Showing 138001 words to 141000 words out of 144591 words

Chapter 47 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2363

fadin to bai yafe ba du Wanda ya sake amsar maganin da za'a cutar da wani , bai hana mutun ya nemi kariyar kansa da ya'yansa ba, Ama in dai dan ka je ace maka an yi maka asiri ne kaima ka amshi abinda zaka rama Allah ya isa, ya dora da nasiha da nunin cewa babu wata riba a sabawa Allah sai shiga uku, kuma a dade ko a jima sai Allah ya fito da halin kowa sannan ya sakawa wanda aka cutar, a je a yi biyayar aure a zauna lafiya, aurenta da mijinta su sai dai su ce gwonda da aka yi, rufin asirin Allah kala kala uwa uba yana girmamata yana girmama ahalinta, to me take so sama da wannan? Idan ta haka zata godewa Allah ai ga fili ga Mai doki, in har baka iya godewa ni'imar Allah ba, to kuwa zaka godewa azabarsa......
Sannan yayi kashedi da Babar murya ya raba y'arsa da auntynta, yace ne in ba dalili kwakwara ba ya ji labarin ta je gidan ita da ita ne, kuma in????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? har ta yarda ta kuma daukan hudubar tsiyarta bai yafe mata ba!, wannan abin ya sake sakata a duniyar tunani da karatun ta nutsu harma ta zo ta nemi komawa irin na da , da din mai karko ba ta tunzurawar auntynta ba, domin a dawowarta har ta sake neman mayar da su Muhammad jikinta, bayan a da yaran yan dakinta ne, a hankali ta ture su da kyara, hantara, daure fuska bisa hudubar auntynta, Ama a yanzu sai take neman su koma irin na da, dan kuwa shi Abdallah tuni ma ya sake, bale da take sakar musu Aliyu ta yi tafiyarta, Muhammad ne dai in tana waje yake kame kansa baya yi mata rashin kunya Ama kuma baya sakin jiki da ita, sai ta tafi yake daukan Aliyu ya rungume yayi shiru, dan har barci suke yi rungume da Aliyu


Tsakaninta da Najeeba kuwa du yadda take boye boyen sai da ta dawo ta saku harma suke shiga lamarin juna, kuma cikin ikon Allah har yanzu da cikin najeeba ya kai wata bakwai da yan kwanaki basu samu sabani ba saboda har zuwa yanzu bata wani sake irin na da ba, sama sama dai suna shiga lamarin juna, bale idan aunty A'isha na gidan ta fi sakewa dan A'isha ta kowa ce, Bama kamar yanzu da cikin najeeba yayi wata irin girma tamkar yan biyar ne a cikin saboda nan da nan cikin ke kara girma kuma kamar abinda ke ciki ya dara biyu.....sai dai du an ajiye a matsayin biyun ne.




A yanzu idan ka ga yada Najeeba ke tafiyar da rayuwarta sai ta baka sha'awa

Yanayin cikin nan nata ya kara kusanci tsakaninta da mijinta........, yana matukar tausaya mata, shi yasa koda yaushe zaka ga ya nemeta koda ba ranar girkinta bane kuma zai daga waya ya ji yaya take.

Cikinta ya zo mata da yannayi na jaraba ne, Duda yanzu ya kai wajen da namiji baya gabanta, Ama sai ya zama namijin ne yake gabanta domin da wahala a kwana biyun nan bata shiga halin neman anini ido rufe........, hakan ya sa shima zuciyarsa ke kan abini dan du inda ya kwana Waya a na biyun zai shiga tunanin yaya za'a yi to a tsoma Lipton a cikin shayin dake nesa? Da kyar dai mata da maza ke hakuri har a matso da Lipton din kafin ya amshi tsome .


A lokacin da ta ba wata takwas baya Docter ta shirya ta zo fada da kanta saboda ta yiwa Anmy magana a kan yanayin cikin da girman cikin da kuma irin yadda a yanzu Najeeba ta zama abin tausayi da ita.


