Showing 123001 words to 126000 words out of 144591 words

Chapter 42 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2364

numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




43



Anmy ta dubi yannayinsu kafin ta dauke kai ta ce"to idan babu isasshen waje a cen din ma duba da bakin da suka cika gidan, ko ku je Sangarensa ku gyara musu dakuna sai su su je cen tunda ai duka na dare daya ne"

Wannan karon kam Najeeba da ta hangame baki sai ta kasa furta koda A ne, Nadiya baki na rawa ta ce" Anmy ina?, a'a su zo bangarena ai shima yau din ta yiwu ta bakinsa yake kawai, su zo bangarena bari ma in je in gyara musu dakuna, Ama anmy kuma bangarensa? Ina shi ina su?"

Anmy ta yi dan murmushi ta ce"
Eh, Nadiya, bakinka ai abin girmamawa ne, kuma ya'yan amininka ai yayanka ne, Shikenan kina iya tafiya sai na ji daga gare ki"

Nadiya kam ta rasa me zata ce, ta mike ta yi gaba hankalinta na son tashi sosai da sosai, cabdijan wani balakin ya kuno.


Najeeba ta gaza motsawa, har sai da Anmy ta dubeta ta ce" yanzu yaya zamu yi kenan?, "

Najeeba ta yi shiru dan ta rasa mene,? Har sai da anmy ta ce" gaskiya bana so ta sauki bakin saboda itama yan uwanta ai suna nan abin zai yi mata yawa, ke kuma da muke fushin nan da kike nan bangaren yaya za'a yi ki je dan kawai ki sauki baki?, bana son abinda zai haWaki da shi , yaron nan zai gane da mu yake zancen, ai jira nake a watse taron nan, sai na gigitashi in bai baki takardar ki ba, ............inaga kawai bari in je da kaina in sa a bude dakunan wancen falon bakin su shiga, ba zaki je cen bangaren ba sam!"

Najeeba a sanyaye ta ce" ANMY wani Falon?"

ANMY ta ce" Nasa mana"

Najeeba ta langwabar da kai a sanyaye ta ce" Aya Anmy, ai zan sauke su a nawa bangaren ma, bayan wannan Anmy ai rigimata da shi a ganina siri ne da iya mu da Iyayenmu ya shafa, ku din ma Anmy in har da hali ai kawai ba sai kun shiga ba, rayuwar ma duka nawa take ANMYNA?, Allah ya huci zuciyarki bari in je in sa a gyara falon nawa Anmy kin ji?"

Anmy ta yi dan tsai kafin ta girgiza kai ta ce" Ke, ba zaki gane ba, ai in fada maki Ni ba abinda ya wani dameni da du mai ji ya ji, ai huja gare mu ta kirki, dan haka kawai bari in sa a gyara musu wadincen dakunan , bari in ga su jakadiya su gyara musu cen din kawai"

Tana gama fada ta fice a dakin , hakan ya sa Najeeba rafka tagumi bayan ta furta" Me yake faruwa ne?, Yayama za'a yi ace a sauki zinariya a bangaren SULTAN ? Ko kuma ace mu zamu sauki zinariya a bangaren mu?, me hadin mu da sauke ta a bangaren mu? Du dakunan wannan wajen?, anmy kamar fushi take ko menene? In ba wannan ba yaya za'a yi Anmy tace wai me zan yi a bangare na? Me yake faruwa ne innalilahi???"

Tana nan zaune msg suka ringa shigowa cikin wayar Tata,

Da sauri ta dauko tana dubawa...., ai kuwa msg din soyayyar da ta bijiro masa kwanakin nan kamar ta kashe shi ce ya turo

Sai ta samu kanta da jin zuciyarta na daukan salon, harma jikinta ya mutu murus kirjinta ya cika da bege....., lahaula wala kuwata, wato idan gangar so ta doka, sai ka ji tamkar kai Waya akewa ....., gaba daya ta nemi fita a hayacinta har sai da ta samu kanta da rubuta msg kamar haka" Abiey M, na gaji...."

