Showing 57001 words to 60000 words out of 144591 words

Chapter 20 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2359

saboda dama yawanci ku maza kunna da son hayewa turbar da ba ita kenan ba dan ku gwada irin girman kwonjinku a kanmu......, to Ama ita Najeeba idan har nace zan talabota a yanzu tabas tana iya jan fitinar nan, bale da yan uwanta suka hade zasu nuna mana sunne jini daya mu bamu san me ake nufi da jini daya ba"

Abiey yayi dariya a tausashe ya ce" Na sani, kuma na san in har ba katse fitinar nan aka yi ba, ba zasu juya dakunnansu ba, shi yasa yanzu idan na ajiye ki zan wuce asibitin nan, idan dai aka sanyayar musu da zukata ai Shikenan ko????"

Ummi ta gyada kai, ta yi murmushi ta ce" Allah ya sanyaya lamarin, Ama likitar nan sam ban yarda da ita ba fa"

Abiey ya mike yana fadin" Tashi mu je, ai a duniya ramin karya kurare ne, in dai bata da gaskiya ina mai tabbatar maki da wuri gaskiyar zata bayana karya kuma ta karaya"

Mikewar ta yi suka fice suka dauki hanyar fada

Yana ajiye ta ya ja motarsa ya dauki hanyar asibiti, sai dai yana zuwa ya tarar da wata fitinar Yaya Dayabu yayi kiran tan sanda ya ja rantsuwar a bashi gwaje gwajen kanwarsa ko a rufe shugaban asibitin, wanda hakan ya dagawa DOCTER MUHSEEN hankali ya yi kiran DOCTER IZRANE ya bata umarnin zuwa yanzu yanzu idan ba haka ba kuwa gaskiya shi zai salameta daga asibitinsa


Abiey na kokarin kashe fitinar ta karaso, nan fa Abiey ya rufeta da fadan shin ba'a kai maganar kilacewarta gidansu ba? Yaya aka yi ta fito da shi irin wace take jikinta ta zo asibitin a haka? Idan zuwan ya zama dole ba'a yi mata bayanin irin hijab da nikaf din da ake so ta ringa sakawa ba????


Tsoro ya kama IZRANE, na irin yadda Abiey ke masifa kamar zai makata da kassss

Jiki na rawa ta sanar masa cewar in dai gwaje gwajen Najeeba ne sunna hannun Sultan tun ranar da ya zo ya tafi da su

Dayabu da tarin takaicinta ya ja tsaki ya fice

Domin shi tunda akace ita din nan ce Sultan zai karra matsayin matar aurensa ya shiga nasa bincikensa a hankali, domin ba zai taba yarda yana ji yana gani dan uwansa ya auro wace zata watsa masa gida ba, ba dan wai NAJEEBA kadai ba, a'a, sarautar dake gidansu mai daraja ce da ba zasu yarda su ji wani abin da bai dace ba su kawar da kai, kuma a yar tambayar da yayi a kanta har ya ji cewar ta taba yin aure......, ta taba yin aure fa, hakan na nufin matar da wani ya take ce zai take? Koda yake Sultan nada addini sosai zai iya nuna cewar ai ba laifi bane, Ama shi sai ya san dalilin da ya rabata da tsohon mijinta, ai akoy rabuwar aure ta ganganci, akoy kuma wace ba ta ganganci ba.

Kofar da ya rufo Abiey ya bi da kallo, kafin yayi murmushi yana girgiza kai, wato du yadda Dayabu zai rinka nuna ya dau shekaru a yanzu yana daga kafa a komai na rayuwa banda a idan aka taba kannensa...., sai ya gama zubar da kalar nasa haukan yake tuna cewar an taba yin hankali a duniya....... Allah ya rufa asiri

Abiey da kula ya dubi IZRANE dake zaune saman kujerarta ta aiki ya ce" A ranar da ya fita daga nan an amshi takardun kika ce? Wa ya amsa?"

