Showing 6001 words to 9000 words out of 144591 words

Chapter 3 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2337

fuskanta da Nadiya du idan ta gama kwanakinta biyu bata tsayawa ta tsaftace kicin din yadda ya kamata, haka take jansa ta rufe ta yi tafiyarta, bata san me yasa take irin haka ba, tana matukar mamakin yadda za'a yi mace ta yi girki ta gama ta bar kwanoni harda ruwan albasar da ta yanka a nan, hatta ruwan nama bari take yi , kwanoni kuwa dama bata iya wankesu ba, a nan take bari ta yi tafiyarta bayan ta Wan babu mai shiga kicin dinsa sai su biyu kawai, kuma kowace da bangaren kayan aikinta Ama kuma sai ta ringa hadewa sannan tana bari a nan

Ai kuwa ta samu aiki, saboda harda su blender a nan a ajiye

Sosai ta so zaginewa ta yi aikin, Ama ya gagara saboda irin yadda mararta ke karra karta mata, sama sama ta soya masa wainar kwai isashiya ta kai dakinsa , ko ruwa bata iya dauka ba ta koma dakin nasa ta shiga kokarin cenza zanin gadon da dai sauransu

Sai da ya gama abinda ya saba sannan ya shigo da tunanin tafiyar da ta Kunno masa dan kauyen dake kusa da damagaran , wato mirya dan zuwa gabatar da gaisuwar rasuwar wani bawan Allah da suke tare shekara da shekaru, yau ya kai sa'i, lokaci yayi

Samunta yayi zaune tana rike da abin turaran wuta

Da kula yake amsa GAISHE shin da ta yi bayan sun hada ido a lokacin da ya shigo

Fuskarta yake kallo gannin ba walwala a tausashe ya ce" me yake damun Beebah? Ko barci ake ji?"

NAJEEBA ta yi dan murmushi ta mike a hankali ta ce" Alhamdulilah Aban Mohammed, zan je bangarena idan ba damuwa in an jima zan dawo in kimtsa nan din"

Hannunsa ya saka ya rikota yana kallon fuskarta hadi da taba gefen wuyanta, a tausashe ya ce" Are You ok ?"

Najeeba ta lumshe idannuwanta ta sakar masa murmushi a hankali ta yi dage ta yi masa pck a kunci sannan a tausashe ta ce" am ok.....Na gaji ne kawai, ina jin barci"

Ajiyar zuciya ya sauke ya rungumeta a jikinsa a hankali ya furta" Ok....., sai na dawo....zan je miriah yau"

NAJEEBA ta gyada kanta a tausashe ta ce" Allah ya tsare min kai MAI MARTABAHHHHHHHH"

Murmushi yayi ya saketa ta tafi bayan ta dauki ky din bangaren nasa da kuma na bangarenta

Sai da ta bacewa ganninsa sannan ya nufi wajen kular da ta saka masa abincin ya zauna yana tunanin ba'a dauko ruwa ba?, da ya bude ya ga abinda ke ciki zuciyarsa ta karra tabbatar masa lalle ba kalau ba, sai dai ba zai takurata yanzu ba zai bari zuwa an jima ya kirayi numbarta ya ji , dan bata cika yi masa wainar kwai kawai na kari ba, idan ranar ta ne ta yi wannan ta yi wannan ne, kullum tafe take da surprise mai kyau da zata birgeshi, har ya zamo Y'ar uwar Tata ma ta koya.



NAJEEBA ta karasa bangarenta da kyar tana jan numfashi ta bude ta shige tana jin gaban jikinta sai karra daukan ciwon suke yi,

Andiya ce ke goge goge , ta dago da fara'a tana amsa salamar NAJEEBA da ta yi kasa kasa sannan ta mike gannin yannayin Najeebar ta ce"







Kun shirya kuwa??????, hummmmmmmmmmm ku dai ku zo mu je.........=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati na airtel ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




3

( Mai bukatar a talata masa hajarsa ya min magana ta numbana 93811618 )


Andiya ce ke goge goge, ta dago da fara'a tana amsa salamar NAJEEBAr ta mike tana sake duban yannayin Najeebar ta ce " Momy, lafiya? Baki da lafiya ne?"

