Showing 129001 words to 132000 words out of 144591 words

Chapter 44 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2351

kallon fuskar ta a hankali ya janyota jikinsa cen ciki ya ce" I'm sorry my bae....., i'm so sorry fr allllll, kin san dan Adam ajizi ne......, but du abinda kike tunanin na maki dan in bata maki ban yi da gangan ba, sabani ne ya riga ya shiga tsakani Bani da abin cewa sai dai in baki hakuri..... plz ki manta"

NAJEEBA ta lumshe idanuwanta tana jin gaba daya ma komai ya fada , duk abinda ya gama rike mata kirji ya sake ta, ..................

A hankali ta dago kanta tana kallon fuskarsa
Cen kasa ta furta" I love U"

Idannuwansa ya lumshe yana sakin murmushi, ya duko kansa yana kallon fuskar ta, ya ce" Duk rintsi, PLZ....kar ki kuma fita daga dakinki da sunan fushi......,harma ki furta kalmar da kika furta...........kin san da sai da na rasa hankalina na lokaci mai tsayi?????"


Ta Wan zaro ido zata yi magana aka buga dakin da dan karfi

A tare suka dubi kofar, ganin da gaske bugawar ake yi ya ce" waye ke bugawa? Ko Andiya ce?"

Kai Najeeba ta girgiza a hankali ta ce" Ba zata min bugawar nan ba, ina zuwa"

Har ta mike ya rikota ya mike yana fadin" A'a Ni zan je"

Sai kawai suka nufi kofar yana gaba tana bayansa

Bude kofar yayi ya leka kansa

Wace ya gane tsaye ta harde hannayanta ya saka shi sake duban ta da kyau da dan mamaki ya ce" To, anmy? Ke ce? Lafiya?"

ANMY ta gyada kai ta ce" Eh lalle, zaka ce lafiya, ina yata? Nace ina yarinyana?, kai wannan yaron ka ga ka guje min fitinar da nake guje maka, idan ka yarda ka tabani da neman fitina zan biye maka, ka kiyayeni, na fada maka, shine zaka dauke min ita ka kawo ta nan ko? Dukanta zaka yi? Wato dai rashin adalci sak a lamarinka ko? Ba laifi ba zan amince ka ci gaba da cutar min yarinya ba, zaka kauce in ga inda take ko ba zaka kauce ba????"

Baki da hanci ya hangame yana duban Anmy da tarin mamaki

Da sauri Najeeba ta fito bayan ta waiga ta hango su pant dinta fa komai a watse, Duda ta san da wahala da matukar wahala Anmy ta shigo dakin nan, domin ko wancen shigar da ta yi wancen dakin ne, bata tunanin Akoy abinda zai sako Anmy dakin nan gaskiya, Ama sai ta bi ta kasan hannunsa ta fito tana yin kiri kiri da idannu kamar an jijiga bera a cikin kwano

Anmy ta riko hannunta tana dubawa ta ce" Da karfi ya kawo ki ko? Mu je, wuce mu je!"

Ta sake ja ta nuno shi da yarda ta ce" Kai baka san na dame ka a neman fitina ba? Tabass da Ni kake maganar, a gama taron nan niyata zan kai karar ka ne a bamu takardarmu, ai ba'a aure dole, yarinyata zaka saka tana haihuwa ta baka abinka ta samo min dan gaske in aura mata, aikin banza ashe ka wani fake a gefe kana cutar min y'a har ta gudu ban sani ba? An yi daya ba za'a yi biyu ba, Ni ina son abina tunda kai baka so!"

Ta yi gaba fuuuu tana cewa Najeeba" biyoni mu je, ai neman ki nake ta yi wayarki na tsinta a dakinki na bangarena ke dai karshe akace kamar an ga kin biyo coridor nan na gane an biyo da ke dai, ina ke ina mutumen nan????"