IZRANE ta amsa Abiey da tabbatar masa hadi da sanar masa cewar Sarkin bulala ne ya amsa

Abiey ya gyada kai da kula ya ce" Ki kula......., ki rike kaffafuwanki, ki kuma kama mutuncin kanki sosai, maganar da aka kai gidanku ta kilacewa idan baki yi ba zaki iya saka kanki da iyayenki a fitina"

Daga haka ya mike ya yi gaba, DOCTER MUHSEEN ya bi bayansa da sauri suka fita suka nufi inda dankareriyar motarsa ke ajiye

Da kula Abiey ya ce"DOCTER MUHSEEN ka yi hakuri da kai kawon da muke yi maka fa, ka san lamarin nan ya saka rashin jituwa ne a tsakanin Sultan da matarsa, domin ita tace da aka bata wani magani ta hadiya ne aka tsankwalo mata fitar jini da ciwon ciki, wai da ya kwonta......, ita kuma likitar Tata tace abinda ya zubar da cikin ta'amali da maganin nan nasu na mata ne......., ba karyatata za'a yi ba, Ama da ace za'a iya ganewa da kyau a tabbatar mata ita Gimbiyar Shikenan rikicin ya mutu "

DOCTER MUHSEEN kansa ya daure, ya dan jima yana dan tunani kafin yace" Idan har marar lafiya yana conscient da abinda aka bashi ya sha yana da damar sanarwa, sannan muna da CCTV Camera a kowani office din mu, in sha Allah zan duba komai......, sai dai idan har a cikin takarda ne ake son gane wani abu ba za'a gane ba saboda shi ficewar cikin ai aka bada ba wani abin daban ba, Ama in sha Allah zamu duba komai zamu samu matsaya guda, kuma zan shigo gobe gobe da bayanan da na samu "

Aba ya gyada kai suka yi salama da DOCTER muhseen ya tafi,

Kwarai bayanan da ya masa sun gamsar da shi harma suka saka jikinsa yayi sanyi, sai dai dole zai kaiwa Anmy bayanin dan a kashe fitinar nan tun da wuri

DOCTER izrane na ofice din ta tana ta girgiza kafa cike da burika a ranta wa'inda take fatan lokaci ya Kaita da rai da lafiya , daya bayan daya sai ta yi anfani da rigar mulkin da za'a saka mata ta yi maganin kowa da kowa da ya raina mata hankali a fadar nan, Docter muhseen ya shigo ofice din ta ko neman izini bai yi ba ya ja kujera ya zauna ya janyo computar dake ajiye ya shiga vidios din da computer ta yi svng na abinda ke zuwa yana dawowa

Vidion ranar ya saka, ya ringa dubawa

Wajen da ta bude ta ciro maganin ya mike ya ja ya yi neman duniya Ama bai ga komai a wajen ba, sannan irin yadda bata wani bada damar da za'a ga yannayin maganin ba ya sake saka shi a shaku, ya dubeta da kyau a lokacin da ta tsaya tana tambayarsa lafiya? Me hakan yake nufi???


A kausashe sosai ya ce" Docter, wani magani kika ba Gimbiya ranar da cikinta ya bare? Me yasa take zarginki da maganar zubewar cikinta ne?"

Docteur IZRANE ta mike tsaye tana faman rantse rantse ta ce" Docter, Ni da kaina na gaza gane abinda ya da nake tsakiyar wannan rikicin, ka duba ka gani tunda aka kawota na rasa sukuni, shin dan tana matar mai damagaran zai bata damar shiga hurumina da neman hannani zaman lafiya a garin da cibiyana ke birne? Ina ruwana da sarautarta? Aikina na yi, ban zubar mata da ciki ba!"

Docteur muhseen ya gyada kai, yana duban ta ya ce" Wani magani ne kika bata????"

