Showing 63001 words to 66000 words out of 144591 words

Chapter 22 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2355

kuma baki cike a shagon dankam sai gyaran fuska ake yi musu, wasu kwalliya, wasu gyaran kai, wasu gyaran kafa, kai aiyukan dai ba kadan ba

Bayan sun gaisa ta karasa kujerarta ta zauna tana tankwashe kafafuwanta a saman kujera tana murmushin firar da Hajiya Turai ke yi, tana faman fadin da ta san Gimbiya zata shigo yau da sai ta nemi service dinta wallahi saboda so take yi a tatso mata kyau ta yadda zata je ta gigita taron da zata halarta

NAJEEBA ta yi murmushi ta ce" Hajiya Turai tawa, ai na yarda da hannun Aida, ko Ni ita ke gyara min , kar ki damu zaki gigita taron, ta gama maki in maki make-up din"

Ai kuwa Hajiya ta ringa godiya kamar kyauta za'a yi mata aikin, ita kuwa NAJEEBA ta bude litafin da suke rubuta duk wani abu mai mahimmanci, misali kwaliyar manyan amaren da za'a je har inda suke a yi musu, wa'inda suke zuba kudi mai yawan gaske dan a je a yi musu

Kwalliya har biyu ta gani, nan da nan zuciyarta ta raya mata cewar zata je daya, idan yaso Aida ta je daya, domin tana son fita daga gidan....sai dai ta yaya? Ta yaya zata samu fitan? Shine Babar damuwar a yanzu domin ta sani ko tana hauka ba za'a yarda ta je ta yiwa wata amarya kwalliya ba, hasalima ba kwaliyar zata kaita waje ba, zata je ne su yi fira tsakaninta da amaryarsu, fira mai mahimmanci sosai take so su yi, wace bata samu sun yi a nan ba

Jarida ta bude ta shiga karatu, har aka gamawa Turai gyaran kai, ta mike ta shiga yi mata kwalliya cikin nutsuwa, wanda hakan ya sa wasu ma cewa su wallahi suma sai ta musu, sai dai a dole ta basu hakuri tana gamawa ta shige cikin dakin gyaran jiki da Aida, ta shiga harhada kayan gyaran jikin, sunna magana da Aida na abinda yake banki, da abinda yake kasa

Kudin ta hade kaf tana gyaran jikinta tana dubawa har ta gama irgawa ta sake kiran Nadiya ta bata umarnin zuwa ta ciro mata kudi masu kauri zata yi wani abin da su

Nadiya ta amsa da fadin cewa gobe zata je banki in sha Allah, Najeeba ta tabbatar mata idan ta amsa ta kai gidansu zata amsa .

Daga haka ta shiga gyaran jikinta sosai da sosai, har yama ta cin mata domin sallah kadai take dakatar wa ta yi, sai kuma irin yadda take dan yawan yin fitsari, wanda tunda jinin Nan ya daina zuba ta hadu da wannan abin, tana shan abu take jin bukatar zuwa fitsari kuma fitsarin ba kadan take yi ba, gashi marar Tata sai ta ringa jin nauyi nauyi, cikin dare har zafi yake dauka zau, ta tabbata abin zubewar cikin nan ne, tana fatan samun saukin abin a hankali

Sai da yamar nufi bangaren Anmy

A lokacin da ta zo ta samu docter Halima, da Abiey, da Anmy a falo sunna ta magana , dama Abiey din ke daf da zuwa neman ta saboda bata fita da waya ba bale a yi kiranta a sanar mata ta yi baki.

Zaunawa ta yi kamar yadda suka bukata,

DOCTER Halima ta dubeta da kula da girmamawa sosai ta ce" Ranki ya dade dangane da maganar takardar nan, da hoton cikin nan ne, inaso in ji bayanai na lokacin da kika fara jin ciwo, irin yadda ciwon ya ringa maki, har zuwa lokacin da kika je asibiti, da abinda ya faru"

NAJEEBA ta sada kanta a hankali ta ce" Aunty, lokacin da.......lokacin da"

Ta yi dan shiru saboda maganar ta yi mata nauyi a baki, sai dai ta san dole zata fada dan haka ta Wan sosa keyarta a tausashe ta ce" Dama, tunda na fito daga bangarensa na fito da ciwon, kuma abin yake ta hauhawa.......shine muka je asibitin, da muka je kuma likitar ta jona min ruwa, sai ya ringa lafawa, to daga baya ne ta bani wani magani fari dogo haka na hadiya , tun daga nan abin ya tsananta har cikin ya fita"

Docter Halima ta dubi Anmy, a tausashe ta ce" Ranki ya dade, a hoton nan fa na farko kin ga poche uku ce, saboda wata biyu ne ya kai ya nuna yannayin abinda ke cikin, misali idan abu daya ne ko sama da haka, saboda tuni halittar abin ta kankama"

Najeeba ta dago da sauri ta dubi likita, hakama Anmy da sauri ta dubeta tana fadi " Kina nufin uku ne suka zube???"

