Showing 42001 words to 45000 words out of 144591 words

Chapter 15 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2367

yi mata maganar me take son ci? Kasa kasa sunna magana, jin shigowa ta yi zaton andiya ce da ta je tsayawa kan shiryawar tagwaye da su nayla , sai ta ga yayansu ne, da sauri ta sada kanta kasa tana furta" Barka da safiya yayah"

Idannuwansa ya lumshe......, sai kuma ya budi bakinsa a hankali ya furta" Barka Jamilah..."

Daga haka ta mike kanta a kasa ta fice a dakin da dan hanzari

A hankali ya karasa bakin bed din ya zauna........., idannuwansa a kan farar rigar dake jikinta, da kuma gashin kanta da ya bazu ko'ina saman gadon........, haka kawai ya ringa tunanin to da wannan rigar din ne Dayabu ya zo ko? Hannnnn.....

Kasa kasa sosai ya ce" yaya sau?in jikin ki ?"

Najeeba dake jin wani irin mugun zafinsa har cen cikin zuciyarta bata bashi amsa ba, sai idannuwanta da ta rintse ta kawar da kanta.........

A hankali ya juyo ya zuba mata ido, kwarai yana kallon yannayinta da yanayin fushin da take ciki.........
A hankali ya ce" Ba zaki amsani ba?......mema na yi maki???? Ko kawai dan nace zan yi aure????"

Wani makuku ya rike wuyan Najeeba, ta dago idannuwanta da suke rine ta Wora a fuskarsa........

A hankali ta dauke kasa kasa sosai ta furta" kana tunanin saboda zaka yi aure ne har zan damu?????"

Ido ya kura mata zuciyarsa na harbawa, saboda irin yadda ta fitar da amon a kausashe

A hakan ta Wora da fadin" Na damu ne saboda a karro na ba adadi za'a zartar da rashin adalci a kaina....., a karro na ba adadi za'a kasa yi min adalcin da ake iya yiwa kowa........., ko dan ma zamo matar cushe ya sa ake nema a takeni a duk lokacin da aka so?????"

"BEEBAH!" Ya fada a kausashe yana dan fitar da idannuwansa

NAJEEBA ta mike daga saman gadon ta sauka a nutse ta saka takalmanta na daki ta zagaya wajen bayi ta dakata ta juyo tana dubansa, a hade ta ce" Ko Y'ar gwal zaka aura , dama ta baka ka aura......, Sai dai Ni Najeeba MUTALAB koda jikina duka kunne ne ba zan lamunci bayanin cewa nice na yi sanadiyar gudan jinina ba har hakan ya ja min wulakanci da tozarci a wajen wanda ya dace ace ya fi kowa dubana!"

Ta sake duban irin mamakin da ya wanzu a fuskarsa, dan har ga Allah rabon su da irin wannan har ya manta shi din da kansa

Ta Wora da fadin" Shan maganin da zai gyara min jiki, da kuma kula da jikina ai yanzu na fara, saboda ba na ila a ciki......., Batun na zubar da ciki nake so amintaciyar mijina ta bani bayanin abinda ta gani a bincike tun kotun damagaran na iya isarmu ba sai na haura sama ba!, tabas sai ta fada min abinda ya kawar da gudan jinina , ko kuma uban y'ayana ya fada min kalar zuwan da ya min wanda daga shi ciwon mara ya sarkeni har cikina ya fice......Ama Ni Najeeba ba makashiya bace kuma zan tabbatar maka da hak....."

