Showing 111001 words to 114000 words out of 144591 words

Chapter 38 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2352

yake zuwa harda na mai ciki, da na mai jego, da na bazawara, da na amarya, da na uwar gida sarautar mata, gyara ne mai motsa gwonji ya motsa mara koda baki da muradi zaki samu muradin nan tashi daya, uhum....lalle Najeeba ta taso da tashi mai zafin gaske a lokacin da ta riki Y'ar mutan Nijar matsayin Aminiya suka kule suka yi siri harma ta watso mata duniyar gyara mai gigita mai gida ( SAMEERA HARUN NO : 85991223)

Masu shan na sha suka shiga shan abinsu, masu shiga na ruwan zafi suka shige abinsu, masu hawa kujerar tsuguno nan da nan suka haye abinsu, wato dai a ya'yan Anmy idan har ka dace da daya ka gama dacewa sai a rufe kofa kawai, domin bayan sun gama aika kayan tsumi sun gasa wajen gasawa sai suka hau gyaran fata da gyaran gashi, ya zamo du wace keda bukatar yin dilka ta hade kayanta ta yi abinta , wace kuwa gyaran kai ne tuni an kankama, abinka da ba hannun mutum daya ba, kuma du sun iya abinsu sai ya zamo nan da nan sunna gyara junna har magariba ta sanyo kai, aka yi sallah , suka gabatar da isha'i sannan du suka cenza tufafin da suka zo da su dan cenzawa idan sun gama kafin su fito suka bar yan saloon da gyara su kuwa suka dauki hanyar bangaren Anmy


Ita humura, wata siri ce mai rike zuciyar duk wani wanda ya ji kanshinta, humura kuwa sunna suka tara, idan har humura kike so ki samu humura mai sanyin kanshi, mai kama fata da tufafi, ki dana mata sansanyan turaran wuta mai dauke da dolar a cikinsa, idan kika yi haka ina mai tabbatar maki ba wai hancin abokin rayuwa ba, harta hancin abokiyar rayuwa sai kin girgiza, dan kuwa wajen da kika zauna kansa sai ya bar shedar kanshin ki, ( Kin shirya?, muna da humura, muna da turaran wutar, ke dai idan kin shirya ki tuntubi Yar mutan Nijar wato SAJIDA Nijar 93811618, PLZ Ama ki shirya=??)

Tun daga nesa kanshin yan matan nan ke fara yi maka Salama, Danma Allah ya sa su Dukansu sanye da nikaf suke, haka kuma tunda suka fito suka samu dogarai na gadi, sunne suka share musu hanya har zuwa bangaren Anmy a lokacin da suka bude musu baban kofar falon Anmy ne suka dakata, ya zamo Najeeba na dan sauraron bayanan jakadiya tana tafiya ba tare da ta tsaya ba saboda a gajiye take, so take yi kawai ta jita saman bed, Danma sun yi salolinsu, ba kuma yinwa a tare da su, da ta ga jikin Anmy ta gana da yaranta take da burin hayewa saman bed din ta dan ta huta...........

Ya zamo ne kamar tana tsakiyar su Aunty zahra'u, kuma tsakanin falon da dakin Anmy ne ke da Akoy coridor din nasu dakin, hakan ya sa suke tafe sunna dan tsayawa har ta kawo daidai corridor din zata yiwa jakadiya magana ta ji gaba daya an jata cikin coridor din wanda hakan ya sa ta budi baki zata tsala ihu, sai dai bai bata damar haka ba sakamakon bayana da yayi a fuskarta harma ya bude mata nikaf din ta suka hada ido

Ummukulsum da ta shigo da gudu ganin an ja y'ar uwarsu kamar za'a yi kijmashin din ta, da karfin gudun da ta shigo din ta fita tana zaro ido ta dauki hanyar dakin Anmy kasa kasa tana furta " Kar ku shiga, Mai DAMAGARAN ne "

Sai ya zamo sauran sun bi bayanta da gudu, jakadiya kuwa ta yi baya itama har kamar zata kifa da gudu gudunta

Irin yada kirjinta ke bugawa tunda suka hada ido da shi, harta idanuwanta sai suka so yin rawa irin na marmare.....

