Showing 21001 words to 24000 words out of 144591 words

Chapter 8 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2333

ci komai, sannan in an zo kwonciya a sha kofi daya, haka har tsayin kwanakin al'ada sai a dakatar, sai wata al'adar , in kuwa an dace Shikenan........ ( Awon zai shigo idan aka gama free page)
Tabasssss, tana neman haihuwa ta dukkan hanyar da aka bata mai sauki, wace a tunaninta neman magani ai ba haramun bane, halak ne!

"Daughter" Muryar Anmy da ta gaza tsayuwar da take tun dazu ta fito ne ya saka NAJEEBA juyawa da sauri ba tare da ta ba Nadiya amsar tambayoyin da take yi mata kan wai maganin ta sha ya hadasa mata bari nan ko me??????

A tausashe Anmy ta ce" Ki je ki kwonta ki huta "

NAJEEBA ta sake zubawa fuskar Anmy ido, kafin ta daga kafa da kyar juwa na kwasarta ta nufi dakin Anmy ta hau gadon ta kwonta tana kallon Aliyu dake barcinsa hankali kwonce

Anmy da kula ta dubi Nadiya ta ce" Bari in dauko maki Aliyu ki je bangaren ki ki huta kema"

Juyawa Anmy ta yi ta shige dakin ta dauko Aliyu ta dawo da shi ta mikawa Nadiya shi

A lokacin da Nadiya ta amshe shi Anmy ta dubeta cikin ido tace" Ki yi zamanki a bangaren ki yau, idan kika tarda shi a haka....tabas zaki bi hukuncin da ya tanadarwa wanda yayi kisa, ku yi hakuri ku daga masa kafa"

Nadiya ta gyada kai tana yiwa Anmy Godiya ta fice ta nufi bangarenta zuciyarta cike da bacin rai da takaicin dama NAJEEBA ta tsokalo shi aka sakata a cikin fadan? A kan me dan tana sha zata ce masa itama tana sha? Kenan NAJEEBA ce ta sanar masa cewa itama tana sha? Ama NAJEEBA an yi yar wulakanci, ina ruwanta to? A inama ta sani ne? Ok kennan bibiyar abinda take ciki take yi ko me????

Tana shiga bangarenta ta tarar da missss callll din mamanta da na kanwar mamanta

Zama ta yi ta mikawa mai kula da Aliyu shi ta sa ta shinfide shi ta turawa mahaifiyarta kira bayan ta shige cen cikin dakinta ta rufe

Maman natama jiran kiran take yi, domin tunda suka dawo suke kiranta basa samu, in ba dan Bama dare yayi sun san ko sun zo haka kansu tsaye ba barin su shiga za'a yi ba da tuni sun zo gidan

Cikin yanayin tashin hankali ta sanar musu abinda yake faruwa da irin yadda ta nuna masa nata da komai

Mahaifiyarta tsabar takaici kasa ce mata komai ta yi, sai auntynta ce ta ce" Yanzu dama Nadiya har yanzu baki da wayo? To ko kamaki yayi ido da ido ba sai ki murje ido ki nuna masa ba komai bane da ya danganci maganin matan, shine kika dauko daga yi maki tambaya kika bude masa kika zayane masa komai? Tambayarki yayi wannan? Amsa daya ce zaki bashi fa itace eh ka hannamu daga nan ki ji me ya zo da shi, Ama tsabar baki da tunani shine kika saka kanki a laifin da baki ji ba baki gani ba? Laifin matarsa ne fa kika rabawa kanki, zuwa yayi dan ya ji daga bakinki dan ki zame masa sheda, ta yiwu da Shikenan Allah ya rabaki da Alkakan zama da ita matsayin kishiya da ace kin yi aiki da damar ki kin nuna eh ya Hanna hasalima ke baki taba sha ba , sai kawai kika fada kika tonawa kanki asiri?, kai subahanalah!"

