Showing 69001 words to 72000 words out of 144591 words

Chapter 24 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2340

bakinki da kiran wata da sunan karuwanci, ya'ya mata Allah ya bamu, koda bamu da ya'ya mata kar ki manta bayan wani na iya zamowa karshen wani, ba kyau izgilanci idan haka halinta ki bita da addu'a Nadiya "

Nadiya ta sake kallon NAJEEBA, gaba daya kamar ba Najeeba ba, wai bata kishin mijinsu ne? Bata jin haushi ne????????,

Zata kuma yin magana zahra'u ta karaso itama cikin shigar alfarmar ta dakata ta ce" Shawara ake yi ta yan uwa?, to ku dakatar haka ku zo , MAI MARTABA ya karaso, kowa ya iso falo"

Nadiya ta juyo tana fadin" Aunty zahra'u harda mutanen nan? Mazan nan ko?"

Zahra'u ta ce" Eh, ai inaga kowa ya zo fa"

Nadiya ta gyada kai, ta yi kwafa ta ce" Zan je, wallahi babu abinda ta isa ta min, kuma in hakane nima zan kirayi iyayena ne ai"

Aunty zahra'u ta ce" Nadiya, wani abin yake faruwa ne?, kuma iyayenki ANMY ba mamanki bace?"

Nadiya ta yi takwaf takwaf da fuska kafin ta juya kamar zata fashe da kuka ta yi gaba

Ido hudu suka yi Najeeba da zahra'u, kafin Najeeba ta koma ciki

Zahra'u ta ce" Ke uban me zaki nema a cikin ne wai?"

NAJEEBA ta ce" Mayafi zan dauko ko a haka kike so in je kuma in janyowa kaina wata fitinar?"

Zahra'u ta gyada kai ta ce" Hakane kuma, sai kin fito"

Ta juya ta koma saboda ta tsaya a yi srvng din mutanen dake falon, da abinci da abin sha kamar yadda suka tsara ita da yan uwanta"

A nutse take tafe bayan ta Wora wata Golding din alkyaba saman shara shara sosai, wace bata boye narkaken lesh din dake kasan suturarta ba, haka kuma bata boye irin daurin dan kwallin da ta kafa a saman kanta ba, sannan gashin dake kwance a bayanta shima lumbuk baki sidik ya bayyana, uwa uba kwaliyar da ta gama haskata wace idan ka kaleta sai ka sake cike da tunanin shin wai da wane ya fi kyau cikin kalolin nan biyu? Dan kuwa tsaf tunanin cewa farar fata ta fi bak'a kyau zai bace a harshenka, domin a gabanka ne zaka ga kyau iya kyau........

A nutse ta shigo falon, a cen kasan makoshinta ta yi salama hadi da cire dogon takalmin dake kafarta daf da cafet din farko, wanda ake goge kafa a kansa kafin a isa cafet din falon

Kusan kowa ya amsa salamarta, Bama kamar Anmy dake zaune saman hakimtaciyar kujera mai zaman mutun guda, gefenta maganin NAJEEBA ne na dare da bata sha ba , sannan da farko fuskarta a hade take , saboda tunda ta fito ta samu ainihin bakin dake falon sai ranta ya bace, bata san me ake nufi ba, Abinda ta sani daya ne ba zata taba yarda da duk wani raini da za'a kawo mata cikin ahalinta ba, tsabar raini yarinyar nan a saman kujera ta fito ta sameta, sai da jakadiya ta saukar da ita kasa sannan ta zauna a kasa, gaba daya bata san dalili ba yannayin yarinyar bai yi mata ba


Tunda NAJEEBA ta tunkaro falon gaban IZRANE ya yanke ya fadi, domin lokaci daya kamar dawowar walkiya buga kanta da ta yi Jiya ya gilma mata, sai da ta rintse ido kafin ta hade kafafuwanta ta rike hannayenta da kyau dan samun kwarin gwuiwa, sai dai du yadda ta so kawar da kan nata abin ya gagara sakamakon irin yadda shigar NAJEEBAN ke janyo ido kanta dan dole da dole.......uwa uba irin alkyabar dake jikinsa shima fara ce mai ratsin Golding, sai ya zamo kamar sun yi zasu saka fari hadi da Golding a yau

A nutse ta doshe shi, a hankali idanuwanta cikin nasa........

