Showing 33001 words to 36000 words out of 144591 words

Chapter 12 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2358

SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati na airtel ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




11



Kansa kasa, cike da girmamawa mai garin magarya ya ce" zumuncin ne farko ASARKI....., sai kuma neman afuwa daga cikin tarin hakurinka da kawar da kai, domin mu mun san cewa Sarkin garin nan mai adalci ne, mai hakuri ne, mai kawar da kai a abinda ke kai kawo na neman daga hankali ne"

Mai DAMAGARAN dake kallonsa, ya dauke idannuwansa a nutse ya dauke kan wanda suke tare, wanda kwarai ya gane cewa mutumen da yayi gwamna na shekara biyu ne a garin nan, wanda sanadiyar juyin mulki du aka cenja su, wanda suka Wan so samun matsala ama daga baya suka zauna suka daidaita kansu suka barshi yayi mulkinsa yadda yake so har sai da kansa ya zo ya nemi sulhu a lokacin da samarin gari suka so daga masa hankali da fitintinu da neman kin amsar mulkinsa saboda ya ki ya yi abinda ya dace, ya nuna hadama da babakere da dukiya kawai yake son yi, sai da suka nuna masa su fa ba zasu amince ba sannan ya zo da kansa ya nemi masalaha, ........a nutse ya dubi mai gari ya ce" Wani abu ya faru ne yayana?"

Mai gari ya gyada kai ya ce" kwarai an yi laifi, dazu dan uwana ya sameni da maganar abinda yake faruwa , cewa yarinyar wajensa likitar su Gimbiya ta yi laifin da ya taba zuciyar Gimbiya mai baban daki, har an tura a kawota nan din ma kuma sai ba'a kawota ba, shine muka zo, mu nemi afuwa, a yafe mata in sha Allah ba zata kuma kwatanta irin wannan laifin ba, zata tsaya a matsayinta ba zata yarda ta haura ba"

Sai yanzu ya fahimci abinda yake faruwa, sannan ya gane mutumen nan mahaifin IZRANE ne kenan, ......oh wai ta tsorata da zuwan su Sarkin bulala ne?, koda yake sai ta ji tsoron ma saboda Sarkin bulala ai ba ruwansa da rigarka in dai har ka shiga huruminsa to zai shiga naka

Murmushi yayi ya dubi mahaifin IZRANE, a tausashe ya ce" Sun samu rashin fahimta ne ....., Ama komai ya wuce, ba za'a kuma tura kowa daukar ta ba in sha Allah "

Mahaifin IZRANE ya sada kai yana fadin" Allah ya saka da ALKHAIRI, mun gode, mun gode Allah ya biya , Ubangiji ya karra girma da daukaka, rabi ya sa a rabu da kujerar mulki lafiya"

A saman lebensa ya amsa a lokacin da mahaifin IZRANE ya kai karshen adu'arsa, sannan mahaifin IZRANE din a tausashe ya ce" Allah ya taimake ka, zata ci gaba da zama likitar gidan nan ne ko za'a cenzata ne?"

Mai DAMAGARAN yayi dan tsai, duda tunawa da yayi in dai NAJEEBA na jin haushinta da wahala ta yarda ta ci gaba da dubata, sai ya ture wannan tunanin daga ransa a nutse ya ce" Itace likitarsu ai, wannan din bai kai wajen da za'a dakatar da ita ba saboda shi"

Mai garin magarya ya gyada kai yana jinjina hannunsa ya furta" Adalci, gidan adalci ASARKI "

A tausashe ya dora da fadin" Bata yi laifi ba, ta daina neman afuwa, sannan a sanar da ita idan mai baban daki ta gama shan magani zata duba min ita dan a tabbatar da ta samu lafiya, babu wani sauran damuwar........."