Tana turawa amsa ta dawo mata yana mai rubuto shima ya gaji.....hakan ya sa ta ce" Da me ka gaji????"

A yanzun ma amsar sai da ta sa ta langwabar da kai cike da tausayi da tunanin bawan Allah marayan Allah, daga dan yin laifi ta hau sai masifa take masa....? Domin sakon ya kunshi kalamai ne kamar haka" Na gaji da fushin ki bb, na gaji sosai, bana iya koda daga yan yatsuna saboda yada kike fushi, PLZ fgv me"

A hankali ta mike ta je ta dauko hijabin ANMY cikin kayanta ta zumbula

A boye ta fito, tana dan Dube Dube ta yi wuf ta bude corridor ta fada ta janyo da sauri sannan ta tsaya tana sauke numfashi.....
Su nasu tsarin zaki fita daga kwananki ne idan dare yayi ya shigo, tunda yanzu yama ce magariba bata yi ba kawai sai ta nufi bangaren sa gaba daya zuciyarta na bugawa da tsoron abinda ya faru yanzu da Anmy

A lokacin da ta shigo falonsa na karshe ta same shi kishingide yana rike da wayar

Ajiye wayar yayi da sauri ya mike tsaye ya bude mata hannayensa.......

Kallonsu take kafin ta noke kafada tana turo baki a hankali ta ce" Da na zo ranar ba korani ka yi ba....."

"Oh cm on Beebahhhhhhhhhhh....., PLZ ki manta...., wani irin rigima ne Bama samu da ke????, why sai wannan ne za'a ki yafe min.....? Kin san irin yadda neman afuwa yake da nauyi a bakin namiji ko?????, na nema ya fi a irga, PLZ zo"

Ganin sai sake neman fitina take sai shi din ya je, a hankali ya sakata jikinsa yana jin abinda ke tsakaninsu wanda yana rungumota ya gane, saboda Najeeba irin matan nan ce masu shafewar ciki luf bayan sun haihu, idan ka ji cikin Najeeba da dan tudu to ta karbo ajiya ne kawai.........

A hankali yake sake sakata a jikinsa, kasa kasa ya furta " I misss U so much"


Najeeba ta sake kwontawa luffff a kirjinsa tana jin kanshin turaransa.....

Cen ciki ta furta " Ina tsoro......, ina tsoron fushin Anmy......"

Saman Babar kujerar ya kwanta tana saman kirjinsa, cen ciki ya ce" Dan kin zo wajen mijinki zata yi fushi ko me?"


NAJEEBA ta dago ta saka idanuwanta cikin nasa, a hankali ta girgiza kai, ta ce" Kamar Anmy tana so ta shiga fadan da babu ruwanta ne fa akhee"

A hankali ya juye da ita, ya zamo tana karkashin sa shi kuma yana daga sama, sai dai sam bai sakar mata nauyin jikinsa ba, a hankali ya shiga gabatar mata da abinda zata iya cewa duniyar muradinta na yanzu, domin kamar wace take jira haka ta rike shi a jikinta tana injgn lokacin har ya dam cika bakin nata kasa kasa ya ce" A nan zaki kwana?????, Beebahhhhhhhhhhh a nan nake so ki kwana....."

A hankali ta ce" Yau ba girkina bane, na Nadiya ne "

Yana ta faman sinsinar wuyanta, hannunsa na kokarin shigewa cikin rigarta ya ce" To itama ba ta zo ranar baki girkin ta kwana ba....., PLZ ki kwana a nan yau.......i.....i........nd U"

NAJEEBA ta dubi idannuwansa da suka kade, cen ciki bayan ta kai hannunta wajen da ta san ya fi komai daga masa hankali ta shiga haukata wajen da salon da ta san da wahala ya iya wani aikatuwa kuma , lokaci daya harshen ta da daf da kunnensa tana aikata masa aikin da ita kadai ta gano lagon wannan eriyar ta ce" Au, da bana zuwa , zuwa take yi a ci lokacina ko?"

