Showing 114001 words to 117000 words out of 144591 words

Chapter 39 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2343

bata tunanin a ilimin Najeeba zata yarda ta haWa Allah da waninsa..... Bale a hanyar da ba ta neman lafiya ba ba ta komai ba, ita gide tsabar tsoron ta aikata abu ya je ya dawo a kamata da shi ya fi komai tsaye mata a zuciya, tana matukar tsoron ta aikata abu irin wannan ta shiga uku, tsananin tsoron ta aikata laifin da mijinta zai kamata da shi ya fi komai rinjayarta, ita ba mahaukaciya bace, ta san wacece Najeeba a duniyar SULTAN, ta san cewa ba lalle ne Najeeba ta kasa yafe laifi idan an yi mata ba, Ama tana da tabbacin shi ba zai yafe laifin da aka yiwa najeebansa ba!, lokutan da suke samun dan sabanin da zai rufe Najeeba da fada ya bata gaskiya lokuta hudu ne, a duk lokutan nan sai ta gwammace kida da karatu, domin idan har abin ya taba zuciyar Najeeba sosai har ta dage masa kafa na kwana biyu ita kuwa a lokacin take gane Allah daya ne, domin ?arara zai nuna halin da duniyarsa take ciki, halin da zuciyarsa take ciki, halin da aka saka shi a ciki, a baibai zai ringa nuna cewar ana so a saka rayuwarsa a halin kaka naka yi, a baibai zai ringa takurawa da takurawarsa harma ya sa ita ta shiga halin tashin hankali da zulumi, domin Akoy fadan da suka yi bata kuma ganin fara'ar fuskarsa ba har sai da suka shirya, saboda a lokacin da Najeeba ta yi kuka sosai tace to ita kam ta bari da Allah bayan ta yi tafiyarta babu irin fadan da itama bai yi mata ba, ya sanar da ita cewar kar ta yarda ta dauki katsewar da yake yiwa NAJEEBA matsayin makamin da zata cin mata, idan har ta yarda ya kawo hankalinsa kacokam a kanta ya gane cewar tana da wani kamasho na fitinar dake kunuwa a tsakaninsu tabas idan ya bata baya sai ta raina kanta, a ranar ne kuma ya yi tafiyar da suka rasa inda ya je har sai da suka ga tana shirin saukarsa suka gane cewar sun shirya kansu.....
........idan ya rufe Najeeba da fadan ta yi mata ba dai-dai ba zaka ga NAJEEBAN tamkar zata haukace , domin gaba daya a fuskarta tashin hankalinta yake bayyana, haka kuma takan ce a yi hakuri sai idan abun ya tabbata sosai sai tace ta barwa Allah, wannan lamarin ke gigitashi harma ya gaza rike fushinsa na lokuta da yawa......kwarai yana matukar daukan wannan matakin ne dan ya nuna yana adalci, yana damkar wuyan wace wuyansa ke hannunta ne dan ya nuna babu abinda ta isa ta yi, yana iya yinsa ne dan ya sani zama da mace sama da daya ya riga ya riki wuyansa, wannan dalili ya sa ita din ma take taka tsantsan da du wani abin da zai ja doguwar magana a tsarin rayuwarsu

"Baki ce komai ba" Aunty ta fada tana duba wayar da shirun yayi yawa

Nadiya ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Idan kun zo bikin gobe in sha Allah ma yi maganar a nutse Aunty, koma meya ma gani, yaya Winkin nawa ya kuwa gama su Aunty? Kin san cewa goben nan zasu yi ta hawa ne , bana so in zama koma baya, kuma yanzu Ni kwaliyar ma ban san wa zai min ba!"

Aunty ta ce" Eh ai da kansa ma ya kawo dinkunan , kuma baki gani ba sun dinku sosai, to kwalliya ku da kuke da saloon a fada ko kwaliyar ma ba za'a maki ba dan an raina ki?"

Nadiya ta ce" Ai Aunty banma yi mata maganar kwaliyar ba da na je muka yi wannan ba dadin, kuma na san da wahala in samu AIDA in ba ita ta sa ta zo ba kin san itace uwar gidanta ai"

Aunty ta ja tsaki ta ce" Shi yasa tun farko na so ki samu wata mai kula da ke daban, Yayama za'a yi Ni yo in hada abin gyara da kishiya? , idan kina so sai in kawo maki mai kwalliya tunda asubahi, in kina iya sakawa a bude mana hanyar shigowa da wuri, ta ga ba su kadai suka iya kwalliya da kafa dauri ba kawai sai sun fito su ganki das da ke"

