Showing 27001 words to 30000 words out of 144591 words

Chapter 10 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2347

shine zata nemi wata fitinar?............

Har ya mike ya sake daukan wayar da iya jama'arsa ke aiki da layin, yar karama ya danna NUMBAR sarkin bulala, domin ya san cewa idan har yanzu bata fito dan amsa kiran da aka je yi mata ba ta yiwu zuwa yanzu ya dauke bulalarsa a jikinta

A lokacin sarkin bulala na daf da Bala kofar ofice din Docter IZRANE wace ke ciki jikinta na rawa kamar zata summa dan tsoro shigowar kiran ya katse masa hanzari

Tana yin RINGIN daya ya daga yana kai gwuiwarsa daya kasa ya furta" ASARKI"

" Umarnin wa ya kai ka dauko likita?"
Ya fada cikin fitar da lafuza a nutse

Da sauri ya ce" Umarni daga hannun Malami cewa umarni ne daga Sangaren mai baban daki, uwargijiyarmu"

SHAHEED ya dan gyada kai, a hankali ya furta" Na soke"

Sarkin bulala ya dake sada kansa ya furta" Umarnin ka shine abin cikawa, Allah ya ja zamani, rabi ya dada lafiya baya goya marayu"

Kashe kiran yayi ya fice ta baya ya murda ky din dake jiki ya bude ya shige ya nufi falonta direct ya nufi dakin ta Wan ya tabbata in dai zata hadu da baki ba zata zauna a bangaren Anmy har warhaka ba, domin ya san cewa in har Anmy ta Wan da zamanta da baki yau ba zata barta ba, bale in har ta san me zaman ya kunsa................., NAJEEBA kenan, karfi da yaji ta gama koya masa masifa da surutu a duniya, idan ta tada fitinarta kuwa dama watan ciwon kansa ya kama ne.


Bude kofar ya sakata dagowa da sauri, dan bata tunanin gannin wani a nan a irin wannan lokacin, kai harma sai da gabanta ya fadi na tsoro dan bata yi tunanin zuwan kowa ba.

A hankali ta furta" SHAHEED"

Idannuwansa a kan fuskarta, idannuwansa a kan sasan jikinta....zuciyarsa bugawa take yi da karfi, gaba daya tunaninsa ya nemi dakatawa daga abinda ya kawo shi...., a hankali ya furta" Beebahhhhhhhhhhh"

Sai kuma ya juyar da bayansa gaba daya ya rintse idannuwansa kafin ya juyo fuskarsa a hade

Fuskarsa take kallo kafin ta janyo hijabinta ta saka sannan ta duka a hankali ta furta" Barka da warhaka Dady >?4? "

Dubansa ya dauke a kanta ba tare da ya bata damar sake furta wani abin ba ya furta " A kan wani dalili zaki sa a dauko maki Docter?"

Da mamaki ta dago tana kallonsa, yaushe kuma aka fara saka musu dokar wanda zasu nema a gidan nan da wanda ba zasu nema ba? Waye ma ya isa ya dauki maganar nan ya kai masa cewar tana son zama da Docter? Yaushe ta yi dogon barcin da har ake son kawo mata raini ita Najeeba MUTALAB a muhallin da take Gimbiya a cikinsa? Waye ya dora dokar nan bata da labari? Kai to ai sai dan masani ya saka hannu za'a kawo likitocin, dan masani kuwa yana sanar da mai martaba abinda ya girmami tunaninsa ne ya fi karfinsa wanda ba zai iya ba sai mai martaba ya shiga dole ba wai wannan ba dan dalilin ba

Kai ta kawar a hankali ta ce" Ina son su gamsar da ni ne, ina son su......."

"Su? waye da wa???" Ya fada yana tsatsareta da ido....

NAJEEBA ta dago ta zubawa fuskarsa ido......, ya subahanalah........tabas a yau zata karra tsinewa lokacin da ya shigeta ya lalata mata duk wani shiri nata har ya zamo a yau baban tashin hankalinta ita Najeeba shine gannin fuskar nan a yannayi na bacin rai........, a hankali ta ce" To Ama, kai me aka ce maka??????

