Showing 84001 words to 87000 words out of 144591 words

Chapter 29 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2331

YA'YA NI KUWA? AI SAI DAI IN KASHE SU DAN MAKASHIYA CE NI, NA BARKA LAFIYA*"

Taga taga din da yayi zai kifa a kas ya ankarar da shi cewar jiri ne ke son maka keyarsa da kasa

Shi dai a saninsa bashi da cutar huka ko kadan, sai dai cikin ikon Allah ya ji rawanin dake fuskarsa zai tsayar da numfashinsa ta hanyar rike masa kirji da karfin gaske da kuma done masa hanci

Hannunsa ya saka ya cire rawanin ya sake shi a nan, sannan ya juya ba tare da ya dauki sandar dake hannunsa ba ya je falonta ya dauki wayar dake jikin bango yayi kiran Sarkin waya

Sarkin waya na dagawa ya ce" A datse kofofin fada, ba shiga ba fita"

Sarkin fada bai riga ya bada amsa ba ya katse kiran, da wani irin saurin da bai san cewa sarautarsa na iya barinsa yi ba ya ringa bin dakunan ta, sai dai harta kicin din ta ya duba babu ita babu alamunta

Da wani irin sauri ya fice , ba tare da ya gane cewar Babar kofa ya bi ba, ba rawani ba sanda ya fito daga Sangaren ta ya nufi na Anmy idannuwansa na sake cenza kala

Du wani mutumen dake giftawa sai kasa ya kai ya sada kai saboda irin yadda Mai DAMAGARAN ya fito ba rawani babu sandar hannunsa kuma fuskarsa kamar hadarin gabas, haka kuma nan da nan aka dana ?atuwar karaurawar da ake yin sanarwa a fadar , lokaci daya amon Sarkin murya ta karade fadar lungu da sako ana sanarwar cewa duk wanda ya shigo ya rike ?afarsa, wanda bai shigo kuwa ya yi baya, ba shiga ba fita daga bakin mai DAMAGARAN ,

Wannan sanarwar ta sa du inda wani mai bada tsaro a lafiyar mai damagaran ya garzayo bangaren Anmy, ciki harda yan zagayen gidan domin du tunaninsu wani ke son kawowa mai wukar yanka hari


Sarkin bulala na bude masa baban falon Anmy ya rufe ya ja ya tsaya yana muzurai da jiran ko ta kwana

Bangaren yan matan Anmy ya nufa kansa tsaye ya bude ya shiga da salama a bakinsa

Kusan du sunna warwatse ne a dakin dan jiran sallah suke yi su gabatar kafin su nufi wani uzurin, sai gannin Mai DAMAGARAN suka yi a kansu

Rige rigen saukowa suke yi dan gaisar da shi, sai dai bai basu wannan damar ba da Muryar da basu taba saninsa da ita ba ya ce" Wr is BEEBAH!?"

A tsorace zahra'u ta dago ta Dube shi, a hankali ta ce" Allah ya kara maka lafiya, Bata dawo ba daga kiran da aka yi mata"

Sultan ya lumshe idannuwansa ya bude a kan zahra'u, a hankali ya ce" Zahra....... Kar ku boye min ita plz.....nima Wan uwanku ne"

A tsorace du suka ringa satar kallon sa, zahra'u kuwa jikinta ya fara daukan rawa, ta ce" Bamu ganta ba yaya, tun dazu da ta fita, ta yiwu tana dakin Anmy ko ta fita wajen saloon din ta, ko kuma tana wajen su Jakadiya???, ko sun shiga kicin da su Muhammad saboda yace cake dinta yake so.........."

