Showing 54001 words to 57000 words out of 144591 words

Chapter 19 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2367

tausashe Najeeba ta ce" Zan sake turawa a amso min gwaje gwajen da kika min din nan, ina fata sunna nan???"

DOCTER IZRANE ta Wan sosa gaban goshinta ta ce" Gwaje gwaje?, akoy abinda ke damunki ne Najeeba??"

Jakadiya dake hada ruwan zafin wankan baby ta dago da sauri da mamaki da kuma tsoron furucin IZRANE

Ta karaso tana kame baki ta ce" Likita? , sunan mai baban dakin ce kike kamawa sak? Subahanalah wannan ai idan maganar nan ta fita sai an baki horon kwana biyu a rufe, kin kuwa san darajar da sunnanta yake da shi? Kamar ki kama sunnan mai wukar yanka ne ai kai tsaye ba sakayawa ba girmamawa fa, ina laifin Hajiya idan ba zaki yi kiranta da Gimbiya ba???"


NAJEEBA ta lumshe idannuwanta, ta yi gyaran murya kadan cikin sigar miskilanci

A hankali jakadiya ta dukar da kai ta ce" Allah ya huci zuciyarki, na fada abinda ba'a SAKANI ba tsoro furucinta ya bani, ai talaka ya iyawa bakinsa shi ya fi ALKHAIRi"

NAJEEBA ta yi mata alamun ta bar wajen da idanuwanta, wanda gaba daya a idannuwan DOCTER IZRANE

NAJEEBA ta yi murmushi tana dubanta da duban tsanaki ta ce" A'a, lafiyata kalau DOCTER, sai dai kin san abinda yake dan damun tunanina, Duda babu wanda ya min maganar, haka kawai nake ta tunanin bayan na sha maganin nan da kika bani ne gaba daya jinin ya idasa tukowa ya fito "

Da sauri DOCTER IZRANE ta dubeta lokaci daya tana fitar da ido, sai kuma ta yi gaggawar neman nutsuwa, Ama Duda haka kirjinta na bugawa hadi da motsinta ta ce" Wa,wa,wani magani? Ko kina nufin na samun sau?in ciwon marar????"

NAJEEBA ta dan dage girarakinta alamun amsar kenan

Da sauri DOCTER IZRANE ta ce" Ai, ai wannan da kika gani maganin kashe ciwo ne kika sha, cikin dai Allah yayi ba zai zauna bane"

NAJEEBA ta dan dafe goshi, sai kuma ta yi murmushi a hankali ta ce" Hakane kuma ......, DOCTER a gaida gida sai na zo amsar gwaje gwajen"

Daga haka Najeeba ta juya ta na nufi wajen su Nadiya, DOCTER IZRANE kuwa ta fice da sauri kamar ana Binta a baya


NAJEEBA na zuwa ta zauna kusa da Nadiya dake Binta da kallo kamar ta ga bakuwar halitta

Ta rage murya sosai ta ce" Nadiya, ki yi hakuri fa, kin ga doctern mu itace mijinki zai karo, kin ga kuwa ai ba wani anfani ace ta ci gaba da gannin sirin jikinmu ko? Ama fa ban san ke ba, Ni dai kam bana ra'ayin hakan, kuma kin ga in ya shigo ya samu haka kaf din mu zai kara hannamu zuwa inda yake ne, kin san amarya da dan karan farin jini, kar aje ma ya bamu hutun shekara, Ni yanzu haka in tace ta zo yau cewa zan yi sam bata zo ba dan gudun kar ta hadani da shi, ko yaya kika ce ummulkhair?"

Ummulkhair ta hade dariyarta ta ce" Kai, wannan ai da gani sai ta kai kara, amarya kuwa da shiga rai, ana iya yin komai, nima ban ganta ba, gaskiya bata zo ba, ai Anmy da jakadiya suka amshi haihuwa ko jakadiya ? Ko ke kya budi baki ki ce abinda uwar dakin ki ra fada ba haka bane?"

