Showing 9001 words to 12000 words out of 144591 words

Chapter 4 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2329

suke nan gaba daya dan a tsawatar a katse abin, domin ita fitina farkon ta aka sani ba'a san karshen ta ba....., Ama gaba daya hankalinsa ya kasu gida biyu ne, gaba daya hankalin nasa nema yake ya bar inda ake rigimar nan ya tarda gidan rigimarsa .


Sun samu gannin likitar da isarsu Babar clinik din garin damagaran

Nan da nan aka yi ciki da ita

DOCTER IZRANE, Itace ainihin likitar dake kula da lafiyar matan SULTAN, tun daga kan haihuwar Nadiya ta biyu da ta yi a asibiti aka saka ta zama likitarsu, kasancewarta kwarariya gogagiyar likita ya sa Docter muhseen hadata da familly din gidan Sultan har ta zamo amintaciyar likitar matan Sultan , domin duk wata damuwa tasu da ta shafi likitar mata itace ke tsaye a kai, ita ke amsar haihuwar Nadiya, ta NAJEEBA kuwa dan bata samu wata haihuwar bane da itama ita din ce zata amsa

Docter IZRANE ta yi dogon karatunta a kasar waje, wato Turkiya, bayan ta dawo aka hada aurenta da cousin dinta wanda suka ji ma sunna soyaya, sai dai bambancin dabi'u da rigingimu mararsa tushe ya katse auren tun bai kai ko'ina ba, ta zamo matashiyar bazawara mai matukar ji da kanta, wace take murza Babar mota take kuma zaune cikin isa da dukiya daidai zamaninta itama

Docter IZRANE ta kasance mace mai mugun ji da kai, da isa da kai, baban abinda ya sa ta fara bijirewa mijin da take aure shine gannin cewa tafiyar su ba zata taba zamowa daya ba, a matsayinta na Babar likita, wace ta keta hazo kasa da kasa ta je ta yi karatu mai zurfin gaske da zafi, ta dawo da takarda mai kyau ba zata taba iya zama da malamin jami'a malamin philosophie tsal ba, mutumen dake fama da yau da goben rayuwa...., gaba Waya ita din ba kalarsa bace, duda shima ya fito ne daga tsatso mai arziki Ama kudin baba ai ba na d'an baba bane bale da ya zamo gidan na baba yaya ne masu yawa ba zata taba iya wannan wahalar ba, wannan ya sa ta dage kai da fata sai da ya gaza hakuri bale da ta ringa saka rashin da'a tana yiwa mahaifiyarsa a dole ya je ya samu iyayensu ya salameta da fatan ALKHAIRI

Docter IZRANE ta yi sunna sosai a asibiti baba na kudi wanda ya fi kowane kudi a DAMAGARAN saboda irin yadda take da dagewa da kuma mugun cusa kai a duk inda ta samu, domin du wani mai kudi tana ?awance da shi ko da matarsa dan samun abin duniya .

Tunda Docter muhseen ya bata damar zuwa ta yi tsaye a kan lamarin Nadiya ya zamo bayan Nadiya ta haihu har ta samu gannin MAI DAMAGARAN hankalinta , tunaninta, burinta ya kai nan ya diga aya, aya mai zafin gaske, kudiri mai zafin gaske, kudirin da ta yiwa kanta alkawari ko ana ruwan muzuru sai ta zamo zakaran da Allah zai ba Sa'a, domin har yanzu rabin fuskar da ta gani a cikin rawani na yi mata gizo, izar da ta dame Tata, isar da ta cinye Tata, aji, dukiya, classss din da suka hade suka shanye nata suka zauna Dar a cikin zuciyarta har ta gama yarda cewar a yanzu ne ta yi dace da daidai da ita ya da take yaki, ba dare ba rana ta dukan hanyar da ta dace dan ta kai ga ci

Sai dai tun bata je ko'ina ba aka bude mata CD, CD mai zaman kansa, labarin da ya so razanata, labarin da ya rike zuciyarta, ya saka kiyaya mai tsananin gaske , da alkawaruruka masu tsaurin gaske, ta rantse da wanda ranta ke hannunsa ita IZRANE sai ta goge GIWAR MAI DAMAGARAN daga duniyarsa ta maye gurbinsa........, in da wani yannayi, in da wace wuka sai ta yi yakin nan, tana kuma da yakinin cewa sai ta kai ga ci!........