A lokacin da ta zo ma, ta samu Muhammad da nayla na matsa mata kafafu, ganin docter ta janye da sauri , dan Docter ta fada mata ba'a yiwa mace mai ciki dane danen jikin nan, ba kyau, tana murmushi hadi da sosa kai ta ce"








>??>??>??>?? Saura kirisssss>??>??>??
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




Karshe 50



Tana murmushi tana sosa kai ta ce" Aaunty ce? Sanu da zuwa aunty, kin ga kuwa yanzu ne Muhammad ya nace sai ya dana min ?afafuwan nan, bari in kirawo Anmy din"

Ta yinkura zata tashi,

Docter bata hanata tashin ba dan ta sake ganin yannayinta, tana murmushi tana kallon ta har ta mike ta nufi ciki


Murmushi Docter ta yi tana zaunawa hadi da amsar jakarta da aka kawo tana duban yannayin Najeeba wace ta dawo daga dakin Anmy ta ce" yaya jikinki Daughter?, hop kina dan sport ko?"

Murmushi ta yi a tausashe ta ce" Ai tunda kika yi maganar sport a gabansa ya mayar da abin ibada, yada Bama fashin Sallah haka Bama fashin sport"

Docter ta yi yar dariya, lokacin Anmy ta taho tana murmushi hadi da yiwa DOCTER sanu da zuwa, sai Najeeba ta yi dakin Anmyn dan ta basu waje

Bayan sun gaisa ne Docter ta ce" Hajiya, zuwa na yi in duba patient din tawa, saboda irin yada na ga kai ya juyo tuni a wanan awon da aka yi mata....."

Anmy ta Wan zaro ido ta ce" Docter, na zata da saura? Watanta takwas da sati uku ne yanzu ko?"

DOCTER ta gyada kai tana cewa" Eh Hajiya, Ama kin san haihuwa kowa da yadda take zuwar masa, wani fa baya taba cike wannan wata taran, da wuri yake samun lafiya, wani kuma ka'ida ne sai ya cike cif, wani kuma sai ya haura , to abinda yasa ma nace bari in zo da kaina Hajiya dan in fada maki da kaina ne, da an ga ta fara jin wani abu a yi gaggawar zuwa asibiti, kar a barta a gida....."

Da dan yannayin tashin hankali Anmy ta ce" Docter akoy wata damuwa ne?"

Docter ta ce" A'a Hajiya, kin ga irin maganin da aka bata din nan ne nake dubawa, da kuma irin yada kowani wata yake zuwar mana da sabon abin da zai sa dole in so ganinta a asibiti da wuri, saboda kin ga hoton nan da ake yi mata na cikin wani lokaci ya nuna biyu, wani lokacin ya nuna uku, bana so a dauki kowani risk din haihuwa a gida ne, sannan a yi ta addu'a Allah ya sauke ta lafiya"

ANMY ta gyada kai, a hankali ta ce" In sha Allah Docter, zan kula, kuma itama zan saka mata ido sosai da sosai, Allah ya biya ki Docter, Allah ya sauke ta lafiya"

Docter ta amsa da amen sannan suka shiga dan taba fira da Anmy domin har awon hawan jini ta yi mata da komai kafin ta tafi, domin Anmy nada kayan awonta a gida tun crise din da ta yi shekarun baya.

A dan tsakin nan Najeeba na fama da nakudar tsayenta ne baki alekum, domin babu wanda ta sanarwa, hasalima ta mayar da hankali kanta da kafarta wajen yin sport na kirki , hakan ya sa ba lalle ka gane cewar tana taba nakuda ba

Dama tunda suka je aka yi hoton cikin nan ya soke mata shan ruwanmu na pampo da na galan, ya zamo ruwan zamzam ne ruwanta a koda yaushe ta yi bukatar sha, sannan malami ya dage kusan KULUN sai Sultan ya shigo mata da rubutun da malami ke yi na tsari ya tila mata ya bata da kansa, itama bata gardama take amsa ta sha abinta , ga zuma a gefe da kayan itaciya da take sha Duda basa bari ta sha abarba saboda risk din da take iya haifarwa na matsalar cikin, da kuma hanta wace itama akace kar ta ci tana hadasa zubar jini wa mai juna biyu.