Nadiya ta yi dan murmushi ta ce" Aunty kenan, to Shikenan bari in tambayo shi idan zai sa a bude maku da duku dukun kawai ki kawo min mai kwaliyar ta wuni a nan tana kula da Ni, saboda fa bikin nan sai kace haihuwar farko, ko kuma cikin Ni ko ita wani ne ya haihu inaga harda Sarkin agadaz zai sauka gobe, wa ya san shi da wa zai zo, Duda wannan yar tasa yanzu ance ta zama abar tausayi, Ama Ni tsoronta nake, wai Aunty baki ga ba rashin kunyar da su ummulkhair suka yi min, ai sai na gwada musu Ni ba Sa'arsu bace sa'ar Najeeba ce saboda ita muke auren miji daya da ita"

Aunty ta ce" Ko ita ke ba sa'arta bace! A kan me zaki wani ce ke sa'ar kishiya ce?, cen da yawarta, Ama ke ai sa'ar mijinki ce tunda shi kike aure, Ni wallahi mamakin da kike bani, ke kawai haka Allah yayi ki , Allah ya sawwaka Ama gaskiya Nadiya kina da aiki, kina zaune da makirar mace matsayin kishiya Ama kuma baki iya ruwan da zaki fida kanki ba, ki yi aniya kowace banza ta taka ki a gidan da mijinki yake sarki ke sarauniya, ke in ba dan ina tsaye ba da Najeeban nan sai ta kwace ya'yan nan ma gaba daya sun zama nata....."

Hudubar da suka yi ta yiwa juna da neman mafita kenan kafin Nadiya ta shiga dakin ta ta cenza tufafi ta saka turare ta duba wajen su Aliyu ta same shi yana barci, sannan ta nufi bangaren SULTAN saboda yada auntynta ta kara mata kwarin gwuiwa ta kuma sa ta je ta sa a bude musu kofar baya da asubahi dan su samu shigowa da wace zata yi mata kwalliyar taron sunan babyn da za'a yi a washe gari.


A lokacin da ta karasa har falonsa na karshe baya nan, hakan ya sa ta shige dakin sa na barci Bayan ta yi Salama sanan ta shiga dubawa ko zata ganshi

A tsaye ta same shi kusan turarukansa , ya gama shafawa ne zai kwonta saboda ya san wunin gobe idan muna cikin masu rai zai zamo wuni ne mai dauke da hayaniya da kwaramniya da kai kawon jama'a fiye da yada aka saba, shi yasa zai samu yayi barci ya dan huta kafin ya tashi ibadar neman lahira wace ta fi duniya tabbata.

Amsa salamarta yayi yana kai hannunsa ya kunna fitila mai haske sosai da kula ya furta" Anmyn Aliyu, baki kwonta ba"

Nadiya ta yi MURMUSHI, saboda idan yayi kiranta da Anmyn Aliyun nan wani farin ciki take ji a ranta

Karasowa ta yi ina ya zauna ta zauna kadan tana furta" A'a Abiey Aliyu, a gaba dai"

Yayi dan MURMUSHI yana matsawa kadan saboda sun matsewa juna waje, cen kasa kasa ya ce" Ta dace ace kin kwonta, kin san ai za'a yi taro a gidan gobe ko? "

Nadiya ta gyada kai ta ce" Eh yanzu zan kwonta in sha Allah,.....dama , cewa na yi , zuwa ne na yi wai......"

Sai kuma ta Wan yi shiru dan ta rasa hanyar bi

Shi din ma shirun ya fara yi, a ransa yana ayyana ' Nadiya Akoy neman fitina, yauma ai ba ranar girkinta bane, bana son abinda zai ringa zamowa cece ku ce , ita kuma tana da son a yi ta tuna mata abu'

Nadiya ta gama tunaninta ta ce" Dama ina so ne a budewa su Aunty kofar baya ta bangaren saloon din NAJEEBA dan su shigo da wuri goben idan Allah ya nuna mana"

Sultan ya yi dan MURMUSHI ya ce" To ai wannan din ba damuwa bane, sunna iya zuwa, masu kula da saloon din ma ai kamar karfe takwas tuni an basu dama sun shigo ko?"

Nadiya ta gyada kai ta ce" Eh, Ama Ni so nake yi su din su shigo tun karfe biyar da rabi haka"

Da dan mamaki ya ce" Biyar da rabi fa kika ce? To ai ko gama sallah ba'a yi ba a wasu masalatan, lafiya dai?"

Nadiya ta Wan sosa keyarta, a hankali ta ce" Lafiya kalau, ina so ne a kawo min wace zata min kwalliya da wuri wuri, ka san idan ba'a fara da wuri ba, ba za'a gama da wuri ba ranka ya dade"

Zuba mata ido yayi na yan dakiku kafin ya dauke kansa zuciyarsa na neman hautsinewa, saboda wasu lokutan idan abin ya hade masa da cikin gida kansa zafi yake dauka sosai, bale idan abin ya tabo masa kahon zuciya direct sai ya ji kamar numfashinsa zai iya tsayawa dan tashin hankali da rashin mafitar da ta dace da shi!