Bai tsaya ya idasa jin abinda take fada ba ya fito da kansa ya dauki hanyar saloon din ta

Tunda ya fito Sarkin bulala ya bude murya yayi sanarwar a bada hanya kuma a kawar da duba......, wannan abin ya sa du wani wanda ya fito komawa sannan wanda abin ya shafa ya sada dubansa

Sai da ya shige gaba sannan suka mara masa baya, tun daga kan Mai rikon bulala, Mai rikon WUKAR babarbara, Mai rikon bulala, Mai rikon sanda har zuwa masu rike da carbi suka nufi saloon din NAJEEBA

Bai tsaya wata wata ba ya shige saloon din , sai dai bai tarar da ita a nan din ba, hakama Aida bata nan sai yaran shagon sunna ta aiki

Fitowa yayi ya ringa bin du inda zahra'u ta fada kafin ya sake komawa bangaren Anmy ya nufi dakin Anmy kansa tsaye ya bude kofar ya shiga

ANMY da ta dawo dan daukan hijabinta ta bi bayansa sakamakon shigowar da zahra'u ta yi hankali tashe ta sanar mata basu ga Najeeba ba, kuma busawar nan da aka yi ta yiwu ta shafeta ne, sannan yanzu Sultan ya fita da kansa ya leko nemanta sai kawai ta ji ta kasa hakurin har ya dawo, su din kuwa ta sa su je har bangaren Najeeban su duba mata, gabanta na faduwa sosai

Juyowar da ta yi idanuwanta suka sauka a kan takardar nan ai sai jiri ya nemi makata da kasa, domin abinda ya fara shiga kwakwalwarta wani tashin hankali suka yi da har ya kai ga saki ita kuma ta gudu

Da sauri ya karasa ya tareta ya zaunar da ita a bakin salayar da ta shinfida

Jikinta na rawa ta saka hannu ta amshi takardar nan ta kasa karantawa tana dubansa ta ce" Sakinta ka yi? Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une"

Sai da zuciyarsa ta buga da jin kalmar nan daga bakin anmy, a hankali ya rike hannayen Anmy yana girgiza kai, Muryarsa cen cikin makoshinsa ya ce" Saki? In saketa in rayu yaya?"

Anmy ta zubawa fuskarsa ido, kirjinta na bugawa

A raunane ta ce" Ne yake faruwa? Kai da na Barka ka bata hakuri? Kai da na Barka ka gane laifinka ka rarasheta? Me ka ce da ita? Me ka yi mata ?"

Sultan ya lumshe idannuwansa, ya girgiza kansa a hankalin nan ya ce" Ban yi mata komai ba, nace mata ta zo mu je bangarena ko nata, dan in bata hakurin ne in rarasheta, sai ta yi maganganu masu zafi ta nufi bangaren ta "

A hankali ya dauki takardar da Anmy ta saki ya bude ya nuna mata , a raunane sosai ya ce" Dubi abinda ta rubuta....., Anmy "

Sai kawai ya dora kansa saman cinyar Anmy

Karantawa Anmy take yi kamar bata gane abinda ake fada

Zahra'u dake tsaye da waya ce ta sake neman iZinin shigowa

ANMY ta dago idannuwanta da suka cika da kwallah ta bata damar shigowa

Irin zaman da yayi kadai ta duba kirjinta ya sake bugawa, ta duka ta mikawa anmy wayar ta ce" Abiey ne"

Da sauri Anmy ta kafa wayar a kunnenta, tun kafin Abiey yayi magana ta ce" Tana wajenka ko yaya? Cen ta je? Ganinan zuwa ganinan"

Abiey ya yi dan Tsai kafin yace" Wace Balkissa ?"

