Showing 120001 words to 123000 words out of 144591 words

Chapter 41 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2334

dadi na dan ka ji abinda ya ishi hancinka ba.

A nutse ta shiga saka kayanta bayan msg ya shigo mata cewar ai tuni SULTAN din ya fito, sannan ta sake yiwa jikinta wanka da turare kafin ta karasa ta Wora alkyabarta sannan ta hau dogon takalminta mai tsaye saboda ta san cewar idan bata saka shi ba sosai zata baje alkyabarta a kasa, Duda a haka din ma in ba dage kafarta ta yi ba ba zaka gane kalar takalmin ba saboda alkyabar ta hau saman doguwar rigar ta yi mugun haskata


Daurin dan kwalin nan baya so ta yi ta fito shi ta kafa, hadi da rufa alkyabar a sama, sai dai hakan ba zai hana ka ga tsarin kwaliyarta daga baya ba.


A nutse ta karasa frij dinta ta ciro abinda take da bukata sannan ta Wora saman tire din da ta riga ta tsaftace da kofi biyu a kai kafin ta dauka a nutse ta nufi Babar kofar ta saboda tuni su jakadiya na nan sunna jiran fitowarta


Bayan ta yi gyaran murya ta ja ta tsaya jakadiya ta bude kofar, sannan du suka zube sunna kawo mata gaisuwa hadi da kirari, harma jakadiya ta so amsar tire din hannunta

A hankali ta furta " Ki barshi jakadi, na Aban Muhammad ne, Ni zan kai"

Gaba daya wajen ya sake dauka, kafin du su jera a bayanta ya zamo tana tafe a hankali sunna gyara mata alkyabarta daga baya har suka karaso hanyar da aka ware dan shigowa wace aka jima da rufewa tunda Sultan ya shigo, sai dai zuwan ta a dole ya sa Sarkin murya ware ?atuwar Muryarsa ya ce"
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




42


Cikin Babar Muryarsa ya shiga fadin" Gafara dai yaro ga toron gwuiwa tafe, gafara yaro ga Gimbiyar DAMAGARAN nan tafe, gafara yaro ga uwar marayu nan tafe, SHI ASARKI ne da kansa ya kirayeta GIWARSA, shi MAI WUKAR YANKA ne da kansa yace da ita Zauna kafin in zaune, shine da kansa ya kirayeta mai baban daki ta goma sha tara a yankin garin DAMAGARAN, tun kafin ta shigo take kafa tarihi, bayan ta shigo kuma ta ajiye mana tarihi , Allah ya raya Muhammad da Abdallah, Allah ya raya mana Aliyu da mai baban suna harda Hajiya Nayla, Allah ya raya mana GIMBIYA ya kara mata lafiya, Sarkin kofa bude kofar da take tata, ka bada hanya ta shige, ku dukar da kawunanku!!!!"

NAJEEBA da ta tsaya har sai da ya gama ta yi dan murmushi ta dubi Jakadiya, kasa kasa ta ce" A saka Sarkin murya da iyalinsa a cikin asusun Mai DAMAGARAN a zuwa hajin bana idan muna da rai"

Wani ihun ya dagargaza wanda a dole ya kara janyo hankalin duk wani dake wajen, ciki kuwa harda Nadiya da yan gidansu, da Zinariya da yan uwanta, uwa uba SULTAN da tun Dazu dama kunnayensa a nan tunda aka sanar da karasowar Tata domin tunda ya fito ya ga kowa banda ita, uwa uba a wajen da suke zaune tunda ya fito ya ga mutanen da ake layawa kujera harda wace bai taba zaton ganinta a damagaran har ta komawa ubangijinta ta zo , kuma wani abin da ya saka shi tunanin me kenan? Ganin ta hau kujerar dake tsakanin ANMY da Nadiya, wace ya tabbata Nadiya bata hau kujerar nan ba dan ta san ko ta wacece, haka kuma suma suka kyaleta ta hau kujerar ta zauna? Shi kam me yasa ake son hadasa masa ciwon kai ne?, Oumi ma na kalo ta kyale? Anmy na kalo bata hana ba?, layin biyu kuwa na su zahra'u ne, a dole a nan ne wajen zamansu su dukkansu,


A hankali take takawa tunda aka bude wajen , haka kuma tunda ta shigo din Sarkin bulala shima ya cira ya hau nasa aikin, ya sake saka du wani wanda ba jinin sarauta ba, da kuma wanda bai kai matsayinta ba sada kansa koda baya so, ya zamo WA'INDA kawunansu ke kalonta ya su ya su ne, ciki harda zinariya wace ta dauke kai tun daga lokacin da ta sauke dubanta a kan fuskar NAJEEBA zuciyarta na babalewa tamkar zata ciro ta fadi daga kirjinta.........