Sai da ya dauki lokaci, kafin ya ce
" Look........Ba shine tambayar da na miki ba!" Ya sake duban ta a kausashe

'ya Allah, dukkan abinda bawan nan naka ke ji da shi a kaina ka sanyaya mana, kwarai ya dauki zafi ya Allah ka sanyaya masa da mu baki daya...., ko me ya tunkaro Ni da mijina Ubangiji ka iya min, bani da karfin iyawa....bani da karfin ganewa....ya rab ka haskaka min.....' ta samu zuciyarta da yin wannan addu'ar

A hankali ta dago daga dukawar da ta yi dan marabatarsa, ta zauna bakin gadonta tana dubansa ta ce" Ina son mu zauna ne mu yi maganar fahimta da ita a kan maganar cikina"

SHAHEED da dan mamaki ya ce" Maganar fahimta a kan cikinki ? Kina da wanda ya dace ace kin yarda cewa kin yiwa barna ki nemi zama da shi sama da Ni ne?, ........No, kin dai ji abinda take fada shine kike son tsoratar da ita?"

Itama da mamaki ta Dube shi ta ce" Tsoratar da ita kuma? ITA WA? WACE ITA?"

Ya dauke kansa yana girgizawa ya juya da nufin tafiya

Da sauri Najeeba ta mike tana dubansa a sanyaye ta ce" SHAHEED Please, ka yi hakuri mana, SHAHEED bani da lafiya fa, me yasa karamin abu ke son zama baba ne? Laifin me na yi?"

Juyowa yayi ya sauke idannuwansa a kanta, kwarai tunda suka gama ganewa junna take da saukin kan nemansa afuwa.....shima ya sani, na yanzu ma bai bashi mamaki ba, dan haka yana duban ta da yanayin tsayuwar ta a hankali , cike da gajiyawa da wannan bacin ran ya ce" Baki da lafiyan ne kike neman wata fitinar?, ko an gaya maki dan ke kadai aka haliceni.....?"

Da tarin duhun kan maganganunsa take dubansa da neman haske a furucinsa, dan bata ga abinda ya kawo wannan maganar ba sam.....

Ya dauke kansa ya ce" Tabas ba dan ke kadai aka haliceni ba, kuma zan tabbatar maki da haka idan na yi aure...., ki shirya amsar abokiyar zama kwana kusa Najeeba...., zan kawo maki wace zata so Ni, zata zo ita ta haifa min......zata zo ta kula da Ni, dama ai kin ce hadamu aka yi ko?, zan kawo wace ke so koda na hadi ne!"

Muryarta a kausashen da ya jima bai ji ba ta ce" SHAHEED!"

Idannuwansa ya saka cikin nata a kausashe bai amsata ba.....suka dauki lokaci a haka....a hankali Najeeba ta furta" Ban zubar maka da ciki ba!"

Idannuwansa ya rintse cike da jin haushin kennan dai ba zata sama musu sauki a zukata ba.....? Ba zata taimaka ta sama masa sauki ba ko??????, ok....Fine.

Daga haka ya fice ya rufo mata kofar yayi tafiyarsa bangarensa yana tunanin Najeeba ta gama samun damarsa ne ga dukkan alamu da har take tunanin tana da karfin Hanna shi kula mata?, tana maganar bata da lafiya ne zata nemi zama da yarinyar da kawai ta nuna tana sonsa?, wato ita damuwarta kenan ko?, ok fine ....zai rikitata da damuwar nan sosai da sosai ne..........., dan ba niyarsa kenan ba, Ama kuma zai gigitata da tunanin niyar tasa kenan

Babu abinda ya fi birkita tunaninta irin su samu matsala da shi ya ringa barinta a cikin duhun abinda bata gane ba.