Gaba daya idannuwansa a lumshe suke, hakan ya sa sam bai san amsar da ya bada wace iri bace, shi dai ya hade eh da a'a a lokaci daya ya bata matsayin amsa ne, hakan ya sa itama ta juye da shi yada zai zamo ita zata ja ragamarsa, a hankali ta kai bakinta bayan ta gama fitar da du abinda take bukata, cikin kwarewa da aikinta ta shiga gabatar da abin da yake iya saka maza ihu bayan ba a filin yaki suke ba, kwarai ya baje ya gama Salama cewar duniya tasa ce yau gaba da baya, sai ya ji diffffffdd

Dif irin mai dif din nan kamar an dauke wuta

A hankali ya bude idannuwansa ya shiga duba wajen wutace dan ya tabbata nan zata je ta kashe, sai dai cikin ikon Allah ba beebah ba labarin ta

A hankali ya budi baki zai yi kiran sunnanta sai kira ya shigo a wayarsa

Juyawa yayi yana ayyana ' shiiiiit, waye zai kirayeni yanzu????'

Sunan da ya gani a jikin wayar ya saka shi kallo da sauri ya janyo ya daga

Tun kafin ta yi magana ya ce" Ban gane ba, waye ya zo yanzu? Kina ina?"

Najeeba ta hana kanta dariya ta ce" Ina wajen Mamana, sai ta ci gaba da zuwan ranar girkin nawa!"

Sultan ya bude idannuwansa da kyau yana son tuno wace? Meye?

Lokaci daya ya gane, ya ce " Beebah, Beebahhhhhhhhhhh, da wannan zaki yi wasa? Kin san kina iya kasheni?, ki dawo yanzu yanzu, idan baki dawo ba kasheni zaki yi!"

NAJEEBA ta murguda baki, da tarin haushin ta zo masa da tashin hankalin da ta hango musu, ya wani ce wai wani Nadiya ta zo ranar girkinta? Kenan su bata ma dame su ba ko? Bama zasu kiyaye hakinta ba ko?, ta ce" Ba zaka mutu ba, ai ba Ni kadai gareka ba, Ni ce zan mutu saboda kai kadai gareni, shi yasa kake wulakantani, kake nemana da balaki, har kace wai ta zo ranar girkina, ai ka san idan ka mu'amalanceta ta samu ciki shine shege ba wai dan gaba da fatiha ba, dama masu sanin nan sun fi take sani,"

"BEEBAH! WALAHI KI BAR BALAKI YAYI BARCI, INA IYA DAUKO KI A GABAN MAMANKI A YANAYIN NAN DA NAKE CIKI!" YA katse ta da ihun da ya sa ta Wan zaro ido kafin ta turo baki ta murda kofar bangaren Nadiya ta shige da sauri kasa kasa tana furta" I love so much muah"

Daga haka ta katse kiran ta kashe wayar hankali kwonce sannan ta shige tana Salama

Ganin shiru basa Falon nan ya sa ta nufi dakin tana yin Salama hadi da kwonkwasawa

Du irin nauyin dakunan su bai hana ta ji kukan Nadiya ba , lokaci daya zuciyarta ta buga hankalinta ya tashi, dan haka ta murda kawai ta shiga da salama tana neman inda nadiyar take

Aunty ce tsaye kanta tana fadin" Kin san na rantse maki da Allah, baki da makiyiya sama da Najeeba, to ke in yace ma zai auro zinariyar ba sai ku hada kai ku yi yakin tare ba tunda du tsoronta kuke ji?, aikin banza ke da an ce Najeeba du sai ki nuna ba haka na, kina zaune zata halakaki, kina ji kina gani zata halaka ki!, na fada maki ga abinda zamu yi a kan cikinta da ita kanta kin ce ke a'a ko?, to bari ki ji, Ni zan janye hannayena daga cikin lamarinki, Nadiya in me zata maki kar ki kuma nemana da zancen, saboda ina tafe maki KULUN da solution ke kina wasa , baki san ciwon kanki ba , shine zaki dora min kuka? Ai ki share hawayenki Najeeba ta maye gurbina Ni kanwar MAMANKI sai ta zame maki uwa da uba !"