Da sauri ta murda bayin ta shige ta rufo da karfi ta murda ky ta daga murya ta ce" SHAHEED, adalcin kenan??????, zan kai karar ka fada SHAHEED, idan har ka yarda ka shiga wannan maganar tabasss sai na duka da kai gaban ANMY ta mana Shari'a......, a yanzu nice ba zan yarda ba, kuma da karfin mulkin Allah mai adalci gagara misali sai na san abinda yake faruwa..........., aure kuwa ka yi dari in ana yi, ba shine damuwata ba!!!!!!!" Ta karashe tana rike garu da sauri saboda juwar dake daukan ta mai karfi kamar zata kifata da kassss.............., tsoro ya kamata.........., ta rike da kyau tana mayar da nunfashi kasa kasa ta furta......" ka yi auren mana SHAHEED?????, a kaina aka fara ne????? Ka yi, ka maido matarka idan kana so, sai me? Nima ai ita na tarar . ......, shin SHAHEED me na sani a aurenka ne Ni banda wahalarsa????, SHAHEED kishiyata ka take ka Worani cikin kazantarta....., SHAHEED idan ka tashi sai ka nuna min wacece Ni........, du idan ka tashi takewa nice abar takewarka da kafa......, SHAHEED har ta kai ka muzantani a kan abinda ba Ni na aikata ba????, ina iliminka SHAHEED? Ina adalcinka? .....ina girman darajar iya Shari'a dake tare da kai??? Shin har wata shashasha ta isa ta fada a gaban maganata ka yarda.....?????? Ba zan yarda ba!, ba zan yarda ba, sai na bi ta kan du Wanda yayi sake da maganata a garin DAMAGARAN daga kai har baran gidan nan!"


SHAHEED kuwa tunda ta fada bayin nan ta rufe ya ringa jin juwa zata Webe shi, hakan ya sa ya juya ya fice ya nufi bangarensa ya cire ky din da mamanta ta saka ya tafi da su baki daya ya shige dakinsa na barci ya rufe ba tare da ya iya bi ta kan su Muhammad da zasu koma makaranta ba........, gaba daya yana da bukatar kilace kansa Wan ya samu karfin jikinsa dawowa cikin jikinsa ....., yana so ya mike da kaffafuwansa ya fuskanci yarinyar nan ya dankwarar da ita da karfi da isar da Allah ya mallaka masa......, yana so idan ya sake haduwa da ita ya zamo haduwa ce da zata nemi sulhu da kanta......tabasssssss sai Najeeba ta nemi sulhu har ta bashi hakurin furucinta a kansa.......

Shine Beebah zata ce ita matar cushe take a wajensa?
Kenan du irin maganar da ya fada mata cewa ta jima a duniyarsa tunda aka fara kawota gidansu tana yar kankanuwarta bata yarda ba?????, wai me yasa ta cika son fitina ne?????, me yasa take da son nuna masa iyakarsa ne????, a kan take so ya nuna isarsa in ba ita ba.....? Ya rab......ya horar masa da ita ta zamo yadda yake soooooooooooooooooo shine addu'ar da ya cika yi a wajen sallah......, shin yadda take din nan din ne yadda yake so?????? Baya son fitina, a kanta ya koyi fitina, bai iya dogon fada ba, a kanta ya iya shi, bai san doguwar fira ba, a kanta ya koya....., yanzu kuma zata koya masa gardama da yaro? Ya salmmmmmm




A bangaren yan agadaz karfe takwas na safe ta yiwa su zahraou da Ummu Kulsum a a?roport, domin a jiya daga uban har dan basu samu barci ba saboda rikicin da matan suka Wora musu kuma suka Hanna su kiran Fadar damagaran din bale su nemi MUTALAB , uwa uba ummulkhair da kanta dake aure har Lagos ta biyo jirgin da zai kaita Kano, daga Kano zata shiga na Niamey, daga Niamey kuwa ta shiga na DAMAGARAN wato dai Nijar ta yi kira ,, umi kuwa dama nakudar gaba ta yi, a tsaye suka kwana ita da mijinta sunna fama, safiya na yi ta saka kayan haihuwa bayan mota tace a Kaita fada, daga cen idan haihuwar ta kama da gaske sa wuce asibiti ko Jakadiya ta amsa!