Da kyar ta iya aro duk wata jarumtarta ta sauke idannuwanta cikin nasa, gashin girar nan da ta saka kuwa suka karawa idannuwan nata wani irin kwarjini da haske, leben bakinta kuwa dama tunda ta yi gyaran fuska shima ta yi masa nasa gyaran da yake kara masa color din pink, hakan ya sa ya sake yin pink ba tare da ta saka jan lebe ba , sai dan man leben da ta mulka masa wanda ke sake saka masa daukan ido da wartar zuciya

A dake ta furta" Lafiya?"

Sultan ya sake duban lebenta, hadi da lumshe idannuwansa, cen kasa kasa ya furta" Ita ta fi yawa"

NAJEEBA ta gyatsina gefen kuncin ta hadi da furta" Ina so in tafiyata wajen ANMYNA"

Sai da ta dire maganar sannan ta kawar da kai da abin daukan yannayin bacin rai

MURMUSHI yayi a hankali ya furta" Bakya ganin ya dace ki sassauta fushin hakanan?, nace na amshi laifina Beebahhhhhhhhhhh "

NAJEEBA ta Dube shi cikin ido, a hankali ta ce" Ai ba laifinka nake so ka amsa ba, so nake yi in samu dalilin da zai tabbatar da Ni bazawara....., daga nan zaka zamo cikin masu bada aurena a wajen wanda zai san daraja..................."

A cikin zuciyarta ta idasa maganar sakamakon hade bakinsa da yayi da nata a hankali ya rike da kyau ta yadda a dole ta yi saranda tana kikifta ido tana sha?ar numfashinsa, wanda hakan ke sauka cikin zuciyarta yana kwontawa , uwa uba du kanshin da ta dauko sai ya garwaye da nasa ya zamo dole zaka ji kamshin turaransa a jikinta

A hankali ya cika mata baki, idannuwansa lumshe sosai yana kallon fuskar ta ta karkashin ido

Murya cen ciki ya furta" Bana tunanin, wani zai kuma min wannan gangancin ba tare da na sauke harshen sa kasa ba....."

Gabanta ya buga, saboda irin yadda ya gaza bude idannuwansa ma bale har ya iya control din fushinsa, hakan ya sa ta ringa kokarin son ganin sun rabu lafiya saboda ita ta fi kowa sanin me hakan yake nufi

A hankali ya dan dago da yatsarsa kusan lebenta , cen cikin ya ce" Ba laifi bane ki yi fushi, ba laifi bane ki hora ni, ba laifi bane ki ja zarenki yadda kike so beebah.....but......."

Da kyar ya iya dan buda idannuwansa da suka tabbatar mata da jan da suka dauka a yanzu yanzu, ya dora da fadin" Laifi ne ki hada kanki da wani, bayan ina raye Beebah......, laifi ne baba ki danganta kanki da wani bayan ke tsaftataciya ce beebah......, idan kuwa har yanzu kina shakun soyayata ne ......Shikenan Beebahhhhhhhhhhh........."

Daga haka ya dan ja baya ya sake lumshe idannuwansa sosai sannan ya juya da nufin tafiyarsa

Cen ciki Najeeba ta iya budar bakinta bayan hawaye ya bi gefe da gefen kumatunta a hankali ta furta " Laifin da kake gani, nima shi na fi tsana SHAHEED!, laifin da ka gama dauka a duniyar ka cewar ba laifi bane, nima a tawa duniyar laifi ne....., to inma ba don kai ba , laifin nan Ni fa harda aminiyata ka aikata min shi, ai ko a yanzu na baka damar ka dauko amintaciyar da ta saka ka kasa dubana a gadon asibiti ......, ta yaya ma za'a ce min wai dan ta shiga alfarmar rigarta aka yarda da ita?????, idan ma ta shiga alfarmar rigar Tata ta shiga harda zuciyar wanda yake nesa da ita nisa mai girman gaske......., yaushe ma wancen zata samu layin Mai DAMAGARAN?, .........in dai ba za'a tauye Ni ba a hana Ni fadin nawa laifin da nake ganin ba laifi bane nima kamar yadda na yi koyi da manyana...., sai a bani dama in kamanta......"