Kasa jimawa ta yi ba tare da ta sake maido da duban nata jan Najeeba ba, wace ta Wan dakata ta sada kanta daidai su Anmy bayan ta sakarwa Anmy murmushi, wace ta jinjina mata kai hadi da mayar mata da murmushin, ya zamo Sarkin bulala da Sarkin murya na fasara cewar GIMBIYA ta gaishe da mamanta, mai baban daki baba ta amsa tana saka maki albarka.

A hankali Najeeba ta ci gaba da takawa da abinda yake hannunta ta nufi Babar kujerar da take tasa wace dogarai suka bada baya tunda ta tunkaro, haka kuma shi din ma ya sake zuba mata ido yana ta tambayar kansa me aka kunso dan a kashe Maraya?

A hankali ta sake yarda cewar ba fa zata taba samu ya mike dan tarbar ta ba, saboda yana wajen da kaf nan shine gaba da su, duk wani sarkin da ya zo ma ya zo ne gayyatarsa , hakan zai sa ba zai yiwu abu karami ya mikar da shi ba

A lokacin da ta gama gane haka a hankali sai ta Wan take alkyabar dake jikinta bayan ta rike farantin nan da kyau

Taga taga din da ta yi ya saka shi Mikewa tsaye, hadi da saukowa da karfin da harta mutanen dake gefensa basu san mikewar tasa ba, sai karasowarsa da suka gani inda ta nemi faduwa, wanda Anmy ma ta zabura ta mike tsaye, hadi da yan uwanta, mu kuwa ta sada kai da sauri saboda kar ta mike din itama domin gani take yi idan ta aikata haka ta aikata abinda zai sa a ga rashin kunyarta......

Da sauri zahra'u ta kama Anmy a hankali ta ce" Bata fadi ba Anmy, yi a hankali kar ki fadi"

Anmy ta sauke wata irin ajiyar zuciya a hankali ta furta" Kar ta fadi, idan ta zauna a cenza mata alkyaba, kin ga ba ita kadai bace....."

Gyada kai zahra'u ta yi, ummulkhair ta fice dan zuwa dauko wata Alkyabar, zinariya kuwa lokaci daya numfashinta ya nemi tsayawa, domin ?arara ta gama ganewa cewar a haka? Idan har tana da wata dama da sauran tunanin sake mallakar abinda ya zamo nata wani lokaci to kuwa sai ta dage koda zai yiwu, bale , ciki ne ashe da Najeeba?, ba an ce tun haihuwar yaran cen bata kuma samu ba? Ya Salam!


Nadiya kuwa itama har ga Allah Tsorata ta yi, dan kuwa to in Najeeba ta kifu a nan ai an shiga uku, bale ai ciki ne da ita, in ba dan auntynta ta zabga mata harara ba, da ta zamo cikin masu mikewar nan dan zuwa inda Najeeba take .


A hankali, bayan ya talabo farantin dake hannunta, ya kuma rikota da kyau, ya zamo kanta na daf da kirjinsa, dogarai kuwa suka zagaye su suka buda rigunansu ya zamo iya shi da ita ke iya duban junna

cen kasa ya ce" Beebah, faduwa zaki yi a nan ki sakani uku???"

Najeeba ta samu kanta da sakin dan murmushi, saboda yadda yace ta saka shi ukun alkur'an ya bada kala

Cen kasa ta ce" Na rike fa, ya zaka tashi gaban mutane , PLZ koma ka zauna in kai maka jus din ka"

Kallonta yake yi da kokarin gane ta saku daga fushin ko kuwa yadda ta saba boye fishinsu a gaban mutane ne zata yi?

Kasa kasa ya ce" a'a, bana so, kin ga ba ke kadai bace ba fa"

Najeeba ta saki dan murmushi , sannan a hankali ta ringa bin sawayensa har suka kusa wajen zaman

A hankali ya furta" A ajiye mata kujera a inda ya dace da ita"

Sarkin bulala ne ya yi ciki shima da sauri ya bada umarni aka kinkimo kujera baba aka kawo daf da tasa aka girka sannan aka ajiye teburi aka ajiye mata ruwa da jus dai na bukata

A hankali suka karasa yana zaunar da ita ya amshi alkyabar da ummulkhair ta kawo ya rufa mata ya janye wancen din sannan ya koma nasa wajen ya zauna wanda suke daf da junna sosai


Ita da kanta kunya ce ta hanata dago da kai, domin sai take tunanin idanuwan kowa ai yanzu da aka bada damar su dago kai a kanta, innalilahi wa ya aike ta??????


Jus din nan ya kala, kasa kasa ya ce" Kin yarda da kanki????, ina nufin in sha ko kar in sha????"