Tunda ta doso shi, zuciyarsa ke daidai cewa daidaiya tana bugawa tamkar ya shigo fili da katon dakarin da zasu yi yakin kwatar rai

Shigarta ta firgita duniyarsa, sannan ta rike zuciyarsa fiye da kima, dan kuwa ta matukar tsaye masa a kahon zuka harma yake ganin ai shigar nan tasa ce, shi mijinta ba wace zata fito filin Shari'a da ita ba

A hankali ta duka, irin dukawar da ta sa alkyabarta bajewa sosai, ta dukar da kanta, hadi da sada idannuwanta kasa sosai, a hankali ta furta" Barka da warhaka......Sh.......sha..............Yayah "

Ta karashe tana dago idannuwanta ta saka cikin nasa kafin ta sakar masa hararan da iya shi ne ya gani dan kuwa alkyabarta ta yiwa sauran iyaka da gaban fuskarta

Mikawa ta yi bayan jakadiya dake duke ta amsa gaisuwar da ta yi, sannan ta juya ta koma daf da Anmy ta kai zaune jikin kafar Anmy sannan ta Wora kanta saman cinyar anmyn

ANMY ta dauko maganinta , ta bale hadi da Waukan faro din nan a lokacin da Sultan ya dubi bakin nan ya basu damar fadin abinda yake tafe da su, sannan idannuwansa suka sauka a kan Mata mafi soyuwa a duniyarsa da zuciyarsa a lokacin da Anmy ta sakarwa NAJEEBA harara saboda kin amsar maganin da ta miko mata sannan ta mata alamun ta bude baki, ta bude din ta saka mata maganin hadi da bude ruwan ta kafa mata a bakinta, ta hadiye ta mayar da kanta saman kafar Anmy wace ke shafa kan nata tana kallon IZRANE da ta bude baki bayan ta sake gaisar da shi cikin irin Tata kisar, wace ko daya bai ji gaisuwar ba har sai da ta fashe da kukan abinda ya faru da ita ya maido dubansa kanta dan kukan gaba daya dakin ya dauka, kukan da yake kira na jahilci domin ta tsani ya ji irin kukan nan sama sama kamar rai zai fita.....

IZRANE ta ce" Wallahi na rantse da Allah da Annabi da fitowar rana........da"


" Ki katse doguwar rantsuwa, a wajen da kake da gaskiya baka farawa da rantsuwa, .....Mai DAMAGARAN adali ne, zai saurareki koda baki rantse ba" Sarkin bulala da aka ba damar shigowa ya katse ta da sauri saboda ya tabbata idan ta mika da wannan rantsuwar, ba lalle ne ya ci gaba da zama a nan ba, tsaf zai mike ya yi tafiyarsa.

Inda inda ta yi, sai kuma ta ce" To ai na zata idan na rantse an fi yarda, Ama Shikenan, tunda ga shedu nan, dama a Jiya da safe Nadiya ce ta fara kirana ta zazageni ta uwa ta uba, umana ce shaida saboda a lokacin da na tsorata ina kuka ita ta rarasheni tace tunda zan auri mijinta dole in yi hakuri in kyaleta zata daina zagina, zagi babu wanda bata min ba harda alkawarin sai ta kasheni....."

Nadiya ta zabura tana zaro ido da karfi ta ce" Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, Allah tsinewa mai karya!"

SHAHEED ya dubeta da sauri, hakan ya sa ta duka ta rarafa kusa da Najeeba ta zauna ta yi kiskirim jikinta na daukan rawa....., to wannan ai shegiyar karya kenan, an mata karya, za'a cuceta, za'a wulakantata innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, yau za'a yita a gidan nan,

IZRANE ta Wora da fadin" Sai kawai Jiya da dare, Najeeba ta tardani gidan aminiyata da yan daba, suka yi mana dukan tsiya, gatanan aminiyar tawa itace shaida domin hatta mijinta sai da yace ba zai yarda ba sai ya daukaka kara an bi mana hakinmu "

Mijin Hajiya ya dubi IZRANE da duba irin na jin haushi ya tare maganarta ya ce" Allah ya kiyaye, Ni tardoku na yi kuna iface iface a gidana, bani da shedar komai, hasalima Ni ba zan ja Shari'a da NAJEEBA ba, ai ko ba komai Akoy zumunci tsakanina da ita"

