Showing 72001 words to 75000 words out of 144591 words

Chapter 25 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2360

Docter IZRANE kadai suka ji, dan haka ta dafe kirji ta yi tsuru tsuru, sai dai irin yadda Docter ke mata alamun ta tafi ya sa ta mike jikin ta na rawa ta fice a falon, sai aminin mahaifin Docter IZRANE shima ya mike ya fita

Bayan sun fice gaba dayansu ya jima yana dan murza azurfar hannunsa kafin ya sake yin gyaran murya a nutse yace" Ban san har wani waje mace ke iya kaiwa a lamarin kishi ba, abinda na sani shine ko me zaka yi ka ji tsoron Allah, sannan ka yi abu da ilimi........."

Ya dubi Nadiya a tausashe ya ce" Ba abinda ke zubar da kima irin cacar baki Gimbiya......., kar a kuma"

Nadiya ta sada kai a hankali ta ce " In sha Allah ASARKI"

Ya mayar da dubansa kan su IZRANE ya ce" Baki da wata gamsashiyar hujjar dake nunin cewa Giwatah ta je inda kike..........dan haka ki kiyayi sako wanda bashi da laifi a cikin maganarki koda zuwa gaba, ki nemi afuwar Giwatah "

Shiru ne ya wanzu a falon, har sai da mahaifinta ya ce" Ana nufin ki bata hakuri IZRANE "

IZRANE kamar zata fashe da kuka ta dubi NAJEEBA ta ce" ki yi hakuri"

NAJEEBA ta dago lumsasun idannuwanta ta sauke a kanta, a nutse ta sakar mata boyayan murmushi hadi da dan dantse gefen lebenta, wanda hakan ya sa izrane dauke dubanta da sauri daga kanta

Ya dan jima yana duban su kafin ya ce" Shi mahaifi, girmama shi ake yi, Iyayenmu ya dace su samu sauki da fitintinunmu daga bakin lokacin da muka mallaki hankalin kanmu........., wanan dalilin ya sa zuwansa na farko na Dube shi, ya dawo na dubi bukatarsa, ya dawo na kuma dubansa, yayi kira Jiya na sake dubawa......., sai dai"

Ya dakatar ya dubi mahaifin IZRANE ya ce" Bama haka, Bama daukan haka, Bama bada umarni a take shi, babu wani uzurin da zai fitar da mace mai daraja a irin wannan lokacin idan ba lafiya ya shafa fa ita kadai babu wani shakiki.........., wannan dalili zai sa a kilaceta a inda muke kilacewar, har bincike a kan Dabi'u da halayanta su kadama ta yadda zamu gane in ita din ta cencenci zama a cikin iyalina ko kuma a'a"

Anmy ya gyada kai, a tausashe ta furta" Haka din shine daidai in sha Allah "

NAJEEBA ta dago a karo na ba adadi ta sake duban ?afafuwan Nadiya ta Wan yatsina fuska saboda gama karantar kafar da ta yi ta juyar da kanta zata kalli nadiya suka sake hada ido da shi, ta dauke dubanta ta mayar kan Anmy

A nutse ya furta" Da safe, idan Allah ya aminta, za'a je a Kaita inda ya dace, du wani shakikinta yana iya Binta idan kuna da ra'ayin hakan, Allah ya bamu alkhairi"

Daga haka yayi shiru, kuma ya ki tashi, har sai da mahaifin IZRANE ya gama godewa suka mike suka fice a falon IZRANE kamar ta rusa ihu tace wayo Allah zata mutu dan takaici

A hankali ya kai dubansa inda Anmy take, a lokacin da NAJEEBA ta mike zata basu waje itama kamar yadda Nadiya ta mike zata fice din itama saboda kanwar mamanta na cen tana jira, haka kuma zata je ta fada mata abinda ya faru,

A hankali ya ce " Dawo ki zauna"