Sosai suke godiya da addu'ar samun lafiya a wajen NAJEEBA........, yana amsawa a saman lebensa har suka gama suka mike suka yi masa salama


A hankali ya lumshe idannuwansa yana sake jin tarin damuwa a cikin zuciyarsa........, yana mugun missing dinta a jikinsa da kunnayensa....., idannuwansa na son ganninta domin tun jiya da magariba rabonsa da ita, , zuciyarsa na matukar son jin labarin ta koda na second daya ne...........
A hankali sosai ya furta" Beebah, laifi fa kika min, wanda kika san ya fi bakanta raina fiye da komai da zaki iya min a duniya....., abu daya na tambayeki Beebah, shine ki yarda kin aikata, mu zauna da ke, mu samu maslaha, harma ki yarda da dokar da zan dora maki......Ama Beebah....maimakun ki yi hakan , sai kike ta kokarin nemo wata fitinar.....?, ba damuwa Allah ya baki Sa'a "

Daga haka ya dan buga sandar tasa shamaki ya shigo da sauri ya duka,

A nutse ya mike tsaye , shamaki ya mike da sauri yana gyara masa rufar alkyabarsa......, sannan suka fice suka nufi dayan falon da zai yi shari'ar dake gabansa.....domin ya san idan ma yace ba zai gansu yau ba damuwa na iya sako shi gaba.

Sai da dare yayi sosai sannan ya koma Sangarensa bayan ya leka Anmy, a yanzu ma ko motsinta bai ji ba, haka ya tafi Sangarensa ya kwonta bayan ya amsa msg din Nadiya na yau domin tunda aka yi abin nan kullum cikin msg da bada hakuri take, ya bata amsa a takaice ne dan ya samu wani dan sukunin, sannan yayi gaggawar hayewa salaya dan ya riga ya gama yarda cewa NAJEEBA itace jarabawar rayuwarsa.


Washe gari
A yau umi ta kawo musu wuni, domin NAJEEBA sai da ta fito ta samu umin a kicin tana girki, Anmy kuwa tana falo da jikoki sai surutu suke sunna shan dariya

Zaunawa ta yi gaban Anmy wace ta sa aka amso abincin Najeebar ta bata umarnin cin abincin hadi da balo mata magungunanta....., a irgensu yau magungunnan zasu kare domin yau kwana hudu kenan da barin, kuma yau ya dace ta je asibiti a sake yin hoton cikin da komai da komai.....domin ko da SHAHEED ya shigo da asubahi ma sai da ya sanar da Anmy cewar yau ta koma DOCTER IZRANE ta aunata ..........

Abincin ta ci ta haWa da maganin , daga inda take tana jiyo firar mamanta dake yi da Anmy har ta gama sannan ta dauke ta kai kwanonin kicin din

Tana ajiyewa a hankali ta je ta rungume mamanta ta baya ta Wora kanta a gadon bayan Maman nata

Murmushi umi ta yi tana motsa miyar a hankali ta ce " kin farka?, yaya sau?in jikin naki?"

NAJEEBA ta kasa yin magana sai sake cusa kanta take yi a bayan umi, hakan ya sa umi rufe tukunyar ta juyo tana rike da hannayenta ta dan dago fuskarta a hankali ta ce" Menene? Har yanzu baki yi hakuri da abinda Allah ya kadarto maki bane?"

NAJEEBA ta sauke ajiyar zuciya ta sada kanta, a hankali ta ce" Bani da ja da hukuncin Ubangiji umi, Ama na kasa yarda da binciken likitar da ta auna Ni, haka kawai nake jin wani abu a maganar da aka sanar masa...."

Umi ta kureta da ido, a tausashe ta ce" Wani abu yake faruwa ne????"

NAJEEBA ta sauke ajiyar zuciya, a sanyaye ta ce" Gaba daya na shiga wani hali umi, fada yake yi ba ji ba gani, wai wani abu na sha ya yi sanadiyar cikina, ina cikin kokarin ganin na samu mafita a kan maganarsa kuma ya fito da wata maganar wai na tura a dauko min likita dan kishina.....?, gaba daya sai na kasa samun matsaya guda, sai nake tunanin anya kuwa ba akoy wani abu dake faruwa ba????"