Da sauri ta daga kafarta ta bi bayansa ta hanyar da ya biyo tana ta addu'ar Allah ya sa bai rufe ba

Ai kuwa ta samu kofar a rufe hakan ya sa ta juya ta koma da sauri ta dauki alkyabarta ta dora saman katon hijabinta ta fice ta Babar kofa ta doshi bangarensa ta Babar kofar ta shige baban get sannan ta nufi ciki , ya zamo duk wani ma'aikaci yana gaisheta da daraja da dukawa, har ta isa kofar baban falonsa ta saka hannu ta bude bata ko nemi izinin shiga ba

Mutun biyu ta samu a nan, suka gaisa sama sama ta wuce bata dakata ba, hakan ya sa su dan masani mikewa suka bar wajen, domin rabon da mai baban daki ta biyo ta nan har sun manta, tunda aka musu hanyar bi din nan ma gaskiya basa biyowa ta jan, shi yasa suke baje kolinsu a nan din saboda matan mai gidansu ba biyowa suke yi ba

Bai tsamaci ganninta a falo na biyu ba sai da ta bude ta shigo,

A kishingiden da yake sai da ya ji kamar an shake shi saboda hanyar da ya ga ta bulo ta ita, hanyar nan fa itace maza ke yin zaman fira ba dare ba rana.....?afafuwan Beebah a fili ba Safa ta ratso ta shigo?, nan da nan nadamar rufe hanyar nan ta shiga zuciyarsa ya mike rai bace ya ce" ta nan kika biyo?"

Ya fada yana nuna hanyar

NAJEEBA ta karaso da sauri tana cire alkyabarta ta ce" ka yi hakuri, shi yasa na Wora alkyabata na rufe jikinnnnnna..... SHAHEED, wai me yake faruwa ne? Gaba daya na gaza gane kanka, SHAHEED ban zubar da ciki ba, ban sha abinda zai yiwa cikina ila ba, cikin da ban san da shi bane zan yi masa gangancin zubewar? SHAHEED me zai sa na zubar da cikin sunna, cikin mijina ? In bana son cikin ai ba zan dauke shi ba SHAHEED, kuma ka yi maganar wai ko bani da lafiya ina neman fitina? Da wa zan nemi fitina SHAHEED?, abinda ya sa na nemi zama da su dan ina son karrin bayani ne, SHAHEED yaya za'a ce Ni na zubda cikina ne?, ta yaya zaka yarda da maganar nan SHAHEED? Ka fi kowa sannin wacece Ni, dan Allah kar ka....."

"Sanin wacece ke din ya sa na yarda cewa babu abinda kika tsana irin abinda zai saka maki rashin lafiya ko zai bata maki jiki ko kuma ya Hanna maki sakewa da tsotsa da jigilar kukan baby...." Ya fada a kausashe yana tare numfashinta

A tsorace take kallonsa, jikinta na sake mutuwa sosai, zuciyarta na daukan radadi

A hankali ta ce" SHAHEED, ka bari su zo mu zauna da kai da su, ko kuma Ni in je in same su idan ba zaka yarda su zo nan ba, DOCTER IZRANE da Docter muhseen plz "

SHAHEED ya koma ya kishingida yana duban tv dinsa

Najeeba ta zuba masa ido zuciyarta sai bugawa take yi

Sai da ya jima kafin dan kansa cike da isa ya ce" Babu inda zaki je, kuma suma ba zasu zo ba........"

Gaba daya Najeeba sai ta fara tunanin ko dai da wani abin bayan wannan? Menene yayi zafi har haka Fisabililahi?, a hankali maganarsa ta dazu ta zo ranta, ta Dube shi da kyau, Muryarta a sanyaye ta ce" Daga na bata maka rai, a kan abinda Allah ne ya kadarto min, sai kace wai zaka karra aure?, haba SHAHEED"

Wani irin bugawa da zuciyarsa ta yi sai da ya rintse idannuwansa kafin ya bude a hankali ya dubeta......, a nutse, sannan kasa kasa ya ce" Wace kike harin zaman lafiyarta, ita din zan aura, dan Ni ba mijin tace bane, ki je bangaren ki in dai ba yarda kika yi cewar kin sha abinda ya min sanadiyar cikina ba kar ki zo inda nake, idan kika yarda kika so zamu iya zaunawa sai ki zo mu yi sulhu!"

