Showing 12001 words to 15000 words out of 144591 words

Chapter 5 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2328

da shi ba , sai fitarsa na sani, ya Allah"

A hankali yake dan murza hancinsa jikin nata, kasa kasa ya ce" Allahn da ya bamu, zai sake bamu wani mai zaman...., idan ma bamu samu ba , Alhamdulilah tunda mun samu su Muhammad"

Idannuwanta ta bude tana kallon fuskarsa, shima ya bude nasan ya saka cikin nata, a dole ta sada idannuwanta tana dauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Allah ya bamu masu albarka"

Murmushi yayi yana kallonta ya ce" In sha Allah, kar ki saka damuwar hakan a ranki nah?"

Najeeba ta gyada kanta tana sake jin hakuri da dangana na sake mamaye zuciyarta, yana shafa hannunta kasa kasa ya ce" Danma kina jinni Beebah, ai da yanzu ma an sake yi miki wani in dai cikin ne"

Ido ta zarro tana kallon bakinsa , kasa kasa ta ce" SHAHEED"

Ya dubi idannuwanta da bakin dake kama sunnansa kai tsaye

A hankali ta yi murmushi tana sine kanta dan ta san shima abinda ke saka shi saurin kallon KENNAN a duniya, ya sha fada mata bai san dalili ba, idan ta kama sunnansa yake jin sunnan kamar ba nasa ba daga bakinta, yakan ce da ita wannan kawai ke saka shi jin shima yana soyayya......, ya zamo du idan ya yi abinda zai sa ta tsayar da dukkan abinda take yi ta Dube shi, itama sai ta rama ta hanyar shamatarsa ta fadi sunnan nan nasa mai daraja da girma a duniyarta.....

Ya dauki lokaci a wajenta kafin ya mike da nufin zai ga likitar in dai dan kawai ?arin ruwa ne ta bashi matarsa ya je gida da ita

Murmushi kawai ta masa har ya fice sannan ta jingina da garu tana jin nutsuwa a zuciyarta har matar yaya Dayabu ta shigo da plate di???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?n abinci tana fadin" Iyeah, Malama gyara zamanki kin wani baza ?afafuwanki, hade min su, kuma ga abinci nan ki ci ki sha kunnun nan dan jikin ki yayi karfi"

Najeeba ta talabe haba ta ce" Ba dai da ke zasu barni ba? Ai da na shiga uku, wai ke me yasa kike takura min ne Ni?"

Ta kai zaune tana harararta ta ce" An takura din, gaskiya sai kin warware Ni ban cika son munafurci ba, kin ga mijinki sai wani langwabewa kike yi, kama ki ci in fada maki amanata da yayanki yake daf da ci"

Ai kuwa Najeeba ta karba tana gyara zama Wan ta tabbata ta kunso mata labari, bale yaya Dayabu ai ya lalace, so yake yi ya koyi son yan mata, in an yi magana dai yace wai shi ba halinsa bane , bayan har takakiya ake yi mata a tardota , sai sun zo su gane shayi ruwa ne da kansu su tatare tsumakaran kaffafuwansu su tafi, dan matarsa ba kyala bace, bata daukan wulakancin yan matan zamani, ta fada bata Hanna shi aure ba, Ama kuma ba zata dauki iskanci da bin namiji gida ba bayan ita tana gidan matsayin matar aurensa...........

A lokacin da SULTAN SHAHEED ya fito su duka suka mike sunna masu tambayar mai jikin, da masu yi masa Barka da fitowa

A mutunce, da yannayin girmamawa shima ya sake yi musu fatan samun lafiyarta sannan ya dubi junior da ya kama hannunsa da nufin zasu wuce dan Anmy ta lalabashi cewar zasu zo shi da Muhammad ya je ya dauko Muhammad, shi yasa ya yarda da tafiya gidan

A tausashe ya ce" Zan ga likita Boy sai mu tafi?"

