Showing 135001 words to 138000 words out of 144591 words

Chapter 46 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2348

sai da ta matsar gefe ta fuskance shi ta yi masa dogon bayanin da ya gamsar da shi, ta Wora da fadin" Abinda ba'a so, ya zamo mace du garin da ta gani na siyarwa ta dira ta ta siya ta sha ba tare da sanin menene ba, bayan wannan ba'a so ya zamo ta mayar da shi KULUN kuma abinda dole sai da shi zata.....zata.....zata, abinda dai KULUN sai ta sha ka fahimta?, an fi so mace ta yawaita anfani da fruits, da su Peak din nan, sannan ka ga su miski din nan su kadai sun wadatar, Ama kuma zamani na tafe da ilimi kala kala, abinda ba'a so a ringa anfani da abu mai dacin tsiya, ko makamancinsa, ba'a son irin haka ...........PLZ ka dai dai sake bincike da mai ilimin abin sosai zaka fi fahimta......., bari in kirawo ta ku tafi a mata awon ko sai kun fito daga masallaci na ga lokacin sallar kamar ya kusa?????"


Da sauri Najeeba ta yi ciki tana kwaso shoki hadi da sakarwa Abdallah rankwashi kadan a gefen kai tana sake dungure kan ta ce" Yaro kauce kauce in shige"

Ya yi dariya yana ganin yada take dariya ya bi bayanta dan rabonsa da ganin haka sun jima ai

Abiey kuwa a falo ya wani gyada kai bayan Anmy ta tashi ya sake kalon SULTAN ya ce" Tashi ka haye sama kar yarinyar nan ta sameka a kasa a zaune saboda ita......, kai yanzu kai da zaka jure ka cire kai in bada umarnin a baka matarka shine ka wani zube kake bada hakuri ? Salon gobe ma a maka iko da matarka? Sai kana cire kai kana jurewa kana hade fuska fa, idan ba haka ba matan nan sai su saka mutun a wani hali......, kuma maganar maganin matan nan da na maza da Ni zamu yi"

Sultan SHAHEED ya dubi Abiey da sauri, sai kuma ya kalli wajen TV a ransa yana ayyana ' innalilahi, ana ta sakayawa shi Abiey ya fadi abinsa kai tsaye, kai ina ka yi maganar nan da wa? A'a zamu yi abinmu da beebah kawai, du abinda ta kwatanta min zan fi ganewa sosai da sosai, Ama kaina a kasa zamu yi magana in gane me?, kuma Ni zan yiwa Anmy garage ta bani ita din mu je mu dawo a hanata bina dakin mu a kasheni? A'a gaskiya a wajen da ake iya kokowa ake jan fada, Ni a bani matata ma yi sallar a hanya'

Sunna dan Zantawa aka fara kiran sallah, sai kawai suka wuce masallaci .

ANMY kuwa na zuwa ta samu Najeeban saman salaya tana zaune, Abdallah kuwa yana buga game da wayarta

Bayan ta dubeshi yana yi mata sanu ta ce" tashi ka je masallaci yanzu za'a kira"

Mikewa yayi ya ajiye wayar ya wuce dakinsu dan ya ja dan uwansa su tafi

Zaunawa Anmy ta yi tana duban Najeeba wace ta ce" Anmy, ai sai mun yi sallah zamu fita ko?, na ga itama bata zuwa da wuri fa asibitin"

ANMY ta zauna da kyau tana fadin" A'a, ai tana cen tana jirnmu ma, tunda ta san da zuwan"

NAJEEBA a ranta ta ayyana ' na shiga uku, Anmy zata kai nin?'

ANMY ta Wora da fadin" Zo nan Daughter"

NAJEEBA ta tashi ta karasa ta zauna daf da Anmy

ANMY a tausashe ta ce" Kina ji na?, ina so in sake yi maki nasiha , saboda Allah kadai ya san ko zan kai gobe ko ba zan kai ba, ina so in san cewa na bar baya mai kyau koda bana nan, hakan kuwa ba zai samu ba sai an samu jigo na kirki"

Jikin Najeeba yayi mugun sanyi tana kallon Anmy, wai me yasa Iyayenmu magana daya biyu sai sun sako mutuwa ne? Gaba daya daga mata hankali ake yi in ana yi mata nasiha hade da maganar mutuwa, sai ta ga kamar wasiyya ake Bara mata

A tausashe Anmy ta ce" Jigon gidan aure kuwa, shine mace ta gari, mace mai hakuri, mace mai tarbiyya,ace mai tatali, mace mai ibada, mace mai tsoron Allah......., NAJEEBA dole zaki ringa ganin wasu abubuwan da basu maki ba, dole yau da gobe zaki ringa haduwa da wasu abubuwan da zasu daga maki hankali, Ama idan kin jure, kin yi hakuri, kin yi addu'a kina zaune Allah zai maki yakin du wani mai son yakarki, kuma mutun ya ji kunya kin fahimta?????, ban ce ki dauki wulakancin rayuwa ta miji ko ta abokiyar zama ba, ban ce ki zama wace kowa ya kwaso shararsa a kanki zai zuba, Ama kuma ina horarki da hakuri, idan har kika zamo mai hakuri da kawar da kai zaki fi kowa jin dadin zaman duniya har ki bar duniyar......"