Najeeba ta sake duban SULTAN a zabure, da idannuwa ta masa alamun wallahi sun shiga uku, kafin ta Wora hannayen nata a saman kanta ta shiga bin Anmy da dan sauri

Fitowa yayi gaba dayansa shima ya bi bayansu suka nufi bangaren Anmy

Sunna shiga Anmy ta juyo zata nunawa Najeeba dakinta dan ta mata umarnin ta shige ta ga SULTAN a bayan ta, uwa uba WA'INDA ke Falon harda zinariya wace ta fito ta zauna dan kawai ta sake gane abinda ake ciki a FADAR

Ummi dake ta faman salamar baki murmushi kawai ta saki ta juyar da kanta, saboda itama a dole a nan zata kwana yau sai dai gobe kuma du su yi gidajensu harda A'isha matar yaya Dayabu, yaya Dayabun ma ai yana fadar kawai yana tare da abokinsa ne

Hannun NAJEEBA ya riko bayan du mutanen Falon sun sada dubansu banda Umi da Anmy

ANMY ta zaro idanuwanta ta masa alamun ya cika mata y'a

Kai ya langwabar , Najeeba kuwa ta ja numfashi tana dafe kirji

ANMY ta yi dakinta fuuuuu, suka mara mata baya su biyun, sai dai sunna shiga dakin Anmy ta ce" Au, biyota ka yi nan din?, to bari ka ji, zan haWaka da ubanka ne, ka bamu lafiya ko ana dole????"

Najeeba jiki na rawa ta girgiza kai tana langwabar da kai ta ce" Aya ANMYNA aya, ai dama fushin na farko shedan ne yayi busa, Ama yanzu a'uzubilahi mina shaidanin rajim, Anmy yayana ne fa, lafiyar Allah ma mai zane Ni bale Ni na ja, dan Allah Anmy kar ki wani biye min rashin hakuri ne irin nawa ya sa har na aikata haka ko SHAHEED?????"

SULTAN ya gyada kai da sauri, kafin ya dan daga kafa zai karasa inda anmy take Ama anmy ta dakatar da shi, ta nuna Najeeba da yatsa ta ce" Kina cikin hayacinki? Amsar da nake so ki bani ke nan, nace kina cikin hayacinki????"

Tsoro ya kara lulube Najeeba a rikice ta girgiza kai

Anmy ta gyada kai ta ce" Gaske, Bakya cikin hayacinki, in ba wannan ba mutumen da ya wulakantaki zaki tarewa magana? Wuce min ciki nace kafin in Bala maki mari!"

NAJEEBA ta Wora hannayen nata a saman kanta, a rikice ta yi ciki tana sakin kuka harda fadin Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une shikenan za'a rabata da mijinta

Anmy ta gyada kai tana dubansa ta ce" Me ka sa a yi mata da har zata rinka kuka saboda kai????"

Kai ya sada, yayi iya yinsa ya dane tashin hankalinsa, a taisashe ya ce" Anmy, fahimtar juna muka yi ,ta yafe min, tace ta yafe min, dan Allah ki yi hakuri Anmy........... Ta yafe................................................................."


" ka je kawai, idan ka rubuto ko Sarkin bulala ne ka ba ya kawo min!" Anmy ta katse shi tana daure fuska

Gana daya Sultan ya rasa kuzarin da zai iya Mikewa bale har ya tafin, har sai da Anmy ta kama shi ta mikar da shi ta nuna masa kofa sannan ya fito tamkar zai kifa, yana jan jiki da kyar ya nufi hanyar coridor


Da sauri Ummi ta shigo ta bude baki zata yi magana ANMY ta mata alamun karma ta yi, sannan ta daga murya ta ce" Maryama, lalle ina cikin tashin hankali, kin san sarakan nan basa zama kalau bale idan sun ga abu zai daga musu hankali, ke Ni banma yarda da shamaki da malami ba sun bi dare sun yiwa yarinyar nan birne birne, kuka take dan na tuna masa maganar takardar sakin mu, an asirce ta...."