Da sauri ta yi shiru sakamakon juyowar da yayi, harma ta ja baya tana shirin ko ta kwana

Sai dai irin duban da yayi mata zuciyarta ta nemi karaya harma ta sada kanta kirjinta na dokawa

Bata ji motsin fitarsa ba, sai Muryar matarsa da ta shigo da sauri tana waige waige

Gannin najeeba a tsaye ta tsaya tana dubanta ta ce " Ai, Najeeba, ashe ke ce a nan? Gaske na ga Mai DAMAGARAN ya fito daga nan din, ashe dai ke ce"

Cikin dabara Najeeba ta share hawayenta, harma ta kakaro MURMUSHI hadi da dago idannuwanta ta zubawa Nadiya ido, kafin ta daga kafa ta zo zata wuce ta gefen Nadiyar

Nadiya ta kasa hakuri tana dubanta hadi da sake tabbatarwa kanta cewar ai kuwa da ita ne yake saboda ga kanshin turaransa nan futuk a jikinta, ta ce" to wai Ni abinda na kasa fahimta,dama ba wani fada kuka yi ba kuke nuna kun yi fada ne? "

Najeeba ta dakata ta juyo tana dubanta ta ce" Pardon?"

Nadiya ta ce" Najeeba nan fa kika nuna bakwa magana har nake zuwa a ranakun da ba nawa Bama bangarensa kuma bana ganin ke din kin je, Ama kuma yanzu sai in ga du ba haka ba, shine nake mamakin wani sabon salon ne kuma ? In ba wannan ba menene na nuna min bakwa magana bayan kuna yi????"

Mamaki ya gama kama Najeeba, ikon Allah, wai me yake damun nadiya ne? Dama ta gama sanin cewa Nadiya Akoy baranci, sai dai bata yi tunanin zata bari barancinta ya Kaita aikata aiki irin na wace bata da kwakwaluwa ba!

Kai ta dauke ta juya zata yi tafiyarta domin har ta fito falo sosai a lokacin da yan matan suka nufo Najeeba da tarin murnar ganinta suka rungumeta

A hankali take shafa kansu, MURMUSHI a kwance saman fuskarta a tausashe ta ce" Naylana yaya karatu?"

Nayla ta ce" Alhamdulilah momy, kwana biyu ban ganki ba, yau a wajenki zan kwana PLZ momy kar mama ta hana Ni Ni dai bin ki zan yi"

NAJEEBA ta sakar mata MURMUSHI a tausashe ta ce" My baby, ba hanaki mamanki zata yi ba ai, karatu ne nake so ki yi sosai, kin ga yau nima a nan zan kwana, gobe sai mu kwana a wajena in sha Allah kin ji?"

Nayla ta gyada kai ba dan ranta ya so ba

NAJEEBA ta dubi anmy karama ta ce" ANMYNA, ja kanwarki ku je ciki wajen su Auta, in an jima sai a kai ku wajen mamanku "

Da girmamawa yarinyar ta kama hannun Nayla suka nufi ciki, Najeeba ta dake kada kai zata yi tafiyarta a nan Nadiya ta ce" Najeeba wai me yasa kike son wulakantani ne? Yaya za'a yi ina maki tambaya kina share Ni kamar wace zaki bani rai?"