ANMY ta bude idannuwanta da kyau, kafin ta dubi Sultan da ya dago fuskarsa yana kallon ta

A raunane ta ce" Aya, na zata ai ta zo Abiey, na zata yarinyata cen ta nufa Abiey, Shikenan mun kure mata waje ta gudu, innalilahi wa Inna ilaihi raj'une "

Abiey ya mike a tsorace domin tunda yake bai taba jin abinda ya soki zuciyarsa irin wannan ba, idan ka cire rashin iyayensa da kuma yarinyarsa guda ba wa'inda ba za'a hada sensation din nan da komai ba, sai irin wannan sukar da ya ji a yanzu, a hankali ya ringa kama sunnan Allah kafin ya ce" Ki bar kuka haka Balkissa, a fadawa masu tsaro idan mun zo a bari mu shigo, in sha Allah zamu gano inda take, mema aka yi mata? Zamu gano inda take"

Anmy ta ringa gyada kai ta katse kiran da kanta ta kai dubanta inda SULTAN yake , wato a jikinta da irin mamukar da idan ba zata manta ba rabonsa da yayi mata irinta tun a lokacin da ya rasa Mahaifinsa, wanda ya yi mata ita kamar zai raba mata kirji ya shige sai saukar ajiyar zuciyarsa da irin yadda ya ringa ambaton Allah da kuma mahaifinsa idan aka barsu daga ita dai shi

Tausayinsa ne ya nemi shigeta a lokaci daya, koma in ce ya shigeta, saboda irin yadda fatar jikinsa ta dau ja kamar an zuba masa ruwan zafi, haka kuma idannuwansa su dinma sun dau jan sosai da sosai

Sai a yanzu ta kula lokacin sallah ya gama karatowa ta dauke dubanta a kansa kafin ta ce" Ka tashi hakanan, ka je ka mayar da suturar da take kara maka kaimin sarakuntarka.........,"

Ta yi dan shiru tana kallon sa, tausayinsa na son rinjayarta sai dai ta Hanna hakan ta ce" Sarautar nan, itace take kokarin shiga tsakanin ka da macen da a yanzu nima mahaifiyarka na yarda da kana son ta........"

Ta sada kanta tana girgiza kai, ta saka hannu ta share hawayenta ta ce" ka sa a bude kofofin fada ka sa a sassauta tsaro, lokacin sallah kar ya shige laifinka ya yi yawa....... Ka je, idan ka fito daga masallaci sai mu yanke shawarar da ta dace, idan zamu fitar da maganar GIMBIYA NAJEEBA ta gudu ta Barka duniya ta ji, ko kuwa zamu yi shiru mu nemeta ne tsakaninmu kawai?????............ Ya Allah idan a ina Najeeba take ka sa ta ji tausayina ta dawo gida, ya Allah idan a ina ta shiga ka saba idannuwan makiyan mijinta da makiyanta ita da kanta a kanta, ya Allah ga yarinyana, ta fita ban san girman abinda ya sa ta fice ba, Ubangiji ka tsare min ita......"

Sai kawai Anmy ta mike ta dauki hijabin nata ta saka ta je ta dauko carbinta ta ajiye ta zauna tana jira a gama kiran sallah

Mikewa yayi, da kyar yake ganin gabansa ya sake duban Anmy kafin ya juya ya fice a dakin

Yanzu ta coridor din Anmy ya bi ya nufi bangaren sa yana jin yadda jikinsa ke karra neman rikicewa da zafi da kuma radadin zuciya

Wata alwallar ya daura kafin ya yafa rawaninsa ba tare da ya dauki wata sandar ba ya wuce masallacin fadar, domin kunnayensa na jiyo kiran sallah .....




A gidan Abiey

Tunda ya mike ya saki shayin da yake sha mai zafi da tururi shayin ya zubunma ?afarsa Ama ya kasa janye kafar Ummi ta dakatar da shan nata kirjinta na neman hauhawa da tsalen kwado ta zuba masa ido zufa na neman karyo mata sakamakon yannayin yadda yake amsa maganar

A lokacin da ya katse kiran ya kai zaune yana kai hannayensa wajen kansa ya shafa cike da tashin hankalin abinda ya nufo shi ya kalli ummi dake tsoron tambayar ba'asin abinda ya saka shi a wannan halin ya ce"
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




29



ABA MUTALAB ya ce" Najeeba ce ta gudu"

Da sauri Ummi ta Dube shi gabanta na wani irin faduwa, a bayyane ta ce " Guduwa? Ta je ina? A kan me to?"