Junior ya gyada kansa yana juyawa wajen su Anmy, shi kuwa ya nufi hanyar office din likitar , dogarai biyu na dafe masa baya, Sarkin gida na shelar a bada hanya a rike kafa Mai DAMAGARAN na tafe har suka karaso kusan ofice din sannan Aba ya dakata shi kuwa ya shiga bayan dogari ya bude masa kofa, dayan kuwa ya je da sauri yana gyara kujerar da zai zauna hadi da dukawa har ya karaso ya zauna sannan ya mike bisa umarnin SULTAN ya fice hadi da jan kofar

Duk irin yadda Docter IZRANE ke tunanin ta feshe office dinta da turare mai kanshin gaske da dadi shigowarsa sai da kanshinsa ya kwace komai, haka kuma zaman da yayi sai ta nemi nutsuwarta ta rasa har sai da ya dago idannuwansa masu Wauke da kwalin dake halitarsa ya sauke duban nasa a kanta bayan yayi gyaran murya kadan ya furta" Likita, AKOY wata damuwar ne bayan zubewar cikin?"

Da kyar ta iya janyo numfashinta, ta daidaita kanta kafin ta aro fuskar da ta gama tsarawa kanta bayan tana rike da takardun a raunane sosai ta ce" Ka yi hakuri sir, a yanzu da ya fice ba wata damuwa Ama idan har aka ci gaba da neman zubewarsa wata rana ana iya yin asarar rai"

Idannuwansa ya sake Worawa a kan takardar dake hannunta kafin ya ce" Pardon?"

Likitar ta dago tana duban alkyabar dake jikinsa dan ta kasa yin ido hudu da shi ta shiga alamun shashekar kuka ta ce" Idan na hadu da cas na barewar ciki hankalina na barin jikina, bale idan har cikin nan wasa aka yi da shi ko aka zubar da shi da gangan ko kuwa da ganganci........, ko dan ina da burin cika ya'ya idan Allah ya bani miji ne? Ina da burin tara ya'ya a rayuwata, in sha Allah idan na yi aure ko tsalaken shekara daya ba zan saka ba wajen haihuwa, domin bana tunanin kokarin rike kyau, ko gudun kar na tsufa,ko kuwa gudun kar in tara tumbi na daya daga cikin abinda zai Hanna Ni daukan ciki"

Wannan karon fuskarta ya kalla na dan lokaci a zuciyarsa yana ayyana magana kamar haka' to Ni me ya hadani da batun rayuwarki....mema ya kawo wannan maganar a maganar rashin lafiyar matata? Hum'

A bayyane kuwa sai ya ce" Ok., idan bata da wata matsala zan tafi"

Gaba daya sai ta nemi tsarguwa da neman rasa zaren da ta rike dan fakewa saboda ta jefi tsuntsu biyu da jifa daya, Ama kuma da sauri sai ta ce" AKOY matsala baba sir, matsalar kuwa itace idan har Gimbiya bata daina anfani da maganin mata masu hatsari ba, lalle haka zata rinka zubar da cikinta, karshema abin ya taba lafiyarta ko Rai."

Da sauri ya dubeta, kallon da ya sakata cikin tsarguwa ta ajiye masa hoton cikin da kuma wata takardar result din da ta rubuta a sanyaye cike da rauni ta ce" Mata sunna da matsala, Yawancin lokuta dan kawai su birge namiji sai su yi ta afka abinda basu san da me aka hada shi ba, basu san menene karfinsa a jikinsu ba, har sai ya hadasa musu ciwo ko ya saka su a wani matsayin marar dadi kuma su dawo su ringa kaka zasu yi da rayuwa....... Ta'amali da maganin mata babu abinda bay......"

