Showing 36001 words to 39000 words out of 144591 words

Chapter 13 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2341

zaman nan bata komai ba, su Muhammad kuwa da Andiya sun tafi da yaya Dayabu ya mayar da umi sannan ya dawo da su, ya zamo a lokacin da Mai martaba ya shigo bangaren Anmy Anmy din na wajen su Jakadiya sunna idasa magana kan dukkan wani shige da fice da aka yi kwanakin nan da matansa basa yi, tana bada umarnin abinda ya dace da wanda za'a dakatar, a dole ya zauna a falon yana jiran shigowar Anmy kafin ya wuce bangarensa dan gobe monday ce, su Muhammad zasu yi safiyar tafiya makaranta zai gansu tun yau kafin ya shige bangarensa

Fitowa ta yi dauke da tsintsiya irin ta tsayen nan ta shara, da nufin mayar da ita wajenta, sai dai kanshin turaransa da kuma irin yadda falon ya dauki shiru ya sa ta ja ta tsaya a lokacin da ta bayyana a inda bata da damar buya, dole ta kawo gaisuwa domin ya riga da ya ganta

Kallon da ya bita da shi tun daga kan gashin kanta dake daure a tsakiyar kanta, da farar rigar dake jikinta sai wando polo ruwan ash color ya bude sosai daga kasa bayan ya kama kugunta......., sai dan siririn abin hannun da yayi mata kyautarsa tun wata tafiya da yayi Chaina aka kera masa abin da sunnanta, Shikenan ko kunnenta babu dan kunne, Ama irin yadda take daukan ido sai da ya kai zuciyarsa nesa sannan ya dauke idannuwansa a kanta ya gyara zamansa du cikin kame kai danma kar wani abu mai kama da raini ya ratsa tsakaninsu dan shi ai ba sa'an yarinya bane!

Tsintsiyar ta rike itama da kyau kamar ta samu wani hanya fa zata samu kwarin gwuiwa, kafin ta karasa shiga falon a nutse ta Wan dangane tsintsiyar sannan ta sada kanta a tausashe ta furta" Barka da warhaka Dadynsu"

A dole ya sake dago idannuwansa ya sauke a kan fuskarta yana ta jira ya ga ta idasa abinda ko a lokacin da yake tunanin tana tsoronsa bata shayin yi, wato daga idannuwanta da saka idannuwanta cikin nasa tsai ba tare da jin tsoro ko Dar ba.

Hada idannuwan da suka yi ya sa ta so sauke nata da sauri, sai dai tambayar da ya jefo mata ya sa a dole sake saka idannuwan cikin nasa a lokacin da yace" Kin je asibitin?, me suka ce dangane da lafiyar ki????"..........


'ashe har yanzu ya damu da lafiyata? Na zata son ya'ya da son sai an ga laifina ta kowace fuska ya shafe damuwa da duk wani abinda ya shafeni ciki harda lafiyata......uhum rayuwa kennan'

A bayyane kuwa bayan ta samu dukan kwarin gwuiwar da take da bukata ta ce"
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati na airtel ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




12




A bayyane kuwa bayan ta samu dukkan kwarin gwuiwar da take bukata ta ce" Ban je ba, gobe nake son zuwa wata asibitin ba wancen ba"

Da mamaki ya dubeta, a nutse ya ce" kina nufin baki je aka dubaki ba? A kan me?"

Najeeba ta sada dubanta, ta sake sanyayar da muryarta a hankali ta ce " Yau din ban gama samun likitar da nake son zuwa ba, shi yasa nace gobe zan je in sha Allah"

Dubansa ya yi tsauri a kanta, a kausashe ya ce" Zaki je wajenta ta duba ki, ita zata duba ki!"

NAJEEBA ta dago tana dubansa, duban cikin ido, zuciyarta cike da tunanin yaya aka yi du idan Shari'a ta kanta ta biyo baya bata dama ne? Yaya aka yi a matsayinsa na baba da iliminsa da komai, harma ake yi masa shedar adalci Ama idan abu ya biyo ta kanta sai an yi mata rashin adalcin sannan ake biyota da adalcin daga baya, anya ana yi mata adalci kuwa? Anya ana mutuntata kuwa, anya ba tana sanya da addu'a ba kuwa? Tabas sai ta dagewa wannan lamari da addu'a domin kamar laifinta yake nema ido rufe, a tunaninta itace zai ririta, itace zai duba, itace zai kusanta fiye da komai a irin wannan lokacin, itace fa ta rasa gudan jinninta, itace ta rasa lafiyarta, Ama sai ya zamo ita ake son yaka ta dukan hanyar da aka samu??????