IZRANE ta yi shiru kafin ta ce" duclofenak ne"

Docteur muhseen ya ce" Matar dake gabar rasa cikin jikinta zaki ba duclofenak dan ya yi mata me?......, koda yake, barshi ba sai kin fada min ba, shi bincike ai baya taba faduwa kasa, in dai tana hayacinta ba zata rasa gane girma da color din maganin da aka bata ba, in kuwa ta fada aka ga ba'a yarda ba dole za'a matse maki wuri har ki fadi abinda ya faru, dan Ni na tabbata haka kawai na zata bata lokacin ta da gardama da ke ba bayan tarin abubuwan dake gabanta"

Docter IZRANE maganganun docter suka shiga zuciyarta sosai suka bata mata rai, tana dubansa ta fashe da kuka ta ce" Docter, Ni ce kake wulakantawa a kan abinda ban aikata ba? Haba Docter a kan wasu bare zaka wulakantani du irin yadda nake aiki a asibitin nan ba dare ba rana?"

Docteur muhseen ya dubeta ya ce" Look, ba wannan zamu yi da ke ba, ba maganar wulakantawa tun farko ban ga dalilin da zai sa ke ki tarbi Sultan da maganar matarsa ba, Sultan din abokin wasanki ne? Yaya za'a yi ki sanar masa wai matarsa zata zubar da cikinta dan tana shan maganin Hausa? Why? Shi kika yiwa allura ko ita? Shi ya fita son lafiyarta ne??????, mu yi abu na hankali da kuma bin dokokin aikin mu, shin aikin ki ne ya baki wannan damar????, koda bayanan nan ne waye a takardar ta a rubuce wanda za'a fara tunkara kafin ita idan ya so in ta yi niya ta sanar da duk wani lalurarta?, ina siri na tsakanin likita da patient ?????, gaskiya ki yi hakuri na dakatar da ke na wata biyu, a yi bincike a gama idan aka daidaita komai kya dawo bakin aikin ki, Ama kuma ba zaki kuma duba matansa ba, zan samo wata ta duba su, tunda kun samu irin wannan matsalar da su dan a gujewa gaba"

Docteur izrane da mamaki da kuma tsoro ta ce" Ka dakatar da Ni kace docter? A kan wannan abin zaka dakatar da Ni? Da gaskiyata da komai? Docter ka san aikin nan shine rufin asirina, kar ka min haka Docter "

Docter muhseen ya juya ya nufi waje yana fadin" Idan kika fito ki bada ky, sai an gama binciken ma yi magana, ta yiwu ki dawo kafin lokacin Ama fa sai an gama binciken nan"

Yayi tafiyarsa ya barta tsaye kamar sumamiya


Wani irin ihu ta saka lokaci daya tana barbaza takardun saman table din ta, ta hade hannayen ta tana dokawa a saman table din kafin ta silale tana yamutsa gashin kanta , da wani ihun ta ce" Ni zaka wulakanta a kan wannan laifin?, MUHSEEN sai na rufe asibitin nan idan har burina ya cika, sai na nuna maka na fi ka mugunta idan har burina ya cika!, zaka san Ni ka wulakanta MUHSEEN!"

Da karfi ta mike ta dauki jakarta ta duba du ta kwashi abinda take da bukata ta dura ciki harda magunguna ta dau ky din motarta ta fice ta bar office din a bude ta nufi motarta

Sai dai a lokacin da ta zo fita masu tsaron kofar asibitin suka bincike jakar Tata tasss, abin kunya abin takaici du wani abin da suka ga ba nata bane basu bar mata ba suka Bara mata iya jakarta da wayarta sannan suka bude mata get

Wani irin kuka ta fashe da shi na takaici , tana tuki tana rizgar kukan kamar ranta zai fita domin bata taSa saka irin wannan cin mutuncin a zuciyarta ba, bata taSa sakawa ba, wai a haka ba'a san abinda ta aikata ba? Tabasss ranar nan Tata ta zo mata a birkice wanda da kyar ta iya daidaita kanta kafin ta isa gidansu zuciyarta cike da tunanin abinda zai iya biyowa baya in suka amshi takardun, fatanta daya kar Allah ya sa a gane wani kalar magani ne ta bata, burinta daya kuma shine Allah ya kai damo ga harawa, tabas sai ya ga mamaki!