Najeeba ta ja ta tsaya, kafin ta juyo ta zauna kanta a kasa

Rai bace ya dubi Anmy ya ce " Zumuncinsa da ita? Tana da zumunci da wani gardi ne a duniya kaf bayan muharamanta? ANMY idan Ni ake nema da fitina tabas na shirya, kuma zan iya yinta da duk wanda ya shirya"

ANMY ta Wan zaroo ido ta ce" To Ama ai ba ita tace hakan ba Fisabililahi ko? Shine ya fada"

Sultan ya dubi NAJEEBA da kanta ke kasa kai ka ce ta Allah ce ya ce"




23
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




24



Sultan ya dubi NAJEEBA da kanta ke kasa sai kace wata saliha ya ce" Ya isa haka? Me kenan Beebah ?"

Najeeba ta dago idanuwanta ta dora saman fuskarsa...., a hankali ta soke kai a sanyaye ta ce" ka yi hakuri, gani na yi bai yi wani laifin da za'a dake shi ba"

"Zaki rufe min bakinki ko sai na rufe maki?" Ya fada a kausashen da ya saka Anmy dagowa ta Dube shi itama

A kausashe ya ce" Laifi? Akoy mai laifi sama da shi? Ke din muharamarsa ce? A kan wani dalili zaki hana a fasa min fatar jikinsa????"

NAJEEBA ta dago, ta yi nare nare da idanuwanta, muryarta a raunane sosai ta ce" Shikenan na zama nice mai laifin yanzu ma?, na zata za'a bani hakurin sharin da aka lakaba mun ne, na zata za'a nuna min nima mai yanci ce irin na wace ta zaunar min da uwata a gaban mamana ta kawo karar karya a kaina dan kawai a tozartani? Anya kuwa da Ni ce na yi zagin da Nadiya ta yi mata ba sai an sakani cikin dakin horo ba kuwa......? In sha Allah zan ci gaba da kiyaye duk wani abu da zai tayar da hankalin mamana, sannan zan kiyaye duk wani abu da zai sa a kara tsana saman wace aka yi min....., ka yi hakuri, ka yi hakuriiiiiii"
Sai kawai ta fashe da kuka ta mike da sauri ta yi coridor da gudu ta nufi dakin su

ANMY ta juyo da dubanta daga hanyar da NAJEEBA ta bi ta sauke dubanta a kan fuskarsa...............
Rai bace ta mike tsaye ta ce" Haka kake so? A ringa saka min yarinya a gaba ana nema a ci min zarafin ta?, ba laifi, Allah ya bada Sa'a sai dai Nima ba zan amince da haka ba, du wace ta yarda ta kuma kawo karan yarinyar nan ya zamo bata da wani laifi Allah sai na yi shara'a da ita!"

Daga haka Anmy ta yi shigewarta nata dakin saboda jaririn da ya fara tsala ihu, ta yiwu mamansa bata fito daga wankan yamar da take yi da dare ba har ya tashi daga barci

Ya jima yana kallon hanyar coridor din nan, kafin ya mike a dake ya nufi nasa bangaren ba tare da ya fita ta Babar kofar ba...
, wani abin mamaki, matar da bata riga ta shigo gidansa ba har ta fice masa a rai, wannan wace irin masifa ce ace mace sai kawo karar balaki? An yi ba'a yi ba ke kullum cikin mita? Shi yasa ya daina bude sakonta dan baya son takura ko kadan, haba dan Allah!

Najeeba kuwa a gujen nan ta bude dakinsu ta fado, wanda abin kukan nata ya sa yan uwan ta dake zaune sunna jiran su ga shigowar ta Wan su san matakin da zasu dauka, su biyu ummulkhair na kicin tana idasa tsaftace kicin din, bayan ta gama rashin mikewar mai DAMAGARAN ya sa bata fito ba sai da ya fice ta biyo baya , ya zamo a lokacin da zahra'u ke fadin" Wallahi ba zai yiwu ba, babu y'ar da ta isa ta takura maki mu kyaleta, y'ar gidan waye ita? To ko me take takama da shi zamu nuna mata muma mun isa, a kan me za'a maki sharin zuwa inda take bayan ke asibiti kika je? Ta kwaso iyayenta a saka ki a gaba a maki me to? Salon su fi karfinki su duka ko? To dan ubanta zamu tardata mu ji abinda take nufi da ke, ta yi daya ba kari, babu wanda ya isa ya daga maki hankali dan an ga Bama nan!"