A hankali ta mayar da dubanta kasa a tausashe ta ce " idan nace bana bukatar ta dubani ina da wannan damar ? Ina nufin duba da yanayin ciwo ake magana in na bukaci wata likitar ta dubani za'a iya bani dama?????"

Gashin kanta yake kallo da goshinta saboda ta sada kanta sosai da sosai ..........., so yake yi kawai ta fadi abin nan daya jal Ama kuma ta kiya

Dan haka ya mike tsaye yana duban hanyar tafiyarsa a kausashe ya ce" Wace na aminta da ita, itace zata kula da lafiyarki,! Ita zata sake duba min ke!, sannan ki koma bangaren ki a yau yau, wannan ma umarni ne daga Ni mijinki!"

Daga haka ya juya yayi tafiyarsa

Najeeba ta zubawa hanyar da ya bi ido, har Anmy ta shigo sannan ta lumshe idannuwanta tana amsa salamar Anmy

Bayan Anmy ta zauna tana furta" Wash, baki ji gajiya ba wannan yar tsayuwar da na yi na jima, bani ruwa NAJEEBA"

Mikewa ta yi ta daukowa Anmy ruwan ta kawo mata sannan ta zauna a nutse ta ce" Anmy, zan koma cen bangaren"

Anmy ta dubeta , ta ce" Ban gane ba, bangaren ki?"

Najeeba ta gyada kai

Anmy ta ce" Ama yanzu ko me kike nufi?"

NAJEEBA ta sake sada kanta a hankali ta ce" Ki yi hakuri Anmy, ina son komawa yanzu , bana son barin wajen hakanan ba kowa kin ji anmyna?"

Anmy ta sake zuba mata ido, yanzu mijinta ya fita ai, sun shirya ne ko kuma wani abu ya faru bata nan ne????, sai dai kasantuwar yarinyar tana da nauyin baki a kan dukan abinda ya shafi mijinta itama sai take yi mata uzuri, ko ba komai tana jin dadin irin yadda Najeeba ke kokarin ganin ta boye laifin mijinta, ta tabbata so da amincin junna ya sa haka...., zata barta ta koma din Ama zata saka ido sosai a lamarinsu

Anmy ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" To shikenan yarinyana, ki koma din, idan mazan nawa suka dawo da yayarsu zan turo maki su gana daya su kwanan maki kin ji? Banda saka damuwa a rai, idan kin ga zaki saka damuwa ki kama carbinki, sannan koda yaushe kike son yin magana ki zo nan ki sameni kin ji?"

Najeeba ta gyada kanta cike da gamsuwa da jin kaunar Anmy na sake ratsa zuciyarta sannan ta yi dakinta ta dau hijabinta da wayoyinta da cazarta sannan ta fito ta yiwa Anmy salama ta wuce ta coridor ta nufi bangaren ta

A lokacin da ta je sai kawai ta shiga gyara bangaren nata , Bama kamar dakinta, dakin da mijinta ke kawo mata ziyara kuwa dama rufe shi ta yi da ky, ta shiga yin abinda zai bata nutsuwa da dauke hankalinta daga tunani, abu daya ta gama yarda da shi shine, wallahi ba zata je asibitin nan ba in har ba'a bata amsar tambayar ta ba!, sannan safiya take jira zata yi magana da Jakadiya kan wata magana da ta tsaye mata a rai

A bangaren SULTAN kuwa da Nadiya gaba daya daren bata same shi yadda take so ba, du yada ta so ta baje kolinta abin ya gagara, ita da kanta sai da ta dawo a zuciyarta ta ringa fatan su shirya shi da matarsa, domin du yadda ta so dauko firar da zata saka hankalinsa zu???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?wa kanta ta yadda zasu mori lokacin harma ta mantar da shi halin da yake ciki irin na matan da suka isa da kansu abin ya gagara, tana kallon lokacin da ya dauki waya ya shiga msg din da aka turo masa, ya jima yana kallon msg din kafin ya ajiye wayar ya yi mata nunin zai yi wani uzurin, ya mike ya barta a dakin ita dai har ta yi barci bai shigo ba.

A bangarensa kuwa a lokacin da ya fice dakin karatunsa ya shige ya nemi waje ya zauna shi daya ya zurfafa a tunani mai nisan gaske da bawa ke yi a rayuwarsa...........