Ko da ta shigo gidan sai ta Worawa mamanta rikicin ance saboda kilacewar fada ba zata kuma fita aiki ba, mahaifiyar Tata kuwa ta yi farin cikin hakan domin ta Wan idan ba daga fadar aka hanata ba, ba zata hannu ba, karshe ma sai ta nuna mata to ai hakane, maganar fada fa ake yi, mahaifinta ya fada ya karra a ji umarnin da aka kawo .........saboda wanda ya nemi aurenta baban mutun ne mai daraja, dan haka ta kiyaye shi ya fi mata ALKHAIRi .


A gidan Anmy wuni suka yi da baki, mijin umi karama da yan gidansu, hakan ya Hanna Abiey yin maganar har sai bayan isha'i bayan jama'a sun watse ya samu Sultan da maganar takardun

A lokacin ne Sultan ya ce Eh takardun nan ai sunna wajensa, sunna dakinsa ma

Da kula sosai Abiey ya ce" Idan har ba damuwa, in sha Allah gobe docter Halima zata zo daga baban asibitin haihuwa na gwamnati ta duba, ta yiwa Anmy da NAJEEBA bayanin komai, in har ba takura sai a bada takardun wajen Anmy"

SULTAN ya gyada kai a tausashe ya ce" In sha Allah, zan bata"

Daga haka suka yi salama da Abiey yayi tafiyarsa, shi kuma ya shige bangarensa dan yanzun ma bai shiga bangaren Anmy ba, waya suka yi........


A lokacin da ya shiga ya samu Nadiya a falo sai da ya dakata yana duban ta da kula bayan ta gaishe shi da girmamawa

Kujera ya karasa bayan ya sabule mata alkyabar jikinsa ya zauna yana mike kaffafuwansa, cen ciki ya ce" Ama....., yaya aka yi, kullum ke ce kadai ke zuwa???"

Nadiya dake kokarin cire masa Safar ?afarsa ta dago da dan mamaki ta Wan saci kalonsa, sai kuma ta sada kai a hankali ta ce"
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne, Vip 1 k
Normal grup 500
Yan Nijar vip 1000francs
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




19




A hankali Nadiya ta ce" Eh, gani na yi ita yanzu bata sin zuwa ne"

Sultan ya Wan dubeta da kyau, kafin ya dauke idannuwansa yana dage kansa ya dora saman kujerar bayansa ya jingina sosai da jikin kujerar a hankali ya lumshe idannuwansa zuciyarsa na sake daukan radadi na rashin ta a kusa da shi........, me yasa ita idan suka samu matsala bata naci da zuwa inda yake har ya sauko ya dubeta???? Sai ta bacewa idannuwansa ya zamo ganninta sai an yi Sa'a hanya ta hado su?????, ikon Allah me yasa take da mugun riko ne ita??????, bai isa yayi mata fada ba ko? Ta haye kan fadan yanzu kuma zata haye kan maganar aurensa tace an yi mata laifi, wani laifi ne aka yi mata Fisabililahi? Me aka yi mata na laifi ne? Gaba daya bai gane irin laifin da aka yi mata ba, ........ya fi ganewa cewar fushinta ta yi niyar yi, domin ba zai taba yarda da maganar cewar Beebah zata iya yin tunanin zai kara aure saboda baya sonta ba......, hum so? Ai ta riga ta gama samun wannan wajen sai dai ta taimaka ta ba wasu dan wajen da zasu rabu...............


Har Nadiya ta cire rai da zai yi wata maganar , ta mike da nufin gabatar masa da abinda zai ci, sai ya katse mata hanzari ta hanyar fadin" Akoy hakinta a kanmu baki daya....., koda bata zo ba............."