NAJEEBA ta saki murmushi tana dan dago idanuwanta a hankali ta muzguta ta zuba masa jus din ta daga zata mika masa idanuwanta suka sauka kan yan uwanta da suke dauka a waya sunna zaro ido, uwa uba zinariya da ta kafe su da ido, ga kuma iyayensu

Idanuwanta ta lumshe ta rike kofin a hannunta saboda kunya da ta lulubeta

A hankali ya mika hannunsa ta cikin alkyabarsa , hakan ya sa ta saka masa kofin a hannunsa sannan ta sake gyara zamanta tana kallon Muhammad da Abdallah irin shigar da aka musu da rawanin da aka musu ta sauke ajiyar zuciya tana jin wannan nauyin da ya dane mata kirji ya fara sakinta......, tana jin a wajen nan idan shine sarki to kuwa itace sarauniya
Tana ji a wajen nan idan har ta ba wata dama tabas ita ba jinin larabawa bace!
Tana jin cewar, babu wata y'a a nan da zata motsa ta motsa da idannuwan mijinta! Nata ne! Sultan nata ne!



"Wai dan Allah kina ganin abinda nake gani? Eh lalle Najeeba, dama fada maki nake yi, yarinyar nan tsaf zata sa ki yi ta fadan da ba riba, duba ki gani shima da bashi da zuciya, in ba haka ba du inkancin da Najeeba ta yi mana zai wani bata waje kusa da shi su ringa magana kasa kasa sunna murmushi? Ikon Allah, dan Allah dubi rashin kunya sai ta Dube mu ta wani sunne kai!" Umi ta fada kasa kasa tana girgiza kanta

ANMY ta saki murmushi a hankali ta ce" dan an kula ku a gaban jama'a ba yana nufin an yafe muku ba, kawai kulaku ne aka yi saboda idannuwan mutane, bayan wannan kar ki dada kar ki rage, zama kusa da ku kuma ai alfarma muka muku, ai ba zan kyale ba sai na kwato mata yancinta, ke Ni fa sai in shigar da karan da kaina!"

Umi ta kama baki tana duban Anmy kafin ta gyada kai kasa kasa ta ce," lalle , da kuwa kin kwaso kunya dan wallahi yarinyar cen tana iya raka mijinta amsa kiran karar da kika kai, Han!"

Murmushi Anmy ke yi har cikin zuciyarta, farin ciki ya gama mamaye mata zuciya, Duda ba zata so zaman Najeeba a cen ya hadasa wata fitina ba, saboda duba da ba ita kadai ce matarsa ba, Ama a yanzu kam cen din ne ya dace da ita, saboda ba za'a tayar da zinariya daga kujerar nan a gaban mutane ba, hakan wulakantar da kai ne , dole za'a barta a wajen ta zauna, Ama kuma idan ta zauna din ina ne ya dace da Najeeba? Ai sai gefen nasa in har bata samu gefen Anmy ba.

Nadiya kam budewa ma take yi, dan ta tabbata yanzu da Najeeba ta fito babu abinda wannan tsohuwar matar tasa ta isa ta yi, yar rainin wayo wai harda wani zama daf da shi, to wallahi ahir dinta Sultan mijin mace biyu ne, Najeeba da Nadiya, ah to!.


Zahra'u kuwa tunda ta zaunar da Anmy ta ringa sakin murmushi sakamakon yada sai yanzu ta gane fushin kanwarta, haka kuma abinda ya faru ita kam a bayyane yake a kwakwalwarta cewar ta yi haka ne dan ta samu abinda take so, ta kuma samu, saboda ita kam tana tunanin ko tsauni Najeeba na iya hawa da dogon takalmi, haka kuma ta tabbata Najeeba ta saka alkyabar da ta fi wannan tsayi ma kuma ta yi tafiya da ita da dogon takalmi ras a wajen da bashi da shafewa da kyau irin wannan ma bale kuma wannan wajen......, kwarai ta sake yarda cewar kisa, iya zama da yan kwal uba ma ba kowa yake da wannan baiwar ba, kuma kwarai zata sake daukan darasi a wajen kanwarta ko dan itama ta sake gogewa wajen zama da nata abokan zaman WA'INDA KULUN sai dai ta ga sabon CD na rainin wayo, a dole sai an fitar da ita a gidan da ta gama sakankancewa cewar itama gidanta, dole sai an rabata da auren namijin da tun tana ganin dajitantakarsa har ta dawo kalonsa dan tawalwalin saurayi saboda yadda ya gama saka aminci da yarda da junna a tsakaninsa da ita......., y'ar abokiyar zamanta tana kawo mata hari a koda yaushe dan kawai ita nata auren ya kare take so ya zamo lalle lalle sai kowace ta dandani abinda take ciki........., ita bata ja da kowa ba, bata ce kuma idan zama ya kare ita da Sarkin garin agadez Akoy wani abu da zai sa dole a zauna ba, sai dai kuma ta gama yarda cewar gwagwarmaya zata yi ta fito na fito da duk wanda yace zai taba lafiyar aurenta.....wannan alkawari ne ta daukarwa kanta.


