Showing 51001 words to 54000 words out of 144591 words

Chapter 18 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2345

da hankalinki, komai zai wuce kin ji Anmy???"

Anmy ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Dayabu, ina NAJEEBAN? A wani hali take???"

Yaya Dayabu ya ce" Anmy, kin san in ranta ya bace, ta fi son kilace kanta , ki yi hakuri zata fito ne da kanta ta zo kin ji Anmy?"

Anmy ta gyada kai, sannan ta ce" Ku gaishe da gida, ka ja A'isha ku je gida Allah ya muku albarka"

Juyawa yayi ya nufi kannensa ya musu alamun su taho

Ai kuwa du suka mike suka bi bayansa suka fice a falon, sunna fita ya Dube su a nutse ya ce" kwanaki nawa aka baku?"

Zahra'u ce kawai da take jin karfi karfi a jikinta ta ce" Ai mun jima rabon mu da gida, Abansu yace muna iya yin sati bibiyu mu ga gida"

Yaya Dayabu ya gyada kai, a hankali ya ce" Dan Allah, idan kun je wajenta, ku yi kokarin kwantar mata da hankali, kar ku ziga fushinta, kar ku daga mata hankali, kun sani sarai du rikicin da zata dauko yana iya juyewa kanta, saboda du yadda take tunanin ta iya rigima ya dameta ya shanye, idan ikon take tunanin zasu dubeta sai dai na wata kasar ba dai na nan ba, bana son abinda zai sa ta zubar da mutuncinta a idannuwan mutane, saboda cewa za'a yi dan zai yi aure ne, dan Allah da kun fahimci zata yi wani abu ku sanar min"

Jikinsu ba karfi suka amsa shi, sannan ya musu umarnin su tafi bangaren NAJEEBA ta baya dan a ba anmy dama ita da Sultan su gana..........


A cikin falo kuwa , tunda suka fice Anmy ta mike ta nufi dakin ta, tana shiga tun kafin ta zauna sawayenta suka dauki dumin hannunsa

A hankali ta lumshe idanuwanta, ta janye kaffafuwanta ta karasa bakin gadonta ta zauna

Tana zama ya sake dawowa nan din kansa a kasa, ya sake dafa kaffafuwanta kansa a kasa, Muryarsa c'en ciki ya ce". ANMY, PLZ..... i'm sorry Anmy "

Anmy ta bude idannuwanta ta sauke a kan lalausan gashin kansa domin ya sauke rawanin kasa ne

Murya a raunane sosai ta ce" Dan ka gane cewar tana sonka ne kake son wulakanta min ita???"

A hankali ya girgiza kai yana rike da kaffafuwanta

Anmy ta ce" Hakane mana, yaya za'a yi ka sakata a halin nan kuma ka fito da maganar zaka auri likitar da du ban yarda da ita ba? Wannan yaron haka kawai nake ji a raina ban yarda da likitar nan ba, yaushe ma ka santa da har magana mai daraja irin ta aure zata shiga tsakanin ka da ita? Su wanene iyayenta? Yaya nasabarsu su din kansu har a gangaro kanta? NAJEEBA tace an bata maganin da ya rikita mata yannayi cikin nan ya fice, yarinyar nan tana fada da bakinta, Ama dan ka san cewa bata da wani karfi a gaban iyayenku in dai kai ta shafa Shikenan sai ka daneta ? Baka san cewa akoy hakinta mai karfi a kanka bane? Baka san cewa idan ka fita hakin jama'ar garin ka nata kadai na iya tsayar da kai a gaban Allah ne? Yaya za'a yi ace ka kasa bata dama ta samu bayanin da zai gamsar da ita ne? Da tace tana son a cenza mata asibiti a kan me zaka nuna sai dai yarinyar nan ta duba ta ne?, yaya kake so yarinyar nan ta kai ranta ta ji sanyi ne? Haba dan Allah.....shin idan ta zubar da hawaye baka ji a ranka ne????, dubi, dago ka gani, idan tana kuka a nan dina nake ji, a nan dina nake jin kukan yarinyar nan"

Da sauri ya mike ya zauna daf da Anmy ya riko hannayenta yana kallonta, murya a tausashe ya ce" Anmy......, babu abinda yake gigita duniyata irin yarinyar ki......"