NAJEEBA ta rike hannunta da ta miko mata a sanyaye ta ce" Andiya marana ke ciwo, Ama da sauki, Please ki sama min ruwa mai dumi in sha ko zai fada min"

Andiya ta kamata suka nufi dakinta wanda take shiga, ba wanda suke shiga ita da SULTAN SHAHEED idan yayi niyar kadaicewa da ita a bangarenta ba

Sunna shiga ta rakata har kusan gadonta sai aikin sannu take yi mata ta ringesa sannan ta fita da sauri ta je ta zuba ruwan a butar da suke tafasa ruwa ta jona, ta dauko flsk ta juye shi ta zuba dan karanfani a ciki ta dauki kofi ta koma dakin da sauri ta zauna tana tsiyaya ruwan a tausashe ta ce" Momy ga ruwan, Momy ko in sanar da jakadiya ta sanar da Docter? Momy ko in je in fadawa Anmy???"

NAJEEBA ta girgiza kanta a tausashe ta ce" A'a, kar ki daga hankalinki andi, idan na sha zai saki in sha Allah"

Andiya ta mika mata sannan ta zauna tana jira har ta gama sha a hankali a hankali sannan ta miko mata kofin ta ajiye , ta kasa mikewa bale ta fice ta je ta yi abinda yake gabanta

A hankali Najeeba ta ce" Ba na hannaki aikace aikacen nan ba Andi? Ki bari su shigo su yi kin ji? Aikin nan ya maki yawa ke kadai"

Andiya ta ce" Momy yau ba school ne, kin ga kuma na yi barci da wuri jiya shi yasa nake aikin, zasu shigo ne in an jima in sha Allah "

Najeeba ta gyada kai tana cije lebenta dan zafin ?ara yi mata yawa yake yi,

Cen ta bude baki ta ce" Andi tashi ki je, da sauki fa, kar ki damu, je ki karya"

Andiya ta mike a dole ta fice tana jin hankalinta sam ya kasa kwonciya saboda uwar rikon nata mutun ce mai juriyar gaske, tana da matukar kokarin ciwo, abinda ya sa ka ga ta shige bargo ba karami bane, bale a kwanakin da take kira sun fi kowane kwanaki daraja a cikin sauran kwanakinta, kwanakin da dadynsu ke a hannunta....., Allah ya bata lafiya.


Kusan karfe goma na safe a bangaren Nadiya ta yiwa auntynta, wato kanwar mahaifiyarta da ta yi safiyar kawo wani maganin da za'a yiwa Aliyu wanka da shi, dan wanda ya bata maganin ya sanar mata ya zamo wankan shine abinda za'a masa na farko da sasafe, kuma a tabbatar da an shanya ruwa ya kwana ne sai a saka maganin a ciki a masa wankan

Nadiya ta amshi maganin ta saka cikin jakarta ta ce" Aunty, in sha Allah za'a jika ruwan yau da dare sai a yi masa gobe, tunda kin ga ai yanzu safiya ta riga ta yi kuma ba'a jika ruwan ba"

Aunty ta ce" Ba damuwa, Ama wallahi kika yarda kika yi wasa da maganin nan Ni da ke ne Nadiya, dan na kula ke baki san zafin yaron nan ba, sai wani abu kike yi wanda bashi da tsari, bayan yaron nan shine mai jiran gadon mahaifinsa"

Nadiya ta yi yar dariya tana dafe haba ta ce" Aunty, kin manta yan biyu ne?"