Kasancewar basu daina yin zaman su na karshen sati ba, wato ranar juma'a da dare, hakan ne yau ma , ya kama daren juma'ar da cikinta ya kai wata tara da kwana uku

Tunda safiya ta waye kafin ta baro bangaren Anmy take jin cewar yau fa da wahala idan abinda ke cikinta bai shigo duniya ba, saboda tunda safe take jin ciwon na yau daban ne da na kwanakin bayan da ta ringa sha, wato ciwon nakudar tsaye.

Tunda suka je bangarensu ita da Auta da Andiya, sai ta sa andiya da Auta suka shiga hidimar zaman da ake yi na karshen mako, ita kuma ta shige dakin ta rike da carbinta ta yi ta kai kawo tana fama da kanta har magariba ta shigo ta samu ta yi wanka a dadafe sannan ta zurma doguwar rigarta hadi da Wora dan baby hijab dinta kafin ta fito Falon ta samu yan matan sun gama shirya duk wani abin da ya dace

Tana murmushi hadi da kame haba ta ce" Lalle yaran nan aure kuke so, kun iya shirya gidan mutun babu abinda yayi saura"

Kunya ta sa yaran soke kai , auta ta ce" kai aunty kai aunty, sai dai in y'arki ke so, Ni kam a barni in kara hankali"

Najeeba ta yi dariya ta je ta zauna tana fadin" Ai fa, ke zan fara kaiwa dakin miji kafin yata, kin ga auta, je ki dauki kuka ki kada min da ruwa mai dan dumi kadan ki kawo min"

Auta ta ce" Kuka dai ita kadai?"

Najeeba ta gyada kai tana dan rintse ido hadi da saurarawa kafin ta ringa sauke ajiyar zuciya

Andiya na ankare da yannayinta ta zo daf da ita ta zauna tana fadin"Mah are You ok?"

NAJEEBA ta mika hannu ta amshi kukan da Auta ta kado mata kofi guda ta rintse ido ta kafa kai ta shanye kafin ta ajiye tana yiwa Andiya alamun ta bata ruwa, ta mike da sauri ya dauko mata ta sha tana yatsine fuska ta ce" Alhamdulilah, kin ga, ki dauke jug din cen da kika fido na babanku, a zuba masa zobo kadai ya ishe shi, auta ke kuma kara turaran wuta a Falon nan bai isa ba"

Du Mikewa suka yi suka shiga yin abinda ta umarce su, zuwa lokacin Nadiya ta shigo , hanunta dauke da wayar ta kadai, bayanta kuwa Abdallah ne rungume da Aliyu, sai Muhammad dake rike da hannun Nayla sai surutu take zuba masa shi kuwa sai dai yayi mata murmushi ko ya dan zaro ido hadi da rike haba irin abu ya bashi mamakin nan, Ama ba zaka ji Muryarsa ba kamar yada zaka ji ta Abdallah

Hannunsa ta saki suna rige rigen ruftawa Najeeba,

Da sauri Nadiya ta tare su tana cewa" Kai ku yi a hankali mana bakwa ganin maman naku nata da lafiya?"

NAJEEBA ta yi murmushi tana fadin" Malama kauce, Ni nace maki banda lafiya ne?, zo nan yayan Mama, ku zo yau du ban ganku ba, aunty Aida ta muku kitson mai kyau kuwa?, Nayla baki yi kukan kitson yau ba?"