Firgit ta fito zani a hannu ta duka ta daga hannu daya tana fashewa da kuka hadi da girgiza kai ta ce" Anmy, dan Allah ki fahimceni ki gane Ni ce a hayacina nake, Anmy babu asiri Anmy zaman lafiya ai ya fi tashin hankali, dan Allah a tausaya a taimaka a rufa min asiri a duba a barni in tafi kawai, fitinar ai bata da wani anfani Anmy, a yafe min laifina na tuba"

ANMY ta girgiza kai tana duban ummi ta ce" Ba kin gani ba? In ba aikin asiri ba me zai sa yarinyar nan ta dubi wancen yaron kuma????, ai Shikenan bari in daura alwallah in kwana a kanta, in sha Allah kafin safiya zai karye, ke share hawayenki je saman gadon mu ki kwonta in sha Allah da safe idan mun tashi in kin ji tsanar ta dawo Shikenan, idan kuwa kin ji har yanzu kina so ki koma Akoy gagarumar matsala, maza je kwonta ganinan!"

Najeeba ta hade hannaye zata sake yin magana, Anmy ta daure fuska ta nuna mata gadonta, a dole ta nufi ciki ta je ta haye gadon tana furta" Wayo zasu kasheni, wayo na shiga uku innalilahi, yo ai nace na yafe ko? Nace na yafe......"




=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?. Su kwate an ji kunya=??
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




47


Ficewa suka yi daga dakin suka nufi KICIN saboda har yanzu da sauran mutane a falo, duda shigowarsa ya sa sauran du suka watse ciki harda zinariya wace ta yi dakin da aka basu ita da yar uwarta ta shige ta rufe ta ci kuka kamar ba gobe cike da nadamar rayuwa da dana sani............
Wato gana daya ta kasa manta mijinta
Bata iya gane cewar tana tare da mutumen da da wahala ta samu irinsa ba sai da ta rasa shi,
Hankalinta du ba a kan manema aurenta ba, domin ya zamo du Wanda ya fito sai ta nemi daidaita shi da mijinta........., tana samun mai kudi, tana samun mai kudin da mulkin, Ama har yanzu ta kasa samun mai yannayinsa..........sarauta, iza, kyan halitta, kai subahanalah.................., ita kam a irin yadda ta koyi rayuwa a yanzu da ace zai dubeta ya mayar da ita dakinta da ta yi zama irin na cikakkiyar mace a gaban mijinta....
., sai dai da wahala zuciyarta ta iya jure ganinsa da Najeeba......., Ama alamu sun gama ganar da ita cewar ba wai ganinsa da Najeeba kadai bane zata jure idan har Allah ya sa ta jajirce ta dage iyaye suka shiga lamarin aka dubeta aka mayar da ita dakin nata......, dole zata jure ganin soyayya a gaban idanuwanta da mijinta da Najeeba, yarinyar da ta tsana tun farkon ganinta a cikin famillyn nan, .......
......ba zata taba iya jure wannan tashin hankalin ba, ba zata iya na!


Anmy da ummi na shigewa kicin suka rufe suka ringa dariyar lamarin nan

Cikin dariya Ummi ta ce" Sunna son junansu, du zafin su sunna iya nemo junan su, shi yasa na kasa bata karfina da lafiyata wajen tuna abin sosai, yarinyar ki bata iya bacin rai bane!"

ANMY ta girgiza kai ta ce" Ba haka bane, ana nuna bacin rai, idan ka ga in ka nuna karami za'a dauke shi a aikin banza dole ka samawa kanka mafita, dole zata nemi mafitar da za'a saurareta ......"

