Showing 87001 words to 90000 words out of 144591 words

Chapter 30 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2339

ko ta mulki, ko ta mata ko namiji waye zai iya juya musu baya in zaba walahil azim zan zabeta, dan kuwa kai dai a yau kana iya haduwa da macen da zata da ka bita duniya MUTALAB! Haba malan ya zaka wani dage kana zazaga min bayan na fada maka abinda yake faruwa ne????"

Yana karasawa parking ya fito daga motarsa ya ga Dayabu jikin tasa motar shima yana jiransu dan ya rigaye su karasowa Fadar

Har dira yake ya nuno mata hannu ya ce" Ni ko? Ni Maryama zaki wulakanta ko? Nine zaki ce wai a kan mace sai in bar y'ayana in tafi in bita ko? Nine zaki rainawa wayo ko Maryama?"

Ummi ta cire kai tana sauke kyaftu ta yi gaba kasa kasa ta ce" Da ace baka aikata din ba ai da sai abin ya zama na gardama, Ama malan zaka tsaya ina nuna maka gaskiya kana rintse ido? Gaba dayanmu masu laifi ne saboda bamu zauna da ita ba, Ama kuma ba shi zai sa ka nuna matar nan mai adalci Y'ar uwar ka da ko yau na shiga kabari na san ban bar marayu ba wai zaka iya yi mata wani abu, Ni din dai ka min, Ama na fada wallahi tsaf zaka iya hade kayanka sai dai mu wayi gari mu samu kun yi nisa mai mutuwa ya mutu!"

Aba MUTALAB ya damki hannun Dayabu sama sama ya ce" Bilahilazi idan baka rabani da uwarka ba sai na bata ran kowa a gidan nan, Ni za'a rainawa wayo? To na fada in ba'a fido min y'a ba daga ke din, har ita Balkissar sai ran kowa ya bace"

Ummi ta Wan daga murya ta ce" Ka haWa harda Sultan din mana tunda ai shima mai laifin ne!"

Aba MUTALAB yayi tsuru tsuru yana kallon dogarai da suka juyo sunna kallonsa dan kuwa ita ta shigewarta doguwar hanyar da zata kaita bangaren Anmy

Kasa kasa ya ce" Ka ga Shari ko? Zata hadani da yaran gidan nan ko?"

Yaya Dayabu fuska cinkushe ya ce" Abiey me yake faruwa?, Me aka yi har ta fita? Ina ta je???"

Abiey ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Ni dai na san rabona da ita tunda aka ce za'a koma a yi hoton cikin nan, bayansa ban san me ya sake hadasu ba, kawai sai kiran zahra'u na samu dazu tana kuka tace wai gidan a rikice saboda Najeeba da Sultan, shine fa maman naku ke ce min Najeebar ce ta gudu wai"

Dayabu ya ringa numfashi sama sama, kafin ya daga kafa fuuuuuuuu

Da sauro Aba ya riko shi ya dawo da shi baya yana dubansa ya ce" Kai me zaka yi?"

Yaya Dayabu ya bude baki hawaye na bale masa ya ce" Idan ba'a zama da kanwata a san inda za'a hau a bani takardarta Ni na zan zafin abina, wallahi na san ciwon abina, in har ba'a zama da ita a salameta ai ba addini ne yace sai ta aikata kisa ko kaucewa hanyar aure za'a iya Sakinta ba, in an ga har an gama cin moriyar ganga za'a yada kwalonta ne dan za'a auro guzumar mace sai a sau min ita in san da lasisin fitowarta in adana abina !"

Gaba daya sai Aba MUTALAB ya rasa habaici ake masa ko iskanci, sai dai ya riga ya dan a yadda suke saman nan idan shi bai sauko ba wani rikicin a gaba

Dan haka a tausashe ya ce" Ama ka san mijinta yana son ta, kuma kai namiji ne karin aure kamawa yake yi ai ba wai dan an tsani ta gidan za'a karo wata ba, kuma bayan wannan ya dace ka sassauta muryarka ka kuma bi komai a hankali, kai fa namiji ne kar ka yi abinda zaka dawo ka ji kunya saboda son zuciya ka kasa shigowa gida???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?n nan daga baya, ka ji abinda na fada maka?"