Jakadiya ta yi gaggawar sada kai ta ce" Allah ya hani bakina Musa maganar uwar dakina Allah ya da bana nan za'a yi maganar a gaban uban dakina, Allah ya kawar mana da fitina ko ta gardama ce"

Najeeba ta yi murmushi, tana kallon yannayin Nadiya

Nadiya da ranta ke tafasa ta dubi NAJEEBA ta ce" Wai kina nufin wannan da ta kwakula min hannu a jini ta fitar min da jinin haihuwa ce zai aura? Dama ba tsohuwar matarsa bace zai maido???"

Najeeba ta dage mata gira tana tabbatar mata

Nadiya ta cije lebe, ta saki ta kuma cijewa, ta mike tana ziziga ta ce" Lalle an yi yar cin amana, shi ne yanzu me muka rage shi da shi da zai auro mana wannan sukumbiyar?"

Zahra'u ta zauna rungume da baby ta ce" Kin san wani lokacin aure ai lokaci ne da shi, in yayi zaki ga wace aka auro din bata da tsari ma Ama kuma Allah yayi ita za'a auro sai a kawota abinta"

Nadiya ta gyada kai ta ce" Wallahi, ji fa Aunty zahra'u wannan abin, lalle nima ko za'a yi ruwan balaki ba zan ce na ganta da idona a gidan nan ba, barima in goge kiran da na mata, matsayaciya anamimiya, kaf ta gama sannin sirin jikinmu zata aure mana miji"

NAJEEBA ta dane dariyarta sosai ta ce" Kar ki ga laifinta fa, mijinki ai ya iya wannan abin, sosai yake da son auran shige yana birge shi, yana son auren munafukai ne, ba ruwanshi kuma da zumunci ai Nadiya "

Nadiya ta yi sororo, sai kuma ta ce" Hum , Ama walahi ni sai na yi mata tatasssss, marar mutunci in sha Allah zata bar mana mijinmu, bari in je in sa a Worawa mai biki girki da kunnun kanwa daga nan in shirya irin zagin da zan mata, munafuka gadkiyarki kamar yana son munafukai"

Najeeba kam lamarin na Nadiya sai ya sa ta bita da kallo baki bude, jakadiya kuwa dama tuni ta koma wajen wuta dan Anmy tace ruwan zafi na kirki take so, dan ta yiwa umi karama wanka sannan likita ta zo ta dubata sosai da sosai.


Tana fita zahra'u ta bushe da dariya tana kama haba ta ce" Kan uba, Allah mai alheri kin ga ke kuma kishiyarki lusara sak"

Najeeba ta yi murmushi tana kallon zahra'u ta ce" in ban mata haka ba tsaf zata saki baki tace masa da ta zo ga abinda ya faru, da kishi kadai zaka samu yadda kake so a wajen Nadiya...., itama wai har kishin mijinta take yi abinta"

Zahra'u ta yi murmushi ta ce" A'a barta ta yi, kema ai yi kike yi, Ni na zata yanka likitar nan zaki yi da kika shige kicin da ita, baki ga tsoron da ya kamani ba, har na hango mun shiga uku mun lalace saboda in kika aikata din sai in rike wukar sauran su damuka a hade a rufe"

NAJEEBA ta yi dariya kadan ta ce" Kin san me, ai ita nan fa gani take yi wata kwaluwar yar iska ce, idan har na yarda na yi hauka hauka tabas kwana zan yi a ciki ba tare da na samu abinda nake so ba, da ace na yi mata hayaniya murya zata bude ta tona mana asiri, ta da ya sa a mayar da kowace dakinta yanzu yanzu, nima ya samu abinda zai ce na yi , kuma banda hujjar kare kaina saboda an kamani tsamo tsamo......, zan tardata a inda daga Ni sai ita sai Allah, in sha Allah sai na samu wani waje na makara mata balakin da zai zamo mata chronique a jiki wanda zai sa ta ringa balar magani kullum saboda zafin ciwo"