Nadiya ta yi tsuru tsuru ta ce" A'a Aunty, Ni ai ina tunanin itace zata ce masa nima ina sha dan kawai ya hade mu ya mana fushin tare, wallahi ya dauka da zafi Aunty, kin ga irin yadda ya fatataketa? Ni ban taba tunanin itama yana iya yi mata haka ba sai yau, ashe itama yana yi mata fada????"

Mamanta ta ja tsaki ta ce" Ke dai jarabawarki wannan yarinyar ne, matsalarki a duniya wannan yarinyar ne, to wai wacece ita da zaki ringa yi mata kallon wata wace ta fi karfin komai?, a kan me zaki ce ita ba zai yi mata fada ba? Yadda kike a wajensa haka take, matansa ne ku duka, kin tsaya kina wulakantar da kanki hadi da nunawa ke ba kowa bace bayan dukkan wani abu da take iya samu a wajensa na kula haka zaki samu tunda kema aurenki yake yi, ke kar fa ki manta ke shi ya nemi aurenki, ita kuwa bashi aka yi ama sai ki ringa neman wulakantar da kanki a banza a wofi!, mtsssss wai wani ta san kina shan maganin mata, a ina ta sani? Yanzu dai kin sanar da ita da shi baki daya, ke kam ban san me yake kwakwaluwarki ba Nadiya!"

Nadiya tamkar an yi mata mugun duka haka jikinta yayi ba karfi, kwarai sai yanzu ta gane da farko ba laifinta yake nema ba, itace ta kawo laifin nata ta baje masa a fili....., ya Allah yanzu yaya zata yi? Kar dai abin nan ya kai har Sultan ya sake ta..... innalilahi

A raunane ta ce" Mama, kar dai ya sakeni saboda abin nan"

Da karfi maman nata ta ce" A bakinki dan ubanki, Nadiya idan ya sake ki ai mu ya saka a uku ba ke ba, tunda har sarakuwarki ta ji ki yi abinda tace din, ki ringa zuwa wajenta ta nan zaki samu halin da ake ciki, wace ta zubar masa da cikinsa ma bai saketa ba sai ke???"

Auntyn ta karSe maganar da fadin" Kin ga, kar ki saki ki yarda maganar nan ta yi nisan da zaki janyo mana wata masifar da ba zamu iya dauka ba, ki yi iya yinki ki tabbatar da ya hakura, zan shigo fadar gobe in sha Allah mu sake zaunawa da ke, dan na san halin ki yanzu kina cen kina neman fita a hayacinki bayan ba laifinki bane! Ba kece mai laifin ba"

Haka dai suka yi ta tattaunawa da Nadiya har ta samu dan kwarin gwuiwa kafin su yi salama .


A bangaren Anmy kuwa dare ya tsala, Anmy na saman salaya tana ibada, Najeeba kuwa na juye juye a saman gadon Anmy din, domin a dazu tashi ta yi ta koma dakinsu bayan an dauke Aliyu, Anmy din ce ta dawo da ita nan din ta bata magungunanta sannan ta umarceta da ta kwonta ta huta


Tana cikin yanayin nan barcin kirki bata samu yi ba har Anmy ta kwonta a shinfidar da ake yi mata yanzu a kasa saboda ciwon baya tana hankalce da NAJEEBA har barci ya dauketa ita, Ama NAJEEBA kirjinta na yi mata mugun zafi da radadi mai azabar tsiya na maganganun SHAHEED...........

Dama haka ake ji idan ana son mutun wani baban sabani ya gifta tsakani?...... Ashe matan dake kuka a kan saurayi ko mijin aurensu sunna da dalili?, ashe har haka zuciya ke yi? Tabasss da ba dan ta san cewa bata da ciwon zuciya ba da tace ciwon zuciyarta ya tashi, lokaci daya ta yi wani irin firi firi da ita, barcin ya gagari idannuwanta , har wata rama ke son damkar jikinta.......