SULTAN ya Dube shi da sauri, da duban da ya saka Sarkin bulala zaburowa Sama sama ya daga bulalar hannunsa ya sauke a gadon bayan lauya, rai bace ya daga zai sake sauke masa NAJEEBA ta bude baki ta ce"




22
A tausashe ta ce" Ya isa haka sarki"

Da sauri Sultan ya maido dubansa kanta a lokacin da lauya ya sa ihun tashin hankali har ya
ya nemi baza burgima a kasa

Kasa Sarkin bulala ya kai Muryarsa a daken Nan ya ce" Yaro nake a gaban manyana GIWAR babana, Yaro nake a dakin nan yaron manyana Allah ya kara maki lafiya, wani zumunci yake ikirarin fada tsakaninsa da GIWAR uban gidana? Karya yake talaka dan talaka ya shigo layin sarkinsa, To ai Allah ne ya saka tazara a tsakani tunda yayi umarnin a yiwa shuwagabani biyaya....wanene shi da zai yi furuci da sunan da uban gidana yake yin furuci dan duban halalinsa? Ba zan juri duba da duban uban gidana a lokacin da amo ke shiga kunnayensa ba, raina fansa ne a gaban duk wani wanda ya nemi daga hankalin mai bautar Allah adali, ja gaban talakawa.......Allah ya huci zuciyar mai wukar yanka, Allah ya huci zuciyar Mai DAMAGARAN umarninka yana gaba da na giwarka, in sauke kansa daga gangar jikinsa ko shakeshi kake so in yi?"

NAJEEBA ta kalli Anmy da sauri, bata ko kalli inda SHAHEED din yake ba bale har ta ga idannuwansa

Anmy ta dauke dubanta daga fuskar NAJEEBA ta sauke kan Fuskar SHAHEED

A hankali ta sada dubanta daga cikin nasa a tausashe ta furta" Allah ya huci zuciyar Mai DAMAGARAN"

Sarkin bulala ya dauka da karfin da ya sa du bakon abin sada kai da tsoron Muryar, Lauya kuwa tuni ya shige tsakiyar matarsa da IZRANE ba tare da ya gane hakan ba, bayansa kuwa ji yake yi kamar ba nasa ba tsabar zafin bulalar nan

ANMY ta sake fadin" Allah ya sanyaya zuciyar Gudaliya Dan muhamadu"

Sarkin bulala ya sake maimaita wa yana sake dukawa hadi da dukan kirjinsa ya kuma rike bulalar nan yana sake sauke jajayen idannuwansa a kan Lauya , wanda kasa kasa ya sake ri?e hijabin matarsa kamar zai saki fitsari a zaune

Anmy ta sake tausasa muryarta ta ce" Sarkin bulala ka je daga waje, Sarkin garin damagaran ya yafe furucin da aka yi daga bakina"

Sarkin bulala ya sada kansa ya ce" Yafiya ta tabbata daga bakin wace ta isa, Allah ya kara maki lafiya mai baban daki"

Daga haka ya juya ya fice ya ja ya tsaya a kofar falon ba tare da ya rufe kofar ba

Idannuwansa ya janye a kan fuskarta ya maida kan IZRANE, hadi da duban Aminiyar Tata da ta yi kira da kuma mijin aminiyar Tata harda iyayenta da suka yi masu rakiya wa'inda suke faman langwabar da kai uwa kadangaru, mahaifinta cike da bacin rai da tashin hankalin irin yadda yarinyar nan ke son saka shi a masifa, abokinsa na tausarsa kasa kasa

ANMY ta mayar da dubanta kan IZRANE, wace mamakinta ya gama kama zuciyarta, tunani take yi wannan kuma wace irin kadara ce zata tunkaro ahalinta ? A ganninta sam bata ga wani abu da zai sa yarinyar nan ta shigo gidan sarauta ba

A tausashe Anmy ta ce" Nan din gidan adalci kika zo, kuma in dai an cuta maki ya zamo kina da huja, koda Najeeba ce sai ta fuskanci hukuncin da ya dace da ita"

Anmy ta dubi NAJEEBA, sannan ta dubi Nadiya, a nutse ta ce" Menene shedar ki na zagin da Gimbiya Nadiya ta ya maki?"