Wato fada ASALAMU ALAIKUM, zata dauki ya'yan MUTALAB.
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati na airtel ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




14

A lokacin da Umi ta karaso tare da mijinta jakadi ta karbo akwatin ta bata nufi ko'ina da akwatin ba sai bangaren Anmy......domin babu inda yaran ke sauka sai wajen mamansu kowani lokaci suka kawo ziyara fadar

A hankali take tafe har ta karasa falon Anmy a lokacin kuwa anmyn na salama da jikokinta ne sai faman tambayar inda su auta suke ko basu da karatu safe ne? Ama ta gaza samun cikakkiyar amsar da zata gamsar da ita har aka wuce da yaran da masu rakiyarsu yayi sauran ita a falo tana jan carbi hadi da sake duba lokaci har tara zata yi Ama su auta basu fita ba sai kawai ta yarda cewar basu da karatun safe ne ai da yayarsu ma bata yarda sun hantse haka ba, bale yau ake komawa makarantar ai ba za'a koma da wasa ba......, tana kokarin mikewa ne aka shigo da akwatin Umi jakadi ta sanar da ita Umi ce.

Zaunawa ta koma ta yi tana bin akwatin da kallo a ranta ta ayyana ' Umi? Kuma da akwati???'

Yan mintuna tsakani Ummi ta karaso falon tana salama hadi da baza idanuwanta dan baban burinta ta ga Y'ar uwarta ne, Allah kadai ya san irin halin da ta iya wayewa tunda ta ringa jiyo numfashin Najeeba...., yaya Dayabu ya sanar musu wai da sauki, ama yaya za'a yi ta iya zama bata shigo fadar ba yau???? Ko ba komai ai gari daya suke babu abinda za'a ce

Dukawa ta yi har kasa, daf da kafar ANMY tana murmushi ta bude baki zata gaisar da ANMY din wani tonon asiri na nakuda ta tashin mata a haka

Ido ta rintse ta d??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????an jimke hijabin ANMY tana sauraron dakan da ake yi mata har ya lafa sannan ta sauke ajiyar zuciya tana dagowa zata gaisar da ANMY ta ga zuba mata idon da ANMY ta yi sai ta wayance ta ce" ANMY, Barka da warhaka, ya gajiya anmyna"

ANMY da mamaki ta ce" Umi? Lafiya? Kamar nakuda kike yi fa? Akwatin mecece wancen?"

Umi ta bi akwatin da kallo kamar itama tana son gane akwatin mecece din, sai kuma ta sosa kai tana murmushi ta ce" Lah ANMY, eh akwati ce, kayan baby ne a ciki, kin san mamansa ta tafi kauye ne ta yiwu ta yi sati, Ni kuma bana tunanin na Kai sati a haka in sha Allah, shine kawai yace bari ya kawo Ni nan din idan yaso in ta dawo da wuri sai in koma in kuwa bata dawo ba koda abin ya tashi......sai a kula a nan"

Kwarai ANMY ta aminta da maganar, hakan ya sa farin ciki mamayeta ta ce" Masha Allah, ai kuwa bari ki ga in sa jakadi ta zo ta kawo kuka in dama maki ki sha, in sha Allah in dai ita din ce da wahala ki kai yama Allah zai budi ido lafiya, tashi ki huta, kin karya ne???"

Umi ta Wan sosa kai zata yi magana A'isha ta shigo da salama itama, sannan Jakadiya na dauke da baban jakar dake dauke da manyan kuloli na abinci....

ANMY da mamaki ta ce" A'a, A'isha ce da safen kema? Ko dai kin san kanwar taki ta taho ne??"

