Showing 30001 words to 33000 words out of 144591 words

Chapter 11 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2356

camerar dake corridor din da ya hade dakunnansu baki daya, haka kuma ya ga ky din da Anmy ta saka hakan ya saka shi dafe haba a lokacin yana ayyana ' to fa , zata shigar wa y'arta fadan da babu ruwanta a ciki........., shi dai ya zuba ido ne dan ya tabbata a irin wannan lokacin itama tana cikin irin halin da yake ciki ne, Ama kuma sai ya ga shiru bata zo ba bata ko wulga ba, ................................., sai msg din da Nadiya ta turo masa, kawai a wayarsa ko wayar bata duba ba bale ta neme shi .
Hum...lalle zasu buga wasan taurin kai shi da ita, sai fa ta nemi sulhu da kanta.


DOCTER IZRANE


Tunda ta duka gaban mahaifinta ta ringa zayane masa maganar karya da hade haden da ta tsara a kwakwalwarta dan kaiwa ga ci yake kallonta da sauraron ta cike da mamaki da kuma tsoron furucinta

Mahaifiyarta dake zaune ta sauke ajiyar zuciya tana dubanta ta ce" yanzu dama sai da maganar nan ta fita IZRANE?, inace da kika min maganar nan na baki shawarar cewa ki yi hakuri da wannan maganar, kin ga su manya ne, ba mutanen da za'a kaiwa wargi bane, na fada maki kawai ki dage da addu'a ki cire maganar a ranki, Ama shine Wan rashin wayo zaki je filin asibiti a ranar da matarsa ke cikin asibitin ba lafiya, kin san kuwa ai du wani kunne da ido a kanki yake ke likitarta shine zaki yi wannan waya da kanwarki?, to ke yanzu ko kunyar fadin wannan kalaman baki ji ba? A yi mace ba kunya ne????"

IZRANE ta sake tsumewa tana kallon mamanta ta ce" Mama, ki yi hakuri, da ace inada hali da na cire ciwon dake raina na huta, saboda Nima na san ba abin wasa bane, sai dai mama kin ga ko a musulunci ba'a Hanna ba , hasalima matar fiyayen halitta ta farko Nana Khadeeja Allah ya karra mata yarda kin ji abinda ya faru tsakaninsu,....mama darajarsa ta kai ta wanda aka yi duniya dominsa ne da za'a ringa cewa ya fi karfin hakanan? Shi bashi da zuciyar a kirjinsa da zai dubeni ne mama???"

Ran mamanta ya nace tana dubanta ta ce" Kin san Allah IZRANE, haka kawai nake tsoron da wata a kasa, tunda kika ki yaron nan kika nuna sam bai maki ba, karshe na gane dogon burinki ke dawainiya da ke nake kyautata zaton wannan ma da wahala in son ne, kike maganar darajarsa da mai daraja wanda ya fi daraja daraja s.a.w? A'a bai kai ba, shi din me zai kai koda darajar baran gidan masoyinmu?, Ama ke fa? Ke din wacece taki darajar a jere da darajar wace bata dauki duniya a bakin komai ba?, ke kece kika saka duniya a rai kika dauketa da zafi, a da mahaifinki ya rike matsayi masu yawa a kasa, a yanzu da ya ajiye komai ke kin dage cewar baki san zancen ba ko a yanzu sai kin yi yadda kike so ko? Ba laifi ga wuri ga Mai doki, sauran sukuwa, ina mai tabbatar maki in har da gasken kukan nan da kike yi har ranki ne kadan daga cikin wanda kika sa mijinki ne a nan a zaune a gaban mahaifinki a lokacin da kika nuna ke fa ba zaki yi aure ba ya nemi dalili da nakasunsa kika nuna kawai ke ba zaki iya zama da shi ba har mahaifinsa ya bashi umarnin sakin ki......., idan baka je inda ake sonka da rawar jiki ba, dama dole ka nufi inda kai ke so da rawar jikinnnnnn"