Ya sada kai, kafin ya sake dagowa yana duban ta ya ce" Babu abinda nake tsoro irin kadarar da zata shafi yarinyar ki....., Anmy ban taba son wata halitta bayan ke sama da ita ba, ko twins na auna na sake aunawa a bayan yarinyar ki suke"

Anmy ta yi gaggawar fadin" Wani irin so ne wannan da zai sa sai dai a fadawa wani ba wanda ake yiwa shi ba? Idan aure ka yi niyar yi baka san cewa idan ka lalaba abarka a daki ka rarasheta sai dai mu taya ku amsar Amaryar ba??"

A hankali ya ce" Anmy......, idan har ta san halin da nake ciki a kanta yaya zamu kare? Ki duba fa, a yanzu ma da take tunanin na fi son watanta a kanta irin yadda take kokarin jana a kasa......, Anmy ban yi niyar auren nan ba, in ba dan iyayenta da suka kara zuwa a kan batun nan ba, sam ban yi niya ba"

Anmy ta kure shi da ido, a hankali ta ce" Ban gane ba, kamar yaya? To meye ita ta yin da zaka ce tana janka a kas"

Ya sauke ajiyar zuciya, a hankali ya ce" likitarta ta aunata, ta sanar min damuwarta, na sameta da fushin hakan, a kan me zata min gardama???"

Anmy a tausashe ta ce" Dan ta kare kanta ne ta yi gardamar????"

Ya girgiza kai yana sake zuba idannuwansa a fuskar Anmy, shin yaya za'a yi su fahimci juna? Da wahala su fahimci juna shi da maman NAJEEBA, dan haka a tausashe ya ce" Dan Allah ki yi hakuri, na tuba, ina zan kai fushin ki ?"

Anmy ta girgiza kai, a hankali ta ce" Idan har kace zaka ja, jayayya mai nisa, ina mai tabbatar maka zaka fice mata a rai, domin babu abinda ke kashe soyaya irin wulakanci, du matar da mijinta ke muzantawa, yana wulakantawa, yana nuna mata fifiko wallahi tsaf zai fita daga ranta ko wanene........"

Ta Wan dakata saboda irin kallon da yake yi mata , kafin ta Wora da fadin" Bai dace ace maganar bare, wata cen ta kama kafar ta matarka ba !"

"Maganarta bata isa ta kama kafar ta Beebah ba, da ba likitar Beebah bace ita da babu abinda zai hada kunena da furucin bakinta...., Anmy itace likitar Beebah, zan ?aryata ta ne ????" Ya fada a hankali

Anmy ta ce" Ama dan tana likitarta shine zai da ta fadi abu ka hau ka zauna ba tare da ka yi aiki da kwalinka na lauya da kuma darajar shari'ar da ka karanta ta Hausa da addinin musulunci ka saurari mai kawo kuka a gaban mai laifi ba?, ba'a haka, idan har hawayen yarinyar nan da gaskiyarta ta zubar ba zan taba tsawatar mata a irin hukuncin da zata yanke maka"

Ya sake zuba idannuwansa da kyau a fuskar Anmy , a hankali ya kai hannayenta wajen kirjinsa ya dora

Sarai ta ji irin yadda kirjinsa ke bugawa, bai hannata fadin" Bani da wani fada da zan iya tare maka a wajen da kake neman fadan ido rufe....., dukan abinda zaka janyowa kanka kuwa ka kuka da kanka, ka guji furucin matar da ta yi kuka saboda lalacewar zuciya, ka guji fushinta, ka guji fushin wace ke son ka, idan ka ci gaba da bata mata wata rana sai ka nemi wace zaka batawa din, .....ina rokon ka kar ka rufe kowace hanya da za'a yi binciken nan dan a kwontar mata da hankali, idan har ka rufe tabasss a nan ne zaka ga fushina...., auren da ka dauko kuma ina addu'ar Allah ya sanya ALKHAIRi a ciki, ya baka ikon yin Adalci,"