Da sauri umi ta ce" Eh ANMY, ai na sanar da Aunty cewar zan zo da sasafe da yake mun yi waya Jiya"

A'isha ta bi umi da kallo tana kaiwa kasa dan gaisar da ANMY

Umi ta nufi coridor tana fadin" ANMY, bari in leko Gimbiya na ga bata nan ta yiwu tana cen tana barcin nata na jin dadi"

ANMY ta bita da kallo kafin ta yi murmushi ta dubi A'isha ta ce" A'ishah Bakya gajiya da dawainiya? Ke dai in zaki zo sai kin min dafe dafe?, Allah yayi albarka, bi min bayan yarinyar cen a kan gwuiwa fa take kin ga ta yi tafiyarta bangaren NAJEEBA, idan kin ga da gaske ta tashi nakudar kar ki kyaleta a cen, fada min mu yi asibiti da ita, zan aiko Jakadiya ta kawo mata hadin kuka yana sakawa nakuda ta tashi gadan gadan kuma ana samun sauki wajen haihuwa in sha Allah "

Cikin girmamawa A'isha ta ce" To ANMY, in sha Allah, Allah ya sauketa lafiya"

Daga haka ta bi bayan Umi dake gaggawar karasawa bangaren NAJEEBA.


ANMY na tsaye dan a dama kukar, mai aikinta ta zo da waya tana fadin" Ranki ya dade kira ne ake ta yi a falo"

Amsar wayar ANMY ta yi tana duba sunan mai kiran

Gannin zahrau ya saka ta daga a tausashe ta amsa salamar zahraun

Zahrau a tausashe ta ce" Barka da warhaka ANMY"

ANMY ta yi murmushi ta furta" Barka kadai yarinyata, ya kike yaya gajiya?"

Zahrau ta furta" Alhamdulilah ANMY, dama ina so a tura direba a?roport ne ya dauko kayan mu, saboda mun shigo taxi ne Ama mun bar takardar da komai a hannun dogari Haliru, idan direba ya je sai su tardo mu"

ANMY ta yi dan tsai, kafin ta ce" a?roport ?, na agadaz? "

Zahrau ta yi dan shiru, sai kuma ta ce" A'a ANMY na nan DAMAGARAN"

ANMY ta juyo ta ce" Ban fahimta ba, ke din kina ina?"

Zahrau da sauri ta kalli Ummukulsum, ta ce" ANMY gamu a kusan kwanar fada, ba Ni kadai bace, Ni da ummukulsum ce"

ANMY ta dago wayar tana dubawa, sai kuma ta katse kiran sakamakon shigowar Dayabu yana ta murmushi hadi da dan kamewa ya duga zai gaisar da ANMY ta ce" Tashi, me yake faruwa a gidan nan?"

Dayabu ya kalli ANMY, ya ga yannayinta, sai kuma ya Wan sake sada kansa a nutse ya ce" wani abu ya faru ne ANMY?"

ANMY ta nuno shi da hannu ta ce" Kar ka yarda ka raina min wayo , me yake faruwa ne na ga kannenka sai harhaduwa suke yi? Ba zaku ce min daya bai san da zuwan daya ba"

Dayabu ya dan zarro ido, a bayyane ya ce" Ba dai umi ce ta taho gidan nan karfe tara na safe ko goma bata cika ba???"

ANMY ta sakar masa harara ta nufi ciki ta karasa saman Babar kujera ta ce" Umi ai mai sauki ce, bari ka ga wa'inda suke hanya, sannan ka sa direba ya je ya dauko kayansu da dogari sannan ku sameni a nan in ji abinda haka yake nufi, me yake faruwa ne?"

Dayabu ya dafe goshi, ya juya ya fice yana sauri

Ai kuwa bakin get din biyu suka hade da su zahrau dake tahowa , kowace da nikaf da katon hijabi dan kar a gane su

Da mamakin ganninsu ya tsaya a gabansu ya ce" Daga gidan uban wa kuke?"

Da sauri ummukulsum ta bi ta gefensa ta daka da gudu ta nufi bangaren NAJEEBA da sauri tana buWe rufar nikaf dinta dan a barta ta shige.....

Ai kuwa kafin ya gama gane ummukulsum gudu ne ta saka da girmanta da komai, zahra'u ta mara mata baya da sauri tana fadin" Yau ga jaraba, an zo din, shi yaya sai neman fitina wallahi......"