"Halima, Ama ba nace a bar maganar nan ba?" Mahaifinta ya fada yana duban mahaifiyarta

Kai ta girgiza ta mike tana fadin" Allah ya bada hakuri, Ama gani ne na yi maganar nan sam ba tsari a ciki, gaba daya sai kukanta ke min shige da na munafukai"

Bai kuma ce mata komai ba sai da ta bar wajen sannan mahaifinta ya fuskanceta ya ce" IZRANE, dago ki nutsu mu yi magana"
IZRANE ta zauna inda mahaifinta ya nuna mata jikinta du a mace, saboda bata taba tunanin samun matsala a kan lamarin nan daga wajen mahaifiyarta ba, ta sakankance cewar mahaifiyarta sai ta fi kowa farin ciki saboda irin yadda take kaunar Sarkin garin nan, hawan sarki bai taba wuce mamanta ba, du wani abu da ya shafi sarautar DAMAGARAN mahaifiyarta na yi masa son so Fisabililahi, a lokacin da ta zo mata da maganar cewa an dauketa matsayin wace zata ringa kula da matan mai martaba irin farin cikin da ta yi ba kadan bane kuma shine yanzu sai ta zo da wannan bayanin? Yaya zata yi kenan

Da kula sosai ya dubeta da kyau ya ce" IZRANE, kin san girman furucin bakinki kuwa?, kin tabbata abinda kika fada gaskiya ne IZRANE??"

IZRANE ta rike kasan rigarta da karfi dan samun kwarin gwuiwa, domin ita ta riga ta san cewa awon da ta yi babu wanda ya isa ya ?aryata tunda ta daka result hakanan, kuma maganar waya kuwa sai da ta gama tsara koda ta kwana ga abinda zata fada ta fida kanta sannan ta tsara abinta, dan haka bata da wani tsoron a gane gaskiya, abinda ta fada kuma aikata shine gaskiyar, dan haka kanta a kasa ta ce" Dady, na rantse maka iya abinda na sani kenan da kuma laifin da na san na yi mata"

Mahaifinta ya yi shiru kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Tashi ki je, zan neme ki idan na yi tunani"

Mikewa ta yi ta nufi dakinta zuciyarta cike da fargaban abinda ke iya zuwa ya dawo, a ce cikin ranta sake saken da take yi shine gwara ta kwana da shirin ko ta kwana, idan har karamin abu ya nemi zame mata baba to kuwa sai ta bar garin saboda irin yadda kowa ke yi mata hannunka mai sanda da shiga lamarin gidan sarautar nan.......... Idan har aka yi rashin Sa'a ta nemi kwana cikin matsala gwara ta kwana da shirin barin garin, dan kuwa babu mai Kaita prison wallahi!.


Mahaifinta ya jima zaune yana tunanin hanyar da ya dace ya bi, abu daya ya gama yankewa shine zai je da kansa Wan ya nema mata afuwa, domin ba za??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????i so ace fadan nan yayi nisa ba, idan har yayi nisa tabas fita sai ta gagareta, gashi yau ya dace ta yi aikin dare Ama saboda tsoron kar aje in ta fita wani abin ya sake faruwa ya sa yace ta zauna zai yi tunani

Sai dai matsalar daya ce, a yanzu anya yana da wani karfin da zai shiga fada kansa tsaye??????, baya tunanin in har yana da wannan karfin domin a lokacin da ya ci nasa zamanin na matakin gwamna sosai ya ki bada hadin kai a yi gyaran kasa a taimaki yan kasa da sarki, hasalima ya nuna musu shi fa ba sa'an yinsu bane, sai dai yana kyautata zaton dole zai samu ya'yansa da maganar, wanda ya tabbata in dai har ya yarda to ko a waya ne zai iya samun mai DAMAGARAN da zancen kuma za'a kashe wutar fitinar, wannan mafitar da ya samu ya sa ya kwonta da wuri saboda ya yi fitar wuri dan ya je har kauyen MAGARYA, ya'yan nasa shine mai garin garin magaryar, mutumen mai DAMAGARAN ne sosai da sosai, sunna da zumunci da junna, a garin magaryar mai DAMAGARAN nada garake da gonaki wa'inda suke karkashin kulawar mai garin magarya, sosai suke zumunci da harkar kasuwanci domin kai DAMAGARAN akoy son kiwo da shuke shuke sosai , yana da yakinin idan ya je ya sanar masa abinda ake ciki Shikenan abinda ya yanke sai su yi.