Anmy karama ta yi dariya tana zaunawa a gefen kujerar ta ce" Mah, ke da kin san y'arki?, harda fitsari da ta saki a wando, yarinyar nan dai Allah ya sawwaka mata Ama ai akoy shagwababiya"

NAJEEBA ta dan harareta tana dan dantse lebe da rike gefen hijabinta tana jin yada mararta ta gama yi mata nauyi sosai, ga wani irin ciwo irin na nakuda mai wuyar fasara, ta Wan kama saboda ta mike ko zata iya takawa sosai, tana cewa" kai fa ANMYNA, ke dai baki kula ba da kyau, jaririyata bata kukan kitso ko anmatana?"

Nayla ta gyada kai tana rike hannun NAJEEBA har ta idasa Mikewa sai kuma ta Wan duke tana rintse ido

Nadiya ce ta fara kula da yanayin nata, da kula ta ce" NAJEEBA jikin ne? Ko in kira Anmy?"

NAJEEBA ta girgiza kai a hankali tana ta kokarin mayar da numfashi kunnayenta na jiyo mata sanarwar shigowar Aban su Muhammad dan haka ta jure iya jurewa har aka bude masa ya shigo, yana sakarwa yayansa murmushi da suka ruga sunna rukunkumeshi hadi da yi masa sannu da zuwa, ya kai dubansa kan Nadiya da ta karaso dan amsar alkyabarsa ya sakar mata murmushi yana dan sada dubansu alamun amsa oyoyon da take masa kafin ya kai dubansa inda Najeeba take , wace ta yi iya yinta dan ta sakar masa murmushin itama Ama ina, yannayin fuskar ta kawai ya nuna bata cikin halin dadi, dan haka da kula ya budi baki ya ce" Beebah, Are U ok?"

Najeeba ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta daga kafa da nufin yin gaba, sai dai abinda ta ji ya tsinke mata ya sa ta zaro ido a tsorace tana dubansa hadi da duban Nadiya murya cen ciki ta ce" Nadiya, i'm not ok, ina zubar da ruwa......."

A tare suka kalleta a tsorace, kafin Nadiya da sauri ta karaso dan ta kamata su zauna, sai dai a yanayin da take ta ganar da ita cewar bafa zata iya zaunawa ba

Da sauri Nadiya ta nufi hanyar Anmy saboda yada ya bata umarnin hakan, kafin Auta ta ja yaran nan gaba daya ciki, shi kuma ya karasa ya kama Najeeba da kyau yana fadin" Zaki iya tafiya? Ko in dauke ki?"

NAJEEBA ta dantse lebe , da kyar ta Wan langwabar da kai kafin ta cira da dukan jarumtarta tana bin sawunsa, yana talabe da ita har Anmy ta shigo da mugun sauri, ga waya a kunnenta tana magana da docter kafin ta ce" Eh kam Docter haihuwa kam ta zo, Nadiya yi maza ku kai kayanta mota ku bi bayanmu......, kai wannan yaron, kana ji? Yi maza a karasa mota da ita kar ta haihu a nan"

Likitar da kanta sai ta mike da sauri tana fadin" Bari mu jira ku a waje, Allah ya sa na shigo duba patient din da na yiwa aiki jiya, Allah ya kawo ku lafiya"

A hankali ya tafiyar da ita har daf da baban falonsa, inda aka kawo mota ya bude ya shigar da ita sannan ya samu kansa da shiga shima jikinsa sai neman daukan rawa yake

Zagayawa Anmy ta yi ta shige tana aikawa Ummi kira ta sanar mata, sai dai kamar yada ta sani ummi sai kawai ta yi addu'a kafin ta kashe, a dole ta yi kiran Abiey ta sanar masa a lokacin SULTAN ji yake yi kamar zuciyarsa zata tsaya da aiki, sai shasheka yake yana yi mata fifita har suka gangara inda aka fitar da gado ake jiransu