Auntyn ta ja tsaki tana turo dan kwalinta gaba ta ce" Ke kika san da su, ai babu yadda Allah baya yi, sha nawa ake daukan Kani a bar yaya idan yayan bashi da qualities din da ake so a matsayin Sarki? Ki duba yaron nan ki gani, duda jariri ne shi ya fi kama da babansa, shine mai jinnin sarauta a jikinsa ba wadincen da Ni kamaninsu ma ban sani ba, kin ga sa a kawo min kari in karya, ga dukkan alamu yau ba kece da kwana bangarensa ba ko?"

Nadiya ta yi murmushi kawai ta mike tana fadin" Aunty KENNAN, yau ai Najeeba ce da girki, bari in yi kira a kawo maki abin karin"

Wayar dake ajiye saman table ta dauka ta danna numbar mai kula da bangaren kicin dinta ta sanar cewa a kawo abinci yanzu, sannan ta dawo ta zauna cike da zulumin abinda ke zuciyarta ta ce" Aunty, wai kin kuwa san cewa idan ita ke girki kamar a bangarenta yake kwana?, zuciyata da tunanina sun kasa cire min wannan tunanin a raina, Ama kuma wani abin ke ce min ta yaya? Yaya za'a yi ace ya kwana a nan?, to Ama idan ba a nan din yake kwana ba me zai sa ace wani zaman in ya fado bangarenta idan ya tashi rakani yakan toge daga dokin Babar kofar falon dake raba falonta na farko da na biyu ya min salama daga nan?, bayan idan nan ya kama sai dai ki ga ya mayar da alkyabarsa ya fice da yi mata rakiya sai dai mu hade da shi a bangarensa?, Aunty wai hala yana iya kwana a nan?"

Auntyn ta dafe haba kafin ta yi kyaftu ta ce" Meye ma ba za'a iya saka shi yayi ba? Ke da har yake ganninki da mutunci har yanzu ai da sauki , ke kin san wa yake aure ai, kuma kina kallo irin yadda mahaifiyarsa ke son yarinyar nan, to ko iya hakanan ai an ringa nuna maki fifiko bale kuma shi dinma da kansa yana sonta, ke kike fadin cewa sun ja sunna makauniyar soyaya tsabar baki san ciwon kanki ba a haka ne na nuna maki ya dace ace kina tsaye da kaffafuwanki wajen neman mallaka sai ki nuna ke a'a ba sai kin wani yi masa mallaka ba, shi din mutun ne adali, kin san duk rintsi ba zai wulakanta ki ba, to idan aka fitar da shi daga hayacinsa fa har ya wulakanta kin ba tare da ya san ya yi ba fa? Sai ki dawo kuma ki gane abinda ake nufi daga baya ko?, Allah shi kyauta Ni dai na yi iya yina wajen nuna maki tun a lokacin da aka kauro da ke bangaren nan, kika kiya , gashi yanzu shekarun ku takwas da aure, hakan na nufin shekaru na karuwa kina karra samun bukatar kula daga wajensa da danginsa, kin ki fahimta kin fi ganewa bin bayan su, sai dai in bi ki da addu'a kawai in dage wajen nemawa yan jikokina na tsari gudun kar a cin masu irin yadda aka cin maki"