Daga haka ya dan karra volume din TV din ya ci gaba da kallonsa hankali kwonce

Ta jima tana kallonsa, ta jima idannuwanta a kansa , a hankali a hankali ta ringa tunani kamar haka' Ga inda maganar ka take ......, maganar auren ce ta shigo cikin maganata har zaka wulakantani?, aure zaka yi? A kan wace huja?...... To wai wacece kake cewa ina harin zaman lafiyarta ne?.'

A hankali ta mike, har ta juya zata tafi ta tuna wata fitinar ce idan ta sake bi ta Babar kofa, sai kawai ta juya ta nufi corridor ta tafi ta bude ta shige ta je har dakinta jikinta na rawa sosai da sosai....., tana zuwa ta zube saman gadonta wani jinnin na yanke mata saboda a cikin zubarsa take dama kuma ga bacin rai sai ya karra yawa ya ringa murda kamar wace take nakuda haka ta yi ta murkususu da ciwo da kuma zufa har aka kira magariba aka gama sallah tana jiyowa a kwance a saman gadonta bata iya tashi ba


Jin shirun yayi yawa ya sa Anmy biyo sawunta

Tana zuwa ta sameta a kwoncen nan sai nishi take yi

Hankalin Anmy ya tashi sosai, ta kamata tana faman tambayar jikin ne??

NAJEEBA na jinta a jikin Anmy ta fashe da kuka tana sake cusa kanta cikin jikin Anmy tana kuka tamkar ranta zai fita

Jikin Anmy har rawa yake yi na tashin hankali , a rikice ta furta" innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, tun da raina zai wulakanta min ke ya saka ki kuka haka?, cikani ina zuwa cikani"

Dif kukan NAJEEBA ya tsaya, da sauri ta sake kankame hannayen Anmy, Muryarta na rawa ta ce" Anmy dan Allah kar ki je, Anmy kin san ko? Na tabbata nice mai laifi, domin duk rintsi baya fushi da Ni har haka idan bani da lafiya, Anmy laifina ne na tabbata akoy abinda na yi "

Anmy rai bace ta ce" NAJEEBA, zan saba maki, zan yi maki duka a wajen nan, yanzu NAJEEBA kin yi lalacewar da zaki kwonta kina kuka a kan namiji? Ok kenan gaba gaba komai na iya samunki? Najeeba idan shi bai ga tsufana ya daga maki kafa kun shirya kanku ba kema ba zaki gani ba sai ki zauna kina kula bacin ran nasa ki nemi kashe kanki nima ki kashe Ni.....?"

A raunane Najeeba ta ce" Anmy plz Anmy am"

Anmy ta tureta ta ce" Kuma nace zan masa magana zaki Hanna Ni Najeeba?"

A raunane sosai Najeeba ta ce" Anmy dan Allah kar ki yi, kar ki daga masa hankali, ko menene zai wuce in sha Allah Anmy, ni Bama shine yake damuna ba Anmy Bama shi bane plz jikina ne kawai ba dadi "

Anmy ta rike ta da kyau tana mikar da ita, itama ta taimaka bata saki jikinta ba saboda a yanzu du karfi ya ja baya ba kamar da bane, a hankali ta kamata ta dauko ky dinta bata ce da ita komai ba ta jata suka nufi bangaren ta ranta a bace

Sunna shiga ta dubi Andiya da du bata cikin hayacinta ta ce" Ke, je ki dauko min kayan mamanki kamar kala biyar ki kawo min yanzu, ki hado da turarukanta da duk wani abin bukata"

Andiya ta amsa ta nufi bangarensu, Anmy kuwa ta ware dan makulin dake sada Najeeba da bangarenta ta je ta saka ky din ta baya irin yadda ya saka nasa daga Sangarensa sannan ta dawo fuska a daure ta ce" Ki tashi yanzu ki yi wankan yamar, tunda dare yayi baki yi ba kafin ki fito zamu gyara maki dakin ki yadda zaki ji dadinsa........"