Itace tsaye a kan Najeeba rike da takardun hoton cikin da ta yiwa NAJEEBA

Ta dago ta dubi NAJEEBAN ya fi a irga, wace ke kwance, jakadi na yi mata fifita du irin sanyin ACn dake dakin kuwa, gashi ta kanainaye ta ki bada kowace kafa da za'a gana da NAJEEBAN

Irin yadda kirjinta ke bugawa na hoton scan din ya fi komai daga mata hankali, juyawa ta yi wajen teburin ta ta ja ta ringa dubawa da sauri da sauri tana neman maganin da takan ba wasu matan a boye, wa'inda take cazar kudi ba na wasa ba wajen mata dan ta taimaka musu, domin taimako ne ba komai ba, zuciyarta cike da tsoron kar aje ko ya kare, ai kuwa ta samo guda daya jal dan haka ta balo shi ta ajiye hoton cikin ta dauki ruwa ta karasa inda Jakadi ke ta addu'a tana tofa mata hadi da fifita a nutse ta ce" Jakadiya, ga maganin nan a kamata ta tashi ta sha, zai sake taimaka mata jinnin ya tsaya "

Ai kuwa jakadiya ta amsa ta gyara rufar NAJEEBA ta taimaka mata ta Wan daga ta bata maganin ta hadiya sannan ta koma ta kwonta

Wata irin ajiyar zuciya IZRANE ta sauke ta koma ta zauna tana kallon skin din NAJEEBA..........
Takan tambayi kanta ko dai sun haWa jinni da yan Ethiopia? Sai dai abinda take ji a ranta dangane da ita ba zai bata damar neman sannin wannan amsar ba, ita dai ta san duk tsiya fara ba zata fi bak'a ba, ko ya wancen matar tasa da bata gabanta ita ta yarda har wannan ta shiga gabanta a gaban mijinsu.

Shan maganin NAJEEBA da yan mintuna wata irin zufa ta karyo mata, lokaci daya ta dago ta damki hannun Jakadiya ta fitar da wani irin nishi wanda ya fito da dunkule mai girman gaske hadi da mugun ciwon mara, lokaci daya ta ce" Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une"

Jakadiya hankali tashe ta rike hannunta da kyau tana furta" Sannu GIWAR Mai WUKAR YANKA, sannu uwar marayu, sannu HALAH DIN Garin DAMAGARAN, sannu Allah ya baki lafiya"

Likitar ta mike da sauri tana saka Safar hannu ta ce" Lafiya Gimbiya? Ciwon ne dai? Ko mu saka karin ruwan da zai sa ki ji sau?in ciwon marar?, ai wannan maganin zai tsayar da zubar jinnin Nan ne gaba daya, saboda ai shigar ciki ne da ke Hajiya"

Jakadiya ta dago da sauri jikinta na daukan rawa hadi da zarro ido

NAJEEBA ta lumshe zara zaran idannuwanta .........Muryarta a kurya sosai ta sake furta innalilahi wa Inna ilaihi raj'une kafin ta Wan motsa ta sake yarda da abinda take ji a jikinta, domin dama shinfida aka yi bayan an dora leda baba sannan aka sake yin wata shinfidar a saman gadon kafin a kamata ta hau

A hankali ta dubi jakadi, Muryarta a raunane sosai ta ce" Ki min kiran Anmy.......inaga cikin nan ya riga ya fice ai jakadi"
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




4



Gaban Jakadiya ya yi mugun faduwa, ta rage tsayinta tana furta" Subahanalah, ciwo ne uwar gidana, ciwo ne, in sha Allah ba zai fita ba wannan cikin"

