Showing 93001 words to 96000 words out of 144591 words

Chapter 32 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2325

ba ta daga

A tausashe Ummi ta ce" Barka kadai, Nadiya ba shi bane, ummi ce, ki taho bangaren MIJINKI ki kula da shi"

Nadiya ta ce" To Ummi, sai da na je sau jiyu ya ce yana da bukatar kadaicewa"

Ummi ta ce" Ki zo yanzun"

Duban ummi yake yi cike da mamakin Nadiya ta zo? Ta masa me?, ta zo fa, da ta zo din dan ta ji abinda yake faruwa aka saka dokar rufe fada da kuma irin yadda fadar ta hargitse da mutane masu bada tsaro, bai iya bata komai a bude ba dan baya bukatar ta sani a yanzu domin ya tabbata idan ta ji sai gidansu sun ji, idan gidan nasu suka ji ne bai san wa da wa kuma zasu ji ba, wannan dalilin ya sa kawai ya salameta da nufin yana da bukatar hutawa, ta kuma dawowa da duka a safiyar nan, nan ma ya nuna mata ta tafi, domin ba zata iya yin shiru ta barshi ya gama abinda yake gabansa ba, shi kuma a yanzu baya bukatar kwaramniya ko ta ya'yansa ce!

Zaunawar ta yi itama tana dubansa a tausashe ta ce" Babu abinda damuwar nan zata saka maka sai ciwo, kamar yadda ya sakawa yar uwata gatacen........."

Da sauri ya dubi Ummi, a hankali ya ce" Anmy bata da lafiya?"

Ummi ta Dube shi a hankali ta ce" SHAHEED, ka san zata saka damuwa a ranta, Ama zai wuce in sha Allah, shi yasa na zo dan in fada maka zan kaita a auna min BP dinta mu dawo"

A hankali ya rintse idannuwansa yana furta" Hasbubalah.............."

"Innalaha ma'asabirin My son, Bana so ka hade damuwar da yawa a ranka saboda gudun ciwo, PLZ ka ba Nadiya dama ta kula da kai, ka samu ka ci wani abin ka huta, in sha Allah za'a ganta kuma ina da yakinin tana cikin aminci domin bana tunanin zata iya aikata abinda ta rubuta a takardar nan, wato zubar da cikin nan, zata kula da cikin nan, saboda Ni na san cewa a duniya ta fi kowa son cikin nan nata son"

A hankali ya girgiza kansa, a tausashe ya ce" Me nake tunani....., da har na yarda da maganar nan? Ya Salam........., kuma Ni ne shaidar irin yadda take da laushi a gaban yayanmu......Ama kuma na iya saka mata damuwa haka......, Ummi....kin san me???"

Ummi ta girgiza kanta tana kallonsa

A hankali ya ce" Da wahala ta yafe min, ba tare da an tursasata ba....., Ni kuma na yi alkawarin babu wanda zai yi mata dole.....zan nemi yafiyarta ne da kaina"

Ummi ta yi murmushi a hankali ta ce" Zata yafe maka, ina da yakinin zata yafe maka in sha Allah, idan har ka yi abinda ya dace din, zata yafe son, ga Nadiya cen ta shigo, bari in Barka sai mun dawo"

Kai kawai ya gyada ya sake mayar da idannuwansa ya lumshe ba tare da ya iya budewa ba har Nadiya ta shigo tana yin salama ta karaso inda yake ta zauna ta ce" Barka da hutawa ranka shi dade"

Idannuwan nasa ya bude a kanta........, a hankali ya mayar ya rufe , ba komai ke dawo masa ba sai maganar BEEBAH da tace ya auri aminiyarta dan ya wulakantata....., yayi yawo da tunaninsa dan ya samo abinda ya musanta maganarta Ama ya rasa, amsar nan dai itace, hakanan ne, kwarai ya auri Nadiya ne dan ya bata mata a lokacin da yake hannun itama ta bata masa........, ya rab yaya zai gyara abubuwan da suka saka tazara da yarinyar da ta gama kama zuciyarsa da duniyarsa ne?????, idan yayi wasa......wankin hula zai kai shi dare, karamin abu zai zamo masa baba...............tsayuwa zata iya gagararshi .................................dama bawa na janyowa kansa fitina cikin halin gajen hakurinsa da rashin kularsa?...........