Nadia ta yi shiru zuciyarta cike da matsanancin kishin da a yanzu bata jin kunyar jinsa, domin tunda ta samu ta kawar da tunanin cewa ba wai mijin Najeeba ta aura ba, mijinta ta aura itama wanda NAJEEBAr itama ta aura, dan haka wajibi ne ta so mijinta ta ji kishin abinta , ya zamo kwarai take fama da kishin Najeeba, du yadda kake tunanin kishi mai wahalarwa irinsa take fama da shi, domin a kullum a cikin zuciyarta kokowarta yadda zata yi ta zamo kamar Najeeba dan itama ta birge mijinta take, hakan ya sa ta zamo mai yawan kwaikwayon wasu dabi'un NAJEEBAr, duda wasun da kanta take shan wahala ta daina, Ama wasun bata daina ba bakin rai bakin fama ne, ko a jiya ta jima tana sauraron Muryar Sarkin gida har kusan karfe daya na dare , har aka kashe FITILUN bangarensu aka kunna wutar lantarki ta jikin get get dinsu wace idan an kunna ta, shikenan ba shiga ba fita sai in daga dakinsa zai fito da asubahi yake kashewa ta bangaren nasu baki daya, ana kunnawa a dole ta nufi dakinta ta zauna kirjinta cike da zafi da tunanin kwarai mutumen nan a dakin Najeeba yake kwana wasu lokutan, bayan bai taba kwonciya a nata dakin ba, duk rintsi sai dai su hade a nasa dakin kawai, kuma wani lokacin tana iya jera kwana hudu da girki wani abu bai shiga tsakaninsu ba, Ama gani take yi da wahala su hadu da Najeeba wani abu bai shiga tsakaninsu ba, anya kuwa ba yarda zata yi da maganar kanwar mahaifiyarta cewar asirce bawan Allahn nan ake yi ta yadda dole sai Najeeba zai fi gani a duniyarsa?.........

"Hum" ta fitar da huci mai zafi tana kunshe maganganu a ranta, zuciyarta cike da wasi wasi,

Haka dai suka ci gaba da zamansu har kusan karfe daya na rana Sannan ta mike tana ciro ky din motarta ta yiwa Nadia Salama tana fadin zata wuce gida ta dauki yan matan sai ta wuce gidanta da su a musu kitso sannan a maido su, karfi da yaji dai sun Hanna yaran zuwa saloon din NAJEEBA dake cikin fada , tun tana kwakwar son yi musu kitso har ta watsar, ta gane mamansu bata so a kai su cen sai ta watsar ta shiga lamarin gabanta, wasu lokutan idan ta Wan ga wani abin dake iya taba zuciyar wanda Allah bai ba haihuwa ba ana yi a wajen su Nadia sai ta ji tausayin wanda Allah bai ba haihuwa ba, harma ta bi shi da addu'a sannan ta sakawa nata da ta samu albarka, ta tabbata kwaya daya ma duniya ne, in dai da rai da lafiya in ita bata kara ba tana kyautata zaton samu daga tsatson su Muhammad, bale a cikin yan uwanta Zahra har takwara ta yi mata ai, nesa ne da darajar aure da ya rabata da yan uwanta Ama ai ba za'a nuna mata rayuwa da mata ba.


Rabin wunin nan Andiya ta yi shi cikin tashin hankali ne, saboda jikin momynsu zafi rau, gashi ta ki shan magani kuma ta ki yarda a sanar da kowa tace zai wuce, Ama gayanan har yanzu da ta yi sallar azahar bai wuce din ba dan kuwa da kyar ta yi sallar itama sannan ta koma ta sake kwontawa ta kudunduna

Tana zaunen nan Muhammad ya shigo shi kadai ta Babar kofa sanye da jalabiya ruwan madara ya zo ya zauna daf da ita yana lumshe idannuwansa abin jin barci ya ce" Aunty, ina Maman junior ne? Yau du ban ganta ba "

Andiya ta yi murmushi tana dan zungurin kansa ta ce" Mamana zaka ce ba na junior ba, kuma ina ruwan ka da mama tunda ka yi fushi dan kawai an yi maka fada?"