Ummukulsum dake rike da hannun NAJEEBA ta ce" Yayama za'a yi wai ace wai wata bare ce ake sauraro sama da maganar Najeeba a gidan nan?, ke yau ba zan iya barci ba idan ban gani gani ga yarinyar nan ba, harda Shari? A ina ta ga NAJEEBAN? A ina,? Ke daina kukan hakanan, a kan zaki musu kuka? Wallahi basu isa ba baki dayansu basu isa ba"

Ummulkhair ta gyada kai ta karaso ta zauna tana duban su ta ce" Lalle, tabas kuwa da kun gane Allah daya ne, saboda wannan da kuke gani a jiya ta je inda yarinyar nan take kuma ita din ce ta sumar da ita din"

NAJEEBA ta kalleta hakama su zahra'u suka kali ummulkhair da sauri da kuma mamakin furucinta

Zahra'u ta ce" Ummulkhair yar uwarki zaki yiwa Shari?"

Ummulkhair ta dubi NAJEEBA ta ce" Shari na maki?"

NAJEEBA ta juya idanuwanta ta dauketa sama da kasa ta watsar da idanuwanta kafin ta mike tana yan wake wakenta zata cire dan kwalin kanta

Zahra'u ta yi sankare kafin ta tafa hannu da karfi ta ce" La ila ha ilalahu Muhammadu rasululahi Sallallahu alaihi Wa salam, ke, dan ubanki ina hawayen?"

Ummulkhulsum ta mike tana bude baki hadi da dafe haba ta ce" Dama ba kukan gaske kike yi ba?, innalilahi na shiga uku, NAJEEBA? Dama kin je din? A ina kika samu yan daba? A ina kika hadu da su? NAJEEBA dama ke din ce kika je? Yaya aka yi to wayar ki ta amsa kuwa a asibiti? Yaya aka yi Sarkin bulala ya ganki a asibiti? Najeeba Sarkin bulala karya ya yiwa uban gidansa saboda ke?, NAJEEBA dama kukan karya kike yi? Innalilahi na shiga uku, yau kuwa sai na fadawa Anmy "

Najeeba ta dubeta da sauri ta ce" Kasheta kike so ki yi? Kin san dai yana iya buga mata zuciya ko?"

Zahra'u ta haye saman gadon ta karasa inda take ta shakota ta rike da kyau ta ce" Dan ubanki kin san da haka kika yi? Da aka kamaki fa?????"

Najeeba ta fara karkari ta ce" Zahra dukanki zan yi cikani cikani!"

Ummulkhair a guje ta haye ta kama ta raba tana fadin" Ke idan tana da ciki fa???"
NAJEEBA da karfi ta ce" Banda, banda komai, banda ciki, idan ma ina da shi din zan zubar masa da abinsa idan ya so ya huta da Ni mai gaba daya, so nake yi ya sakeni, so nake yi ya sawake min...., ni ni SHAHEED zai ce na zubarwa da cikinsa? Ashe arniya wace bata tsoron Allah yake daukana? Ashe kallon da SHAHEED yake min kenan? Ashe ko kisa akace masa na yi ba zai nemi bincike ba zai mikani?, Ni aka cewa SHAHEED a halin da nake ciki zan sa a dauko wata dan ina kishinta? Ashe shaheed ya tsane Ni? Ashe SHAHEED zaune yake da Ni dan biyayya wa iyayenmu? Na rantse sai ya sakeni, da kansa zai sawake min, ina nan zai sakeni, idan shaheed bai sakeni ba sai na gigita tunaninsa, na gaji, na gaji da zamowa kullum ta biyu a cikin alfarmarsa, so? Son karya? Karya yake yi,".......