Wayar da ta dauki RINGIN ne ya da Nadiya mikewa ta dauko masa ta sake zaunawarta dan jira yake ya gama ai ta ji abinda yake faruwa, ita fa du a tsarge take, tabas Akoy abinda yake faruwa da aka ki sanarwa kowa ya ji


A hankali ya kara a kunnensa, daga dayan bangaren Sarkin tsaro ya sanar masa cewa har yanzu fa masu laifin nan sunna nan a tsare a dakin tsaro na cikin gida

Gaba daya shi ya manta cewar ya sa a dauko su, a yanzu kuma bashi da lokacin dubansu, sai kawai ya budi baki a hankali ya ce" Ka sanar da su, sai jibi zan zartar da shari'ar su idan har na samu sukunin zuciyata"

Da girmamawa ya amsa , sannan ya kashe ya dubi mai garin magarya da ya zo da iyayen IZRANE a kofar dakin da su IZRANE din suke a rufe ita da Hajiya Turai, ya ce" Mai gari, ba za'a gabatar da Shari'a yau ba, sai nan da kwana biyu in ji Mai DAMAGARAN"

IZRANE ta zarro ido jikinta na daukan rawa na tashin hankali, ta mike da kyau ta rike karafunan KURKUKUN tana sosa uwar atash din da ta saka a Jiya da safe saboda an ce daga gidan kilacewa za'a yi gidanta da ita, shi yasa ta kashe makudan kudi aka kafa mata atash din nan mai kama da gashin mutun ta mugun hau fatarta ta kama kai kace gashinta ne ta yi mata dassssssss, bayan magariba zuwa karfe goma aka dauko ta ita daya a wata bak'ar mota, sai dai maimakun a yi kilatacen waje mai ni'ima da ita sai ta samu kanta hade da Hajiya Turai a cikin dakin horo na gidan Sarautar DAMAGARAN, tun Jiya da dare take cikin firgici da tashin hankali, yadda Mai DAMAGARAN bai rintsa ba haka suma?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? basu rintsa ba, saboda tashin hankalin da suke ciki, me ya kawo su nan? Me suka yi? Sai ga wata fitinar wace ta fi wancen wai Shari'a sai nan da kwana biyu


A firgice ta ce"
https://chat.whatsapp.com/BuEB69AOiqBKg0PMiBzdG3
*Kayan kitchen kike nema?* *Laces ko atamfa ko* *materials?? Yar uwa muna da takalma ,jaka akwatuna d kayan parlor* *nd toiletries, d sauran* *abubuwa d dama kuma* *delivery nationwide In* *sha ALLAH=?
? sannan* *muna bada kaya a* *farashi mai sauqi domin masu siya su siyar kiyi* *joining domin ki amfana* >??>??



>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




32




A firgice Izrane ta ce" kwana biyu? wani irin sai nan da kwana biyu? Shari'a? To me na yi Ni da za'a yi Shari'a da Ni?, Jiya fa yace za'a kaini kilatacen wajen da zai sa in nutsu in yi zamana da an fito da Ni daga cen sai dakinsa matsayin matarsa, to kuma me na yi da za'a kawoni KURKUKUN gidan nan a rufeni?"

Dogari ne ya daga sanda ya maka jikin karfen , hakan ya sa IZRANE komawa da gudu ta zauna daf da Hajiya Turai wace ta ja nesa da ita tana harararta

Dogari ya ce" Kar ki yarda, ki kuma dauko maganar Mai DAMAGARAN kina daga murya kina kawo zaurancen rashin kunya a ciki, zan datse harshenki a wajen nan ta yadda idan kin je gabansa zaki rasa harshen kare kanki ma bale har ki iya kare kan naki, yarinya a nan Bakya shigowa da rashin sani, du abinda kika aikata ya kawo ki nan, kin san shi, sai ki zage dantse ki amshi sakamakon laifinki idan lokaci ya zo!"