Yaya Dayabu ya fashe da kuka ya ce" Ina zata je? Wajen wa zata je? Idan wani abu ya sameta fa? Wayo Aba "

Tausayin yaya Dayabu ya kama zuciyar Aba, ya sani ne ko shi da ya haifi ya'yan nan bashi da kusanci da su irin yayansu, ya sani ne idan ba'a ga Najeeba ba komai na iya faruwa da y'an uwanta, dan haka sai kawai ya dadaba gefen kafadarsa a hankali ya ce" Ka jajirce, ka yi hakuri, kai fa namiji ne, mu je mu ji abinda yake faruwa kafin ka daga hankalinka "

Hawayensa ya riga sharewa sannan suka dauki hanyar suma

Irin yadda suka samu Falon ya sa hankalin yaya Dayabu sake tashi, saboda Anmy a zaune take saman kafet hannunta rike da carbi da kuma tissu tana ta share hawayen fuskarta, Ummi na zaune rike da hannunta sunna magana, kusa da su su zahra'u ne ?owace fuska ta cabe da hawaye, uwa uba SULTAN dake zaune saman shinfidar da zahra'u ta yi masa wanda idan yace a kasa zai zauna ake fitarwar, dama kuma tunda suka ga Anmy a kasa sun tabata shi ba zai hau kujera ba, ya kawo mayafin rawaninsa ya rufa a saman kansa yadda ka san sabon liman , kansa a kasa, ba zaka gane me fuskarsa take ciki ba sai idan ya dago ne, a haka kuwa kansa a kasa yake bai dago din ba

Yaya Dayabu na sanyo kafa ya'yan Anmy suka samu baki, saboda gaba daya sai suka nufe shi suka rukunkume shi har suka kai shi kasa saboda sun masa yawa, hankali tashe sunna kukan da suka tsagaita saboda zuwan Ummi da tace zata ci uban mutun, yanzu da suka san ko yayane zai tare suka baje masa nasa kukan kowace na faman fadin ina Najeeba ta tafi?????

Aba ya tsallaka ya je kusa da Sultan ya dage mayafin

Dago idannuwan da SULTAN yayi sai da gaban Aba ya fadi, saboda idonsa ya hade da kwalin nan yayi jajajir , fuskar kanta ta dau ja kamar kosan gwana

Mayar masa da mayafinsa yayi ya rufa harda hade gefe da gefen ya mike ya koma kusa da matan dan a gaskiya shi bai cika son hayaniya da saraki bane Bama tun asali

Ai kuwa yana zuwa ya bude murya ya shiga zabga balaki , fadi yake" Najeeban Ni zata rainawa wayo? Gidan wa zata je? Duk inda ta je idan na ganta na kama dukanta sai ta suma a gidan nan!"

Ummi ta zubawa mijinta ido, kai da ba dan ba dan cewa miji ashe munafiki bane yau da ta fada, mutumen nan Akoy Are aren fuska, sak halinsa ne ai Najeeban ta yi
Ta dauke kai tana girgiza kai a ranta ta ayyana ' Ai dama sai dai ka yiwa Maryama da Balkissa ihu, Ama ba zaka yiwa d'anka ba , da ka isa ka masa mana ai gayanan!'

Aba yi yake yi kamar zai ari baki, Sai da anmy ta fashe masa da kuka tana dubansa ta ce" Haba yaya, haba yaya, kaima maimakun ka tayani da addu'ar Allah ya kare min ita a duk inda take ta dawo min da wuri sai ka nemi daga min hankali? Haba yaya"

Aba ya hade fuska ya ce" Yi min shiru, shi yasa ai ya'yan nan suke tunanin sun fi karfin mu, to basu isa ba, ba zamu bi su ba, ba fita ta yi ba? Ina nan ina jiranta du inda ta je ai za'a ganeta a daure a kawo mana ita gidan nan mu hadu mu ci ubanta!"