Cikin gaggawa likitocin suka dorata saman gadon, sai dai cikin ikon Allah Sultan na biye da su yana rike da hannunta a hankali yana faman yi mata sannu, har aka zo shigar da ita kafin Docter a tausashe ta ce" Allah ya taimake ka a nan zamu Barka, a yi mana addu'a"

Daga haka Anmy ta riko hannunsa suka dakata baya kadan aka shige da ita dakin haihuwar

Tunda aka shige da ita ya harde hannayensa a kirjinsa ya zubawa hanyar da aka bi da ita ido yayi shiru ya kasa kwakwaran motsi, har sai da Sarkin bulala ya ringa shigowa da kujerun zama sannan Anmy ta nuna masa a tausashe ta ce" Zo zauna .......ka yi mata addu'a ya fi tsayuwar"

Da kyar ya iya sauke ajiyar zuciya, a hankali ya je ya zauna yana hangen isowar motar dake dauke da jakadiya da Nadiya da kuma ungozomar fada, sai dai du baya suka tsaya Nadiya kadai ce ta ringa sanyo kayan kafin ta zauna itama suka ci gaba da jira........

Cikin lokaci kankani su Dayabu suka karaso suma , shi da matarsa, sai kuma su Ummi suka zo suma iya da Abiey, suka hade ya zamo sun cike dakin jiran kowa na faman jan carbi sunna sauraro.......

Minti talatin tsakani kakarfan nishin fitar da kan d'a ya karade kunnayensu......

Da sauri SULTAN ya mike saboda shigar nishin kunnensa sai da juziyarsa ta wani irin bugawa......, sai dai Ummi bata bashi damar karasawa ba a tausashe bayan ta rike hannunsa ta mayar da shi ta ce" Ka yi hakuri, ka zauna, an fara samun lafiya ne, haihuwar ta zo ne..."

Gumi ya RINGA wanke goshinsa da jikinsa.....hakan ya sa yaya Dayabu komawa daf da shi ya zauna hadi da rike hannunsa a tausashe ya ce" In sha Allah zata samu lafiya yaya "

A hankali ya gyada kansa yana ci gaba da jan carbi, Abiey kuwa dama tunda suka zo yake kai kawo kai kace shine ke rike da cikin ba Najeeba ba.........

Daga inda suke sunna iya jiyo kukan baby, wanda hakan ya sa du suka mike sunna ta kalon kofar, sai dai ba damar shiga saboda likitoci ne ke ciki harda likitan jarirai wanda yake dakin jarirai du idan za'a yi haihuwa yake zuwa da an haihu ake mika masa ya kula da jarirai su kuwa masu amsar haihuwa su kula da maman baby

Fitowar Docter da sauri tana tambayar a bata kayan baby ya sa Nadiya juyawa da sauri ta ciro kaya unisexe ta mika mata

Amsa ta yi ta koma tana yiwa su Anmy alamun tana zuwa

Jim kadan ta dawo ta sake tambayar wasu kayan, hakan ya sa Anmy fara zubar da hawaye tana duban Ummi ta ce" Wayo allahna, biyu ne , wayo biyu ne? Likita biyu ne?"

Likitar da itama take cikin halin rabuwar hankali saboda Docter baba na sakata wasu aikin, docter din yara na sakata wasu, dan haka ta sake nunawa cewar likita zata fito ta musu bayani.......

Bayan wannan an dauki wani lokaci kusan minti ashirin du sunna tsaye sun kasa zama, sun kasa tafiya, likitar ta sake fitowa itama jikinta na rawa ta ce" A bani wasu kayan"

Da sauri Ummi ta tare Anmy da ta nemi zubewa jikinta na daukan rawa, SULTAN kuwa sai ya tsaya kikam ya bude baki ya ce" Nurse, uku ne?"

A dole wannan karon likitar ta dakata da girmamawa ta ce" Uku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login