Ta dan rage murya a sanyaye ta ce" Sai dai lamarin nan ya tsoratani fiye da tunanin ki......., kwarai na Tsorata, a jiya idan na tuna gaba daya jikinta je kwasan rawa......., sai in ce da ace Bama duniyar nan suna iya yanke alakar juna cikin sauki haka?????, wannan bai kai ya raba aure ba a ganina "

Ummi itama jikin nata yayi sanyi ainun, a hankali ta ce" Kina da gaskiya, Duda idan Allah ya kadarta cewar ba zasu rayu da junna har karshen rayuwarsu ba, bamu da abinda zamu iya yi, Ama kuma ina addu'ar kar Allah ya sa da haka a rayuwarsu......, Anmyn su, ina kyautata musu zato sosai, saboda a shekarun da suka dauka sunna ihun an mu su auren hadi da junna, har yanzu suna son junan nasu fiye da tunanin bawa, to kuwa muna iya cewa alhamdulilah mun ci ribar daya cikin darin auren hadin da ake yi ana samun matsala ......, damuwata a lamarinsu shine su dukansu zafi ne da su, kin ga idan kace zaka daga hankalinka ka hana kanka nutsuwa da matukar riko a lamarin da ya shafe su, to kai zaka zo kana motsewa su kuma suna caskalar juna suna nemo juna......, PLZ, ki yi kokari ki dauke kanki, idan ta nufo ki fuuuuuu ita mai uwa ki saka mata ido kawai , kina zaune zaki nemeta ki rasa ta tarda abinta "
Ta karashe tana murmushi hadi da girgiza kai

ANMY ta ce" Wai kin ga yadda ta bi ta coridor ta tafi? Kai jama'a, ai kya kara ja masa rai ko?....., hum barni da su ke dai, na san ba zan hana su fada da junan nan ba, Ama kuma tabas sai na sa sun ji tsoron nemana a karamin abu gabanan.............., sun kai wajen da zasu rayu da juna ta hanyar zaunar da juna su fahimci juna....., koda yake wasu fa yan rigimar idan aure ya haWa su zaki ga har a tsufa ana musu Shari'a" itama ta karashe da yanayin tsokana, hakan ya sa Ummi yin dariya ta nufi fita ta ce " To ai Shikenan, sai ki yi ki gama tunda kin fara neman fitina, Ni na yi nan"

Itama Anmy din dariyar ta yi kafin ta shiga bude kayan abinci ta zuba a plate ta daukarwa Najeeba ta koma dakin

Samunta ta yi zuru da carbinta a hannu tana ja, ga dukan alamu nafila ma ta yi ta gama

Abincin ta bata tana fadin" Cinye min shi tasss ki ban plate din"

NAJEEBA ta karba da hannu bibiyu tana sake duban fuskar Anmy sannan ta zauna ta shiga ci gabanta na faduwa

Ci ta yi sosai kafin ta mike ta mayar da plate din ta sha ruwa ta dawo ta sake zaunawa daf da Anmy suka yi shiru.......

Cen ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" ANMY, ana tashin hankali a duniya , tashin hankali irin na a ji za'a mutun nan fa"

ANMY ta Wan zaro ido ta dubeta, kafin ta kwonta da kanta saman cinyarta a hankali ta ce" Asha asha subahanalah, me ya faru haka autana?"

Najeeba ta Wan daga kan nata kafin ta mayar a hankali ta ce" Uhum, ke dai bari Anmy, wai yanzu rabe raben aure kuma ake Tata yi, Allah dai ya kiyaye, to abinda malan yace saki Allah ya halatta shi Ama kuma baya sonsa? Wai fa idan aka yi shi sai samaniya ta bakwai ta girgiza, kai Allah ka hanemu zamowa sanadiyar girgizar samaniya ta bakwai ya Allah, Allah amen"

ANMY ta yi murmushi ta ce" Amen ke dai waga diya, Ama in sakin ya zama wajibi to yaya za'a yi,? Bale in namiji yana tunanin ko ba'a son yarinyar ne aka bashi, sai ya bada yarinyar ya gani in abinda zata ci zai gagari iyayenta ne!"

NAJEEBA ta yi dan shiru na dan lokaci kafin ta ce" Kai, Anmy ba zai gagara ba , Ama ai ba tuwo kadai bane, ga su asibiti, su anko, su jaka da takalma, ke dai Anmy Allah ya sa a yi ta hakuri ana barin ya'ya a dakunan su kawai........."