NAJEEBA ta mike jiki ba karfi zata nufi ciki Anmy ta kirayi sunnanta

Dawowa ta yi ta sake sada kai, a tausashe anmy ta ce" Ky din da na saka ko da wasa kar na ji kin cire da hannun ki, ki bar masa idan ya tashi cirewa zai bi hanyar da ta dace ya cire, sannan ki kama kanki, na fada maki ki kama kanki in ba haka ba zan saba maki, maza ki yi abinda ya dace ga abinci da magani ki sha, Allah ya baki lafiya"
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati na airtel ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




10



A daren yau , ?a?anta da suka zo ganin jikinta bayan sun baro bangaren mahaifinsu Muhammad ya haye gadon ya kwonta daf da ita ya dora kansa a tafin hannunta yana kallon ta ya ce"Momy, haka Anmy take min idan nace Ni sai na je wajenki na kwana, plz ki barni in yi barci a haka...."

Abdallah na kallonsa ya dan kame haba ya ce" Kai kawai ba zaka girma ba?"

Muhammad ya kyale shi saboda ya san mamansu bata son mitar nan tasu da rigima, bale yanzu da dare yayi kowa ya kwonta

A tausashe bayan ta yi murmushi ta ce" Yi kwonciyarka yaron kirki, kaima idan kana so taho Abdallah mu kwonta"

Abdallah ya dan zarro ido kafin ya girgiza kai abinsa ya nufi doguwar kujerar dake dakin yana cire rigarsa ya haye yayi kwonciyarsa ya ce"momy Ni kam ai soja ne, bana son ragonta irin ta yaron nan, good night "

NAJEEBA ta saki murmushi ta juyo tana kallonsa ta ce" Ka yi addu'a fa kafin ka yi barci"

Ya zauna yana yi, shima Muhammad ya zauna yana yin addu'ar zuciyarsa cike da farin cikin zai kwonta kusa da mamansa, domin shi baya taba gannin girmansa, a kullum gani yake yi karami ne shi, shekara bakwai ne fa kadai, Ama sai mamansu ta ringa cewa sun girma su ringa kwonciya a dakinsu ko kuma su yi tafiyarsu wajen Anmy, wani lokacin idan rigimar ta ki fasuwa mahaifinsu ke tafiya da su Sangarensa kuma yayi kwonciyarsa a tsakiyarsu su yi barcinsu, dan dai tana iya yinta ne wajen kin hakan ko dan kar Nadiya ta ga ba'a kyauta mata .


Bayan riko da carbi, da kokarin ganin ta cire damuwar dake zuciyarta ta samu barci mai dadi ya yi awon gaba da ita , zuciya cike da sake sake ama kuma barcin na dauketa ta manta komai ta ringa yin barcinta hankali kwonce........


A bangaren SHAHEED kuwa ya duba hanyar da zata iya biyowa ta tardo shi ya fi a irga ama shiru bata dawo ba, ..........kwarai yayi tunanin zata dawo din saboda doka daya ya saka mata a cikin abinda zai sa su shirya, dokar kuwa itace ta yarda itace sanadiyar zubewar cikinsa ta yadda zasu zauna su yi maganar fahimta harma ya hannata shan koma menene da zai iya haifar da haka gaba, dan ta dauki maganarsa da mahimmanci sosai ta yarda da abinda ya fada, Ama ta ki ta yarda da haka, tsabar taurin kai ta ki ta yarda da hakan, ita ta kokarin kaima mai sonsa hari take, ko me tunanin yarinyar nan?????, Allah ya kyauta, sai dai du yadda zuciyarsa ta kai da kekyashewa yannayinta da yanayin fuskarsa sun kasa fita daga idannuwansa da zuciyarsa......, ya san tana wajen mamanta saboda cctv

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login