ANMY ta Wan sassauta tana dubanta ta ce" Duk rintsi kuma, idan kika fita daga dakinki ki tabbatar kin nufo inda nake, ko kuma kin nufi inda yar uwata take, ko ki je wajen yan uwanki, baki da wani gata a cikin duniya sama da mu, kuma in sha Allah har rai yayi halinsa mu iyayenku zamu tsaya maku "

A tausashe ta sake fadin" Ki tabbatar da kin yafewa mijinki kafin ki koma masa, ki tabbatar da kin cire komai daga ranki saboda kazafi ne mai girma aka maki ya hukunta ki a kan aikin da ba laifinki ba, idan baki yafe haka ba za'a yi rayuwar ne cikin wani yannayin na ana dane da haushin juna......, shin kin yafe masa?"

NAJEEBA ta gyada kansa, a sanyaye ta ce" ANMY na yafe masa, kuma itama Ni na yafe mata, tunda Allah ya bayyana komai ai Shikenan"

Anmy ta yi murmushi tana shafar gefen fuskarta ta ce" to maza tashi ki yi sallah sai ki fito ku je a dubaki ku dawo, kar ki manta da takardun wadincen fa, nima bari in je wajen wancen mai sunan wanan yaron in goye shi, haka kawai miji sai son goyo gayacen sai ihu yake uwar kuwa har yanzu bata dawo daga saloon din ba ko wani irin kitso ne Aida ke mata haka tun da yama?"

Najeeba ta yi dariya tana fadin" ai baban Aliyu Akoy rigima yadda kika san ya yi wata biyar , kamar ya gane mamansa ne fa Anmy "

ANMY dake ware ky din bangaren Najeeba da wanda ta rufe coridor ta mikawa Najeeban tana fadin" ya ganeta fa, ai ya'yan yanzu sai wayon tsiya, ki tafi bangarenki idan kika dawo, Ama su Aida sa je gobe dan su gyara maki bangaren, saboda a cenza harda kujerun da labulaye da cafet, Allah ya kade du wata fitina ya haWa kanku baki daya, Allah ya muku albarka"

Najeeba ta sada kai cike da kunya, har Anmy ta fice a dakin tana yi mata dariya sannan ta dago kan zuciyarta cike da tausayin anmynta, da tarin kaunarta a ranta, uwa uba tarin farin cikin da take ji a zuciyarta

A hankali ta Wan shafa cikin da bai gama rufewa wata hudu ba ama take jin yannayinsa a jikinta wanda hakan ke bata mamaki ainun, saboda a kwana biyar din nan zata iya cewa har ya kara girma, koda yake ko jita sai da umi karama tace anya a cikin nan kwaya biyun ne kuwa? Ciki du safiya sai ya Wan ?ara yannayin girma? Ita da kanta ta san yannayin wannan cikin ba iri daya bane da na yan biyu, Allah dai ya bar koma menene ya sa albarka ya sa a rabu lafiya da shi.
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




49




Bayan an fito daga sallah suka wuce bayan jakadiya ta rakata har kusan mota ta dakata aka bude mata ta shige sannan ta koma ta zauna dan zata yi jira har su dawo ne kafin ta rakata inda zata sauka


Tana shiga motar ta Wan juyo saboda yada ya riko hannunta

Murmushi ta sakar masa hadi da sada dubanta kasa saboda direba da Sarkin bulala dake gaba

A hankali yake dan murza hannun nata yana sake sauke ajiyar zuciya...., ikon Allah ji yake yi kamar ya shekara bai ganta ba, kai gaskiya an hora su ta hanyar horon da zasu fi fahimtar abinda ake so su fahimta.

Sun je asibiti , docter ta yi mata dukan binciken da zata yi mata, kuma ta ga hoton cikin a cikin hoton da ta dake yi mata kwaro kwaro, harma abinda ya bata mamaki a bayyane gayanan poche uku ce, harma ta nuna masa da kyau tana sake yi masa bayanin ai a hoton cikin na farko da aka yi biyu ne, wanda IZRANE ta yi mata, wanda bayan jinin ya zuba sosai daga jikin Najeeba ne aka yi hoton, wanda ba'a gani da kyau din nan, Ama a wannan da aka sake sai kuma abin ya fito Rado Rado

Jikin Najeeba rawa ya fara, a hankali ta ce" Docter kina nufin wai uku ne?"