Ta yi luuuuuuuuuu saboda jirin dake son kayar da ita, muryarta a raunane ta fashe da kukan da ya sa gaba dayansu tsorata saboda na yanzu kam tun daga cikin zuciyarta yake fitowa
A raunane ainun ta ce" Sai da ya sa na gama sabawa da shi zai saka kafa ya harbeni?, sai da ya da na gama sabawa cewar ina iya samun wani gurbin komai kankantarsa a duniyarsa zai nuna min ba haka ba?, Ni SHAHEED zai ce na zubar da cikinsa? Ina kyautata zaton ko Ni na fada masa sai ya hukuntani......saboda Ni ai ina sonsa.....dama kana kin hada jini da wanda kake so ne? Har shege ake halastawa a hadu da balakin duniya dan karfin SO, ashe shi SHAHEED a lokacin da ya sakani a irin wannan halin yana cen yana soyaya da wata? Ni SHAHEED zai kara maimaita abinda ya min da Nadiya a lokacin da ya SAKANI a wani hali????, me yake nufi? Ba zan iya rayuwa babu shi ba? Me yake nufi? Na yi lalacewar wasu matan da suke zaune ana gana musu azabar duniya kala kala? Yana tunanin har ba zan iya kai karar kaina wajen Allah ba idan na nace masa? Karya ne! Bai isa ba, bai isa ba.......wayo Allahna zuciyata innalilahi wa Inna ilaihi raj'une Ni da so sai dai in ce Allah ya isa, ina rokon Allah ya saka min tsakanina da so, ....wayo Allahna....."

Da sauri ummulkhair ta duka ta rukunkumeta tana fashewa da kukan itama ta ce" Najeeba, haba najeebanmu, dan Allah ki yi hakuri, tabas an wulakantaki, Ama ki yi hakuri Najeeba dan Allah "

NAJEEBA ta dago idanuwanta da suka hade da hawaye ta ce" Na daina hakurin, idan har baku tsaya ya bani takardata ba ku din da kanku sai na hukuntaku, kun ji na rantse na gama zama da SHAHEED!"

Zahra'u ta karaso ta ce" Najeeba, saki? Uhum, saki? A ina? Saki a gidan nan? To ai tunda har aka daura kin san saki sai dai in mutuwa yayi ko kika mutu, dan kuwa abinda zai janyo maki saki a wajensa abu ne da har wajen Allah kin gama lalata komai bale a duniya! Dan haka ki yi hakuri mu nemi mafita dan Allah kar ki daga mana hankali"

NAJEEBA ta yi tsit da kukan da take yi tana duban ta, kwarai an riga an yi mata auren da yake da karfin tsiya, bayan karfinsa na auren sarki, da karfinsa na zumunci..........., kwarai idan har tace abinda take nema a yanzu kenan ba ?aramin abu zata aikata da zai bata haka ba? Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une......a yanzu fa, zaunar da ita ne yayi a gaban Anmy da iyayen wannan marar mutuncin ya tuhumeta a kan laifin da akace ta yi?, da ace ta bar wata kafar da zai tabbatar da ta aikata din, shin da wani hukunci zai yanke mata??????,

Wannan tunanin ya sa ta mike ta yi bayi ta barsu sunna kallon kofar da ta shige

Da kyar zahra'u ta kalli ummulkhair dake kuka ta ce" ki yi hakuri da kukan haka, ranta ne a bace, dole zamu ringa yi mata uzuri a yanzu, saboda du abinda ya shafi Sultan bata daukansa da wasa, in sha Allah zata daina rigimar nan"

Ummukulsum ta girgiza kai tana dubanta ta ce" bana tunanin zata daina, idan har bamu yi gaggawar sanarwa ummi abinda ke karra hauhawa ba ina tsoron a je inda ba zamu iya tsawatarwa ba, saboda furucin saki daga bakinta ba karamin abu bane"