A hankali ya lumshe idannuwansa da suka yi masa nauyi sosai.........sannan ya Wan sake langwabar da kan nasa yana duban Anmy kafin a hankali ya furta" Allah ya huci zuciyar ki "

Anmy ta sauke ajiyar zuciya ta lalubi rawaninsa ta mika masa

Amsa yayi ya mike jiki ba karfi ko kadan ya juya ya fice a dakin

Gaba daya abinda NAJEEBA ta fada ke dawo mata a kunnayenta......, tabasssss tana da fushi irin wanda ake cewa da an yi ake sakewar nan, Ama kuma wannan fushin da ya sa ta manta duk wani dake fala ta yi furucin nan ya tsoratata sosai, sai dai gani take yi gana daya sauran sun dauki haka irin fushin nan na sama sama wanda zai wuce da gaggawa....shi yasa ko bi ta kanta mamanta bata yi ba, tana addu'ar Allah ya sanyaya lamarin, kwarai tana addu'ar haka..........



A bangaren yan matan anmy, da suka je dakin NAJEEBA sun samu fitila a kashe, Najeebar a kwance a tsakiyar gado ta rufa har kanta

Du yadda suka so ta tashi su yi magana abin ya gagara karshe sai kwontawa suka yi suka sakata tsakiya, sai umi karama da ta KWONTA a kasa domin an fara sukanta kuma, alamun ciwon na iya sake motsawa kowani lokaci.

Da sasafe nakudar Umi ta tashe su baki daya, nakudar kuwa irin ta zo gadan gadan din nan

A lokacin da suke haya haya din tafiya wata asibitin Nadiya ta yi kiran DOCTER IZRANE, domin ita bata san wainar da ake toyawa cewar DOCTER IZRANE ce amaryarsu, hasalima tunda aka yi maganar auren nan take samun baki daga wajen mamanta masu zuwa da abubuwan taimako irin nasu kala kala....., sai yau da asusubahi ta zo gaishe da Anmy ne ta same su a falon anmyn sunna ta dako da addu'a ma umi karama shine ta ga bari ta yi taimako ta yi kiran DOCTER IZRANE idan ya so in tace su hade a asibiti sai su je......

Anmy na daki tana neman NUMBAR aminiyarta tsohuwar ungozomar fada dan ta sanar mata wace likita zasu dauka dan ta zama likitar yaran , jakadi ta shigo ta duka ta sanar da mutanen falon cewa an ce likita ta karaso ta shigo ne????

Su dukansu basu san wace likita bane, domin shigar anmy ta dauki minti goma sha biyar sun zata likitar da ake jira ce, dan haka ummulkhair ta mike tana fadin" Bari in sanar da su anmy din sai a shigo da ita"

A lokacin da ta shiga dakin Anmy, sosai kan d'a ya bado, domin Anmy ta saki wayar da sauri ta kama umi tana daidaita mata kwonciya sannan tana fadawa NAJEEBA dake tsaye sai zaro ido take yi yadda zata kama mata domin haihuwa kam ta zo ..........

Rikicewa ummulkhair ta yi ta yi baya ta tsaya tana fadin" ina likitar?????"

A lokacin da DOCTER IZRANE ta shigo falon cikin shiga ta likitoci da dan baby hijab dinta da dogon takalminta kamar zata je gasar sarauniyar Ingila ta karaso, Muryar Nadiya ta bude tana yi mata murmushi hadi da fadin DOCTER IZRANE Bismillah, bari mu gani ki shige kawai, a lokacin ne gaba daya matan falon suka kalli Nadiya a tare, hadi da kallon DOCTER IZRANE wace ta nemi nufar dakin Anmy, sai dai da sauro zahra'u ta mike zata yi magana ummulkhair ta janyo kofar dakin da karfi ta rufe hadi da dan tare kofar ta dan dage girarakinta a hankali ta furta" Dakin nan..........ya fi karfin bako fa"

Nadiya ta karaso tana jan yarbeben hijabinta ta ce" Lah ai ba bakuwa bace wannan din ummulkhair, likitarmu ce fa, Ni na kirawo ta Wan mai martaba ya Hanna muna haihuwa a gida da kanmu"

Ummulkhair ta dauki Nadiya da idanuwanta ta watsar bata ce da ita ufan ba, ta ki bada hanyar sannan ta daure fuska , wanda hakan ya sa DOCTER IZRANE zuba mata ido da yanayin son gane wacece ita kuma?????, sai kukan baby ya karade wajen wanda hakan ya sa DOCTER IZRANE sake kokarin shiga tana fadin" Excuse me, ki bani hanya in shiga saboda kin ji ta haihu , ko ke likita ce?????"