Ya Wan dakata ya dago yana kallon ta a hankali ya furta" Dole a bar mata kwanakinta......, ki je bangaren ki"

Daga haka ya sake mayar da kan nasa ya lumshe yana son hancinsa ya shaki kanshinta, yana matukar son ta fado jikinsa ta gala masa cizo, yana so ya ji ta cakumi rigar jikinsa har ta yakunata...., yana matukar son ya ji hannunta a saman kirjinsa tana mintsinin du inda ta yi niya da sigar da ita kadai ta iya shi.....
Yana missing din lokutan da take yi masa magana daga nesa ta kwala ihun kiran sunnansa ta hanyar fadin SHAHEED ya zaka kyale Ni, ka amsa Ni mana ina yi maka magana kuma?????

Dan murmushi ya sauka a kan lebensa....., yana tunanin lokutan da su Muhammad suke kananu......., a falon nan ta taSa saka shi yi mata goyo yana rarafawa da ita a bayansa sunna bin su Muhammad da gudu irin zasu kamo su, su kuwa sunna ta ihun dariya da farin ciki.......

Firgit ya bude idannuwansa ya mike tsaye, wanda hakan ya sa Nadiya dake yi masa kallon ai an wulakantata juyawa da sauri ta nufi coridor din ta zuciyarta na zafi da fushi na irin yadda za'a ce wai ta tafi bangarenta bayan ita wace ake maganar hakin nata itama bata damu da hakin nata ba? Anya da ace itace ta yi gigin yin wannan fushin zai cewa NAJEEBA ta zauna kar ta je inda yake? Wai me yasa ake son wulakantata ne? Yanzu haka in ba dan mahaifiyarta ta yi mata kaca kaca ta nuna mata kar ta saki ta nuna masa fushinta da aka fada mata likitarta zai aura ba da Bama zata iya zuwa ba fa, to mamanta ne tace ta koyi kisa ta taya shi son abinda yake so, tabas sai ta fi NAJEEBA a wajensa saboda zuciya tana son mai kyautata mata, bale ita najeeban nan ai ba zata taba nuna masa soyaya ba , girman kai ba zai barta ba a irin wannan lokacin, bale ai du gani zata yi ita kadai zai yiwa kishiya saboda ita ke juya shi son ranta,....kai a shawarar da auntynta ta bada harda wai zata je mata gidan su Docter izrane ta nuna mata sunna maraba da ita , ita dai kamar hakan ba dadi Ama kuma gaskiya zata nemawa kanta yanci, ina!

Da ido ya bita ......., sai kuma ya juya ya karasa wajen wayar dake jikin bango Ya dauka ya daga Sangaren Anmy yana duban time da tunanin tabasss du inda suke warhaka sun shige dakinsu sunna kulawa da kuncewa

Zahra'u ce ta daga kiran dan a tunaninta anmy ce, ta yi salama hadi da fadin" Anmy kira ne???"

Shiru ya wanzu a wayar, sakamakon Muryar Najeeba da ta shiga kunnensa tana ihun fadin " Umi kar ki cire min da yawa, daidaita yanke rabin, bari ja min zafi....."

Zahra'u ta sake fadin" Hello?"

Har zata ajiye dan ta je da kanta domin ta yi tunanin anmy ce ke kiransu, sai ta ji ya furta" Su Muhammad, su zo"

Da sauri ta zarro ido , wayar na kubce mata sai igiyar wayar ta rike wayar, da sauri ta raruma ta ce" To, to yanzu yanzu"

Ajiye kiran yayi, ita kuma tana rike idanuwanta waje ta ce" NAJEEBA mijinki ne, bilahilazi mijinki ne"

Najeeban ta tabe baki, wani kiran ya sake shigowa

Kasancewar wayar a hannunta sai kawai ta dana wajen blue ta kara a tsorace ta kasa yin magana

A hankali ya ce" Kar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login