IZRANE ta sada kai ta ce" Allah ya kara maki lafiya, ita din da kanta zata iya tunawa, in kuwa ta ?aryata zan iya kunna inda ta yi zagin"

Anmy ta dubi Nadiya, ta ce" Zaki iya kwatar kanki, ko kuma kin aikata laifin da akace kin yi?"

Nadiya ta dubi NAJEEBA, ta kai dubanta kan SULTAN da idannuwansa ke kallon kasa

Muryarta a sanyaye hadi da abin kuka ta ce" Anmy, tsabar kishin mijinmu ne ya sa muka aikata haka, na tabbata da ace a gaban Gimbiya NAJEEBA na yi kiranta ma da zagin da zamu yi mata sai ya fi haka Anmy, ko Gimbiya NAJEEBA?"

Najeeba ta zuba mata ido, gaba daya mamakin nadiya ya gama kasheta, wai dan Allah ina hankalin Nadiya yake zuwa ne? Kalau take kuwa????

A hankali ta dauke idanuwanta tana girgiza kai

Nadiya ta dubeta da mamaki ta ce" NAJEEBA? Yi magana mana?"

Najeeba ta dubeta, a tausashe ta ce" A'a, ba zan aikata haka saboda kishi ba gaskiya, to ai aure ne yace zai yi, kuma ba ita tace a aureta dan dole ba, wannan ba hurumina bane , ai babu abinda zai hadani da wata mace saboda zata auri mijin................k"

Nadiya ta kusa suma a zaune tana kallon NAJEEBA, kwal ubancen, ita NAJEEBA zata kwayewa baya? Wani irin ba zata iya yin fada a kan Sultan ba? Bayan irin yadda suke jin haushin IZRANE ne?, a gabanta fa suka kusan dukan IZRANE din, ai ta zata ita nata mai sauki ne , na Najeeba sai ta kusan halaka IZRANE din, ama sai Najeeba ke fadin haka?

Anmy ta ce" Subahanalah, nadiya da bakinki kike fadin haka?, yaushe rabon duniya da irin wannan kishin?, dan kawai MIJINKI zai auri wata sai ki yi kiranta ki zageta? Me yasa bakwa tunani ne ya'yan zamani? Ke da za'a zo a tarar, a girmama ki a darajanta ki, kin yi kiran wace zata shigo matsayin kanwarki kin zageta ta rama, wani irin girma kike tunanin samu idan zaman ya tabbata?, zagin zai hana a auro maki ita ne ko menene?, furucin kin ce zaki kasheta kin yi ko baki yi ba?"

Nadiya ta sada kai hawaye na wanke fuskar ta ta ce" Ban yi ba Anmy, Ni dai na san nace mata zamu ci......"

"Yi min shiru, kar ki yarda ki karasa zagi a nan" Anmy ta katse ta a lokacin da Najeeba ta kame baki saboda dariyar da ta tukota

Anmy ta ce " Kar na kuma ji, daraja gareki, koda yau MIJINKI ba sarki bane auren dake wuyan ki ya baki daraja mai karfin gaske da ya dace ace kin kiyaye aikata wasu abubuwan da zasu zubar maki da mutunci ya kuma zubar da na mijinki!, ki kula, sannan a kiyaye furucin baki, domin shi baki shi yake yanka wuya, "

Anmy ta juya wajen IZRANE da iyayenta ta ce" Ku yi hakuri, in sha Allah ba zata kuma kiran wayarta da sunan neman fitina ba, sai dai dan su yi zumunci"

Mahaifin IZRANE ya sada kai ya ce" Muna sake bada hakuri Gimbiya, dama abinda ya kawo mu dan mu kara nada hakuri ne kamar yadda muka bayar kwanakin baya, saboda Bama son rigimar ta mika haka, domin nan din gida ne na kowa da za'a amshi ALKHAIRi ba a ji tsoro ba, kuma a lokacin da aka kirayeni sunna asibiti hankalina tashe da na je ne na samu abinda ya faru dan bamu da nisa sosai da gidan aminiyar Tata shine na yi kira na sanar dan a taushi abin a rarashi mai baban daki"

ANMY ta gyada kai, cike da iza ta sauke dubanta a kan NAJEEBA, sannan ta sake dubansa, a hankali ta ce" Shin ba'a kai umarnin kilacewa wa likita bane?"