Hannun da ta sa da nufin matsar da ummulkhair, ummulkhair ta saka hannunta na hagu ta yi mata wata irin fuzga da ta saka ta yi taga taga ta dire a kas saboda takalman dake kaffafuwanta masu tsini ne,

Ido Nadiya ta zarro cike da tsoro ta ce" Kai, ummulkhair????? Kin san wacece? Likitarmu ce"

"Dila ki kama min bakinki a nan!, meye baki gane ba ke da ita din? Nace ba dakin da bako zai shiga bane, ke din ma ba zaki shiga ba saboda ke din ma bakuwar ce bale ita banzar bazara!,.....look Nadiya Abubakar, ki kama kanki ko in sauke maki shi a kas!" Ta fada da karfin da ya saka NAJEEBA kallon kofar da sauri, sai kuma ta ajiyewa Anmy dake fadin ta kirawa Jakadiya ta basu waje su kimtsa baby da mamansa

Anmy ta faman hade uwa take hakan ya sa hankalinta bai kawo ba........, Najeeba ta bude kofar ta fito a lokacin da DOCTER IZRANE ta mike tsaye idanuwanta waje , Ummulkhair kuwa ta karaso daf da ita sosai ido cikin ido ta ce" Sai dai ki zama likitar Nadiya......., Ama in sha Allah koda ke kadai zaki rage likita a duniya ba zaki ga al'aurar jinnin MUTALAB ba!"

DOCTER IZRANE tana dubanta rai bace ta daga hannu zata sauke mata nata itama salon balakin, Najeeba ta fito da mugun sauri ta damki hannun DOCTER IZRANE, a lokacin da Muryar Sarkin bulala ke sanar da isowar MAI MARTABA wanda bai samu shigowa da asubahin yau ba saboda ciwon kan da ya kwana da shi,

Da wani irin karfin da DOCTER IZRANE bata taba tunanin wannan jikin mai laushin masifa ya malakeshi ba ta fuzgota ta yi mata wani irin ja, da hannunta ta yiwa Nadiya alamun kama bakinta ko ta yankata, ta mata nunin wuyanta hadi ta nuna sama ta sauke rantsuwar da hannunta sannan ta ja DOCTER IZRANE da karfi ta yi kicin da ita saboda idan har ta nufi coridor tabasss yana iya sanin tana nan, sai kawai ta danata kicin din da karfin tsiya ta mako kofar ta dana NUMBAR cod din kicin din , a lokacin ne tak tak aka budewa mai damagaran Babar kofar falon Anmy ya shigo........


Zahra'u da jikinta ya kwashi rawa, tsoronta daya kar Najeeba ta hurmawa likitar nan wuka ta saka su uku, ta fara kai gwuiwoyinta kada kanta a kasa saboda bayanarsa a falon hadi da sauke idannuwansa a kansu baki dayansu......


Da sauri du suka kai gwuiwoyinsu kasa, hakama kawunansu, ciki harda Nadiya da jikinta ke mugun rawa saboda wannan salamamen balakin da ya diro mata wanda bata san farkonsa ba sai tsintar kanta ta yi a tsakiyarsa tsundum, jiki na rawa ta sake satar kallon hanyar kicin, hankalinta a tashe, hawaye ya shiga neman wanke mata ido, a lokacin da zahra'u ta furta"
A hankali zahra'u ta furta" Barka da safiya Yayah"

A hankali ummulkhair ta karSe da fadin" Barka da fitowa Abiey"......

Ummukulsum ta sada kanta tana jin zuciyarta kamar zata fito ta bakinta dan bugawar da take yi a hankali itama ta furta" Barka da gannin hantsi baban talakawa"................