"Abokina, to wai wacece wannan da SULTAN ya tarbo? Kutttt, yau na ga iza a gidan nan, lalle da ake yi masa kirarin dawisu ne shi wajen ado ban yarda ba sai da yau na samu halartar wannan taron, ya rab, to wai wannan mai irin adon nasa itama matarsa ce?" Amini, aboki, tun abotar University shi da Dayabu , wanda zama ya kai shi wata kasar ne ya zo ziyara damagaran wajen danginsa, dangin iyayensa saboda iyayen nasa sun rasu, hakan ya sa ya jima bai shigo ba sai baya bayan nan da ya ringa jin wa'azi a kan cewar koda iyayenka sun rasu ka ci gaba da kyautatawa makusantansu, abokansu, kai harta makotansu idan kana da hali, jin wannan ya garzayo ya zo kasar dan ya sada zumunci, shine Dayabu ya gayace shi fada yau, daga nan kuma zasu fasa cikin gari tare ne

Dayabu yayi murmushi ya ce" Wai baka ganeta ba?. Najeeba ce fa, KANWAR nan tawa Najeeba, to ai matarsa ce yanzu shi yake aurenta"

Sai da ya zabura yana zaro ido, ya sake duban inda Najeeba take kafin ya dauke kai da sauri yana furta" Astagfrullah, Astagfrullah, Astagfrullah, wai kama nufin Najeeban da na yi ta kwawa a kanta?, ikon Allah, ka gani ko? Dama kalarta ai ta manya ce, shi yasa ma ban samu damar yin soyayya da ita Bama"

Yaya Dayabu yayi yar dariya kawai yana girgiza kai, domin ai ba zai manta ba lokacin da ya ringa nacin yana son Najeeba, ita kuma sai ta yi ta masa dariya tace dan Allah dan Annabi ta so dan makaranta ta bi ina ta ga haske? Ko salon ya yi aiki da abcd ya koya mata muguwar soyayar da Allah ya hana? Ai soyayya da dan makaranta hatsari ce, tsaf zaka fada tarkon soyayya mai zafi irin wannan da ake ji kamar za'a rasu in ba'a auri mutun ba, gashi dai mutun din a tsaye mutun ne mai hatsari, saboda Fisabililahi ai abcd din ne kawai ake da shi a yanzu, ah kai yayi hakuri yaya ne kawai za'a girmama girmansa.....

Yar dariya yayi yana girgiza kai....., rashin ji fa a cikin jini yake, idan aka halicci bawa da rashin ji sai hakuri kawai a kuma bi shi da addu'a, Najeeba kam bata jin magana sai addu'a.


An gabatar da wannan taro lafiya, an ci an sha an yi addu'a sosai kafin a yiwa jariri kyaututuka na garari saboda sunan mai DAMAGARAN da ya ci, ciki harda Hajiya Najeeba ta gwangwaje baby da kyautar da ta sa aka yi ta guda da murna, kyautar da ta gabatar kafin kasa kasa ta ce da mijinta" Daga ALJIHUNKA"
Shi kuma ya saki murmushi da wani farin ciki da ya gama mamaye masa zuciya, saboda ya gama sakankancewa cewar kuma wannan yannayi da suka shiga an bashi baya, dan ita da kanta ta gama yarda da hakan har cikin zuciyarta.


Karfe goma sha biyu du aka watse bayan SULTAN ya koma Sangarensa dan shima zai hau dokin nan ne yau , domin Sultan YUSUF, Sultan din agadaz , da na maradi du sun halarta kuma zasu hau suma dokin, dan haka hawan ma zai dauki mutane da yanayi mai dadi.


Da yama likissssss Anmy ta yi kiran Najeeba da Nadiya bangarenta, domin Nadiya sai da ta fito daga cikin yan uwanta ma ta zo ta samu Najeeba a wajen Anmyn ta cenza shadarta zuwa danyen lesh mai ruwan sararin samaniya sai walwali yake.

Zaunawa ta yi bayan ta gaishe su

Anmy na murmushi ta ce" Yauwa, yau girkin waye ne a cikin ku?"

Nadiya ta ce" Nawa ne Anmy "

Anmy ta gyada kai, ta Wan yi shiru kafin ta ce" Ok, dama da ace ba naki bane sai baki su je bangarenki ki samawa wasu wajen zama, su zinariya, tunda ke Bakya nan ba zai yiwu a kai maki baki ba, sai su sauka a bangaren Najeeba "

Daga Najeeba har Nadiya a tare suka ce" Zinariya kuma anmy?????"

Anmy ta dubi yanayinsu, kafin ta dauke kai ta ce"
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login