Likitar nan ta tabe baki ita dai ta matsar da jakadiya , fatanta ta yi ta kautar da duk wani abin da sai saka a yi tunanin magani ya zubar da cikin , dan haka cikin gaggawa ta nemi da NAJEEBA ta gyara kwoncinta ta dubata

NAJEEBA dake jin jinni na daukar ta a zaunen nan ta dago zuciyarta cike da mugun rauni ta sauke idannuwanta a kan abin awon dake hannun Docter a tausashe sosai ta ce" Docter, bayi nake son shiga, marana ke ciwo"

Shigowar Anmy da sauri ta karaso tana rike hannun NAJEEBA, sai kuma Najeebar ta dubi Anmy, ta sada kanta, ta sake dagowa a hankali ta rike hannun Anmy din itama sai kawai ta Wora kanta a kafar Anmy a hankali ta fashe da kukan dake saman kirjinta

Anmy ta lumshe idannuwanta zuciyarta cike da rauni, a sanyaye ta dubi Docter ta ce" Docter, a duba a gani, idan har ya fice ne sai a yi mata du abinda ya dace"

Docter ta sake sakawa Najeeba ta kwonta, Anmy na rike da hannunta likitar ta shiga auna Najeeba ta hanyar sake bude rigarta ta shiga sake auna cikinta, domin cikin ya kai wata biyu ana iya ganninsa a hoton ciki

Ai kuwa ta duba ta duba bata ga irin abinda ta gani na dazu ba, fuska cike da alhini ta dubi Anmy tana girgiza kanta

Anmy ta sauke ajiyar zuciyar zuciya ta yi mata umarnin a ba Najeeba dukan kular da ta dace, sannan tana gefe har aka yiwa NAJEEBA ?arin ruwa sau biyu ciwon ya lafa sosai, sannan ita fa kanta ta kamata suka yi bayi, Jakadiya kuwa ta hade duka abin jinnin ta dauke ta kai mota sannan ta sake dauko wani zannin gadon ta dawo da shi ta sake shinfidawa hadi da zuwa clinik ta karbo auduga harda su sababin pant na maternity ta dawo tana jira , har suka gama suka fito aka wuce da NAJEEBA dakin hutu, sannan likitar da jakadi suka je da sauri suka gyara shinfidar da kyau ta kwonta likitar ta sake jona mata wani karin ruwan mai haWe da maganin barci sannan ta sanar da Anmy cewar sai gobe zata saki NAJEEBA


Da yama Umi ta karaso asibitin janye da hannun Anissa, Y'ar wajen zahrau ce wace take da shakuwa da ummi sosai, sai Elhaji MUTALAB da mai aikin dake rike da kwondon abinci da fruits din da suka zo da shi

Nan suka samu matar Dayabu saboda Andiya ta kasa hakuri ta yi kira ta sanar mata tana kuka, shine ta nemi layin Anmy ta sanar mata ga inda suke, haka kuma Anmy din ce ta yi kiran yaya MUTALAB ta sanar masa saboda ta san in ba shi din ta sanarwa ba Hajiya bilkissu ba zata zo ba, zata ce ne ba tana nan ba, ita kuma tana matukar son ta zo din, saboda kukan Najeeba na zubewar cikin nan ya matukar shiga zuciyarta, bata san ko tana da karfin da zata iya rarashinta ba, domin lamarin haihuwa itama uwar kanta shine jarabawarta kafin ta tattara komai ta ajiye gefe ta fuskanci rayuwa kuma ta sha fama bale Najeeba dake yarinya

Gaisawa suka yi a mutunci a dan filin da yake na kofar dakin hutun ne, kawatuwar asibitin ya sa a kowani dakin jinya aka tanadi irin wajen nan mai dauke da kujeru da kuma abin shinfidawa kwaya daya dan yan zuwa dubiya saboda kar su taru a dakin mai jinya su hadasa masa wani lamarin na takura , bale idan baya son hayaniyar mutane

Jajantawa suka yi da fatan samun lafiya, Oumi ta ce" To Anmy ai ya dace ki je gida ki huta, ga Jakadiya dai ta kwana a wajenta ko?"