Me yasa mata suke da fitina ne? Me yasa suke da neman rigima ne? Me yasa suke da riko ne? Me yasa suke da son manta ALKHAIRi ne? Me yasa suke da gaggawar fushi da saurin hawa ne? Me yasa suka cika son kansu fiye da wanin su wasu lokutan ne????????????????????


A tunaninsa, idan har bai manta ba, yawancin lokuta idan Akoy taro a familly din nan, sukan fito karfe takwas saura cikin shigar da suka gama SHIRYAWA..........
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




40


A tunaninsa, idan har bai manta ba, yawancin lokuta idan Akoy taro a familly din nan, sukan fito karfe takwas saura cikin shigar da suka gama shiryawa.....wace ya taba tambayar to wai a yaushe ake yin kwalliya da sauran su? A nan ne ya san cewar Najeeba nada gaggawar kwalliya , domin ko ta amarya bai wuce ta daukar mata minti ashirin ba bale ta yan cin biki......., to ko dai wani abin ya faru tsakaninta da Najeeban ne???

Da kula ya ce" Wani abu ya faru tsakaninki da beebah ne?"

Nadiya ta Dube shi, sai kuma ta kali kasa, ta yi haka har sau biyu kafin ta sauke ajiyar zuciya, maimakun ta zagaye ta tsaya a kan bukatarta dan hakan take so a yi mata, sai ta ce" Ni ban san me na yi mata da har take nemana da masifa ba, ka dai ga a gidan nan Ni bana nemanta da tashin hankali ko kadan, Ama ita ba ruwanta abu kadan sai ta nemi daga min hankali, wai har ta iya ce min wai ba ruwanta da yaran nan ta bar min y'ayana?????????"

Kirjinsa sai da ya buga da furucin nan na karshe.........

Ya'ya.....duniyar iyaye
Ya'ya karshen zance kenan

Sai dai kuma wace ake maganar tace ba zata kuma duban ya'yansa ba, itace mutun ta farko bayan Anmy da yake da yakinin yana raye ko ya mutu tana nan domin ya'yansa, yana da yakinin koda ya'ya dari zai samu da mata dari zata zama uwa daya jal ma kowane , ko dan zumunci, hakan ya sa ya dubi Nadiya da kula ya ce" Nadiya"

Nadiya ta Dube shi tana amsawa itama

A hankali ya ce" Zaki iya fada min Fisabililahi me ya haWa ki da ita????"

Nadiya ta yi shiru na dan lokaci tana ta aunawa a ranta dan kar aje ta balowa kanta ruwa, sai dai ta gama aunawa ta gane cewar a abinda zata fada gaskiya da gaskiyar kenan kuma babu abinda ta yi da zata bata masa rai sai ta ce" Ni kam ban san takamaiman abinda ya faru ba, abinda na sani shine tun ranar karshe da muka yi zama a bangaren ta na karshen mako da ta amshi Aliyu sai ta cire masa shadar da na saka masa dan ka gani na dinka masa irin shadar nan da nake kwasa a nan du idan an kawo dinkunan ka, sai kawai ta tube masa tun kafin ka ganin, Ni kuma nace mata bana son irin hakanan, tun daga lokacin na ga yanayin ta ya cenza, karshema sai ta sa andiya ta ba Abdallah shadar aka dawo da ita ta cire masa kayan da ta saka masa aka mayar ta bani shi da shadar , to Ni tun daga ranar ma fa ban kuma ganin ta dauke shi ba, kuma tun daga ranar ko doguwar magana bamu kuma yi da ita ba, to ko yanzu ma fa da na zo falo har na gaisheka na ganta a coridor nake zolayarta nace ana wani nuna ana yi maka fushi ashema ba haka bane, shine fa ta sake nunan ba ruwana da ita harda cewa in daina yi mata tambayoyi tunda ba Ni na ajiyeta ba, shi yasa Ni kuma banma yi mata maganar kwaliyata ba kawai nace Aunty ta kawo min mai kwaliyar..........."

Magana take yi yana kallon ta, har ta dire aya , ta sake bude baki ta ce" Kwanaki fa akace ta yi bari, babu irin yadda ban yi dan gane abinda yake faruwa ba, ashe dai cikin na nan, Ni kam ban san me take nufi ba, Ama ko menene gaskiya Ni ba ruwana ta yi haka ta ga dama ai!"

Idannuwansa ya dauke daga kanta yana sauke ajiyar zuciya a boye yana dubanta a tausashe ya ce" Tun yaushe hakan ke faruwa a tsakaninku? Itama tana hana ki hulda da su Muhammad Kenan?"