A lokacin da aka yi kiran sallar farko Anmy ta mike ta sake kallon inda Najeeba take, ta kuwa gane idon yarinyar biyu , ta nufi bayi dan dauro alwallah ita kuma a lokacin ta samu ta sadada ta nufi dakinsu na da ta shige ta rufe ta nufi gadon nan ta hau ta je cen jikin bango ta hade jikinta hadi da rintse idannuwanta ta kankanme kirjinta lokaci daya ta saki hawayen dake cen cikin zuciyarta ya bale mata.........mmm

Hanci ta ringa ja kirjinta na bugawa......, a hankali ta zubawa wayarta ido lokaci daya maganar likitar nan na dawo mata kwakwalwarta a jiya da take cewa idan ya gama ya je su gana........

A jiya din, kafin ya fita sun rabu cikin aminci ne, bayan ya fita ne har ya fice basu yi salama ba......., tabas du inda maganar nan ta fito daga bakin likitar nan ne

Mikewa ta yi tsaye tana dafe kugunta, lokaci daya jikinta ya dauki rawa na bacin rai da jin haushi

Wayarta ta dauka ta danna layin Aida.......

Duda asubahi ne Ama aida ta farka tuni, dan tana yin Sallah take zuwa tana tsaye a yi share sharen saloon da komai da komai

Amsa kiran ta yi da girmamawa ta gaisar da NAJEEBA din sannan ta yi shiru tana sauraron ta

A hade NAJEEBA ta ce" Ki min binciken wacece DOCTER IZRANE, ba sunnan iyayenta nake bukata ba, ina son in san wacece ita a zahiri, ki yi kokari a yau ki samo min informations a kanta , sannan ki nemo min tushen ta!"

Aida ta ce" Ok ma'am in sha Allah, kennan yau kar in bude saloon?"

NAJEEBA ta ce" Idan baki bude ba zai zamo abin tsegumi da tunanin Bakya nan bana nan, Ni kuwa so nake yi ki yi komai a sirance, in nawa zaki kashe ki kashe ki samo min komai "

Aida ta amsa da biyaya sannan suka kashe

NAJEEBA na kashewa ta danna NUMBAR librairie na gidan, wanda a nan ake kula da duk wani sakwaninsu ba shiga da na fita

Ba'a jima ba aka daga dan dawowar Malami kenan daga masallaci a lokacin mai DAMAGARAN ya shige gida shima

A nutse ta gaishe shi, domin malami ba yaro bane kuma shima jinnin sarautar ne, sannan mutun ne da yayi dogon karatu a waje , yake aikin matsayin wanda ke kula da dukkan ragamar fannin tarihi na masarautar

A tausashe da darajantawa ya sake gaisar da ita, domin daukaka Allah ke badata Allah ya nadata matsayin shugabarsa dole zai yi mata biyayya, bale ita da kanta ta sake siyawa kanta mutuncin domin ta nemi daraja kuma ta samu ta hanyar darajanta kowa a fada.

A tausashe ta amsa, kafin ta yi dan tsam, a hankali ta ce" Baba Malami, A tura gaya daga dakina zuwa asibitin da ake duba mu, a gayyato min baban asibitin da matemakiyarsa Docter IZRANE......, su zo yau da yama bangarena"

Malami ya sake rage tsayinsa a tausashe ya ce" Gayyatar rashin lafiya ce mai baban daki?"

NAJEEBA ta ce" Gayyatar tattaunawa ce "

Ya sake cewa" ta laluma zasu zo ko ta duk yadda hali ya kama a kawo maki su gabanki?"