Ummulkhair ta ce" Dan Allah ki je da Ni kafin a kora mu, dan Allah ki taimakeni ki bani dama in mata mari daya, shegiya mai kama da yan iska"

Ummukulsum dake mulke baby da man kadanya tana kokarin shirya shi cikin kayan sanyi ta ce" Ke dila a je da mu dai, ai ni kafin in shige Najeriya sai na yi guzurin hakorinta guda, tabasss sai na hannata cin nama da dadin rai fitsarariya, ke bata da gaskiya yanzu na yarda da sa hannunta a matsalar zubewar cikin nan, Ama ai Aba yace zai je ya amso gwajin ko? Muna nan muna jira"


Haka suke ta shan firarsu har suka rufe babin a lokacin da Anmy ta fito domin ko ita ba zasu yarda ta san cewa DOCTER IZRANE ta zo ba, sai dai idan ta cctv Camera za'a gani .


A lokacin da DOCTER IZRANE ta fito ta nufi inda ta ajiye motarta da sauri ta shiga

Tana shiga ta cire takalman nan nata ta zubar a cikin motar ta tayar da motar ta samu ta fice daga gidan sannan ta dakata bakin hanya tana Hanna kanta barin jikin da take yi

Gaba daya a tsorace take da maganar maganin da Najeeba ta yi, da kuma maganar ummulkhair........ Yaya za'a yi Najeeba ta nuna dan kawai ta so shiga dakin anmy ne ummulkhair ta yi furucin da ta yi?, a furucinta me ya kawo maganar ba ita ba sake gannin sirrin ya'yan MUTALAB???, tabasss maganar kilacewar da aka ce ta yi a gidansu ce, da akace ko Sultan ke neman aurenta? Sai dai mahaifiyarta tace itama bata sani ba, sako ne ya zo dan haka ta kula ko waye za'a bata an gani ana so ne , kuma mai daraja ne ko waye tunda har aka bata damar kilace kanta, sai dai su sun sakata a rudani, da farko ta zata Sultan ne, Ama gaba daya matarsa ta nuna mata ba haka bane domin sam bata nuna mata kishinta take yi ba, sam ba kishinta a idannuwan Najeeba, ko kadan ba kishinta, kenan waye? Kai ina, wallahi ba zai yiwu ba, ita fa baban take so, mai gayar take so ba yaransa ba, to in yaransa ne ta komawa tsohon mijinta mana? Cabdijan.........

Rasa madafa ta yi, da kyar ta iya ciro wayarta ta shiga whatsup msg......

Ta rubuta msg din da zai sanar da shi ta zo, kuma ga abinda ya faru ya fi a irga tana gogewa......, da ta rasa madafa sai kawai ta rubuta msg kamar haka' bayan gaisuwa da fatan ALKHAIRi a gare ka sarkina, ina mai miko sakon barkata da samun baby a gida, Allah ya raya, sannan mai baban daki ta tambayi takardun gwaje gwajenta , sai dai ban sanar mata sunna wajenka ba dan kar na yi laifi, a huta lafiya , Allah ya karra lafiya"

Daga haka ta tura ta ajiye wayar zuciyarta cike da kunci da bacin ran abinda ya faru

Daga nan sai kawai ta nufi gidan aminiyarta

Tana zuwa ta sameta a kofar gida ita da ?a?anta yan mata uku sunna zaune sunna shan fira

Zama ta yi cikinsu sunna tafawa harda uwar tana dan daurewa, har ta sanar mata abinda ya gama faruwa

A lokacin da mai aikinta ta kawo ruwa saboda bakuwar ta ajiye mata, daya daga cikin ya'yan hajiar ta bude kai a nan ta saka mai aikin tsefe mata gashinta tana fadi da karfi, hajiar na dariya ta ce" Kai , bebe dai an yi asarar haihuwa"