Zahra'u ta yi shiru kafin ta langwabar da kai, a sanyaye ta ce" Ko shi din muke tardawa? Ko kuma mu fara samun haya Dayabu?, rabonsa da gidan nan tunda ya zo da fadan nan cewar shi in dai yarinyar nan ce za'a aura shima baya so, muka ce masa ba huruminsa bane wannan, yau kwana biyu fa sai dai a waya kawai yake tambayar Najeeba"

Ummulkhair a raunane ta ce" Fushi yake yi ko? To in ba yaya ba idan yayi fushi ya barmu da wa? Ai wanda zai yiwa fushin baima san yana yi ba, kuma sai tsoro, dan yadda yake tsoron yaya abin har mamaki yake bani"

Zahra'u ta sauke ajiyar zuciya ta zauna ta ce" In sha Allah gobe gobe zamu je a yi mata hoton cikin nan, ba sai mun jira sati biyu ba, abinda aka gani kawai sai mu zo mu ga abinda ya dace mu yi, fara bani wayata in yi kiran yaya Dayabu, ya zo goben mu je tare da magariba in sha Allah, ba zan iya rigimar Najeeba ba, gaba daya ta hade Ummi da Abiey, ba zan iya ba Ni kadai"


A bayi kuwa tunda Najeeba ta shige ta hade bayanta jikin kofar bayin a hankali ta lumshe idanuwanta kirjinta na daukan zafi da wani bacin rai na daban ....

A hankali ta maimaita " Saki? "

Hannunta ta dauka ta kai wajen lebenta, a hankali ta shafa ta sake fadin kalmar........
Tabas daci bakinta ke dauka duk idan ta ambaci kalmar nan,.........wani irin haushinsa ke tukota duk idan ta hango zaman da likitar nan ta yi tana wani laudi wai itama gata a gaban saurayinta......, a hankali ta yatsine fuska tana mai tabbatarwa kanta in sha Allah in dai likita ta zamo gonar da SHAHEED zai shiga, bi izinilah ita kuwa sai ta zama gonar da ba tasa ba, sai dai a mutu, ta shirya zata yi yaki da duk wanda yace ba haka ba!.....

Ta sake rintse idanuwanta cike da dacin zuciya na irin abinda yayi mata ta sake furta" In sha Allah, sai na rikita duniyarta, ba wajen kilacewa ba, Allah ya sa kabari zaka haka ka sakata sai na tonota...., zan nuna mata ita karamar Y'ar duniya ce!"
Ta yi kwafa tana jin takaicinta na raguwa saboda kukan da ta yi ta ji sanyi, haka kuma lokaci daya har ta gama hango wani abin da zata yiwa IZRANE.....zata yi bayani ne!

A lokacin da ta zo wanke fuskar ta har ta duka ta fara wankewa ta dago da sauri Nadiya na fado mata a rai
A hankali ta rufe bakinta saboda dariyar da ta so kubce mata, sai kuma ta langwabar da ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?kanta a ranta ta ayyana ' Aya nadidina, ke ko irin koyon halayyar abokin zama ba zaki yi ba? Yaya za'a yi ki furta wannan maganar kuma ki so in bi bayanki? Ai mun nuna rashin tarbiyya nadidina...., barima in zo mu sha kukan mu dan na san kina cen kina sheka shi , su nadiya an san ciwon kishiya.......'

Gamawa ta yi ta fito daga bayin, sai dai du yadda ta so ta fice hanata suka yi, karshema sai kwontawa ta yi ta musu shiru kawai tana kallonsu dan gaba suka sakata sunna ta yi mata firar da bata tambaya Bama.


SULTAN
A lokacin da ya karasa dakinsa na barci direct ya isa wajen madubin dake jikin bango wanda Najeeba ce ta da aka makala nata shi Wan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login