Tabas shi da kansa ya san a yanzu a gidan duniya bayan Anmy Najeeba ce mutun ta biyu da idan sunna halin fushi ko fada yake rada dukan nutsuwarsa......, kuma baban tashin hankalinsa ita din da kanta ta san yana da shakuwa da ita da lamarinta fiye da kima.
Gayanan dai, yana son hukuntata abu yana neman gagara......, shin wai mace nawa take dukawa a laifin da bata yi Bama bale ita da ta aikata?, ba zata duka masa ba ko????, tabasssss abin nan kawai ne zai yi ya dawo da ita hayacinta........., in sha Allah wannan ne kawai zai yi ya ganar da ita cewar ba a kanta aka rufe mata a duniya ba bale ya rasa inda zai saka zuciyarsa.............., yarda da yayi da wannan hukuncin da ya yanke ya saka shi mikewa ya koma dakinsa......., zuciyarsa cike da yakinin in dai har Najeeba bata je asibitin nan gobe ba shi kuwa zai nuna mata abinda take yiwa kishi da jin haushin zata zo su zauna tare sai ya ga abinda zata yi! Da wannan yayi kwonciyarsa bayan ya dan matsar da Nadiya wace tuni take munshari abinta.

Washe gari yara suka shirya gaba daya suka koma makaranta harda Andiya wace take University yanzu, domin an sakata makaranta da wuri, kuma tana da manemi harma an san da shi a gida, Mai DAMAGARAN ake jira ya saka ranar aurenta, shi kuwa yace sai ta kawo sakamakon shekarar farko a University idan ya ga da gaske zata mayar da hankali a dakinta ma sai a yi bikin nata, haka kuma ba'a basu damar yin zance ba saboda ba'a saka musu rana ba.

Wunin ranar gaba Waya ita najeeba tama manta da wani batun zuwa asibiti, domin bata jin komai a jikinta, hakan ya sa ta wuni cenje cenjen bangarenta da su labulaye ita da masu aikinta, har sai da yama ta yi sannan ta yi wanka ta shirya cikin sasaukar shiga ta zauna a falo ta yi kiran Jakadiya

A lokacin da Jakadiya ta zo bakinta cike da maganar da take ta cin ranta, Ama kuma tsoro ya fi damunta fiye da fadin maganar dan ta san halin uwar dakin ta, idan har ka kawo mata maganar da ta daga mata hankali ba boye wanda ya fada mata zata yi ba, ita abin nema ya dameta a ranta saboda zuwan likitar nan fada ta nemi gannin Malami, uwa uba ta nemi gannin Mai Martaba da gani cikin gida, wato gani irin wanda ake ba ya'yan cikin gida damar yi, tun dazu take kai kawo dan ta san abinda ya kawota Ama ta rasa sani, saima da ta ga sai share ido take yi da tissu gaba daya ta tsamtsamta da ita.

NAJEEBA dake shan fruits ta dubeta da kula ta ce " Jakadi, ranar da muka je asibiti....., dan Allah wani abu ne ya dan shige min kwakwaluwa....., a lokacin da ciwon cikina ya lafa, sosai ya lafa, ko?"

Jakadiya ta gyada kai, ta ce" Kwarai uwar dakina, da farko da muka je ciwon ya lafa sosai, daga baya kuma ya tashi gadan gadan kafin ya karra lafawa"

NAJEEBA ta dubeta da kula ta ce" Tashin da yayi na biyu, bayan likita ta bani maganin da zai kwontar min da ciwon ne ai ko????"

Jakadiya ta amsa cike da bata tabaci ta Wora da fadin" Ai likitar da kanta ce tace ciwon cikin yana lafawa idan kika sha maganin nan zai idasa lafawa kuma abinda yake cikin ba zai fita ba"

NAJEEBA ta dubeta....., ta kawar da kanta, zuciyarta cike da sake sake , sai kuma ta mike ta ce" Shikenan jakadi, kina iya tafiya"

Jakadiya ta bi bayan Najeeba da kallo zuciyarta cike da son yi mata gulmar wace ta zo ama kuma ta boye ta tashi ta tafi

Najeeba ta zauna a dakinta tana gutsurar goron da ta amsa a wajen Anmy saboda tashin zuciyar da take ji tunda ta sha jus din lemun tsami da ta yi, a hankali ta dubi wayarta dake ajiye.....zuciyarta cike da son sako y'an uwanta a lamarin, sai dai tsoron kashedin umi na dawainiya da ita.........

A hankali ta kwonta tana taunar goronta........, tuni jinin da take yi ya dauke sai dan abinda ba za'a rasa ba, dan haka gadan gadan take ibada hadi da kai sunan SHAHEED wajen wanda ya halicce shi, ita ta san mutun ce ita kamar kowa, kuma zaman aure take yi irin na kowace mace....., tana fatan Allah ya shiryar mata da mijinta, ya sa yayi hakuri ya gane abinda take nufi, Ama ta rantse ba zata taba yarda da maganar ita ta sha abinda ya zubar mata da ciki ba, kuma ba zata taba yarda da likitar nan matsayin likitarta ba. Zata yi jiran amsar Umi kafin ta daukaka kara, tabasssss ba zata yarda da binciken da likitar nan ta yi mata ba, kuma dole ta kawo maganin da ta bata ko gidansa a gani, babu abinda baya faruwa a duniya......, babu wanda zai sakata cikin abinda ba Shikenan ba kuma ace ta kyale shi!