"No, bata anfani da ire Iren abin nan!" Ya katse ta yana duba takardar hadi da sake kallon hoton cikin duda ba fahimtar abinda ke ciki yake yi ba, ya ajiye mata su a gabanta ya dubeta da kakkausar kallo ya ce" Sai dai idan wani abin ne...., bana jin AKOY wace ta kaita son ta karra samun haihuwa a rayuwa...., ba zata sha wani abin da ta san zai yiwa abinda ke cikinta ila ba!" Ya fada cike da tabbatarwa sannan ya sake tsareta da kallon da ya sa ta ji kamar an kama barawo ne a cikin lokacin da yake aikata sata , wato tsamo tsamo dai.

A birkice ta dauki takardar hadi da gyara zamanta da kyau tana dubansa ta ce" Ai ita bata san da cikin ba sai da ya zube, sannan wannan takardar ta binciken da aka yi mata ne na jinninta da na dauka, haka kuma ga ledar hannun da na duba jikinta a jikin ledar AKOY sauran abin magani sir....."

Sai ta ajiye maganar a hankali ta janye takardar tana sauke ajiyar zuciya ta ce" Ka yi hakuri sir, ban san hakan zai sa ranka Saci ba, hasalima na fadi haka ne dan a taimaka a Hanna gimbiyarmu aiki da maganin mata saboda yanzu an ci gaba sosai, ba komai bane ake sha ko cusawa a jiki dan a samu biyan bukata da namiji ko dan a birge shi ba, in sha Allah zan kwatanta mata nima, ina fatan wanda za'a samu gaba ya zo duniya lafiya kalau"

SHAHEED ya dauke idannuwansa daga kan table din dake gabanta, du maganar da ta yi a sanyaye, sannan a tausashe ainun ne, haka kuma cike da girmamawa ne, sai dai duda haka batun cewa har jikinta ta gani ya sake dukan kirjinsa da karfin gaske.....shin ina dokar saka mayafi a tsakanin wajen da yake rufafen siri nasa da idon wata halittar bayan mamalakin wajen koda kuwa likita ne??

Mikewa yayi, bai ce da ita komai ba ya juya ya nufi hanyar ficewa, hakan ya daga hankalinta sosai domin har jikinta rawa yake yi, a lokacin da ya buga sandarsa sau daya Sarkin bulala ya bude kofar ya kai gwuiwarsa daya kasa, daya ya dora gwuiwar hannunsa zai fara magana irin wace yake yi idan ya budewa uban gidan nasa kofa sai idannuwansa suka sauka a kan wace ke daf da rigar ASARKI, ya zamo su Aba du sun ga bayanuwar Sultan SHAHEED, haka kuma a kan idannuwan kowa suka ga dukawar Docter kasa daf da shi, Muryarta a raunane ta ce"
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati na airtel ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




5



Tana daf da fara magana Sarkin bulala da ya ga dukawar da ta yi tana kusa da takalmin SULTAN, sannan yannayin SULTAN ba yannayin da ya shiga bane, wanda ya fito da shi yanzu yayi daidai da idan ransa a bace ko hankalinsa a tashe, hakan ya sa ya mike da ?atuwar Muryar nan tasa ya daka mata tsawa yana fadin" Ja baya, saka tazara tsakaninki da Sarkin ki talaka! Ki rike numfashinki kar ya sauka a jikin tufafin ZAKINA!, Kul da ke Y'ar talakawa, yi baya ko yanzu kanki ya sauka daga gangar jikink....."

Da sauri SULTAN ya saka sandarsa tsakanin bulalar hannun Sarkin bulala da DOCTER IZRANE , wace ta zabura jikinta ya dauki mahaukacin rawa da tarin tsoron Sarkin bulala, wanda nan da nan tuni ta hango kanta yayi mata mugun duka kamar jaka kuma kuwa da ya daki banza dan babu ikon da zai rike shi da wannan domin takarda gareshi rubutaciya wace ke kare shi daga dukkan wani dan Shari, dan kuwa an fada an shelanta kuma an fadawa bako cewar du tsakaninka da SULTAN kar ka yarda ka matse masa waje a gaban jama'arsa, bale Sarkin bulala......, idan har hakan ta faru ya ga wani yannayi na rashin gamsuwa tabasss zaka amshi bulalarsa tsumamiya ta dukan ra?umi wace kwanan duniya take kwana cikin man jimina da jikaken barkonon tsohuwa marar hadi, wannan ya sa a kullum laudi take karra yi da zafin balaki.