Mai aikin ta bi bakin hajiyar da kallo ta mike ta shiga tsefema yarinyar hajiyar kai ranta du a jagule a nan ne IZRANE ta ce" Kin san Allah ko? Gaba daya a tsorace nake, kar aje ba shi bane ya bada sakon kilacewar nan"

Hajiya ta ce" Ke, karfa ki daga hankalinki, dan kilacewa in dai aka bada umarnin yi to daga fadar sarki ce, kuma in ba sarki ba aminin Sarkin ne mai sarautar ne, ke dai bari lokaci yayi mu sha bidiri"

IZRANE ta girgiza kai ta ce" Kin san me ya sake bata mini rai? Wannan Najeebar, wai kin ga yadda yarinyar nan ta keru? Subahanalah sai da na raina kaina, kuma in gaya miki kamar ba ita ta yi ciwon rasa ciki ba, sai kyali take tana zuba kanshi, Ni na rasa wannan kanshin nata wasu irin turaruka ne, kai zan shiga kasuwa da kaina wajen tubawa in kashe kudi na kirki in amso turaruka, Allah baki ganta ba, kugun nan nata kamar ba na wace ta haihu ba, yayi pankaka ya cika ko'ina Pam, cikin kuwa a shafe sumul, hum kin ga gashinta? Wani irin haushi da ya kamani sai da na ji ina addu'ar inama ta sake yin wata rashin lafiyar a kawota in saka mata karin ruwan da jinninta baya dauka ya aikata kiyama, anya kuwa a gaban matar nan zan birge shi????"


Hajiya ta ture hannunta ta ce" Ke dan Allah kar ki sare, to me zata gwada maki? Aikin banza har wani kyau gareta? Ke baka ce fa"

Mai aikin Hajiya ta Wan tabe baki a zuciyarta tana mamakinsu, cabdijan mai Gimbiyar damagaran? Wai wa suke nufi? GIWAR mai DAMAGARAN? Itace suke haWawa da wannan? Lalle wai GIWAR mai DAMAGARAN zata kashe? Hohoho, ai ko cikin da ta barar mata Sa'a ta ci, ita dai in ta ga zasu taba lafiyar GIWAR mai DAMAGARAN wallahi zata kai maganar gaba, dan ba zai yiwu ba, ba zata taba iya kyalewa tana kallo matar dake ciyar da iyayenta ba tare da sun mata aikin komai ba, ba wulakanci, ba tozarci a ce za'a wulaka??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ntata ta kyale ba, kak!

Izrane ta ce" ke ba zaki gane ba, wallahi matar nan ta gama samun halitta dole ta dagawa mazanku hankali....., hum Ni yanzu ai gaba daya wani tunani nake yi, zan je Tunisia ne a min aiki, a kara min duwawu a rage girman nonon nawa"

Y'ar Hajiya ta kalleta a zabure ta ce" Wayo Allahna mafarkina, dan Allah Aunty ki je da Ni"

Hajiya ta maketa tana fadin" Ke dan Allah tafi cen sakarya, baki san mutuwa ake yi ba ? Ki rufawa kanki asiri Ni ba a haka na yi auren ba?"

Ta tabe baki tana sosa inda uwar ta daka ta ce" A yaya aka yi auren? Saki nawa aka yi? Yan matan baba nawa? Ni dai gaskiya kin cuceni da na yo ki, ina ai Ni kudi kawai nake jira ina samu sai na isa zaku san na tafi"

Yan uwanta suka bushe da dariya, hakama uwar dan su dariya ta basu, IZRANE kuwa takaici ya sa ta kasa ci gaba da maganar, sai faman leka WhatsApp dinta take tana karawa, Ama kamar yadda aka saba ba amsa, bata taba yin msg ya bata amsa ba, sai kiran nan da ta masa ya daga, in dai magana take son yi da shi to ta nuna ta shafi lafiyar matarsa ne, Ama in ba wannan ba babu hanyar da take samun yi masa magana.........ya Allah




