauta? Sarauta ai ta masu son duniya da raina manya ce, ire Iren haka dai.....


A tausashe ta furta" Baba Malami, dama wata tambaya gareni, kuma bana s Shah...............m"
Ta yi dan shiru kafin ta ce" Bana so mai martaba ya ji cewar na zo, idan har hakan ba zai samu ba in rike tambayar in juya? "

Malami yayi shiru kansa a kasa shima, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Na tabbata a dogon zango da zagaye irin na shekaru, da zamantakewar tare, da addinin da muke rike da shi, da kuma kauna irin ta jini ba zata sa uwar dakina ta zo da wannan maganar in har ta san cewa maganar da take tafe da ita zata cutar da Mai wukar yanka, dan haka in sha Allah zai zamo magana da muka yi ta tsakanin dakin karatu da uwar marayu, Allah ya karra maki lafiya Bismillah "

NAJEEBA ta yi murmushi, tabas ta san mutanen nan yan gani kashenin shaheed ne, bata kokonta ko kadan, ta san du Wanda ya yarda ya zo musu da wata maganar da zata iya cutarwa mai damagaran ko wani da ya rabe shi dai inda karfinsu ya kare

A tausashe ta ce " Dangane da kiran da na yi ne, kan a kawo min likita ....., sai na tsinci maganar a bakin Mai Martaba, shine nake son karin bayani"

Sai da ya dan dago, kafin ya sada kansa, a tausashe ya ce" Allah ya huci zuciyarki, tabas dukan abinda ya zamo hurumi ne a wajenki baya fita daga baki ko takardar malami , sai dai idan daga hannun shamaki zance ya je wajen Rai ya dade, Ama du abinda zai shigo ta nan ki dauka cewar cikin kabari kika birne maganar bakinki babu mai ji sai ke sai Ni da kika sanarwa sai kuma aikin da kike so a cika, magana ta fita ne daga bakin likitar, domin a lokacin da Sarkin bulala ya dawo ya zo ya nemi takardar shiga bangaren mai wukar yanka a daren nan yake sanar min cewa likita ce ta sanar da sunna nan, domin Mai wukar yanka ne ya bada umarnin dawowarsa fada...., a lokacin har ya nemi jin dalilin da yasa take da damar yin maganar da shi Mai DAMAGARAN? Na tabbatar masa cewa likita ce, likitoci sunna da dama sosai, dama kala kala, ciki harda irin damar da zasu iya magana da manyan da suke yiwa manyan masu kuWi wahalar gani, shugaban kasa ne, gwamnoni ne, da sarakunan mu, iya abinda na sani kenan"

NAJEEBA ta gyada kai, ta yi murmushi sannan ta furta" A huta lafiya Aba Malami "

Shima ya sada kansa sosai ya furta" Allah ya mayar da ke lafiya, Ubangiji ya hutar da zuciyar GIWAR mai baban doki"

Ita dai a nutse ta ficewarta, tana tafe tana sha?ar iskar duniya har ta karasa saloon din ta, wanda a lokacin da ta zo shiga sai da ta nunawa masu tsaron kofar ka???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?tinta, sannan ta daga kai ta bi droon dinsa dake yawo a dai-dai kanta, wanda tunda ta koro da tafiya ta ga biyo bayanta da yayi

Sai da ta shige sannan ta cire nikaf din ta a filin wajen wanda hakan ya sa drn din daukan fuskarta da kyau sannan ta karasa ciki hankali kwance tana tabe baki a cikin zuciyarta ta ayyana ' Yanzu na fara fita ba alkyaba....., Bama zaka gane cewar na ajiye alkyaba ba sai ka gane cewar mai alkyabar ma na ajiye shi!'


Ajiye iPad din dake control din drn din ya sa drn din faduwa kasa da karfi, wanda hakan ya sa polisan wajen shiryawa du sunna kallo da tsoron kar ya kama da wuta saboda shi abu kadan ke iya sakawa ya kama da wuta, sai dai gannin bai kama din ba ya sa suka so nufar shi, Ama basu samu yin hakan ba sanadiyar nufo wajen da shamaki yayi da sauri ya dauka sannan ya nufi bangaren mai damagaran hankalinsa a tashe saboda abinda ya ga ya fadi a kan idannuwansa........

A lokacin da ya je bangaren da sauri ya samu shiga ya karasa har baban falon ya shiga bayan salamar da yayi ya karasa da sauri ya duka kansa a kasa yana fitar da ajiyar zuciya bayan ya ga iPad din daf da kaffafuwan mai damagaran a yashe ya kuma ga ba abinda ya damu sarakin sai salama ta ratsa zuciyarsa, a hankali ya furta" Allah ya kara maka lafiya, ina tafe zan doso nan ne na ga faduwar jirgin nan, shine hankalina ya tashi dan na san bai cika yin nesa da hannunka ba"

SHAHEED da ya amsa gaisuwarsa tunda ya shigo ya fahimci abinda ke hannunsa ya firgita shi, ya sauke ajiyar zuciya a tausashe ya ce" ka zata na mutu ne shamaki?"

Shamaki ya kame baki kafin ya furta" Subahanalah, subahanalah a'a, bana wannan fatan ranka shi dade"

SHAHEED yayi murmushi yana dubansa ya ce" Ai kuwa, ka ga abu ne da zai tabbata, ko yanzu ko an jima shamaki, Allah dai ya sa mutuwarmu ta zamo baban jin dadin da zamu je mu tarar a kiyama"


Shamaki ya sada kansa zuciyarsa na daukan rawa irin na tsoron furucin uban gidansa, sai dai du yadda zai kai da tsoron hakan bashi da abinda ya wuce ya amsa addu'ar saboda mutuwa dai rigar kowa ce, babu wanda ba zai dandanata ba, Allah ya sa karshen mu yayi kyau

A sanyaye ya amsa addu'ar nan, jikinsa du yayi sanyi

SHAHEED ya dan sauke ajiyar zuciya ya ce" Mata sunna da damuwa, abu kadan ke sakawa su nemi dagawa mutun hankali, Allah ya kyauta"

Kasancewar shamaki ya san da maganar neman auren, domin binciken da ya shafi fada a hannunsa yake, wanda tunda ya ji maganar cewa yarinyar fa ta taba yin aure du abin ya fice masa a rai, Ama kuma bai daina binciken ba dan ya san ba wannan dalilin zai Hanna uban gidansa aurenta ba sai dai idan Akoy wani dalilin da ya fi shi karfi, ya dubi SULTAN a hankali ya ce" Iyayenmu ke nan, abokan rayuwarmu, yayunmu kannenmu, yayanmu, Allah ya sanyaya lamarin GIWAR uban gidana da maman hamrah"

SHAHEED ya yi dan murmushi sannan ya mika hannu , shamaki ya dauko sandarsa da sauri ya miko masa ya amsa ya rike, yana dubawa a tausashe ya ce" Yaya maganar binciken nan?"

Shamaki ya sada kansa a hankali ya ce" Allah ya taimake ka ina kai"

Sultan ya gyada kai sannan ya mike ya nufi ciki, shi kuwa ya koma falon farko yana duba lokaci kafin ya wuce wajen Malami


A bangaren Najeeba kuwa tana shiga saloon ta cire hijabinta, Aida ta yi ta murnar ganninta , hakama yaran shagon da suke sanye da uniform ta dogon sket da riga budadiya har gwuiwoyinsu, saloon din sai kanshin turaren wuta yake fitarwa, haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login