Gimtse dariyar da anmy ta yi ya hanata sake yin magana, ita kuma ta yi ta Wan dagowa ko ta ji an sake bata amsa Ama abin ya gagara, karshe dai jiki ba karfi ta ce" ANMY in tafi wajen su aunty zahra'u???"

ANMY ta gyada kai, saboda su Muhammad ma yanzu sa shigo, kuma idan suka ga yannayin uwar suma yanzu sa nemi rikice mata, idan ka ji Najeeba na fadin aunty zahra'u tana cikin wani hali

Najeeba harda su sake dukawa kafin ta tafi ta ce" Wallahi ma kuma Anmy Ni sai in ga ba wani asiri fa, Ama Shikenan Allah ya kai mu da asubar in dai na tashin yadda kike so Shikenan ko Anmy?"

ANMY ta dauke kai tana hade fuska ta ki bata amsa, hakan ya sa ta mike ta fice sai waiwayowa take yi, Ama tashin hankali ya sa har ta fice bata ji Anmy ta yi kiranta tace ta yafe musu ba, innalilahi wa Inna ilaihi raj'une

Ta zo fita Muhammad ya zo shigowa ya rungumeta yana fadin" Mah, Ni yinwa nake ji"

NAJEEBA ta nuna masa yatsa idannuwanta na cika da hawaye ta ce" Ka ga ka kiyayeni Ni nake baka abinci? Ka kiyayeni ka ji na fada maka"

Anmy ta mike tana fadin" Zo nan masoyi, rabu da masu hali, Allah ya kyauta musu, ina nan kan bakana sai an bamu abinda muke so, jeki kar ki taban lafiyar motsin zuciya"

Najeeba ta fice tana turo baki ta nufi wajen yan uwan ta

Ta same su ciki ALKHAIRAI dumu dumu, sun gama raraba kayan gyaran su sun koma firar duniya , sun kirayi wayarta sun ga wayar a dakin sai suka hakura , kuma tun Dazu Sultan ke kiran wayar Ama bata dawo ba sai kawai suka ajiye in ta shigo ta neme shi

Tsakiyarsu ta zauna tana cire hijabin hadi da kunce ribom din kanta saboda a jike yake har yanzu

A hankali ta kamo hannun zahra'u ta kai wajen wuyanta ta ce " Zafin jiki na ya kai saba'in yanzu ko aunty zahra'u?"

Zahra'u ta dubeta bayan ta taSa ta girgiza kai t?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 a ce" Saba'in kuma? Ai da kina cikin likafani yanzu"

NAJEEBA ta dantse lebe tana kallon ummulkhair ta ce" Allah ne yayi da sauran numfashin ama ai ina daf da tafiyar ma, wayo Allahna!"

Ummukulsum ta ce" Dama tunda na ji kina kiran aunty na san ba kalau ba, meye ? Me aka yi?"

NAJEEBA ta dubi ummukulsum bayan ta rafka tagumi ta ce" Kin ga, wai so ake lalle a raba mace da gidan mijinta, Ni abin mamaki ma yake bani Allah na tuba"

Zahra'u ta ce" Wace za'a raba da mijinta kuma?"

Najeeba ta dauko yatsarta, ta daga yatsarta jama'a a gaban jama'ar da ta gama ihun ba ita ba mijin nata a yanzu ta nuna kanta ta ce" Ni, Ni ce, Anmy tace lalle lalle sai an san yadda za'a yi a bani takarda, Allah na tuba ace kawai an gaji da Ni mana? Ni fa sam ban cika son girgiza samaniya ta bakwai ba, bana son take abinda Allah baya so, dubawa za'a yi kawai a yi abinda ya dace ko mace ta gudu wajen mijinta!"


Bayan ta yi shiru, sun jima sunna kallonta kafin zahra'u ta gyada kai ta ce" um, in ji mai ciwon hakori........., to Allah ya kyauta, "

Ummulkhair ta dubeta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login