Aba MUTALAB Muryarsa a birkice ya ce" Har a kan me zaki ce?, yaya za'a yi ki ce min a kan me?, nan na zaunar da ke nace ki fa yiwa yata maganar da zata ji sanyi, ba zai yiwu ace muna tuturata gaba dayanmu ba, Ama kika ki yi, ke a dole idan ba'a biyowa Najeeba ta bayan gida ba ba za'a samu yadda ake so da ita ba, kina manta cewar Najeeba bamu bata irin wannan horon ba, kina manta cewar idan tsanani yayi yawa wani lokacin maimakun a gyara lalatawa ake yi, ke kina son idan abu ne dole in zauna in Dube ki in baki yadda kike so, Ama ita Najeeba ba haka ba, kar ki manta yarinyar nan yaya aka yi aurenta, Ama kuma ta shiga fushi mai girma irin wannan kin ki bada hadin kai wajen ganin an taimaketa, kin je gidan baki zauna da ita ba, gayanan ai abinda ya bada"

Ummi ta sada kai, saboda ganin yadda ya hau, a hankali ta ce" Gani na yi an zauna da ita zama nawa , gani na yi ka samo bayanin da ba lalle ta so jin sauran zancen ba , tunda na tabbata maganar cikin zata fi komai dadada mata zuciya da shi din ma"

Aba MUTALAB ya kare mata kallo ya girgiza kai ya fice fuuuuuuuuuu kamar zai tashi sama yana dana layin Dayabu dan ya tabbata da wahala ta kasa neman layinsa


Ai kuwa yayi mugun rashin Sa'a saboda yaya dayabu dai bai san da zancen bata nan ba sai yanzu, hakan ya sa a rikice ya ce" Abiey, ta gudu? Wallahi ba zan yarda ba, wallahi ba zan yarda ba, Abiey duk abinda take so sai an yi mata saboda itama mutum ce, irin yadda ake zuwa a sakata a gaba daga ita dai Anmy a daga mata hankali ba zai kuma faruwa ba, Abiey ba zan yarda ba!"

Abiey na son dakatar da shi ya katse kiran, hakan ya sa ya gaggauta tada motar a lokacin da Anmy ta karaso da gudu ta shige saboda ta san tsaf zai yi tafiyarsa ya barta

Bata ce komai ba, shima bai ce ba suka dauki hanya, bayan ta barwa mai aikin ta salahun idan Najeeba ta zo basa nan ta sanar mata


Sunna tafe Aba MUTALAB na fada kamar zai ari baki, gaba daya gani yake yi Ummi ta saki role dinta na mahaifiya a wajen Najeeba, idan ka ga ta zauna da Najeeba Najeeban ce ta kure mata waje kuma idan ta fada mata damuwarta sai ta jira Anmy ta sanar mata kafin ta dau matakin abinda ya dace, Ama in sauran ne nan take ta ke zuwa ta san abinda ake ciki harma ta samu mafita, rai a bace ya ce" Ita kuma ta yi yaya kenan? Gidan sarauta take aure, ko ba'a hadata da fadi tashin yau da gobe na fitintinun miji da abokiyar zama ba ya dace ace tana da mai sauraronta na fanin rayuwar yau da gobe na mutanen dake ?ar?ashin su, Ama ina ke komai da ya shafeta sai ki yi shiru ki zuba ido, to idan wani abu ya samu y'ata ba zan kyale ki ba ki san da wannan"