A gidan su Ummi baba da Aba MUTALAB



17
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne, Vip 1 k
Normal grup 500
Yan Nijar vip 1000francs
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




18



Tun Jiya da dare da suka dawo Aba ke hankalce da ita, da tunanin ko zata yi masa maganar wannan fitina da ta doso su? Sai dai tunda suka shigo gidan ta yi dan fadan ta da nuni cewar ana yiwa yaran nan sake da yawa ta hade komai ta zuba a kwondon shara, ......kwarai ya san irin yadda take da kawar da kai da kara a lamarin da ya shafi Najeeba, Ama a irin yadda najeeba ta fashe da kukan nan a Jiya da ace wani ne cen take aure ba SHAHEED ba da bai san ko zai iya jurewa ya fito ya bata baya ba, sai dai irin karar kanwarsa ya sa baya iya cewa ufan a kan lamarin ya'yan nan, domin in har zai yi halaya irin ta mai kunya tabasss zai cire idannuwansa a kan lamarin da ya shafi Balkissa da ya'yansa, dan shi ya sani a lokacin da ba ya'yan a gabansa itace mamansu itace babansu.

Kiran da ya shigo wayar ta aka sanar mata haihuwar umi karama ya sa ta mike ta shiga shirin tafiya sai murna take ya saka shi bin bayanta

A lokacin da ya sameta a daki tana nada lafayarta ya dubeta da kula ya ce" Maman auta, zauna mu yi magana"

Kallonsa umi baba ta yi sai kuma ta zauna din tana fadin" To baban Auta "

Zaunawa yayi bayan yayi murmushi, sannan ya dubeta da kula ya ce" Bakya gannin ya dace ki zanta da NAJEEBA? Inaga ya kamata ki sameta ku yi fira a tsakaninku wace zata sa ta yi hakuri da duk wani abu dake damunta, kin ga yanzu zan koma asibitin nan a yau sai an bani takardun nata na kaima mamansu, Ama zan so ace ta kwontar da hankalinta saboda bana son irin yadda take daga hankalin nan nata dan Allah "

Ummi ta sauke ajiyar zuciya, da ace ya san irin yadda take ture komai tana tafe da ya jinjina mata, gaba daya hankalinta, tunaninta, komai nata a kan NAJEEBA ne tun daga Jiya har yau, kwarai ta san Najeeba ba zata taba saurarawa a kan maganar nan ba, sai dai ta fi so a fara kwontar mata da hankali in aka sanarwa da mijinta babu hannunta a cikin zubar da cikin nan Shikenan, sai ta rarasheta ta sa ta bar maganar, Ama a yanzu ita da kanta ta san yarinyar nada bukatar addu'a da kuma magana mai dadi, bale da ya zamo ta yi furucin nan a coridor, shi ya fi tsaye mata a rai, irin furucin da ta yi ne itama a lokacin da ta juya baya ta bar babansu, sai da ta shekara kusan ashirin da wani abu kafin ta dawo, tun da jan sawayenta sai da suka bace ta dawo har ta iya dubansa,

A hankali ta ringa murza hannayenta, a sanyaye sosai ta ce" Bana so ne ta samu wata kafar da zata bata damar yin wani tunanin da bashi da anfani a kan mijinta da kuma duk wani abinda yake tare da shi........."

A hankali ta langwabar da kai ta ce"lokuta da yawa mace na kamuwa da son namiji fiye da yadda shi yake sonta....., ban san ko wannan dalilin yake sakawa du abinda ya shafi namijin sai ya zamo mace na dauka da karfi har ta yi riko mai karfi ba????"

Ta Dube shi da kyau ta ce" Abinsu, ka san irin yadda take da taka tsantsan a abinda ya shafe shi, shine dalilin da yasa ta kasa sakewa da ya kasa bi hanyar da ya dace dan ya saurareta....., Ama kuma ka ga tsawatarwa ake yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login