NAJEEBA ta lumshe idannuwanta, sannan ta sake budewa a tausashe ta ce" Idan sun ki amsa gaya ta laluma, a barsu da jinin MUTALAB Baba"

Malami ya duka ya furta" Allah ya huci zuciyar Gimbiya, Allah ya huci zuciyar mahaifiyar Abdallah da Muhammadu, tuba muke da tuban mai laifi, zasu zo koda basu so ba, wane su, wane karshen zamanin su, ai baban goro sai magogin karfe, zasu halara a falon baki da yama in sha Allah"

A hankali ta furta " Madallah " sannan ta katse kiran ta ringa kai kawo tana dantse lebenta cike da jin idannuwanta sun soye tassssssssssss

Kamar yadda ya saba shiga da asusubahi gaishe da Anmy haka din ce yauma, bale jiya bai samu ganninta ba sai yau

A lokacin da ya shigo dakin nata ya sameta saman salayarta yadda ta saba

A hankali ya zauna daf da ita kansa a kasa ya furta" Barka da yau Anmy"

Anmy dake kallonsa tunda ya shigo ta dan sada idannuwanta, sai kuma ta kai hannunta a nutse da nufin dafa wuyansa, sai kuma ta ga ya dan kauce kadan, hakan ya tabbatar mata jikinsa da zafi shi yasa fatarsa ta Wan yi ja kadan.....

Kai ta dauke a tausashe ta furta" Barka, ya gajiya "

A saman lebensa ya iya amsawa , yayi dan shiru na dan lokaci kafin ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya furta" Allah ya bamu wuni lafiya "

Anmy na kallonsa ya yi alamun zai tashi, a tausashe ta ce" Dawo ka zauna "
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati na airtel ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




8



Anmy na kallonsa ya yi alamun zai tashi, a tausashe ta ce" Dawo ka zauna "

Dan dago idannuwansa yayi ya kalli Anmy , sai kuma ya zauna a hankali yana duban yannayinta

Anmy ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" Kamar baka da lafiya???"

SULTAN ya dan shafa wajen idannuwansa a hankali ya ce" A'a, barci ne ban yi ba isashe Anmy, ama alhamdulilah"

Da kyar Anmy ta iya dane zuciyarta ta Hanna kanta yi masa maganar abinda yake faruwa tsakaninsa da iyalinsa, ba komai ya sa ta ki yi din ba sai dan gudun kar ya dake tuhumarta cewa yana bin bayan najeeba, domin an yi haka har ya sa MUTALAB a cikin lamarin suka titsiyeta da cewa in dai abu Najeeba ya shafa bata kyalewa sai ta shiga........
Ba zata shiga ba, ta tabbata gumu zata gumu kawunansu daga shi din har ita, tana fatan idan sun tashi yin sulhu su yi shi kwana kusa kuma su fahimci junna, domin dalilin fadansu ba wata hujja mai karfi da zata sa a jima cikin fadan.

A hankali ta furta" Allah ya karra lafiya........, Ama ka san cewa kula da lamarin sadaka da ake yi da sauransu sai idan matanka sun rubuta mabukatan da suka gana da su suke kai maka har ka bada abinda Allah ya hore maka a taimakawa mutane, yanzu da ka rufe hanyar da suke bi dan su sameka da wannan maganar ta ina zasu iya samun ka kenan?"

SHAHEED ya dago idannuwansa ya sauke a fuskar Anmy, ba wani alamun rigima ko bacin rai a tare da ita....., irin anmy tace da shi din nan ma yaya aka yi bai leko jikin matarsa ba bata yi ba, Anmy na kallonsa bata yi ba.......um, A tausashe ya ce" Ban Hanna su bi ta hanya baba ba dan ajiye sakon da suke da shi Anmy , du wace ke son ganina zata gani ne "

Anmy ta gyada kai a ranta ta sake ayyana' Eh lalle......., zan gani kuwa, zan nuna maka y'ata ba abar wulakantawa bace......, wato in ba neman rigima irin naka ba ka san irin tarin tsegumin gidan nan, kowa ya san cewa in dai bangaren ka ne matanka sunna da hanyar dake kai su, shine yanzu zaka fito da wannan sirfar?, ya zamo an san abinda kuke ciki?, to ai Shikenan a yi mu gani '

Anmy ta gyada kai tana dauke kanta ta ce" Hakan ma yayi, a huta lafiya"