Gaba dayansu binsu yake yi da ido a tsayen da yake, a bayyane firgicinsu ya gama bayana, gaba dayansu yannayinsu ya nuna basa cikin hayacinsu

Fitowar jakadiya da babyn dake rusa ihun tabatuwar ya shigo duniya da lafiya ya saka shi kai dubansa a lokacin da ta duka kanta a kasa tana kai gaisuwa a wajensa

Lokaci daya ya gane abinda ya fitar da su a hayacinsu, wato umi karama ce ta haihu a nan? Ikon Allah

Babyn ya amsa cike da fara yayi masa addu'a sannan ya mayar wa jakadiya shi

Har ya juya zai tafi ya Wan dakata ya furta" A tabbatar da an ga likita idan aka gama kimtsata"

Daga haka ya fice a falon jakadiya sai kirari take zubawa

Yana ficewa zahra'u ta fara mikewar da sauri ta nufi wajen kicin din

A lokacin da Najeeba ta shigo kicin din nan da DOCTER IZRANE bata yi wata wata ba ta yi mata wata hankadar da ta sa DOCTER IZRANE doka bayanta da ginanen frij din dake girke a kicin din, lokaci daya ta zarro ido tana waigowa ta furta" Ya Salam, sorry DOCTER, gaggawa ce nake yi na rufe kar aje a tardo ku a irin yanayin nan, ya Salam ummulkhair idan har aka ce za'a shiga dakin Anmy in ta ga bakuwar fuska ce ranta ke bacewa sosai, sorry DOCTER"

Wannan abin, da irin shiga rudun da ta yi suka hadu suka sake sakata a wani rudun , shine dalilin da ya hannata magana na dan lokaci har bata san shigowar Sultan da fitarsa ba, da ace NAJEEBA tana shiga ta hauta da wani balakin tabas da IZRANE ta sake cin galaba a kanta , bale a irin wannan lokacin da ya yarda cewar NAJEEBAN na iya yi mata wani abu saboda kishinta.

A lokacin da Najeeba ta gane me kirarin jakadiya ke nufi ta fitar da boyayan murmushi , zata fara yiwa DOCTER IZRANE magana zahra'u ta buga kasa kasa ta ce" Najeeba bude min, bude tun kafin in sa a zo a bude"

Karasawa ta yi cikin rausaya ta bude kofar, hakan ya ba IZRANE damar bin kugunta da kallo, wanda hakan ya sa gabanta ya kwonci kwonci ya fadi domin dama shigar dake jikin Najeeba sket ne irin mai rawar nan wanda iya kugu ya rike ya baje daga kasa sannan tsayinsa bakinsa kasan gwuiwarta da ?adan, sai riga mai hannu daidai gwuiwar hannu da dan sakewa sai dai itama rigar a saman jikinta take dassss ta bayyanar da yanayin albarkatun kirjinta madaidaita cikakku Pam

Kai ta dauke hankalinta na neman tashi da yanayin halittar jikin Najeeba..... innalilahi wa Inna ilaihi raj'une dama haka ta keru wannan yarinyar???? Gaba daya sai abinda ya faru yake neman bacewa a kwakwalwarta ta nemi fadawa tunanin yannayin jikin Najeeba tana aunawa da nata jikin wanda hakan ya bata mata rai ya daga mata hankali harma a nan inda take tsaye bata san lokacin da Najeeba ta bude kofar ta yi magana da zahra'u ba har ta bada hanya tana nuna mata DOCTER IZRANE din suka yi magana kasa kasa sannan ta juyo inda take da kyau ta ce" DOCTER? Are U ok???"

Zabura DOCTER IZRANE ta yi ta kikifta ido gabanta na sake faduwa dan ta zata zahra'un ce ummulkhair, domin dama du kama suke yi kawai Najeeba ce baka a cikinsu ta dauko fatar babanta, wato shuwa Arab masu duhun fata

Harhado kwarin gwuiwarta ta yi tana jin kamar zata kifa dan tsoro ta karaso ta raba ta shige su

A hankali Najeeba dake kare mata kallo ta ce" DOCTER......?"

DOCTER IZRANE ta dakata ta juyo gabanta na sake faduwa

A

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login