A hankali Najeeba ta juya zata wuce Muryar nadeeya dake rike da kanta ta sa ta dakata a lokacin da ta ce" Aunty, dan Allah ki zauna mu yi magana ta fahimta, Aunty wai yanzu idan na yi mata haka in ce Na ci ribar me? Aunty maganar ita ta yiwa Aliyu asiri fa malamanki suka fada maki, muna da huja tsayayya ne?, bayan wannan Aunty Ni idan na mata me kenan? Aunty wallahi zan sake fada maki Najeeba nada fada Ama ban santa da bin bokaye ba, Aunty dan Allah kar ki ce zaki yi fushi ki fita harkata, Aunty so nake ki fahimci abinda nake kwatanta maki, daga Ni har Najeeba idan aka sako mana zinariyar nan sai mun san yadda zamu sa kanmu saboda mahaifiyarta ma bata da dadi, Aunty wai Ni me yasa ba zaki gane ba? Aunty ba zan iya aiki da maganin nan ba, to wai in na mutu yanzu yanzu in ce ma Allah me????"

Rai bace Auntyn Tata ta ce" Ashe du abinda zan fada ba zaki yarda ba? Fadar malamaina ne zaki ce?, Nadiya haka najeeba ta shanye ki? Haka kike tunani a kan kishiya?"

Nadiya ta girgiza kai da sauri ta dago zata yi magana idanuwanta suka sauka a kan fuskar NAJEEBA

A tsorace ta mike tana duban Najeeban wace ta sake juyawa da sauri zata fita

Da sauri ta biyota ta riko hannayenta muryarta a raunane sosai ta ce" NAJEEBA, innalilahi wa Inna ilaihi raj'une tun yaushe kike nan? Me da me kika ji? Na shiga uku dan Allah kar ki fada masa , idan kika fada masa koda bai sake Ni ba zai bani baya, Najeeba na san in ya ji na bata maki har haka tsanata zai yi har abada"

"Ni wa?, a kan me? Dan kin bata min? Ni wa? Ke wacece a wajensa?????" Najeeba ta katse ta sama sama

Ta Wora da fadin" ko da muna makaranta fada maki nake yi, babu wata yar da ta fi ki, kema mace ce, kema mai iko ce, kema isashiya ce, babu wata da zata kada maki datin dan kwali bayan ba ciyar da ke take ba, sunana matarsa, kamar yadda kike matarsa, kawai dan na je na ce masa kin min abu kaza sai ya tsane ki? Sha nawa yake bin bayanki a gabana bayan Ni da ke mun san baki min adalci a abinda kika yi ba????, ko kuma kina tunanin shi din jahili ne da zai maki haka? Sunanmu matansa na aure, idan wani abu ya faru zai bi didigi ne ya hukunta mai laifi ko wacece, ko ke a naki tunanin zai iya hukuntaki a kan laifin da bashi da tabas???, Nadiya baki san mijinmu ba, baki san waye shi ba, tunda har ya aureki zai zauna da ke ne ya aureki, kuma koda Anmy da ta haife shi ce bata son ki zai mata biyayya da abinda Allah ya sa yayi mata, ba zai shiga hakinki ba, bale Ni kishiyar ki!"