Washe gari tunda safe ya dauki hanyar karamin garin magarya cikin motar wajen IZRANE din domin tasa sai da aka zo fitarwa ta ki tashi, ko dan ya jima bai hauta bane kuma ba'a kunnata?, a dole dai ya hau motar IZRANE din ya tafi , ita kuma yayi mata kashedin kar ta yarda ta fito nan da nan, saboda idan wani abu ya sameta kafin a samu maslaha babu abinda za'a yi sai dai a bata hakuri a kuma yiwa yaran gidan Mai wukar yanka fada Shikenan.


Tafiya ce dake daukan awa biyu ko kasa da haka , daga DAMAGARAN zuwa kauyen , danma hanya ce da bata cika kyau ba, sai an bi wasu guraran a hankali , shi yasa ya dan jima a hanyar kafin ya karasa kauyen

Kwarai dan uwansa yayi mamakin ganinsa duba da basu yi wayar cewa gayanan zuwa ba, sai dai a lokacin da ya sanar masa damuwar da aka shiga sai shima hankalinsa ya tashi, cikin yanayin damuwa ya ce" Subahanalah, ai da ace a lokacin da Sarkin bulala yayi kiran fitowarta dan ta amsa kiran Gimbiya bata fito a kan lokaci ba da ya rike ta da yanzu haka sai dai mu tarbeta a asibiti, ya Salam, yarinya a cikin mutuncinki kin samu wajen aikin ki mai daraja ki nemi daukowa kanki matsalar da zata Hanna ki walwala a garin da aka haife ki?, mutanen nan da ka gani sunna da kusanci da talakawansu sosai da sosai, talakan garin DAMAGARAN dan a mutu ne idan aka taba darajar sarkinsa......, yaya zata saka kanta a tsakiyar fitinar tauraran mutane masu fadan a mutu irin jama'ar DAMAGARAN ne?, inaga yanzu abinda zamu yi bari in yi kiran NUMBAR Malami, tunda karfe goma ce ta yi na san zuwa sha daya sha biyu Sarki zai yi fitar safe zuwa dakin tarihi su yi dan zaman minti talatin da suke yi, daga nan komawa yake yi Sangarensa sai idan yayi sallar la'asar yake yin zaman sirri da bakin cikin gida na awa daya, bayan nan ne idan yana da Shari'a baba da ta fi karfin su shamaki yake zaunawa ya yi da kansa.....misali shari'ar ku ta yan siyasa, ko abinda ya shafi kisa, ko abinda ya shafi wani tsagera, ko abinda ya shafi wani baba barawo dai da sauransu....., bari mu yi kira mu ji ko zai saka mu cikin zaman awa daya ta sarki sai mu yi aniya mu je DAMAGARAN din ka shirya sosai sai mu je mu wuni a fadar har yamar, in sha Allah idan dai muka bashi hakuri da kanmu an gama , zai yiwa kowa magana kuma ba zasu take abinda ya fada ba tun daga kan Mai baban dakin har zuwa yaran fada"

Ajiyar zuciya mahaifin IZRANE ya sauke ya ce" Allah ya sa, Ni ba abinda ya fi damuna irin yadda a jiya ma ta dawo a tsoracen nan ta yi ta kuka, kwarai ta yi laifi saboda ba'a yi musu hayen nan, kuma da ace ta bi shawarar mahaifiyarta da ta samu mafita saboda ai Allah ya halicce shi , bai fi karfin ikon Allah ba, kai ita da kanta matarsa sai ka ga Allah ya saka mata kaunar abin a ranta bale shi....., Ama sai ta ringa ganganci irin wannan, mata kuwa da lamarin kishi ai ba'a magana sai dai a yi shiru a bi su da addu'a "