Gaban izrane ya yanke ya fadi, da sauri ta kalli mahaifinta da ya budi baki ya ce" An kai"

Anmy ta dago ta Dube su baki daya ta ce" Ba'a fadi girma da darajar abinda zai hau kanta bane ?"

Nanma ya bada amsar an fada

Anmy ta Dube su muryarta na kausasa ta ce" Menene girman abinda ya sa, ta take dokar nan, ta fita waje?, abin ya shafi rai da mutuwa ne????"

Nanma Kowa yayi shiru, wanda hakan ya tabbatarwa Anmy fita ce ta ganin dama, dan haka ta kalli SULTAN da ya dubi IZRANE din shima , sannan ta Wora da fadin" Menene shedar ki bayananiya na cewa Gimbiya NAJEEBA ce ta je inda kike?"

IZRANE ta bude baki ta ce" Na rantse itace, a lokacin da ta shakeni na ganeta, fuskarta ce, da jar abaya , ta dakeni kafin ta sumar da Ni"

NAJEEBA ta dubeta da mamaki har tana zaro ido, kafin ta girgiza kai ta sada kanta, wanda hakan a kan idannuwan mai DAMAGARAN, domin dama yakan daga ya dubeta ne ya mayar da dubansa

Anmy ta ce" Jar abaya?, wace iri ce Jar abaya bayan a Jiya da ta fita abayar dake jikinta bak'a ce?, sannan da ta fita daga nan asibiti ta je direct tare da Sarkin bulala wanda ya tabbatar da kasantuwarta a nan ko ba haka ba?"

Ta fada tana duban Sultan, wanda ya gyada kansa ya sake soke kai

Anmy ta ce" Ita da wa kika gani din? A daidai wani lokaci ne?"

Gaba daya IZRANE sai ta rasa bakin magana, tsoro take yi ta fadi lokacin ace ashe da dare ne ta fitan, haka kuma ita ai NAJEEBA kadai ta gani a wajen jiya, dan haka a raunane ta ce" Ita kadai ne na gani Anmy"

Anmy ta dauki maganin NAJEEBA, ta mike zata nufi wajen SULTAN, ya mike da sauri ya karaso ya rage tsayinsa ya amshi maganin sannan ya tsaya yana dubawa a lokacin da anmy ta ce" Ni dai na san ita ba aljanna bace bale ta kasance a waje biyu a lokaci guda, sai dai ban sani ba ko haka din ne, wannan fa kake ganin maganin da docter Halima ta kaita wajen docter A'isha aka rubuta mata ne na athsma, wanda aka cenza mata ne, a Jiya ummulkhair ce ta yi mata rakiya asibitin, kuma rashin lafiya ne ya Kaita, sannan shigar ma da take nufin ta ganta da ita ba da ita ta fita ba gaskiya, dan haka a sake dubawa a nemo wa'inda suka kai hari, ba Najeeba bace"

IZRANE kamar ta cira take ji, gaba daya hankalinta kamar ba a jikinta yake ba, tashin hankalin da ba'a saka masa rana, gashi dai an mata laifin kuma kiri kiri an take? Yau ita ta ga masifa, ita ta ga balaki, yau ta yarda da maganar Hajiya Turai a kan wannan Yar balakin.......lalle ta yarda sai ta sake shiryawa in dai wannan zata tunkaro.

A nutse ya ajiye maganin a lokacin kuma suka hada ido da NAJEEBA, ido cikin ido

Kakausan kallon da ya sakar mata ya sa ta sada idannuwanta tana turo bakinta

Mikewa yayi ya je ya zauna saman kujera a nutse ya bi matansa da kallo, ya dubi Anmy, sannan ya kalli mutanen dake falon...........

A hankali ya ce" Du Wanda ya san babu abinda ya shafe shi a maganar nan ya fita"

Lauya ya fara zabura yayi gaba yana duban Hajiya Turai ya ce" Sai ki zo mu je in ci kakan ubanki kafin ki je gidanku yau"

Kasa kasa ya fada, ita da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login