Docter ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" Abinda hoto ya nuna mana kenan, Ama kin san Allah kadai ya san gaibu, mu dauka cewar eh dan ciki kam ga ciki nan, sai dai ba'a san nawa bane, saboda wasu lokutan zaki ga an yi hoton an ga biyu, sai a haifo sama da biyu, ko kuwa ga an ga daya, kuma a haifo biyu, ko ki ga an ga biyu kuma a haifi daya....., duka suna faruwa dan haka ki kwontar da hankalinki, ki ci gaba da kiyaye duk wani abin da aka dora ki a kai, ki ringa zuwa awo a kan lokaci har Allah ya raba lafiya kin fahimta?"

NAJEEBA ta sauke ajiyar zuciya tana gyada kai , saboda har ga Allah sai da ta ji tsoro, to uku ta yi yaya da su? Cabdijan ta yiwu ma ace sai dai a fasata saboda lamarin haihuwar uku ai ba nan bane

Docter ta kali SULTAN, wanda shima ya kaleta, da idannuwanta ta masa alamun da ya sa ya kai hannunsa wajen hancinsa a hankali ya dan shafa hadi da sauke ajiyar zuciya a hankali ya rike hannun NAJEEBA hadi da shafa gefen fuskar ta ya sakar mata murmushi yana sake duban cikin nata.......
Ikon Allah, shi fa ba ?aramin mamaki yayi ba, duka duka rabonsa da ganin cikin kwana nawa ne? Ama cikin ya kara girma?

A hankali ya lumshe idannuwansa , a ransa ya ayyana ' Ya rab, kai ka san me yake cikin cikin nan, Ubangiji ka bata lafiya ka sauke ta lafiya'

Daga nan suka fito, maimakun su nufi fada sai suka nufi wajen da suke zama, dan ita bata san cen zasu je ba sai da suka iso aka bude musu bayan an shinfida musu abin zama an kai abinda zasu ci sannan ya fito yana kamo hannunta suka nufi wajen, su kuwa suka yi baya saboda basu waje


Kalon wajen zaman nasu take yi da mamakin yadda aka gyara wajen

Bayan sun zauna ta ce" Wajen nan haka aka gyara shi? Kenan ana kawo ziyara yanzu sosai ko?"

Murmushi kawai yayi ya dawo da ita jikinsa yana dake nikaf din ta, a hankali ya dago habarta yana kallon fuskarta..............
Cen kasa ya furta" I love You beebahhhhhhh"

A hankali ya hade bakinsa da nata yana lumshe idannuwansa ya shiga kising kamar ba gobe

Luffffff ta yi , idannuwanta lumshe tana bashi hadin kai har ya gama a hankali ya sakar mata baki yana hade goshinsa da nata, cen ciki ya ce" mu je gida, kar.....kar in dane kkkkkkkkk"

Da sauri ta rufe masa bakin tana zaro ido hadi da yin dariya ta ce" Wai wa yake koya maka magana irin wannan?"


Shima sai da ya ji dariyar na son kubce masa, ya shafa kai yana sake lumshe ido yana binta da kallo ta koma gefe tana bude kular da aka ajiye tana murmushi ta ce" Kaza ce?, wa ya gasa?"

Yanzun ma bai iya bata amsa ba sai kallonta da yake yi har ta fara yaga tana ci , tana nufo bakinsa da shi

Amsa ya ringa yi, saboda ya san yana jin yinwa, kuma idan bai ci ba da wahala in zai iya hakurin ci din in sun je gida.....


Sai da suka gama ci sannan ya mike yana riko hannunta

Najeeba ta turo baki ta ce" To bamu jima ba fa"

A raunane ya juyo yana dubanta cen kasa kasa ya ce" Please Beebahhhhhhhhhhh?, zamu dawo, in ba so kike yi in ba babyna madara a nan ba???"


Zungui zungui ta shige motar dan bata san me zai iya aikatawar a nan din ba

Sunna karasawa fada ya dakatar da jakadiya da su Sarkin bulala suka nufi ciki shi da ita

Gana daya a bukace yake, hakan ya sa sunna shigar a hanzarce ya shiga cire alkyabar jikinsa da sauransu

Shigewa Najeeba ta yi ciki da dan gudu gudu tana masa dariya

Ai kuwa ya bi bayanta, yana shiga ya mika hannu ya kashe fitilar da take da haske sosai ya bar mai duhun hasken sannan ya nufi inda yake tsaye hannunta harde ta Wan langwabar da kai tana kallonsa

Yana karasowa ya zamo tana daf da gadonsa ne, sai ta juya a hankali da shi kafin ta saka karfinta da kyau ta tura shi , ta yada ya bata dama ta tura shi saman gadon ya kwanta ta bayansa

Hijabin dake jikinta ta cire, ta jire abayar, ta kunce zanin dake ?ar?ashin abayar sannan ta bar yar ficikar rigar da ta saka a cen kasa,

A hankali ta haye saman gadon hadi da hayewa saman ruwan cikinsa a hankali ta shiga shafar cikinsa hadi da Wora kanta a gefen wuyansa tana shafar gefen kunnansa da hancinta cen kasa kuma hannunta na yawo a cikin gajeran wandonsa , murya cen ciki ta ce" SHAHEED........., i love U tooo my khalb........"