Bai ce masa komai ba sai zaunawa da yayi bayan ya dauko wayarsa ya shiga cikin sunna ya dauko sunan Malami sannan ya tura kira

Ta jima tana RINGIN har ta katse ba'a daga ba, ya sake tura kiran da fatan samunsa a na biyu dan idan bai daga ba yanzu sai gobe kuma yake da damar sake kira in dai ba kiran wani tashin hankali bane misali in ba hari aka kawowa garinsa ba.


Allah ya taimake shi ya daga a kiran na biyu
Gaisawa suka yi, Malami na sake tambayarsa iyali da jama'ar gari

Da mutuntawa mai gari ya ce" Alhamdulilah Malami, ka ga na yi kira ki?, cewa na yi ko za'a bamu damar gannin Mai martaba yau a zamansa na yama?"

Malami yayi dan shiru, ya juya ya sake buda littafin karbar baki ya duba, ya ga eh yau bashi da wani zama na cikin gida sai Shari'a dake gabansa har guda hudu .....dan haka ya ce" Kai da wa zaku zo?"

Mai gari ya ce" Ni da Wan uwana ne, kanina , dan DAMAGARAN "

Malami ya sake yin dan tsai, sai kuma ya ce" Allah ya kawo ku lafiya"

Ya fara katse kiran yana tunanin me mutumen nan zai zo yi? Dan ya tabbata tafiyar ba ta mai garin bace..........., ture tunanin yayi ya mike yana sake gyara wajen da mai Martaba zai zauna idan ya shigo, wani lokacin yakan dauki littafi ne yayi nazari a ciki, wani lokacin yakan zakulo litafin tarihi ne ya bude ya baje a hau fafatawa domin zai ringa cenko du pajin da yayi niya ne ya yiwa jama'arsa tambaya a ciki, idan aka yi Sa'a aka rasa mai bada amsa da kyar wani ya samo to fa wanda ya samo din zai samu kyauta mai kyau, shi yasa har dogarai suke zuwa su bi layi in dai akace mai martaba ya dauko litafin kundin tarihin garuruwa.


A kauyen MAGARYA kuwa mai garin shigewa yayi ciki shima ya shiga shiryawa , ya saka tufafi mai kyan gaske ya dora hularsa ya dan zagaye fuskarsa da sasaukan nadi sannan suka dauki hanyar DAMAGARAN

A lokacin da suka karaso tuni an fara sallar azahar dan haka sai da suka yi sallah sannan suka shige gidan mahaifin IZRANE

A nan ma shima shiryawar yayi, suka taba abinci sama sama sannan ya sanarwa mahaifiyarta abinda zasu je yi, ta yi musu addu'a da fatan dawowa lafiya

Bayan sun tafi ne ta samu IZRANE a dakinta, wace ke sheka barcin rana ta tashe ta fuska a daure ta ce" IZRANE kina nan kina barci Bayan kin dagawa mahaifinki hankali ko?, Sai ki tashi ki yi jira dan ya tafi fadar mai DAMAGARAN yanzu"

A zabure ta mike zaune daga kwoncen da take hangen mahaifiyar Tata, a birkice ta ce" Ya tafi fada? Kamar yaya ya tafi fada?"

Mamanta ta yi mata duban takaici ta ce" Baki gane meye fadar ba ko me kike son ganewa?"