Anmy ta kalli Oumi da mamakin furucinta kafin ta kalli yaya MUTALAB ta yi kwafa ta ku bata amsa, shi kuwa ya ya jinjina kai ya ce" Idan kin san ba zaki zo duba mata y'a ba ai da zamanki kika yi bilkissu da ki zo ku raba hali a nan, ke dai da ba zaki kwana ba sai ki koma gida Ama batun kwana wajenta Bama hurumin ki bane ai"

Umi ta yi murmushi hadi da kame baki ta ce" Au, ban san zagin sarakuwa laifi bane, da ban yi ba ai, gani na yi matar nan fa ta tsufa, sai wani lumtu take yi abinka da hutu sak"

Anmy ta yi murmushi tana nunota ta ce" Kin dai ga bana son neman magana, tam"

Itama ta yi yar dariya sannan a tausashe ta ce" Ki kwontar da hankalinki , ki yi hakuri, in har tana da rabon na tabbata wankin ciki hakan zai zamo mata ta sake samun wani, Allah ya bata lafiya"

Anmy ta amsa cen kasan makogwaronta, kafin a hankali ta dubi umi ta ce" Ya kai wata biyu , ta yiwu shi yasa ta yi kuka......, kin ga ta Wora kanta a saman cinyata kafin ta fashe da kuka "

Yaya MUTALAB ya kame haba ya ce" Wai Gimbiyar? Lalle abin ya taba zuciyarta , ko kuma sangarta ce dan ta ga babarta a kusa, dan yarinyar nan na jima da gane abinda zata yi a gabanki daban da wanda zata yi a gaban al'umma "

Anmy ta ce" Yaya fa, Allah hankalina du ba a jikina ba"

Ummi ta yi murmushi tana katse kiran Ummu Kulsum, dan ta tabbata ta yiwu ta nemi layin Y'ar uwar bata samu ba shine zata fara aiko mata kira, yanzu kuwa da daya ta ji cikinsu sun ga damar cika asibitin nan har biyun dake agadaz ba zai ce musu komai ba su taso gobe gobe saboda wannan

Nan dai suke dan taba firarsu har lokacin sallar magariba ta yi , matan suka shiga dauro alwallah, shi kuwa yaya MUTALAB ya wuce dan samun sallah a masallaci

Bayan sun gama sallar magariba tare suka shigo shi da SULTAN SHAHEED da kuma JUNIOR

Gaba daya asibitin ta cika da dogarai da special masu bashi tsaro , wato sojawan dake bashi tsaro duk inda zai je, sunna ta aikin kai kawo da kuma dakatar da masu shiga da fita in dai dan dubiya ne kawai da nunin za'a basu damar shiga su Wan dakata nan da mintuna kadan, sai wa'inda zuwansu na emergency ne ake bari su shige

Kai tsaye dakin da take ya nufa tare da Aba, sunna tafe sunna dan taba fira har suka karasa sannan ya gaishe da iyayen nasa kafin ya nufi dakin da take din, junior na son binsa umi ta rike shi da fira dan a bar baban nasa ya fara shiga dakin , saboda ta farka daga barcin, abin maganin ne kawai bai saketa ba shi yasa bata da karfi a jikinta

A hankali ya karasa gaban gadon ya zauna bakin gadon sannan ya saka hannayensa ya dagota gaba dayanta ya rungumeta tsam a kirjinsa yana sake rufa mata alkyabarsa sosai a jikinta

Idannuwanta ta lumshe , kirjinta na sake tsananta bugawa da radadi a cen cikin zuciyarta, ....., tabasssss ta dangana tun kukan da ta yiwa Anmy ta yi hakuri ta roki Allah ya bata wani, Ama kuma yanzun da ya zo sai ta ji rauni sosai na lulubeta

A hankali ya furta" Beebah, kirjinki yana bugawa sosai, nd jikin ki da zafi, har yanzu jikin ne?"