Juyowa yayi ya bi bayansu yana daga murya ya ce" Ni zaku rainawa wayo? Ni zaku dauka shashasha? Jiya ban ce kar in ga kafar kowace a gidan nan ba? Shine kuka nuna min kun isa yanzu gashin kanku kuke ci???"

Yana balakin yana ratsawa ne har ya iso falon Najeeba a lokacin da su umi suka sakata a tsakiya ita fa A'isha kan sai ta ci abinda andiya ta dafa mata, shigowar su ummukulsum ya da suka juyo da mugun mamakin ganninsu....., basu kai ga dire mamakinsu ba ya shigo yana janyo wayar caza ya ce" Ni zaku nunawa taurin kai? Uban me ya kawo ku??????"

Ihu suka saka harda Najeeba dake zaune ta daga hannayenta ta ce" Yaya ka daki kowa banda ni, ka ga banda lafiya ko?????"

Umi ta mike tirtsitsi da ciki tana nishi ta ce" to Ni ai yanzu du rashin imanin mutun dai ai ba zai taba lafiyata ba, dan haka ku shige bayana"

A'isha dake musu dariya ta ce" Honey PLZ, ka bari su ga jikinta , tunda har suka zo ai ka san ba zai yiwu yanzu yanzu a mayar da su ba, ko ba komai dole sai an yi jiran jirgi tunda ba irin mota bane ba lokacin da aka yi niyar shigarsa ake samunsa ba, bayan wannan tunda suka zo da izinin mazansu ai a barsu su ga yan uwa"

Dayabu ya zauna yana kallon ta ya ce" Ba zaki gane ba, du wani abu da zai sa a yi min kallon Nine nake musu ja gabar wani rashin zaman lafiyan bana so, na fi so mu ji abinda yake faruwa , kuma idan mun jin du jama'ar garin nan bamu isa mu magance mata damuwarta ba sai sun zo????"

A sanyaye zahra'u ta zauna daf da shi ta ce" Haba yaya, ka san ba haka muke nufi ba, Ama idan muka zauna a cen a halin da take ciki yaya kake so mu yi?, yaya kai da kanka ka san ba zamu iya ba, zuciyarmu ba zata iya ba ko???"

Dayabu ya dubi NAJEEBA, ya nuna mata gabansa ya ce" Zo nan ki zauna, taho ki zauna mu yi magana a tsakaninmu wace baki isa ki boye min komai ba, kuma mu yi magana domin Allah "

Karasowa ta yi ta zauna , sauran ma suka zauna , su Andiya kuwa suka yi ciki ita da Auta dan firar ubansu za'a yi , ba zasu zauna ba.

A nutse ya bi su da kallo ya ce" Me yasa har yanzu da kuma ba shekara talatin baya ba zaku daina shirme bane? Yanzu ace dan kawai ta yi dan fada da mijinta gaba daya kun kwaso kun zo, kun zo gidan da ku da kanku kun san take da gata gaba da baya, kun shigo zaku dagawa wace take uwa a wajenku kuma mahaifiyar wanda yar uwar taku ta yi fada da shi hankali, dan Allah ba zaku ji kunyar haka ba?"

Ya dubi zahra'u da kyau ya ce" Zahra'u, ke kin san sai inda karfin ANMY ya kare a kan NAJEEBA, kuma ku kun fi kowa sannin cewa mijinta yana son ta, menene da zaburowa tun daga garin agadaz ku zo sai kace wa'inda kuka fi karfin mazahenku?, sarakai kuke aure, ku kun san kadan fuskar ku ta fita waje a irin wannan lokacin zaku janyowa kanku da iyayenku magana, harma da mazajenku.....ko du wannan bai dame ku ba?????"

Ya maido hankalinsa kan NAJEEBA ya ce" Na dawo kanki ke kuma, yanzu NAJEEBA ba zaki ji tsoron Allah ki bi bawan Allahn nan a hankali ba? Me kika nema a wajensa kika rasa? Ko dan kawai ku mata idan kuka gane cewa ana son ku Shikenan sai ku kama wulakanci har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login