Hajiya Turai dake kallon ta sama da kasa ta ce" Kin ga, du abinda ya sa na ga an hadoni a mota daya da ke na san kece kika janyo min, ki rufawa kanki asiri ki kama dan iskan bakinki tun kafin ki saki zancen da zai ja mana kurkuku, dama kin gama ja min wata masifar dan Ni daga nan in na fita ban san inda zan fita ba sai dai in je makota a hadu a ba mijina hakuri ya mayar da Ni dakina domin babu abinda zai mayar da Ni Difa a irin wannan lokacin, kina wani neman abinda kika yi ta yiwu garin sai kin samo laifin matarsa kika aikata naki laifin kamar kullum "

Mahaifin IZRANE kuwa tunda dogari ya daki karfen nan ya samu yayi baya jikinsa na daukan rawa da mugun tsoron irin laifin da yarinyar tasa ta aikata ta janyo masa irin wannan tashin hankalin , a Jiya basu san inda aka zo da ita ba kena, sai yau da labarin ya zo musu bayan mahaifiyarta ta je inda ake kyautata zaton yarinyar na cen ta tarar da sai masu gadi a gidan, nan suke sanar da ita ai ba'a kawota Bama gidan, shine fa suka nemi inda take din suka sameta a nan, tunda suka sameta a nan dama mahaifiyarta ta ce to kuma garin ciye ciye tana tsoron in IZRANE bata ciyo tsabar da ta fi karfinta ba, shine ya yi kiran Wan uwan nasa suka sake dawowa, shi da kansa ya gama kudurtawa kansa idan har suka sake samun ganin mai damagaran in dai wani fadan ne ya sake hada IZRANE da Gimbiya zai nemi alfarmar idan har ba laifi hakan zai kasance ba kar a auri IZRANE dan a katse fitinar nan , sai dai bai sani bane, Bama zai iya samu ganin mai DAMAGARAN a yanzu ba dan shi da kansa ba ganin kan nasa yake yi a yanzu ba, haka kuma jama'arsa du a hasale suke da lamarin , wato makusantansa sosai, domin Malami ya dan nuna musu yannayin bacin ran kadan, Duda girma da ilimi ya sa ya iya dane wani, ama ita zuciyar masoyi na fallasa abinda ke cikinta ne , dadi ko akasinsa.

Mai garin MAGARYA ne bayan dogari ya lafa da fushinsa a tausashe ya ce" Allah ya huci zuciyar ka, a yi hakuri in sha Allah zata iya bakinta"

Sannan ya matsa kusan karfen nan tausashe ya ce" Taho IZRANE"

Sake tasowa ta yi, sai dai yanzu bata kama karfen Bama bale a sake doke mata yan yatsu

A tausashe ya ce" Yarinyata, ki fada min gaskiyar abinda yake faruwa dan mu san hanyar da zamu bi mu nemi sau?in lamarin nan, domin a banza ba za'a taba kawo ki dakin nan a rufe ba, ki yi kokari ki ragewa kanki wahala, ki tausayawa iyayenki kin ji?"

IZRANE ta rasa to me zata ce, abinda take tunanin zai kawota nan ai ba za'a taba sani ba, saboda a saninta daga ita sai matar nan suka san abinda ta aikata din, kuma ta san ko hauka ake yi Hajiya Turai ba zata fallasa maganar nan ba dan ta san itama tana ciki domin in ta yarda ta fada ita kuma zata tona musu asiri baki dayansu cewar ita din itace ke amsar kudaden yan matan dake dauko ciki tana bata sunna zubarwa su raba........ Ire Iren wannan tunanin ya sa ta kafe kai da fata cewar babu abinda ta yi , a dole suka juya suka sake komawa wajen Malami ya sanarwa malami cewar yana garin damagaran sunna jiran kira daga fadar dan su ji abinda yake faruwa, sannan suka wuce bayan an tabbatar musu ba za'a bari su ringa kawo abinci ba, kuma in sun ga zasu daukaka kara fine, su ma haka suke so.