SHAHEED yayi shiru yana kallon Anmy......, kai, Anmy ta kuwa ji me yace? Yana nufin fa su ringa fitowa su zagaya ta Babar hanya su kai dukkan bukatar da suke da ita da kansu wajensa ta gaban kowa ta gaban masu tsaron fada, ta gaban mutanen fada fa.....? Kuma shine ba zata Hanna ba? Ya zamo ta sanar da su ita ta Hanna shima ta bashi umarnin kar a yi haka din? Me yake damun anmy ne yau?........., gaba daya bata wani damu da fadan nasu Bama ga dukkan alamu, kuma ya tabbata zuwa yanzu ta ji fadan dan kuwa Nadiya nada rashin wayon zuwa ta sanar mata idan sunna wani rikicin....

Juyawa Anmy ta yi, a tausashe ta ce" Ko zaka kwonta ka dan huta ne?"

Idannuwansa ya lumshe, a hankali ya girgiza kansa sannan ya mike ya juya bayan ya furta" A huta lafiya Anmy"

Anmy ta bi shi da kallo, sai da ya bacewa ganninta sannan ta sauke ajiyar zuciya hadi da murmushi bayanane a hankali ta furta" Allah ya jikan mahaifinka........, tabasssss babu abinda aka bari nasa......., haka muka zauna, kafin in koyi zama da shi na fi shekara goma ina kuka idan mun yi fada, ...... Allah ya jadada rahama a gare ka mijina"
Dan rikicin dake iya samuwa tsakanin kowace mace da mijinta....., gaba daya sai ya daga mata hankali har jikinta ya ringa rawa....., a lokacin ko za'a sa ta rantse zata iya tunanin bai damu ba, babu abinda ya dame shi wai dan sun samu sabani, sai da aka fahimtar da ita cewa ya fita damuwar , wannan jinni na Basarake dake jikinsa ke sakawa yake gimtse mata, sai ta samu nutsuwa da kwonciyar hankali.........., A yanzu haka hakan ke faruwa shi da NAJEEBA, in dai wani abinsu ya hada su zai zamo yana yawan zuwa wajen ta ya zauna yayi shiru......, wani lokacin yayi ta kallon fuskarta da jiran ta fara kawo masa abinda yake damunsa....., hakan ke bata tausayi sosai da sosai, domin takan yi tunanin da ace bashi da jinin sarauta a jikinsa da ba'a ga haka ba, takan yi tunanin izar dake dawainiya da jinin dake gudada a jikinsa ne ke yawan wahalar da shi......, ita da kanta shaida ce wani lokacin NAJEEBAr ke ajiye Tata sarautar ta mata ta duka masa harma ta bashi hakurin laifin da ba nata bas shi yasa duk rintsi take yi musu addu'a tare da nasiha......., bata fatan wani abin da zai ja dagar rikicin su, sai dai zata samu yarinyar ta da kanta ta fada mata, kar ta yarda ta ga ta fara neman sulhu wannan karon, ta barshi da kansa ya gane cewar ba zata zubar masa da ciki ba, domin maganar zubar da ciki ba karamar magana bace da za'a iya tsawatarwa a tursasa barin maganar, zata so ya barta dan kansa da yarda cewar ba zata aikata ba, ya fi ALKHAIRI.

Bangarensa ya wuce direct ba tare da ya tsaya sake duba lamarin Najeeba ba

Shi kadai ya san halin da zuciya da gangar jikinsa suke ciki, sai dai fushinsa ya ture komai
Kwarai yana cikin fushi da ita saboda idan ya yi duba da wasu abubuwan zai iya yarda cewar lalle da walakin goro a miya.
Najeeba mutun ce mai mugun son gyara da mugun kula da jikinta......, wannan dalili kadai ya isa ya sa ta dakatar da haihuwa tunda yan matan yanzu tsabar son duniya sukan iya tsayar da ita haihuwar idan suka samu kwaya daya ma dan kawai kar jikinsu ya lalace bale ita.
Gaba daya ya yarda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login