Ya turo baki yana zaunawa da kyau ya ce" Kin ga Abiey baya dukanmu, ita kuma Momy idan ka yi laifi sai ta daki mutun, kin ga da bata min magana ba jiya ya sa yau Ni ban bi Abiey ba, junior ya bi shi, kuma tun dazu bata shigo din Bama bale in bata hakuri"

Andiya ta yi murmushi tana fuskantarsa, dama shi ya fi junior sarkafar Momy , dan dai kawai halayyarsa ya da ba'a cika fahimta ba, Ama haka yake ko sunna zaman fada sai yayi shigowa hudu kawai ya dan zauna daf da ita sannan ya tashi ya koma kafin a tashi, dan dai Anmy nada sarkafarsu ne fiye da tunani ya sa har suke kwana a wajenta, da ba dan wannan ba da ba zasu iya kwana ko'ina Bama in ba tare da mahaifiyarsu ba

Wayar dake ta kuka ya da jakadi kawowa Andiya ta duka ta bata sannan ta koma wajen da suke du sunna jiran fitowar Mai baban daki karama, Ama shiru yau bata fito ba, hakan ya sa suke ta tunanin ko ba lafiya ba? Domin ba halinta bane wannan

A tausashe Andiya ta gaisar da Anmy sannan ta Wan saurara sai kuma ta ce" Anmy, Momyn ce bata da lafiya, cikinta ke ciwo kuma tace kar in je in fada zai daina, shi yasa bata shigo bangaren ki ba yau"

Anmy da yannayin tashin hankali ta ce" Subahanalah, bude min kofar baya ganinan"

Ba'a dauki lokaci ba Anmy ta shigo ta hanyar baya , direct ta nufi dakin NAJEEBA tana sake tambayar Andiya abinda yake faruwa har ta bude ta shiga hadi da kunna fitila

A saman salayar nan da ta samu ta yi sallah ta sake dukunkunewa jikinta sai rawa yake yi ga ciwon nan sai sukarta yake yi
Da sauri Anmy ta karasa tana sake furta"Subahanalah, yi maza bani wayarta in yi kiran Docter, ya Salam NAJEEBA jini ne a jikin ki?...."

NAJEEBA kanta ya sake sarawa, ita da kanta sai ta ji tamkar numfashinta zai tsaya saboda tsoron jin abinda ya dunkule mata mara ashe jinni ne har ya fara fita? Sai dai ita da kanta ta san jinin Nan ba na lafiya bane saboda ita dai rabonta da ciwon mara dan zata yi al'ada tun kafin a yi mata aure

Tana jiyo wayar Anmy da yadda likitarsu ta ce sai an zo dole saboda an ce jinni ake zubar wa, haka kuma tana jin lokacin da aka yi kiran wayarsa aka sanar masa cewa za'a fita saboda ba'a isa a fitan ba tare da ya sani ba, bale harka da ciwo ko yayane an sanar......., Anmy ce da kanta ta lafta mata katon hijab sannan jakadi ta shigo ta kama mata ita suka luluba mata alkyaba mai girma da duhu dan ta kare yannayinta, Andiya ta dauko kayanta kamar yadda Anmy ta Umarta ta kai motar da aka kawo har cikin get dinsu aka shige da ita sannan suka koma ciki ita da Muhammad wanda ke rike da waya sunna msg da mahaifinsa, msg din da Muhammad din ke sake daga masa hankali da rigima , shi kuwa yana kwontar masa da hankalin cewa ba komai bane, ciwo ne, ibada ne, in sha Allah zata warke shima gayanan zai taso da an yi suturar da suka zo, saboda ba'a yi sutura ba an samu wata matsala ce da ta saka tsaikon dole sakamakon iyalin mamacin sun nuna ai kashe musu miji aka yi, wannan fitinar ce ta saka rigima ba ta wasa ba dan wanda suka yi accus? din shima da nasa ahalin kuma suka nuna basu yarda ba dan kawai sunna daya daga cikin bayin da Allah ya yiwa baiwa irin ta maita kuma wajen kasuwanci ya haWa d'ansu da shi Marigayin dan kawai yayi ta yin ciwo dan ya rasu sai ace shine.........? Kowa dai ya san mecece shari'ar da aka jefi mutun da kalmar maita a gidan sarki, a dole wankin hula ya kai dare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login