Ummi ta dau Anmy ta kaita asibiti, sai dai bayan ta ga likita sai ya jona mata ?arin ruwa da fadin cewar zai yi mata trtmnt, idan jikin yayi yadda yake so zai salameta Ama idan har ya ga a haka gaba jikin ke yi sai su zaba ko ya kwantar da ita a nan asibitin ko kuma su je fadar ya ringa zuwa yana daura mata karin ruwan yana dawowa

Sosai hankalin Umi ya tashi, damuwa ce ta tarar da ciwo domin kuwa dama Anmy ba iya damuwa ta yi ba, ko kadan, idan ta shiga damuwa nan da nan jikinta ke dauka har a kai ga lafiyar jikinta, bale ta saka lamarin Najeeba a ranta sosai

Bayan sallar la'asar ta yi kiran Abiey ta sanar masa halin da ake ciki ta fada masa cewar jira take yi karin ruwan ya kare, karin ruwan kadan kadan sosai yake shiga shi yasa har yanzu bai kare ba, ya je fada ya samu ya sanar da Sultan cikin hikima domin shima ba lafiya ce da shi ba.

Abiey ya nufi fada yana gwada layin Dayabu, Ama yanzun ma sweet off, saboda a lokacin Dayabu yana farkawa ya fice masallaci, wayarsa kuwa dama tunda ya yi barci matarsa ta kashe dan ya samu hutu mai kyau , domin bata so a yi kiransa ma aje ya fallasa abinda yake faruwa

Rashin samunsa da yayi ya sa ya ajiye kawai ya nufi fadar

Ya samu ganin SULTAN saboda lokacin aka gama sallar la'asar , yana grdng dinsa yana ringeshe rike da Alkur'ani mai girma yana karatu a cikin zuciyarsa, domin ya gama gane shine kawai abinda zai yi ya samu sauki a cikin zuciyar tasa, zaman bangaren nasa ya ishe shi saboda irin yadda Nadiya ke faman takura masa da tambayoyi da firar da yake ganin surutu ne kawai saboda baya jin dadin maganganun ko kadan, gashi ya kasa barci, ya kasa yin kwakwaran abu guda da zai dauki hankalinsa, ya kasa zama da su Muhammad saboda kiri kiri yaron nan da yake ganin ya girma ashe bai wani girma ba, saboda irin yadda yake kukan mamansa kai kace mama yake sha, shi kuwa Abdallah dama fushi kawai yake ciki, baya cewa kowa komai sai hade fuska da yake fama da ita.......gaba daya sun gama daga hankalinsu sun kuma daga masa domin daga school ma dawo da su aka yi, shi Muhammad tunda suka je ya kifa kai yake kuka, shi kuwa Abdallah daga abokinsu ya takura sai ya san dalilin kukan Muhammad din ya daki abokin nasu harda fasa masa goshi, karshe dai aka hada su aka dawo da su gida da takardar abinda yake faruwa da rokon a san halin da suke ciki dan a sama musu sau?in lamarin.

Sai da aka sanar da shi wanda ya zo , sannan ya mike daga kishingidar yana dasa aya a nutse ya rufe ya ajiye Alkur'anin cikin abin ajiyarsa sannan ya fuskanci Abiey da ya zauna suka gaisa yana dubansa a tausashe ya ce" yaya aka ji da abinda yake faruwa?"