Gannin yannayin maman nata ya sa ta yi shiru kawai ta mike ta nufi bayinta ta rufo ta je wajen mirror tana dantse lebenta......, ita fa ta san darajar kanta, ita fa babu wanda zai ringa neman wulakantata a kan zabinta , ita maman waye yayi mata auren dole da zata dage sai a kanta ? Yan uwa ta waye aka yiwa auren dole ne da ita za'a ce sai ta zauna? Ita fa tun farko kyansa ya jata, domin a lokacin da babansu keda ya'yan banki kudin ba sune a gabanta ba, shi yasa har ta yarda tafiyarsu ta yi nisa ita da shi, kuma a lokacin shi dinma yana karatun lauya ne, ai ta zata an yi abin kirki, Ama tsabar rashin aiki a garin nan sai ka yi dogon karatun ka kare a malamin makaranta?......, a'a ba zata iya kayan wahala ba, ai kyansa tunda yayi accident ya ragu, uwa uba kuma kudi dama basu zauna ba bale su ragu, bashi da su ne kawai ake so a takurata......, ita yanzu abinda ya fi damunta tafiyar babanta shi kadai fada, ita da ta so ace an je da ita ta karra narkewa ta tabo zuciyar tausayin da akace yana da ita ko an dace? Ama shine sai ya yi tafiyarsa? Kai mtssssssssss!, dole dai zata fita yanzu saboda dole ta san abinda zai faru kafin babanta ya dawo ya sanar mata!


Yama ta yi tuni, an fito daga sallar la'asar tuni, Ama har karfe hudu da rabi ta yi mai Martaba bai shigo dakin da yake ganawa da bakin gida ba, Ama kasancewar bai sanar cewa ba zai fito ba ya sa aka ci gaba da jiransa har ya fito

Kusan karfe biyar shamaki ya shige falon ya kai gaisuwa , nan ya sanar da wa'inda ke jiran iso , shin a basu damar su shiga ne ko ba yau ba??????


Mai DAMAGARAN ya lumshe idannuwansa hadi da furta" Su shigo"

Daga haka shamaki ya sake dukawa yana sake godiya sannan ya mike ya fice dan shigo da mahaifin IZRANE da yayansa wato mai garin magarya.


Shamaki ya fara shigowa bayan Sarkin bulala ya bude kofar ya sake dukawa yana sake yiwa mai DAMAGARAN ban gajiya, sannan ya basu damar shigowa

A inda shamaki ya duka suma suka duka sunna jimke hannayensu na dama sunna kai gaisuwa a wajen mai wukar yanka

Mai DAMAGARAN ya yi murmushi yana duban su ya daga hannunsa, sannan shamaki ya mike ya fita yana fadin" A gama lafiya, a fito lafiya"

Bayan fitarsa mai garin magarya ya sake dukar da kansa ya furta" Takawa lafiya mai garin garina, takawa lafiya asarki, takawa lafiya bijimi gagara gasa....., Allah ya sa da mun samu Mai DAMAGARAN a kan gabar da zamu iya kawo kokenmu "

SHAHEED ya sake bin su da kallo, a nutse ya gyara zamansa sannan ya fitar da hannunsa daga cikin sasaukar alkyabar dake jikinsa da hannu ya musu nuni kusa da shi ya furta" Haba mai gari, ku dawo nan ku zauna"

Mai gari ya mike da sauri cike da jin dadin karamawar da aka basu ya yiwa dan uwansa nunin inda zasu zauna din, suka je suka zauna su duka sunna sake nuna alamun girmamawarsu a gare shi

A tausashe ya ce" Me ke tafe da ku? Ko zumunci aka kawo min ne?"

Mai gari yayi murmushi yana sake sada kansa ya ce"


Kai ta kuma gyadawa sannan ta juya jiki ba karfi ta nufi ciki

Anmy cike da tausayinta ta juya ta nufi dakin ta tana dudubawa har Andiya ta zo suka shiga gyara dakin sosai da sosai, Anmy na yin du yadda zai yiwa NAJEEBA dadi a ranta, tana addu'a a cen kasan zuciyarta kan Allah ya daidaita lamarin, tabasss tana tausaya musu, sai dai tunda baya tausayinsu shi din Shikenan sai a zuba masa ido. ( Anmy kenan, mama a wajen Najeeba, )






Rabee inee lima anzalta ilaya min khairin fakeer
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login