Umi ta kure fuskarta da kallo, irin yadda take magana zaka gane a cikin halin tashin hankali take, hakan ya sa a nutse ta ce" ban fahimci maganar nan taki ba, kina nufin da aka yi maki bincike likitar ta sanar da ke kina shan maganin dake iya zubar maki da ciki ne ko tana nufin kin sha din ne?"

Najeeba ta girgiza kai ta ce" umi, likitar nan bata yi magana da Ni a kan abinda ya shafi ciwona ba, farawa da iyawa da shi ta yi magana, ban san me ta sanar masa ba a kan lamarin nan, kuma yanzu haka maganar da nake maki ban san daga cewa a je a kawo min ita nima ta min bayani a kan lamarin lafiyata ya shafi maganar kishi ba, wani kishi? Meye tsakanina da ita da zan yi wani kishinta?"

Umi ta yi tsai, da mamaki ta ce" Dama idan abu ya shafi lafiyarku, shi take yin magana da shi kia tsaye ba ku da kuma anmynku ba?"

NAJEEBA ta dubi Umi ta ce" A sanina idan abu ba dadi zata sanar da jakadi ne, ita kuma ta sanar da Anmy...., ban taba sannin cewa tana waya da SHAHEED ba da har zata sanar masa abinda ya shafi lafiyata .....umi zan sanar da yaya Dayabu ya ga Malami dan bana son fara kiran malamin tun yanzu, ina so a sanar min wanda ya sanar masa na tura a dauko min ita, a kan wani dalili aka kawo maganar kishi a cikin maganar!"



Umi ta sake kure najeeba da ido ta ce" mamanki ta san me yake faruwa???"

Najeeba ta girgiza kai ta ce" Iya abinda ta sani irin fadan da yake yi, da fushin da yake yi da mu duka kan lamarin......., ya dage sai na yarda cewa na sha abinda ya lalata masa ciki Umi, bayan babu abinda na sha na rantse maki"

Umi Maryama ta juya ta rage wutar gazzz sosai, ta kashe na vermicelles din da ta turara sannan ta juyo tana kallon NAJEEBA a nutse ta zauna saman kujerar dake kicin din ta yi mata nuni da wajen zama ta ce" Zauna"

Zaunawa Najeeba ta yi tana kallon ta

A tausashe ta ce" Da ya zo maki da maganar kin sha wani abu ya zubar masa da ciki ke me kika ce dan kwontar masa da hankali ta yadda zaku fahimci junna???"

NAJEEBA ta sada kai tana wasa da yan yatsunta ta ce" Umi......, mutumen da bai tsaya ya ji daga gareni ba?, fada yake yi cike da yarda cewar na aikata, har ya tuno abinda ya taSa faruwa da mu a nan wanda ya marenin nan, umi ya yarda cewar na zubar masa da ciki ne cikin gangancina, Umi idan adalci ake kiran mai DAMAGARAN da shi sai dai a kan wasu, Ama ba Ni ba. "

Shiru mahaifiyarta ta yi, na lokaci mai dan tsayi, kafin ta ce" , ki daina fadin haka..... wai Wacece likitar? Waye likitan?"

NAJEEBA ta ce" Wannan DOCTER IZRANE din ce wace ke duba mu ai"

Umi ta Wan dubeta da kula ta ce" kina nufin yarinyar dake duba ku?"