Likitar ta sake daukan dayan hoton cikin ta zuba masa ido tana kallo da karawa, ta sake duban su ta ce" Ama dayan hoton cikin nan, ai ba za'a iya fahimta ba, saboda idan har hoto yayi duhu haka kyansa a sake shi shine mafi a'ala, ko Akoy wani hoton da aka yi???"

Anmy ta mike da sauri ya amshi hoton tana dubawa kamar zata iya karanta wani abu, ta dubi likita ta ce" Docter, wai, kina nufin mene? Ni fa du ban gane ba"

Likita a tausashe ta ce" Hajiya, idan har hoton farko ya fito fesss haka, hoton biyu ya dace shima a ganshi a haka, kuma magani fari dogo gaskiya ba shi bane duclo, in saboda shi duclo ba haka yake ba, maganin da likitar ta bata kam ba duclo bane, Ama tunda har Docter izrane ce ai zan nemeta, na santa na koyar da ita a University, sannan hoton nan ina so nan fa sati biyu in sha Allah Gimbiya ta sameni a asibiti in yi mata hoto da kaina , saboda ina so a dauki kamar wata da maganar zubewar cikin sai mu dake aunawa......., kin ga nan wajen fa kamar alamun wata poche din, Ama kuma ba zamu tantance ba sai mun yi hoto mai kyau, "

Anmy ta daga hannayenta ta ce" Allah, ya Allah, ka sa cikin nan na nan"

NAJEEBA ta sada kanta tana lumshe idanuwanta, likita ta amsa sosai tana murmushi ta ce" Ai yawanci lokuta idan har ba daya bane zaki ga in an samu matsalar zubewar cikin ba duka suke fita ba, Ama matsalar dake faruwa a nan shine, a hoton nan ba zan iya ganin magani aka sha ko akasinsa dan zubar da ciki ba, hasalima ba a hoto zamu gani ba, likitar da ta aunata ne zata iya gane hakanan, shima sai idan ta yi tambayar abinda ta gani misali na matsawa ne idan ta ga alamunsa a cikin jinin , sai ko idan ta zo a lokacin da take cikin wahalar ta fada da kanta cewar ga abinda ta sha, Ama a haka ai ba za'a iya yanke hukuncin maganin mata ko na Hausa ko na nasara aka sha ba, sai gwajin da ake yi na jini wanda shima yake nunawa, gaskiya in dai iya takardun kenan babu wannan maganar a ciki"

Anmy ta girgiza kai tana duban Abiey ta ce" Ka gani ko yaya? Ka gani ko? Yaya za'a yi yarinya tana fada tana karawa Ama a hannata magana dan son zuciya? Ka san ko, idan har yarinyar nan karya take yiwa yata ba zan yarda ba!"

Abiey ya ce" Ki yi hakuri mana, yanzu dai ai ko dan abinda kika ji dayan kwa yi hakuri ku saurarawa zukatanku ku bar maganar ko?, tunda har Allah ya sa wannan bayani ya shigo inaga ko meye a barshi gefe , idan Allah ya tabbatar cikin na nan ba Shikenan ba???"


"Kana nufin du irin hayagagar da ya mata a kan abin nan zai wuce???" Anmy ta fada

Abiey ya girgiza kai ya dubi likita ya ce" Docter, yaya bai isa ya yiwa kanwarsa fada ba?, haba , a bar maganar nan kawai, takardu kuwa likita ta je da su nan da sati biyun in sha Allah sai a sake yi, Allah ya tabbatar mana da ALKHAIRi"

ANMY ta sake sakin wani murmushi tana ta amsawa da amen, Najeeba kuwa kanta a kasa gaba daya ta afka duniyar tunani

Kenan dai tunanin da take yi cewar yarinyar nan na Binta da wani abu hakanan ne? Tabas hakanan ne, to Ama meye hadinta da ita? Ko kuma sanadiyar maganar auren da ta fito ce? Ko kuma budurwarsa ce ta tun ba yau ba????? Tabas ga inda maganar take, wannan din budurwarsa ce, kwarai sun jima tare shi yasa har ta fara harin rayuwata??????, tabasssss a yau yau sai na fara nuna mata ita karamar mahaukaciya ce, in sha Allah a yau sai na nuna mata ita bata iya hauka ba

A sanyaye Najeeba ta ce " Anmy, idan ba damuwa ina so in je wajen su Aunty yau a dubani, Anmy numfashina tun Jiya yake wahalar da Ni abin athsma din nan"

Anmy ta dubi Docter dake fadin Subahanalah kina da asthma ne??