A birkice ya juye da ita jikinsa na daukan rawa, a gigice ya shiga bata kulawar da zata fitar da ita a hayacinta....hadi da kalaman da suka gama kashe duk wani kuzarin kwatar kanta dake iya bijiro mata koda bata yi niya ba

A sukwane ya sada kansa da duniyar da take da wadatacen ruwa da dumi mai saka zuciya dokawa a alert din da ya wuce misali.......
A gigice ya sauke wani irin Gwauron numfashi da ya ji kansa a duniyar nan kafin ya rukunkumeta a jikinsa yana sake samun waje ya nutsu sosai a ciki kafin ya shiga kai kawo dan idasa yada manufofinsa.......
Ita da kanta duniyar da suka je ta yi.mata dadin da ya sa hawaye ya ringa bin gefe da gefen kumatunta.....a hankali ta idasa bashi damar idasa haukata mata zuciya da sake sakawa ranta cewar gayen nan in ba shi ba, du duniya babu wanda zai sa ta ringa kuka wiwi bayan ba duka ta sha ba, ba zaginta aka yi ba, ba iyayenta suka rasu ba, ba kudi ta nema ta rasa ba....., kai Allah ya yiwa aure albarka ya karawa maza lafiya.(>??=? ?=??? @&?).


Tun daga wannan ranar duniya sabuwa ta bude musu

Da ake cewa bayan saukar ruwa sai dadadan yanayi haka din ne, domin su din ma bayan wannan dogon rikicin da suka samu sai ya zamo a yanzu sun fi da yin kafa kafa da juna.
Suna kiyaye hakkin juna fiye da tunanin bawa, nutsuwarsa ta dawo jikinsa a yanzu har ya koma bakin aikin da Allah ya nada shi, wato kula da garinsa .

A bangaren Najeeba da nadiya kuwa sun ci gaba da gabatar da mu'amala wace hankali zai dauka....., domin kwana biyu Nadiya ta yi tana buya wa duk mutanen gidan uwa uba wa mijinta dan ko a ranar girkin nan nata abinda ya hanata zuwa bangarensa kennan, dan a yadda Najeeba ta fita ta gama SAREWA cewar zata je ta tona mata asirin dukan abinda ya faru, ta zuba ido tana jiran ta ga hukuncin da zai hau kanta, sai dai cikin ikon Allah babu abinda aka yi, tun tana tunani da hangen wani abu zai biyo baya har Anmy ta lekota ganin kwana biyu bata leka ba, ta dauki Aliyu ta tafi da shi bayan ta yi mata fadan ta daina zama ita kadai, dan su Nayla kam sun koma sun likewa mamansu, ta ringa zuwa bangaren na anmy ko ta je wajen yar uwarta su yi zumunci, nan ta gane ko Anmy bata san abinda ya faru ba, daga nan kuma ta sake yarda Najeeba daban take a cikin mutane, a lokacin da kake tunanin zata yi wani abin sai ka ga bata yi ba, a lokacin da ba zata yin ba kuwa sai ka ga ta yi.......

Wani irin nauyin ta take ji, da kunyarta,

Gaskiya Najeeba ta fada, shin a zumuncin da suka yi a baya bai kai ace ta zama uwar ?a?anta ba? Ko ba maganar wanda take aure kadai ya isa ya sa ta zama uwar ?a?anta?, lalle ta yi wauta da ta yarda cewar Najeeba ce fa shiga ta fita ta lalata mata lafiyar yaro, bayan ta san Aliyu marigayi ma haka yake, ? Inma ba hawa kan keken bera da aka turata ta yi ba ai yaci ace ta gane cewar Najeeba mai son ya'yanta ce, saboda sanadiyar Winkin shadar nan da ta matsa masa da sakawa sai da yayi rashin lafiyar da likita yayi ta fada ya fada mata yana da alrgi a duk suturar da ba coton ba, sannan a ringa barinsa ba kaya yana shan iska da ni'imar Allah..., tubeshi da ta yi dan ta taimaka masa ne ya samu numfashi mai kyau.......

Sai ma da mahaifinta yayi kira ta je bayan ta tambaya ya bata dama ta samu tashin hankalin da ya fi na fada girma, saboda mahaifinta ya ji abinda yake faruwa ya hade su daga ita har mamanta ya musu wankin baban bargo kafin ya karashe da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login