A tausashe SULTAN ya furta " Alhamdulilah"

Abiey ya sauke ajiyar zuciya, Duda ya san amsar daya ce cewar bashi da wani labari a kan Najeeba, bai Hanna shi tambaya ba

A hankali SULTAN ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Babu wani labari Abiey......., ban samu labarin BEEBAH ba Abiey "

Abiey ya sauke ajiyar zuciya shima ya ce" in sha Allah za'a ganta"


Suka Wan yi shiru

A hankali Abiey ya ce" Ka san jikin mamanku baya son damuwa, damuwar da ta saka ne ya kwantar da ita, Ama alhamdulilah da sauki fa, likitanta ne yace ba zai salameta ba sai ya gamsu da yannayin jikin, shine nace bari in sanar maka da kaina"

Wata sukar zuciyarsa ta yi, wace ta so katse numfashinsa daga zaunen da yake, domin har sai da Abiey ya fahimci irin yadda ya rike gaban kirjinsa da hannunsa

Da sauri ya mike ya dawo daf da shi yana dubansa a tausashe ya ce" SULTAN"

Shaheed ya kama hannunsa da ya miko yana son dafa shi, ya rike da kyau idannuwansa lumshe har sukar nan ta lafa masa, a hankali ya furta" Ya Salam, yaya jikin ta Abiey?"

Abiey a hankali ya ce" Alhamdulilah fa, kar ka daga hankalinka PLZ, she wl b fine in sha Allah"

A hankali ya gyada kansa, a tausashe sosai ya ce" Allah ya bata lafiya, zan shiga asibitin idan na fito daga masallaci in sha Allah "

Abiey ya gyada kai, Ama kuma ya ki tashi yana zaune da shi dan karshema sai ya shiga ziga shayi kawai, domin zuciyarsa ta ki aminta ya barshi shi kadai bayan irin abinda ya faru da shi yanzu, Duda ya bude Alkur'aninsa ya ci gaba da karatunsa cen kasa cikin zazakar Muryar da shi da kansa Abiey din ya ringa jin nutsuwa na ratsa zuciyarsa......



______________________________


Yaya Dayabu na dawowa daga masallacin sallar la'asar direct dakin Najeeba ya wuce

A saman salaya ya sameta rike da Alkur'ani mai girma tana karatu

Waje ya damu ya zauna yana sauraronta, Ama da yake nemansa take da fitina a kala ta dauki minti arba'in kafin ta dangana ta rufe ta mike ta ajiye a wajen ajiyarsa ta zo ta zauna a kasa tana turo baki

Shekeke ya kalleta kafin ya ce" Ai na zata sai kin sauke zaki dangana"

NAJEEBA ta dan girgiza kai, a hankali ta ce" Su yaya yanzu karatun ma idan na yi na yi laifi?"

Yaya Dayabu ya dubeta ya ce" Ki ji tsoron Allah haka nace maki?"

Najeeba ta girgiza kai kafin ta sada kan nata ta yi shiru

Yaya Dayabu ya sauko kasan shima ya harde hannayensa yana duban ta a hankali ya ce" Dago kanki mu yi magana an kanwata"

Najeeba ta Dago kan nata tana dubansa

A sanyaye ya ce" Najeeba, yaya kike so in iya da wannan rigimar da kike son dora min?, kin san cewa duk isata da ke da takamar da zan iya wanzarwa dole zan yi karar da iyayenmu suke yi a kanki nima in sada kai in yi biyayya in dai Anmy na wajen...., Najeeba in tambayeki dan Allah da zaki aikata haka kin tuna anmynki?"

NAJEEBA ta ji zuciyarta na bugawa, a hankali ta Dago tana dubansa

Muryarta a raunane ta ce" So kake yi ka yi anfani da wajen da ka gama sanin cewa ko me nake ciki idan maganarta ta shigo na zubar da makaman yakina ? Yaya kake so in iya kwato yancina ne a gaban wanda ya gama nuna min, da Ni , da duniya cewar Ni ba kowa bace? ......"

Ta langwabar da kanta kirjinta na daukan nauyi ta ce" Tunda ya gane cewar Ni jininsa ce,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login