Haka aka yi wani daren kowani bangare cike da tunanin abinda ya sako shi a gaba gadan gadan, Bama kamar Mai danagaran dake cike da tunanin hanyar da zai sanar musu d?cision dinsa, gashi dai ya dauki d?cision a matsayinsa na dakaken namiji, kuma ya rasa hanyar da zai isar da hukuncin da ya yanke na karin aure kwana kusa............. Bale irin yadda yarinyar nan yau ta zo ta sake kawo Tata damuwar, kuma mahaifinta ya zo shima ya sake neman wata gafarar abinda ba zai taba so ace daya daga cikin ya'yansa mata na cikin irin halin da har shi zai rinka sintiri yana neman mafita da bayar da hakuri a kan lamarin.....? Tabasssss idan da halin zai duba lamarin kuma zai samu abinda yake nema ta kowani bangare....., ya tabbata sanadiyar haka Najeebansa zata horu, zata nutsu zata rinka jin maganarsa da zarar yayi, domin a yanzu ai bata dauki Nadiya a kishiya ba bale har ta ji tsoron kishi da ita, idan ta samu wace zasu yi kishi mai sunnan kishi a nan zata gyara zamanta.


Bayan kwana biyar


A kwanakin nan sunna nan yadda suke, tunda Najeeba ta san cewa bata je abinda ya ce ba sai ta sake ri?e kafarta, take ta gyaran jikinta tana gada jikinta sosai da gyaran fatarta da shan fruits dinta dan gyaran jikinta da hadin madaidaicin tsuminta Wan sake gyara kanta, sai kuma addu'ar da take yi ba ji ba gani dan samun sauki a wajen ubangijinta, har yau takarda ta sameta daga Sangaren mijinta cewar yana gayatarsu a dakin da suke yin zama Wan tattaunawa a yau da daren nan kusan karfe goma

Kwarai sai da gabanta ya fadi da ta ji gayyatar, Ama kuma ta dake ta jure ta mike ta shiga shiryawa saboda lokacin ya kusa ai, zuciyarta cike da sake saken abinda ya sa ake nemansu zama a wancen dakin da daren nan.

Karfe goma da minti ashirin ta isa dakin, a nutse ta karasa kujerar dake nesa da tasa ta zauna bayan sun gaisa da Nadiya wace ke dakin tun karfe tara da rabi tana jiran shigowarsu su duka.


Karfe goma da minti arba'in aka bude kofar dakin ya shigo a nutse ya karasa tasa kujerar ya zauna shima sannan ya basu damar zama saboda sun mike sun marabaceshi dan nuna girmamawa a gareshi

Bayan sun zauna Nadiya ta sake gaishe shi harda dan dukawa, , ya amsa yana dubanta

Bayan ta yi shiru NAJEEBA ta gaishe shi tana kin hada ido da shi, saboda zuwa yanzu ita din da kanta ta fara daukan zafi da shi, fiye da tunanin bawa

Dubanta yake yi, zuciyarsa na kokarin neman fin karfinsa, da kyar ya dauke idannuwansa daga kanta yana jin irin yadda jikinsa ke amsawa da azabar rashin ta a kusa da shi

A nutse ya furta" Na yi kiranku nan ne dan ina son sanar maku, in sha Allah nan da sati biyu za'a kawo maku yar uwa, abokiyar zama, ina fatan zaku dauki hakan ba komai ba ta yada zamu samu zaman lafiya da aminta a tsakani"

Ba wai Najeeba ba, Nadiya kanta sai da gabanta yayi muguwar faduwa, a tsorace ta kalle shi har bakinta na kubcewa wajen furta" Aure kuma? Mun shiga uku"

Sai dai kallon da yayi mata ya sakata kame bakinta da hannayenta ta sada kanta tana kokarin hana jikinta bari a sanyaye ta furta" Allah ya nuna mana, Allah ya sa abokiyar arzikin mu ce"

Idannuwansa ya lumshe mata yana ganin lokacin da take dauke hawaye kafin ya kai dubansa kan NAJEEBA

Ta yi shiru ne tana kallon waje daya i, idannuwanta a kafe a waje daya ne nata motsa ba

Sam bai yi tunanin bakinsa zai iya ambaton sunnanta ba, sai da ya ji bakin nasa ya furta sunan nata yana kallon ta a lokacin da yace " BEEBAH"
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati na airtel ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login