NAJEEBA ta sauke ajiyar zuciya zata bashi amsa aka bude dakin aka shigo

Du irin yadda ta shigo da karfinta sai da ta ji kamar za'a bugata da garu sanadiyar irin yadda ta tarar da matar nan a jikin bawan Allahn nan

A lokacin da nurse ke sanar da ita masu garin ne fa suka karaso asibitin sai da ta yi mugun mamaki, sannan ta sake yarda cewar kusancin dake tsakaninsa da Najeeba ba zaka taba hada shi da Nadiya ba, saboda ita dai haka Salim alim ai bata ga ?afarsa a asibitin nan ba, sai dai ita ta je ta sanar masa abinda ya shafi rashin lafiyar matarsa dan kawai ta samu damar ganninsa, Sai gashi ya shigo yau saboda ciwon wannan bak'ar? Lalle,
Shine fa ta yi gaggawar mikewa ta shirya da kyau sannan ta dauko takardun awon cikin Najeebar ta nufo dakin , sai dai sai da ta yi dana sannin shigowa ta samu wannan abin bugawar zuciyar, ita bata san cewa da ace iya shi da ita ne a asibitin Sarkin bulala Bama zai bari ta shiga ba sai in mai DAMAGARAN ya fito, Ama yanzu Anmy ta bada damar ta shiga din, dan ta tabbata dan ta fada masa komai da kanta ne, ta riga ta san cewa shi zai fi Najeeban jurewa da jin wannan labari sannan zai karfafa mata gwuiwa ne

A nutse ya sake saka alkyabarsa ya lulube cinyoyinta dake waje saboda rigar dake jikinta doguwa ce dakakiya kuma tana ja sama da sauri, ta ja din ne sanadiyar dagota da yayi ya dora a saman cinyarsa


Dubansa ya dago ya dora kan Docter dake tsaye tana hade dukan bacin ranta ,

Cike da basarwa ta dauke kanta daga haka din ta karaso tana dan dakatawa daga nesa kadan ta furta" Barka da warhaka excellency, Madame yaya sau?in jikin? Ina fata zuwa yanzu zubar jinnin ba zafi?"

SHAHEED ya sake duban likitar a karro na biyu kafin ya saka hannunsa ya dago habar Najeeba ya zamo ta dago idannuwanta ta saka cikin nasa......, a hankali ya furta" Bleading?, what hpn Beebah.........ko mnstr ne ya zo maki da zafi?????"

Furucinsa a hankali ne, sannan a tausashe , hakan ya sake tsuma zuciyar IZRANE, har ta ji ta kasa tsayawa ta furta" Ba mnstr bane , bari ne, Ama da sauki ya fice bai bata wahala ba, idan ka gama zan yi bayanin komai na lafiyarta Allah ya karra maka lafiya"

NAJEEBA ta dan juyo dan irin yadda likitar nan ta shiga tsakanin maganar ta da mijinta ya matukar bata mamaki, koda yake likitar nan ai tana da wani abin mamaki nata na kanta, domin idan basu da lafiya ko maganin ta rubuta musu kafin su sanar masa ita take fara sanar masa, bata san dalilin da yasa take yin haka ba, ta yiwu ko dan ta sake samun gurbinta na zamowa likitar gidan su ne? Koma meye dai ita ta sani

Da yan yatsunsa kawai yayi mata alamun ya fahimta, gaba daya hankalinsa a kan yanayin Najeeban da irin yadda jikinta yake, dan haka bayan likitar ta fice ya bude rawaninsa sosai fuskarsa ta bayyana ya sake talabo fuskarta ya hade goshinsa da nata a hankali ya furta" Dama mun samu ciki baki fada min ba?"

Najeeba ta lumshe idannuwanta, a hankali ta furta" Ban san

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login