Ummi ta Dube shi ta ce" Aban su, ya dace ka sassauta zuciyarka haka, ba wannan ne zai sa mu gano inda take ba, ba wannan ne zai sa mu san inda ta je ba, kai ka sani ina yin karar nan ne saboda Anmy, yau da ace a lokacin da na dawo Anmy ta sakar min ya'yan nan tabas da na nuna iyawata a kai, Ama ka duba ka gani, a tsaye take a kan lamarin yarinyar nan, kafin ma mu ji wani abun ta yi maganinsa, Shikenan dan nice Sarkin yan son zuciya da rashin kara da rashin godiyar Allah sai in tashi in je in ce me a lamarin da ya shafi SHAHEED da NAJEEBA?, idan har ba zan yi mata fadan ta bi mijinta ba Allah ban yi rashin kunyar da zan ce a kan me ya yi mata wani abu ba, dama yawancin lokuta auren dan uwa ai ya gaji haka, ana haka ba a kanta aka fara ba, wasu lokutan ma bari ka ji, wallahi macen zata rayu ne ba wata kula ta kirki tun daga kan ciyarwa shayarwa tufatarwa kai harma a je kan kula irin ta aurataya ta yau da gobe, Ama dan Wan uwanta ne zaka ga bata isa ta kai kara wajen kowa ba, domin ko a cikin dangi ta samu wani da maganar cibi zai zame mata kari ne, karamar magana sai ta zame mata baba, sai dai ta je ta yi ta rayuwa cikin bakin ciki har daya ya mutu cikin ita da mijin, Ama ita fa? Najeeban ta rasa ci sha ko sutura ne????"

Kuuuu ya ja wani birkin da ya sa ummi kusan doka goshi da gaban mota, ya sauke nata harara kafin ya fice daga motar

Da sauri ta waiga, ashe masallaci ya shiga, ta dafe kirji tana tunanin anya ba sauka zata yi su hade a fadar ba? Sai kuma ta ga kar ya zo musu a haka ba zata taba so yayi wata maganar da zuciyar Balkissa zata daidaice da damuwa da tashin hankali,

A hankali ta saka belt ta daure kanta da kyau ta gyara daurin dan kwalinta ta ja hannayen rigarta domin koda ya ja ta ja su dimi juna a motar nan


Ana gama sallah salatin Annabi kadai yayi da ASTAGAFARI ya fito fuuuuuuuu, ya bude bangaren da take zaune ya nunota da yatsa ya ce "Kar ki kawo min maganar ci, sha ko sutura a gida irin na yarinyata, idan ana so karma a ciyar da ita din mana, ai Ni ban bar y'ayana babu sana'a ba, bale ko shagunanta kadai na cikin gari sun isa su sa ta zama hamshakiya dan dai ina katse ta ne ana saka mata kudaden ta a abin anfani ya sa bana yarda ta ji kanta aljihunta ya isa ya sa ta botsarewa mijinta ba, ki gane ina bin komai a hankali da ?a?ana ne dan saboda rayuwa , Ama idan kuka yarda kuka kaini inda ba zan jura ba rayuka zasu bace, me ta nema? Cewa ta yi bata aikata ba, Ni na yarda da furucinta, saboda bata karya!" Ya fada sama sama

"NAJEEBAN ce bata karya? Cabdijan, to na rantse ai yarinyar nan ta kware wajen lauya karya kuma ta tsaya a kan karyarta har a yarda cewa gaskiya ce, kai fa bari ka ji babansu ko tarar da likitar nan da Anmy ke fadan dan raini har likita ta mata sharin ta tardata gaskiyar kenan, ta tarda likita!"

Aba MUTALAB ya ce" Ok, haka kika ce ko? Mu je fadar!" Ya rufe mata motar da karfi ya zagaya ya bude ya shiga ya warci motar

Ummi ta tare shi tana zaro ido itama, a lokacin da aka basu damar shiga kofar fada ta ce" Me zaka yi? Wai me zaka yi? Sai dai Ni ka min, Ama ka san kanwarka ta fi karfin ka yi mata wani abu a kan ya'yan nan, saboda Ni zan iya saka hannu a wuta idan akace a duba tsakanin kai da ita waye za'a iya yarda Duk rintsi, giyar kudi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login