Najeeba ta rintse idanuwanta, ta juyo yannayinta a cenje ta nuno Nadiya da yatsa ta ce" Kin ga, ki fita harkata tun kafin in baje maki nawa kalar haukan kin ji?, ki barni haka , wai meye wannan masifar, ke kawai tunda kika yi aure maganarki sai ta sake lalacewa kika zama baki da tunanin kanki? Ki kula Ni ba shashasha bace da zan zauna da ke muna hawa muna saukowa ba!, bayan wannan duk wani abu da kike tunani, ko in ce da har kike bada fuska ana saka maki a kwakwaluwa a kaina ki dauka ni baya gabana, ya'yanki kuwa shima ki sakawa ranki na bar maki kayan ki!, !"

Rai bace ta sake dubanta ta ce" Nadiya, baki ajiyeni ba, ba dan ke nake zaune ba, ki kiyaye rayuwata ta siri, ki kiyaye yi min tambayoyin da hankalina ba zasu dauka ba, babu abinda ya shafe ki da yadda nake zaune da shi, kamar yada babu ab????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? inda ya shafe ni da yada kike zaune da shi, respect yr slf PLZ!"

Daga haka ta yi ciki ta bar Nadiya tsaye sai huruwa take kamar zata fashe

Ta daga murya ta ce" To sai me, kar ki taba min yaran mana, sai me, to dama Ni ina ruwana da wai wata rayuwarki ta siri, munafuntata aka yi nake tambayar ba'asi bayan wannan meye a ciki, kema kin yi ciki zaki fara yi min dagin kai ko? Nima ai zan yi cikin sai in ga ta tsiya!"

Daga haka itama ta wuce ta nufi bangaren ta sai fada take yi, dan kuwa ko abinda ya kawotan bata yi ba, domin zuwa ta yi fa dan ta cewa Najeeban gobe aida ta zo bangarenta ta yi mata mak'up da safe, saboda ta san su sa yiwa junansu, ita kuma ba zata shiga cikinsu ba dan ta kula nemanta suke da masifa so suke su kawo mata raini, zata kama kanta ta nuna musu itama matar ?a?ansu ce ba Sa'ar yinsu bace, shine fa ta ga fitowarsa daga hanyar da zata iya cewa ita tunda ta zo gidan nan bata taba ganin ya bi hanyar ba, kuma gashi ko da ta gaishe shi yan yatsu kawai ya daga mata bai ce mata komai ba, shine ta leka dan ta ga abinda yake faruwa shine ta ga Najeeba a tsaye , uhum dama tastuniyar gizo ai bata wuce ta koki , sunna abu kamar wasu sabin aure ko soyayar samari da yan mata

Rashin madafa ne? Neman mafita ne? Ko kuwa tsabar rashin sanin mahanga ne???? A lokacin da Nadiya ta kadaice kanta sai ta yi kiran KANWAR mahaifiyarta ta labarta mata dukan abinda yake faruwa tun daga kan jiya har zuwa yau

A matsayin kanwar mahaifiyarta na Macen da ya dace ace tana sakata a hanya mai bilewa, sai ta shiga kora mata bayanan da ta saba wa'inda a ganinta itama da su ne zata ci yakin wannan zama mai wuyar sha'ani ta ce"......
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




39


A dake Aunty ta ce" Nadiya, wai kina nufin cikinta bai zube ba?"

Nadiya ta ce" Wallahi Aunty Akoy ciki, kuma abinda yake kara bakanta min rai wannan salon da suka dauko suke nuna min basa jituwa bayan ba haka bane, uwa uba Aunty so yake yi fa ta nuna ba ruwanta da ya'yan nan, to in ba bata da gaskiya ba meye dan na kare y'ayana? Tunda ta tube Aliyu na nuna rashin jin dadina take wasu abubuwa!"

"Hum Nadiya kenan, ina tsoron a lokacin da zaku bada kai dari bisa dari a abinda nake nuna muku da wannan matar kar ya zamo lokaci ya gama kure muku, saboda Ni na gama ganewa wacece Najeeba MUTALAB tun lokacin da kuke ?awance bale yanzu da kuka hada miji!"