NAJEEBA ta gyada kai

Umi ta dan girgiza kai tana mikewa ta kashe wutar girkin gaba daya ta ce" Ba damuwa, zan duba....., Ama ki kula kin san halin babanku da yan uwanki, kar ki fada musu bari har in ga abinda yake faruwa dan nima ban yarda da result din ba, yaya maganar kin tura a dauko ta dan kishi? Wani irin kishi? Dama akoy wani abu tsakaninki da ita ne da ya hado kishi a ciki? A kan me zata rinka maganar rashin lafiyarki da mijinki maimakun ke? ......gaba daya abin nan akoy wani abu a ciki"

NAJEEBA ta yi murmushi tana dan girgiza kai ta ce" a sanina dai babu umi, Ama kuma ban san tsakaninsa da ita ba ai"

Umi ta dubeta cikin kura mata ido, kafin ta juyo ta zo daf da ita sosai tana dubanta ta ce" Ina fatan koda haka din ne ba zaki yi abinda zai sa a dubeki da wani duba ba?, ba zaki sa a dauko maki ita ba, ba kuma zaki tardata ba, saboda dama kin san mijinki ai zai karra ko yanzu ko an jima in dai da ransa......, kuma kin san cewa zinariya na bayansa ba hakura ta yi ba, kenan ko menene kar ki yarda ki saka wata damuwar hakan a ranki, abinda ba zan yarda da shi ba shine maganar zubar da ciki, .........., in dai da ita a ciki ba zan kyaleta ba, shima kuma ina matukar jin kunyar yin hakan domin idan har abinda aka lakaba maki karya ne kwarai zan ji kunya da bai bi hanyar da ya dace ba, ke kuma ba wannan ne zai baki damar shiga ciki ba, ki bani lokaci kankani Najeeba , sai na shawarci mamanki domin ina girmama tsakaninta da ke, abinda tace a yi sai mu yi kin fahimta???"

Najeeba kallon mamanta ne kawai take yi, Ama gaba daya tunaninta ya tafi wani wajen......., tunda mahaifiyarta ta yi furucin ta san cewa mijinta sai ya karra aure tunaninta ya tsaya cak......, a'a fa, bata san da wannan batun ba, batama san dalilin da zai sa ace wai mijinta sai ya karra aure ba, a kan wani dalili fa??????? Ta yaya???????...........


"NAJEEBA" mamanta ta fada tana dafa gefen kafarta, hakan ya sa ta dago da sauri tana dubanta

Itama kallon da ta yi mata na kurewar tuhuma ne, da yar yatsarta ta ce" Idan kika yarda kika nuna min jinnin ubanki ya fi nawa karfi a jikin ki sai na ci ubanki kin san da wannan? Najeeba ina girmama yadda yanzu kike da hakuri a zamantakewar aure, kar in ji kin yi abinda zai sa mu haura da ke kin gane??"

NAJEEBA ta gyada kai tana kallon fuskar mamanta

Umi ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" In sha Allah, Allah zai baki wata haihuwar kin ji?????, ke dai ki yi ta addu'a"

NAJEEBA ta gyada kai tana sake neman afkawa wani tunanin hakan ya sa ta mike ta fice daga kicin din ta yi niyar nufa dakinta, Anmy ta yi kiran sunnanta

Dawowa ta yi ta duka kusa da Anmy din , a nutse Anmy ta ce " Yaushe zaki je asibitin?, kin san yau ya dace ku koma ko???"

NAJEEBA ta yi dan tsammmmm, kafin a tausashe ta ce" Anmy....idan ba damuwa, ina son zuwa wani asibitin , shima sai gobe plz"

Anmy ta Wan zuba mata ido tana karantar yannayinta, kafin ta ce" Ok , gobe idan Allah ya kai mu sai ki shirya ki je wace kike son zuwa"

Kai ta sake sadawa a tausashe ta furta" Allah ya karra lafiya anmyi"

Daga haka ta mike ta nufi dakinta ta zauna bakin bed , lokaci daya ta fara tunanin abinda ba Shikenan ba,

Tana tsakiya da tunanin nan Nadiya ta yi salama dakin nata

Amsawa ta yi tana duban hanyar shigowar nadiyar

Nadiya ta shigo tana dubanta fuskarta a sake da walwala ta zauna tana fadin" Barka da hutawa Najeeba, yaya sau?in jikin ki?"