Da sauri Sarkin bulala ya duka kansa a kasa yana furta" Tuba nake ranka ya dade, Allah ya huci zuciyar mai wukar yanka, Allah ya saka ruwan sanyi a zuciyar uban gidana "

Sandar tasa ya maida a nutse ya ya cakata daf da shi kafin ya bude bakinsa a hankali ya furta" Ba komai likita......."
Ya ajiye maganar a hankali sosai kafin ya dora da fadin" Giwatah zata kiyaye in sha Allah "

Daga haka ya sa kai ya wuce, yana yin gaba Sarkin bulala ya mara masa baya sannan Aba ya shige cikin tawagar yan rakiyarsa , ya zamo Sarkin murya na sake shelar a bada hanya, a kiyaye fitowa, Mai DAMAGARAN zai wuce......., Muryar da ta ratsa ko'ina a asibitin har suka gama fita daga asibitin

Wata irin ajiyar zuciya Docter IZRANE ke saukewa har yanzu jikinta na rawa,
Hannunta ta daka ta cire dan kwalin dake nade a fuskarta zata wurgar aka sake bude office din nata aka shigo

Da mugun sauri ta nufi wajen table din ta tana saka ihu hadi da fadin" Innalilahi wallahi wallahi ban taba rigarsa ba, security, security!"

Sarkin bulala ya bude darjejiyar Muryarsa ya ce" Uba yace a harhada takardun awon da aka yiwa Giwarsa, harda ledar da kika yi awo da ita a bani"

Da sauri ta gyada kai tana bin bulalar nan tasa mai laudi da kallo cike da tsoro ta shiga harhada komai din, ta je har cikin abin sharar ta dauko ledar hannun, kirjinta sai bugawa yake yi cike da tsoro ta saka a leda fara ta hade cikin kayan ta mika masa harda dan rage tsayinta

Amsa kawai yayi ya juya ya tafi motar dake jiransa ya shige suka tafi

Hannaye ta dora saman kanta cike da tsoro bayan ta sakawa kofar ky ta furta" Innalilahi, na shiga uku, me zai yi da takardun? Ba dai bai yarda da abinda na fada ba, me zai yi ne? Innalilahi, kar dai ya tsane Ni......wayo Allahna yaya zan yi? Na shiga uku"........tashin hankalin da ta shiga mai girman gaske ne, shin yaya za'a yi daga yi masa wannan bayanin ransa ya bace har haka? Yanzu ina zata nufa? .......A dole ta cire rigarta ta asibiti ta dauki ky din motarta da jakarta ta barawa nurse din da zata kwana salahun wajen karfe uku a sakawa Najeeba travar wanda zai sake sauke mata zafin radadin , da safe kuwa a saketa idan Docter ya zo, ita bata da lafiya zata je gida ......., haka ta fice tana gwada NUMBAR matar alkali.....wace itace ta fara bata CD din wacece Najeeba, itace ta sanar mata labarin NAJEEBA fila fila harda rikicin da suka yi a kan mijinta a lokacin da NAJEEBAr take budurwa, wanda sanadiyar Najeeba mijinta ya taba sakinta..............., a yanzu haka itace man injin dake ?ara zuga mafarkin IZRANE, ta gabatarwa IZRANE cewar dukkan abinda Najeeba ke takama da shi itama ta malakeshi, kwarai tana iya samun SHAHEED!


A daki kuwa NAJEEBA na saurare da tunanin gannin dawowar SHAHEED dan su wuce gida sai jin sanarwar fitarsa suka yi, wanda hakan ya saka ta Wan yi mamaki kafin ta ture abin a ranta da tunanin ta yiwu kiran gaggawa ya samu, ta tabbata zai yi kiranta ne idan ya nutsu dan su yi fira da dare..........