Nadiya ta girgiza kai ta ce" A'a, gaskiya, to su ai Bama a ganinsu in ba zuwa aka yi wajen Anmy ba, kuma ita ba ruwanta da wannan"

Mamaki ya kama Sultan, a hankali ya ce" To ke, me yasa ranki ya bace dan kawai ban ga shigar da kika masa ba? Kin tabbata wannan kadai ne ko Akoy wani abin?"

Nadiya ta yi shiru, a hankali ta girgiza kai

Sultan ya Wan murza gaban goshinsa, a hankali ya sauke numfashi ya ce" Nadiya........, kina nufin saboda wannan ne kika nunawa mai son danki ta maki shishigi?????"

Nadiya ta zuba masa ido

Ya gyara zama saboda doguwar maganar da zai yi ya ce" Nadiya......, zan lamunci komai banda wannan, kin ga, ko ke ko ita ba zan taba yarda wata ta kawo min hanyar da za'a samu rarabewar kan y'ayana a cikin gidan nan ba, ina iya hakura da kowace a cikinku in hade y'ayana in musu tarbiyya......... Nadiya a kan me zaki nemi ki fido hanyar da zai sa ta guji duban ya'yanki bayan ya'yan Wan uwanta ne ko ba aure tsakanina da ita wanda zai bata damar zama mamansu saboda tana aurena tana da ikon zama mamansu saboda jinina ce ita.....???"

Gaban Nadiya ya fara faduwa saboda yadda ya tsareta da ido

A hankali ya girgiza kansa ya sassauta saboda ya fara fahimtar da wahala idan Nadiya a kan tunaninta ta ke, ta yiwu wani na tayata tunani, dan haka a tausashe ya ce" Nadiya, bana tunanin zata yi wani abu da zai cutar maki da ya'yanki kin ji?, kar ki yarda ki kawo abinda ran kowa zai Saci domin in har zaki fadi gaskiya itama ta haifa kuma nata ya'yan ba zasu taba hadata da kowa ba ko?, to me yasa ke zaki nuna ke kika fi son naki? .............., idan har kika dubi WA'INDA suka bata tarbiyya kin san basu bata wace zata tsani ya'yanki dan sunna ya'yan abokiyar zamanta ba, bayan wannan Nadiya kina ganin yada suke rayuwa, kusan kowane da mamansa ita da yan uwanta, Ama kin ga yadda kansu yake hade ko......?"

Nadiya ta gyada kanta

Sultan ya ce" Haka nake son ganin su Muhammad, da Abdallah, da Aliyu, da su Nayla da Anmy sun zama , PLZ kar in sake jin irin wannan daga wajenki ok?????"

Nadiya ta rasa yaya zata yi da ya wuce amsawa harma ta bashi hakuri

Yana duban ta yana karantar idan har ta gane abinda yake nufi, sai dai irin yadda du hankalinta ke rarrabe ya sa ya gane idan ma ta gane din ba duka ba, Akoy abinda ke ranta

A tausashe bayan ya riko hannayenta yana dubanta ya ce" Kina da damar sanyo mai maki gyara, mai yi maki abinku na mata , ba dole sai a wajen beebah ba, dama ke kika zabi na wajenta saboda kin ce Akoy experience a wajen ko????"

Nadiya ta gyada kai, jininta du a mace, ba zata manta lokacin da auntynta ta nuna zasu daukar mata abone na masu gyara tun daga kan kitso, kunshi, gyaran fata da sauransu ba, a lokacin ita da kanta ta yi ta dariya tace cabdijan ai in meye zata yi a Saloon din Najeeba, bcz a yanzu a damagaran dai, shine numba one, wanda sai Macen da ta isa da kanta take zuwa, babu abinda basa yi, dan idan budget din ki karami ne dama ba wajen da zaki je bane, ko dan ki yi hotuna na garari kya ziyarci SPAR din Najeeba MUTALAB, dan lokaci lokaci take cenza d?coration na komai , harta wajen hotuna idan an yi mak'up ba daya bane, ba biyu ba........., shi yasa tunda aka kafa wajen yake cin record har yanzu kuma bai yi baya ba dan Akoy riko da gaskiya da tsayawa tsayin daka wajen kwarewa da aiki gamsashe......., sai yanzu ma take tunanin to wace zata yi mata kwalliyar a damagaran ne ta ganta zanzan kamar yadda Najeeba ko Nadiya suka san kan fukarta??????????????


A tausashe SULTAN yace" Beeban ki ce fa, Najeeban ki ce fa....., aminiyarki ce............."

Ya dan lumshe idannuwansa, dan ya sani ne shi kam shara'a domin ta ya zo duniya, a waje yayi da karfin murya a daka ya yi da rarashi ko zai samu yadda yake so da masu mulki, asalin masu mulkin , wato Mata, dan haka ya ce" Bana tunanin Akoy wani da zai fadi halayanta a kawayenta sama da ke......, ki yiwa kanki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login