NAJEEBA ta furta" Alhamdulilah, ya gida ya yara"

Nadiya ta ce" Lafiya kalau, ai yau za'a dauko su nayla, saboda school din na gobe"

NAJEEBA ta dan gyada kai bata ce komai ba

Nadiya ta dubeta, domin ta zata da tace mata yau za'a dauko nayla zata ga ta saki fara'a sosai da sosai, saboda irin shakuwar dake tsakaninta da yan matan, Ama sai ta ga bata wani nuna farin cikin haka a bayyane ba, karshema sai kawai ta Wan gyara ta kwonta

Nadiya ta sauke ajiyar zuciya a ranta tana ayyana ' ba dai zata manta maganar nan ta shekaran jiya ba?, sai dai ki yi hakuri kuwa dan gaskiya Ni ba zan kuma bari ace za'a min iko da ya'yana ba, bayan ke naki ya'yan sai idan sun zo wajen babansu nake ganninsu , ko kuma in Abdallah ya zo daukan Aliyu, to shima ba zan kuma bashi shi ba kar aje a kayar min da shi ina lalaba lafiyarsa.....haka kawai rashin son gaskiya?'

A bayyane kuwa sai ta ce" Jiya sai ga msg din Abansu a WAYANA, nayi ta farin ciki ina godewa Allah cewar kenan ya huce? Yaushe zaki dauki kwananki ne? Saboda mu jona irgenmu? Ko kin bari in yi kwanakin da ban yi masa ba ya shiga fushin? Idan kina tune nice zan je Sangarensa sai kika bata masa ran nan Nima abin ya shafe ni "

NAJEEBA ta bude idannuwanta dake lumshe ta sauke su a kan Nadiya........, ta yi mata duba daya tak kafin ta dauke kanta ta mike tana sauko kaffafuwanta wani abu na bijiro mata mai kama da mugun kishi da tsohon miki hadi da jin zafin nadiyar da shi SHAHEED din tun daga zuciyarta

Bayi ta nufa, har sai da ta kama kofar zata shiga ta dakatar ta juyo tana kallon Nadiya ta ce" Nadiya.....Ni yanzu fa nake bldng ai Bama sai na je ba, ki je kawai lafiya lau ne na Bara maki kwanakin "

Nadiya dake kallon ta zata sake yin wata maganar ta shigewarta ta rufe bayin ta kunna pampos ta shiga wanke hannunta a fili ta ja wani uban tsaki tana dantse lebenta a zuciyarta ta ayyana ' Shikenan dan na zama abar takawa sai kema ki ringa kawo min rainin wayo ko?, ba damuwa ki zage dantse ki yi du abinda kika ga ya maki kyau......, daidai nake da ke da shi din mijin naki aikin banza!'


Nadiya kuwa mikewa ta yi ta tafi cike da zulumi, sai dai tana zuwa ta shiga shirya tafiya Sangarensa domin ta nemi izinin hakan kuma ya bata amsa, duda a takaice amsar take Ama ta san za'a bata dama ne dan haka ta mayar da hankali sosai ta shiga shiryawa ta wuce Sangarensa ta shige kicin ta shiga girke girke , danma ta tarar da kicin din a hargitse yadda ta barta tun wancen aikin da ta yi? Domin dama NAJEEBA ce mai gyaran, ranar da zata yi gyaran kuwa hankalinta ba'a kwonce ba , daga nan kuwa ba'a shigar musu kicin din ba, daga wajen Anmy ake kula da cikinsa domin du idan wani abu ya gifta da zai Hanna iyalinsa yi masa girki daga Sangaren Anmy ake kaiwa hatta breakfast.

Ta daku da aiki, sai kusan sallar isha'i ta gama komai ta saka turaran wuta a falon ta rufo kicin din kacan kacan da tunanin zata gyara gobe , sannan ta yi bangarenta dan ta shirya ta zo , yau so take yi ta bar Aliyu wajen mai kula da shi ma dan ta ba babansa hakuri sosai

A bangaren NAJEEBA bayan an yi sallar isha'i sai ta shige kicin tana kyalkyalewa domin ba zata iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login