Anmy ta ce" Eh docter, kuma ta yi crise kwanakin nan, na san shine bai barta ba har yanzu, idan har kina nan ta je in an jima a dubata in magani za'a cenza mata sai a cenza mata????"

Likita ta ce" Ai ba damuwa Hajiya, in sha Allah ta sameni bayan magariba, na san fitar dare Gimbiya ke yi, zan yi jiranta in sha Allah "

NAJEEBA ta ji wani irin farin ciki na mamaye zuciyarta ta ringa godema Allah a zuciyarta

Anmy na godiya ta ce" Masha Allah, na gode likita, in sha Allah zata zo"

Abiey da mamaki ya dubi Anmy ya ce" Zata zo? To mijinta ya amince da haka ne????"

Da sauri Najeeba ta dubi Abiey, tana kikifta ido, harda kokarin neman tayar da tari dan kuwa ba zata so ace wani abu ya hannata fitar nan ba

Anmy na dubansa ta ce"
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




21



Anmy na dubansa a tausashe ta ce" Yaya, ai abinda ya shafi lafiya ne, ka ga ba zan so koda wasa hukar nan ta kuma tashi ba, idan Akoy abin nan gwara a ringa yin taka tsantsan da lafiyarta da addu'a in sha Allah komai zai wuce ko yaya?, kuma shine da kansa ya bani damar ire irin haka a zartar kawai tunda shi bai cika zama ba, ka ga kafin ya shigo gidan yau ai dare yayi sosai ba zan so ace har bayan isha'i basu dawo ba"

Abiey ya gyada kai yana mikewa ya ce" Hakane, to Shikenan, Allah ya bada lafiya, Docter mun gode mun gode Allah ya saka da alkhairi, thank you so much"

Likita itama ta yi godiyar saboda a yau kadai kafin a saka hannu a takardar da zata bata damar zamowa mai kula da Gimbiya alkhairan da ta samu harda na maganar da ministan kiwon lafiya, wanda a da bata taba samun wannan damar ba, shekara kusan ashirin tana aikin nan , domin bai fi mata yan shekaru ta ajiye ba, Ama cikin darajar aikin nan da take haduwa da ita kala kala yau har waya suka yi da ministan kiwon lafiya a kan cewa komai na hannunta na ragamar kula da kai kawo, maganar ya'yan banki kuwa account numberta kawai aka tambaya sai gingimemen alert ta gani har daga banki biyu, domin Abiey ne da Anmy suka saka yar kyauta a wajensu wai ta da mai dan zuwa fadar, ita kam ai alhamdulilah ta mori aikin gwamnati, dan kuwa tunda ta zauna da zuciya daya take aikinta da zuciya daya Allah ke hadata da mutanen kirki mutanen arziki, wa'inda du idan abin ALKHAIRi ya haWaka da su to fa suma sai sun bar maka abin alkhairin da zai dadada maka zuciya .

NAJEEBA kam mikewa ta yi ta shige ciki saboda wayar da take son yi da mutumen da zata ba wani dan aiki dan kuwa a yau yau take son aikin

Tana bude dakin ta samu yan uwanta na fira sun baje kaya a saman gadon sunna ta dubawa, kayayyaki ne na gyara, gyara irin na mata, wato gyara mai daraja, domin fita suka yi su biyu suka je wajen balaraba suka kai mata gaisuwa hadi da neman iri, ta kuwa hadasu da kaya kala kala

Najeeba ta cire hijabinta tana dan zarro ido ta ce" au wai da ganimar nan zaku kwashe ku kadai? Baku isa ba wallahi bari in yi Waya in zo kar a cuceni"

Zahra'u ta ce" Ai dai kin san babu ke a wannan haja saboda mijinki ya Hanna ki sha ko???"

Najeeba ta sakar mata harara ta ce " Haka fa, sai kace ba shine ya fi kowa amfanuwa da su ba, ku ware min irin nawa, ai mu da gyara jiki da fata sai idan rai yayi halinsa, a nan ne kuma ba wani abu da zamu yi da gangar jikin komai ya tsaya na nan duniya, ku ware min plz kar ku rabe banda Ni"

Dariya ummulkhair ta yi tana duban umi karama da ta rafka tagumi tana kallon NAJEEBA ta ce" Dama na fada muku, ku raba da ita, bafa zata dauki maganar rashin gyara ba, kun ga irin nata nan, wadinnan da basu da daci, basu da matsala , ga itacensu nan a jiki kawai dafa abinta ne zata yi ta sha daidai dandanon bakinta, idan ba lamarin yaya ba ai da dandano girki ya fi dadi"

Dariya suka saka a tsakaninsu kasa kasa dan kar Anmy ta karkato ta ritsa su, domin baby na barci a dakinta cikin gadonsa da babansa ya kawo yau da sauran tarkace, domin mahaifiyarsa ba lafiya ta dawo daga wajen yan uwanta jirgat, yanzu haka sunna Niamey saboda jirgi suka bi, yace idan ya ga ba dama zai fita da ita, shine dalilin da yasa aka bar umi a nan har su dawo, domin gidan umi irin ginin nan ne da ake yi cen shiga gari, basu fi su uku a anguwar tasu ba, jeji ne sosai, Duda da masu gadi da yan aikinta da komai Ama bata saba kwonciya ta tashi ita kadai ba mijinta ba mamansa ba, shi yasa yace su yi zamansu a nan idan Allah ya dawo da shi lafiya sai su koma kawai.