Shigowar Muhammad da gudu daga coridor ya nufi mahaifinsa ya fada jikinsa , jikinsa na rawa hadi da Waukan zafi lokaci daya Muryarsa a raunane ya ce" Abiey, wai, wai andiya ce take ta kuka, da na matsa mata menene sai tace wai ba'a ga Anmina ba? Abiey, ina Anmina?, ita da tace zamu yi cake da ita dazu?????"

Cike da tausayi ummi ta mike dan zuwa ta kama Muhammad saboda gaba daya ya yaye rufar ta mahaifinsa wanda ya auna a kan kamar amarya yana nema ya bayyanar musu da fuskarsa bayan babu mai bukatar gannin yannayin nan a nan, ta karaso ta kama hannunsa a hankali ta ce" Mijin, taso taso masoyin, kai an san inda take fa, taso"

A hankali Sultan ya rike hannun Ummi, Muryarsa cen ciki ya ce" Ina so in ji abinda aka yanke, a sanar a gidajen yada labarai batanta ne, ko a cikin sirri zamu nemota? Saboda dare yi yake yi, bana tunanin in har zan iya rintsa ido a daren nan idan ban ganta ba........"

Yaya Dayabu ya rintse idannuwansa, baya sannin yana tausayin baban mutumen nan sai abu ya hadasu shi da Najeeba, innalilahi wa Inna ilaihi raj'une NAJEEBAH ina kike? Me kike yi? Ke da wa???????


Ummi a sanyaye ta dubi Abiey ta ce" Ka zauna mana dan Allah, a yanke shawarar in a je a sanar a duk wani kafar sada labarai ko? "

Abiey ya zauna yana dubansu ya ce" A je a kai kawai ko???, ko Akoy wani dalilin da zai sa kar a kai????"

Yaya Dayabu ya dubi Sultan yana jiran amsar sa domin da zarar an ce a je a kai din yanzu yanzu zai tashi ya je du inda ya dace ya kai

Sultan ya dubi Abiey, a hankali ya ce" A kai din zai zamo an samu masu tayamu nemota sannan za'a iya gaggawar sannin inda take saboda da an ganta za'a fallasa ga inda take......., sai dai kuma........ A kai din ma zai sanar da magautana cewar.......abinda ya fi gaggawar kaini kasa na filin farauta, ta yadda ranta zai iya shiga cikin lamarin....."

A tsorace du suka kalle shi, Anmy muryarta na rawa ta ce"
https://chat.whatsapp.com/BuEB69AOiqBKg0PMiBzdG3
*Kayan kitchen kike nema?* *Laces ko atamfa ko* *materials?? Yar uwa muna da takalma ,jaka akwatuna d kayan parlor* *nd toiletries, d sauran* *abubuwa d dama kuma* *delivery nationwide In* *sha ALLAH=?
? sannan* *muna bada kaya a* *farashi mai sauqi domin masu siya su siyar kiyi* *joining domin ki amfana* >??>??



>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




30





A tsorace du suka kalle shi,, Anmy muryarta na rawa ta ce" Na shiga uku, kar dai mutanen da suke da ido a kanka su san da maganar nan a nemeta a ilata ta? Tana da wata kama fa"

Abiey ya dubi Anmy, ya kalli Ummi da kanta ke kasa, yanzun kam Muryarsa da sanyi sosai ya ce" Inaga, ya fi dacewa mu bar maganar a nan, ko har an sanar a fada abinda yake faruwa?"

Kai SULTAN ya girgiza ya ce" Babu wanda ya sani"

Abiey ya ce" Hakan ya fi, mu sai mu bi du inda muke tunanin samunta
in sha Allah Bama zata yi nisa ba"

A hankali Anmy ta ce" To yaya za'a yi da batun WA'INDA ake tunanin idannuwansu a kanku?"