NAJEEBA ta ja numfashi da bakinta, wannan karon a raunane tana duban Nadiya ta ce" Ashe shi yasa kike kafa kafa da su?, ......"
Ta ja wani shashekar kuka lokaci daya hawaye na bale mata ta ce" Ashe shi yasa kike kiyayewa kar na cutar da su??????, Nadiya Ni ce fa, aminiyarki, lokacin da muke ?awance da ke Bama fada?????, mafiya fadanmu daban, yayanmu daban....., Nadiya ko wani waje kike aure ya'yanki nawa ne Nadiya, nawa ne Nadiya........."

Ta riko hannun Nadiya ta dora saman mararta ta ce" Nawa kuma naki ne, a tunanina........, a yadda na dauka....., saboda Nadiya ba zan Boye maki ba, ina kishi da ke, kishi irin na wanda ko da muna ?awance in kin taba Ni muke yin ba dadi, a yanzun ma ina iya yin ba dadi da ke ne in kawai na ga kin tabani, bayan wannan Nadiya ban san boka ko malan ba, Nadiya ban iya ba......, ko ba wannan ba Nadiya koda ace na sani zaki yarda cewar Ni Najeeba zan kai Aliyu wajen boka......... innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, baki san Aliyu marigayi Bama irinsa ne? Ko an fada maki Ni Allah ba zai iya kadarto min samun irinsa bane Nadiya.....?, wayo Allahna zuciyata, Nadiya......m"

A hankali ta sake ta ta juya zata yi tafiyarta

Aunty rai bace ta ce"
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




44



Rai bace Aunty ta ce" Ke Najeeba ai sai dai ki birge wani da munafurcinki ba dai Ni ba, dan haka kawai ki tafi, bayan wannan a kan me zaki shigo ki tsallake ko'ina ki sauka har nan dakin? Ai dakinta na siri iya ita da mijinta zasu shiga ba wai kishiya ba!"


Fuuuu najeeba ta juyo ta karaso inda aunty take, ta matse mata waje sosai ta yada auntyn ta yi baya sau daya, Najeeba ta take sawunta da mugun karfin da ya sa aunty neman rike wuyan Najeeba

Da sauri Najeeba ta tare hannayanta ta rike nata wuyan ta zaro ido sosai ta matseta sosai a jikin bango

Da gudu Nadiya ta zagayo ta kama hannayen Najeeba tana son bambarewa saboda aunty tuni ta shiga kokarin mutuwa

NAJEEBA ta bangaje Nadiya ta rike aunty da kyau kafin ya Bala mata wani mahaukacin mari tana sake dane kafafuwanta da nata ?afafuwan ta ce" Ke dama na jima ina mangarin wanan lokacin, tun lokacin da kika samemu a dakin Nadiya kike tatare kayanta kar a sata na rike ki a rai, ashe dai Allah zai cika min burina?????"

Nadiya a rikice ta ce" Najeeba saketa, saketa najeeba, kar ki yi ta dake ki a ciki ta ji maki, Najeeba ki saketa"

Najeeba ta sake ri?e ta ta ce" Idan bata suma ba Ni zan suma, idan har anamimiyar nan bata suma ba Ni zan suma, ke in banda baki da hankali an fada maki kowama irin ki ne?, Ni zaki ce ina bin malamai? Ni? Ni zaki yiwa iyaka da ya'yan yayana? Ni zaki nemi yiwa iyaka da ya'yan Aminiya daya jal da na rike a raina? Ke yanzu in rasa wa zan birge sai ke? In rasa wa zan birge sai ke?, shigowa dakin nan kuwa kema uwarta kika shigo bale Ni da abu daya muke rabawa da ita?, ..............ki ji, ba zan hana ki munafurcinki ba dan dole ai sai kin samu abinda zai sa ki jima a gaban Allah, Ama kika kuskure kika kuma shiga sabgata sai na nuna maki Ni mahaukaciya ce!, aikin banza aikin wofi!"

Shigowar su jakadiya da gudu du suka duka sunna faman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login