NAJEEBA ta shige dakin Muhammad ta zauna saman kujera ta dana kiran wayar yaron

Yana dagawa ya fara gaisheta sannan ya saurara

A nutse ta ce" Na tura maka wata numba, idan ka bude msg din kar ka rufe dan gogewa zai yi da kansa....., ina so ka gwada kiran layin ka min tracking dinsa ....."

Da girmamawa ya ce" An gama"

Najeeba ta yi dan tsai, kafin ta ce" Ka duba my nita dinka"

Daga haka ta katse kiran ta kuna shiga whatsup dinta ta tura masa msg din lambar sannan ta koma cikin yan uwan ta suka jone sunna shan fira

Anmy kam tana raka likita bakin get din farko ta dawo zuciyarta cike da farin ciki da addu'a, ayanawa take yi kamar haka' Allah ya ALLAH, Allah ka sa cikin nan bai zube ba, ya rab ka sa cikin nan na nan.....'

Da wannan farin cikin ta je ta shige kicin da kanta ta shiga Wora girki da ta san a lokacin cikin Najeeba na farko ta so shi sosai , du burinta dan ta ga in yanzun ma zata so ne? Domin tunda ta haihu ta daina sha'awar abincin, wato taliya da man ja da yaji da kuma lemun tsami, haka kuma gefe guda tana tsaye kan harkar ruwan zafin umi karama.


Najeeba na ganin magariba ta yi ta shirya sannan ta ce da ummulkhair ta zo ta rakata su ga likita su dawo yanzu

Kasancewar itama a shirye take kawai abaya suka saka bakake manya irin budadun nan sannan suka bi da nikaf da su Safa,

A lokacin da suka zo yiwa anmy salama ta so hada su da Jakadiya, sai dai Najeeba ta zile ta hanyar nunawa Anmy din jakadiya ta je bangarenga da andiya su dauko mata wasu kaya a kilace mata, haka dai suka wuce ba tare da jakadiya ta bi su ba suka samu Sarkin bulala da direba na jiransu

A lokacin da Najeeba ta turawa Aida msg kan aikin da ta sakata a lokacin ta duba msg din yaron da ta ba aiki

Ai kuwa ta ga localisation ya turo hadi da adrss da komai.....sannan ya rubuto msg cewar idan ta fito zai sake kiran layin saboda ya jonata ne cewar yana sonta yana so zai shigo gari daga Niamey, yanzu haka yana son saka mata kudi, kuma ya tabbata zata daga Dan har ta turo account numberta dan a saka kudin katin da yace zai saka mata

Ai kuwa Najeeba ta mayar da wayar jakarta ta yi dan murmushi har suka isa asibitin

Sunna shiga Sarkin bulala ya ajiye su, Najeeba ta duba wayarta a tausashe ta ce" Sarkin bulala"

Sarkin bulala ya sada kansa da girmamawa ya ce" Umarnin ki nake jira uwar dakina"

Najeeba ta ce" Zaku yi jiranmu fa, domin likitar bata shigo ba tukunan"

Sarkin bulala ya ce" In sha Allah uwar dakina muna nan muna jira"

Daga haka suka wuce suka nufi ciki

A lokacin da suka tunkaro wajen da zasu shige saboda su ga likitar Najeeba ta kama hannun ummulkhair suka shige kwana inda aika ke tsaye

Cikin gaggawa Najeeba ta amshi abayar hannunta ruwan ja mai haske ta saka, ta yane fuskarta ta Wora wani katon glassss fari sannan ta bata abayar da ta fito da ita ta amshi ky din motar da ta zo da shi ta juyo inda ummulkhair ta yi summan tsaye ta riko hannunta ta girgiza ta tana dubanta ta saka mata jakarta da wayarta ta ce" Ummulkhair, ke dubeni"

Ummulkhair ta dubeta a zabure

NAJEEBA ta ce" Rike min jakar nan, da wayata a ciki saboda na san a lokacin da labari zai je kunnensa sai ya fara sakawa an yi lokalize dina......, sannan zai nemi Sarkin bulala, idan Sarkin bulala ya zo nan inda ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login