A hankali Sultan yace" A da, na basu damar gama kallon duk abinda suke so...., Ama a yanzu har Allah ya bayyana min ita Nine zan maida dubana kansu....."

Abiey ya gyada kai ya ce" Hakane Allah ya aminta, Allah ya tsareta a duk inda take"

Sultan ya dago kan Muhammad yana dubansa a hankali ya ce" Ba na hanaka kuka ba?, ka yi addu'a zata zo ba nisa ta yi ba in sha Allah ka ji???"

Kai Muhammad ya gyada, sai dai yana cikin kukansa, ummi ta kama Muhammad ta hada shi da ummi karama suka wuce Sangaren yan matan

A hankali SULTAN ya furta" Na rasa gane girman laifina......., Na rasa gane wani adalci ne na gaza yi"

Anmy ta Dube shi, ta girgiza kai ta ce" Wani irin ka gaza ganewa bayan a takardar nan ma sai da ta fada cewar baran gidan nan ya fi ta fada a dauka a wajenka ?, yaya ma za'a yi a kawo maka magana irin wannan ka hau ka zauna?, Najeeban mahaukaciya ce ita da ba zata ji ka fice mata a rai ba? Dole zata ji ka fice mata a rai ai"

"Haba ke kuwa besty, ki sassauta masa hakanan please, ya dace mu tashi kowa ya nufi inda yake tunanin zata iya zuwa"

A hankali Anmy ta ce" Maryam, kin san Allah, ina so in ji abinda ya yi mata, yace bai mata komai ba Ama Ni bana tunanin in har hakane, saboda ai a tunanina lokacin su samu maslaha ne tunda har gaskiya ta bulo cewar wannan yarinyar likitar nan itace munafukar da ta bata maganin, daga tashina Shikenan sai ya dawo min da maganar bata nan?"

Abiey ya dubeta ya ce" Yaushe gaskiyar ta bulo? Ikon Allah, Maryam kin ga da nace maki bata iya karya ba ko?"

ANMY ta ce" Dazu fa wata yarinya suka zo da iyayenta , kurma ce ita ke yiwa aminiyar likitar nan aiki, yarinyar ce ta fallasa komai a nan, Ni dama na san fa yarinyar nan bata aikata abinda ake tuhumarta da shi ba, Shikenan sai kuma ace min bata nan? Me ka yi mata ne dan ALLAH????"

Sultan ya rasa mema zai ce yayi mata, shi da kansa da ace ya gane abinda yayi matan da ya samu sukuni a zuciyarsa, saboda a Dazu dai shi a cikin hankalinsa ya san bai yi wani abin da zai sake daga mata hankali ba, hasalima ya so su je bangarenta ko nasa dan ya bata hakurin abinda ya faru ya tabbatar da ta yafe masa Shikenan a ci gaba da rayuwa, sabani ne ba yau suka fara samu ba, sai dai fir ta Kiya karshema ta aikata aikin nan? Ya rab.

A hankali yaya Dayabu ya ce" Allah ya sanyaya zuciyarki Anmy, abinda ya bata mata rai inaga da aka yarda da maganar yarinyar ne"

Ummi ta dubi Dayabu, a ranta ta ayyana ' Tabass a duniya kafin kowa ya fadi su waye ya'yan nan sai Dayabu ya fara fada, ita da kanta ta gama gano abinda ya karra harzuka Najeeba ke nan, sai dai ba zata iya fada ba .

A hankali Dayabu ya dora da fadin" Babu abinda yake saka bawa jin rashin karfi da rashin kuzarin walwala a tare da wanda yake rayuwa sai irin ya samu kansa da tunanin bashi da wani power, bai wani isa ba, ba'a wani yarda da shi ba......"

Kansa a sade ya ce" Ka yi hakuri yaya, abinda na fahimta ne nake son fahimtar da kai, ba raini bane, ba kuma dan in bata maka bane....."