Aunty ta fada ranta bace ta dora da fadin" Ko a lokacin da kuke zuwa gidan nan ke da ita , a lokacin dan uwanki ya nuna yana sonta ki duba ki ga yadda take wani MURMUSHI irin na ta raina shin nan, Ama ke a haka kina rawar jiki kina murna ,ko magana kika yi irin yadda Najeeba ke MURMUSHI ta girgiza kai kece Bakya ganin hakan a matsayin wani abin, Ama ita ta gama raina maki wayo kin zamo abin sakata nishadi ne , kin zamo irin tana tafe da ke ne kawai dan nishadinta ba wai dan ta auna hankalinki da nata ba, tana maki wayo ke kuwa kina kakaba dariya da sakin jiki a zuwan kawarki ce aminiyarki ce!"

Nadiya ta ce" Aunty, wallahi ba haka bane, kin san menene Ni na san Najeeba, kuma Ni abinda yake bani mamaki kin ga kafin aurensu bata da makiyi sama da shi, Duda dan uwanta ne Ama yanzu sai in ringa ganin kamar haushina take ji, ba na fada maki ranar da ya mana maganar karin auren nan abinda tace min ba?, bayan ta sani sarai Ni ai ba makiyiyarta bace!"

Takaici kam ya gama kama Aunty, a dakenta ta ce" Kin san Allah Nadiya da ace ke din nan wata ce cen ba jinina ba, da ko magana ba zan kuma maki ba a duniya, saboda irin yadda kike nuna halayyar nan naki kamar rainon gauro!, Nadiya KULUN saka ki a hanya nake Ama tsabar fitina idan kika tashi kika fadi wata maganar sai in rasa to ke ina ake saka maki tunaninki ne, yanzu kika gama fada min cewa harta ya'yanki ta nuna ba ruwanta da su, Ama kuma ina tunatar da ke dama zumuncinku ke ce ke shan wahala ke ce a ciki, kuna tafe ne kamar uban gida da Wan gidansa kin wani tareni zaki kareta? To ai sai ki, ba'a cenzawa tuwo suna dai, Najeeba kishiyarki ce, bakin cikinki take yi, bakin cikin ya'yan da kika haifa fiye da nata take yi, idan da so samu ta yi Aliyu kar ya rayu, idan ta ita ne karma a kuma jin labarin ki daga ke har ya'yanki, in zaki bada hadin kai a yi abinda ya dace ki bada, cikinta babu abinda ba za'a iya yi masa ba, a kwontar da shi, a salwantar da shi kamar yadda ta salwantar da Aliyu, a nuna mata ba ita kadai ta san hanyar da ake bi a ja kunnen kishiya marar mutunci ba, in kuma kin ga ba haka ba Shikenan Ama Ni gaskiya idan har ba zaki daukarwa kanki matakin da ya dace da zama da kishiyar nan taki ba ki bani lafiya hakanan da maganarta dan Ni kike cusawa bakin ciki ke kuma kina zubewa tana taka ki!"

Nadiya ta jima tana sauraron auntynta, kuma har ga Allah gaba daya gaskiyar maganar take gani zuwa yanzu, sai dai cen kasan zuciyarta ta fi ganewa bari da Allah a kan ta bi bokaye a lalata cikin Najeeba, ita da kanta ta san Najeeba na iya aikata komai banda bin bokaye, kawarta ce ta kud da kud, tare suke yawonsu, a shagonta take wuni idan sun fito kuma ta kawota har gida, wani lokacin har gidan Abiey take kwana, haka itama wani lokacin har gidan su take kwana, ta sha mayarwa da samarin Najeeba amsa kafin aurensu, ta sha rike wayar Najeeba fin wuni a hannunta, ta san cewa Najeeba nada fitina, tana da fada, tana da neman magana, Ama bata san Najeeba da leke leken wajen bokaye ba, Duda mutun na cenzawa, rayuwa na cenza dan adam, yau da gobe sai Allah, Ama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login