Kusan karfe takwassss su Anmy da umi suka tafi bayan an ajiye dogarai da sojawa hudu da zasu kula da dakin nata, zata kwana tare da jakadiya da kuma Matar yaya Dayabu.


IZRANE
Tuki ta yi na ganganci har ta isa gidan alkali Karuge alkalin manya

Tana zuwa mai gadi ya bata damar shiga duda daren da ya tsala, domin dama daga mai gidan har matarsa sunna iya amsar bako karfe ukun dare ba damuwarsu bace, bale ta ga matar na zuwa lokaci zuwa lokaci wajen matar gidan sai kawai ya bata dama

A lokacin da ta shigo cikin gidan dama sama ta rings jiyo Muryar matar gidan tana waya tana fadin" Sai me alkali? Nace sai me? Idan kana so ka je gidan giya ka kwana, meye ban gani wanda zai fito daga wajen ka? Babu abinda baka nuna min ba ai alkali, in ka cika dan halal ne kai ka kwana da mata dari a daren yau a gidan yan bariki nan zan yarda cewa kwallon dan iska kace!"

Hannu ta saka ta bude kofar ta shiga da mamakin maganganun da take jiyowa, ai kuwa tana ganninta ta datse kiran hadi da cije baki kafin ta daki tana huci ta ce" Docter ce, Bismillah"

Docter IZRANE ta ce" Hajiya kamar na same ki ba daidai ba, waye ya tabo ki haka?"

Ta girgiza kai ta ce" Kin san a duniya babu macen da ta yi asarar aure irin wace ke zaune da d'an bariki, a kullum hankalinta ba zai kwonta, idan yau ya bi karya gobe akuya zai bi, wai Ni alkali zai yiwa karyar wani aiki ya diro masa mai zafi ba zai shigo da wuri ba sai kusan karfe hudu in ya gama? Yana maganar Muryar mace kasa kasa na tashi , wato sai ya gama watsewar zai dawo min karfe hudun dare ya yasu a daki ba sallar asubahi bale in sa ran zai farka ya karya da ya'yansa, sai ya wuni yana sharar barcin asara? Kai wannan mutumin an yi tambadade dan asara!"

DOCTER IZRANE ta zauna a ranta tana girmama rashin mutun matar nan, yanzu mijin nata ne take kira da dukkan sunnan da ya zo bakinta? To in ba zata iya zama da shi ba ta fita mana, Ama dan masifa auren irinsu shine auren nan da baya mutuwa, kullum cikin tura kai a halaka da tura abokin zama, basu kiyaye dokokin Allah ba bale su ba auren hakinsa, kuma ba za'a rabu da junna ba
Docter IZRANE ta ce" ai sai hakuri lamarin mazan nan, Ni kam na zo na sameki ba a daidai ba bari in wuce kawai"

Hajiya ta ce" Kai haba, wannan abin zai daga min hankali? Sai kace zancen kudi? Ai ya saba wannan da kika gani, bani labarin abinda ke tafe da ke, wai ya lamarin SULTAN ne? Ina nan ina tayaki da addu'a kawata na tabbata sai kin shiga gidan SULTAN dinmu"

Ajiyar zuciya Docter IZRANE ta sauke ta ce" Hum, yau ina aiki ba sai ga NAJEEBA an kawota ba, bata da lafiya? Wai kin san yar balakin nan da nake tunanin yayanki biyu kawai na zasu bani wahalar kawarwa ba shine ta zo min da ciki??"

Sai da Hajiya ta dafe kirji ta ce" Ke dan Allah fa? Innalilahi ai kuwa in dai ta haihu ai ban ga hanyar da zai dubeki ba, kin kuwa san cewa hanyar da zata sa ya iya dubanki kawai ta maganar haihuwar nan ce? "

Docter IZRANE ta tabe baki ta ce" Yar iska ce Ni zan bari ta haihu?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login