Sultan ya zuba masa ido yana sauraron sa lokaci daya haske na shiga zuciyarsa da wani irin tunani da kuma gane gaskiyar kenan

Yaya Dayabu a hankali ya ce" Yaya, NAJEEBA, tana da fada, idan aka shiga hurumin ta bata cika yafewa ba, idan har mutun ya shiga sabgarta in ta tashi ita sai ta ninka......., wannan akidar da take da ita ya sa Najeeba bata cika shiga sabgar da ba'a gayaceta ba, ......sanin da ta yi cewar ba lalle bane ta hakura da abinda aka yi mata ya sa bata shiga abinda bai shafeta ba......"

A hankali ya dago ya dubi mutanen Falon, a sanyaye ya ce" A hankali, a hankali ta ringa zamowa mai laushi, ta ringa ajiye makaman yakinta, tun daga lokacin da zama ya zaunu ita da kai, na yarda cewar ta samu cenji mai girman gaske na halaya da dabi'u sanadiyar so......"

A hankali ya rike hannun zahra'u da ta gama murzar ido ya dan girgiza mata kai alamun ta daina kukan haka ya dora da fadin" Yaya Najeeba na son ka sosai, son nan ya sa lokuta da yawa sai dai ta sameni ta yi kuka kafin mu rufe mu birne........, domin babu gidan da babu hawa da saukan da take fuskanta, abu daya ne ya bambanta, irin yadda dama ta haduwar jini ya sa dole zata dauki wasu nauye nauye a kanta da kuma wasu hukunce hukuncen da ya dace ace itama ta samu yarda daga wajen wanda take da yakinin sunna da kusanci fiye da kowani dan Adam ..........."

"YAYAH"

Ya Wan yi shiru, idannuwansa na cika da kwallah

A hankali ya ce" Yaya zubar da ciki? Yaya ba tarbiyyar Iyayenmu bace, a tunanina ko shege ne suka samo Allah ya kiyaye, idan akace maka zasu zubar zaka ce a'a ne yaya"

Ummi a hankali ta ce " Dayabu ya isa haka"

Anmy ta share hawayenta, gaba daya jikinta sai daukan mijirya yake yi, kanta kuwa ciwo yake yi sosai, a raunane ta ce" Ki barshi dan Allah, ki barshi ya sanar masa, ko zai gane, ki barshi ya tunatar da shi domin du saninka wasu lokutan sai karamin abu ya shige maka......."

ANMY ta Dube shi, a hankali ta ce" Aban Muhammad"


Sultan ya kalli Anmy, wanda itama sai da hakan ya sa zuciyarta sake tsinkewa

A tausashe Anmy ta ce" Aban Muhammad, ka san menene laifinka?, laifinka shine kana manta cewar matarka sunnanta matarka, wace Allah ya saka hukunce hukuncen na hakin dake wuyanka nata, wa'inda suke da daraja ya zamo idan ka kiyaye tabas zaka samu yadda kake so da ita , ita din ma"

A hankali ta ci gaba da fadin" Ni na yarda da kana son ta, na Kuma yarda cewar a duniya tana cikin WA'INDA kake yiwa so daya da ba algussss, sai dai kashhhhhhhh, soyayar da kake yi mata ya sa kake tunanin idan ma wani ya zo maka da batun ta yi laifi zaku shanye abinku zaka hukunta kayanka , ciki harda abokiyar zamanta wace idan suka samu sabani zaka nuna Najeeba ta dau laifin, exactly irin yadda uwa mai alkunya ke yi idan an kawo karar ?a?anta, takan fatattaki ya'yan nata ne , ta basu rashin gaskiya sai daga baya zata nuna musu abin a cikin hikima, wanda hakan ba yana nufin bata son su ba, du cikin so da kaunarsu ne........ SAI DAI"

A hankali ta langwabar da kanta ta ce" Sai dai, kai ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login