Showing 66001 words to 69000 words out of 144591 words

Chapter 23 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2356

ga mun shigo ba nan bane zan ga likitar, cen baya ne, likitar kuwa ga msg din ta ko zata zo sai nan da minti arba'in saboda kiranta aka yi yarinyarta ta bata, Ama tace an ganta a sabon Gari gidan mai gari, zasu amso yarinyar ne su karaso asibiti, lokacin zai isheni in je inda zan je in dawo......., plz kaleni, kaleni Ummu"

Ummu dake zarro ido tace" Ina zaki je?, Najeeba kin manta waye Sultan???"

Najeeba ta damka mata ta ce" Duk rintsi kar ki yarda Sarkin bulala ya san fita na yi, zan dawo yanzu in sha Allah "

Da gudu gudu NAJEEBAN ta juya ita da Aida suka bar ummulkhair tsaye jiki na mata rawa

Ta kofar fita daga asibiti suka fita da motar Aida, bayan Aida ta sanarwa sojan dake tsaron kofar fitan cewa sunna dawowa, dama shi ya barta ta shiga ta nan, saurayinta ne, ya kuwa ce mata sai ta dawo

Hanya suka dauka bayan mai yi mata lokalizen wayar ya dana kira, da wayar Aida ya yi a minti biyar ya sanar mata inda IZRANE take ....wanda hakan ya sa Najeeba sake duba adrss din ta ce" Nan ai gidan lauya ne, me take yi a gidansa????"

Aida ta ce" Ban sani ba Aunty, yanzu yaya zamu yi kennan?, na san yanzu haka sunna kofar gidan da suka saba zama kin san yan anguwa sun yi sun yi sun kawo ido sun zuba musu da an yi sallar magariba suke fitar da abubuwan zama su cika kofar gidan da kawayenta da yan duniyan anguwa irinta su yi ta iface iface har dare ya ratsa"

Najeeba na duba time ta ce" Mu je"

A haka Aida ta dau hanyar, ta falfala gudun da minti goma sha uku ya kai su Najeeba anguwar

A lokacin da suka tsayar da motar daga nesa Najeeba ta sauka tana hangensu ta ga yawansu ta kuma tabbata idan ta je a haka komai na iya faruwa sai kawai ta amshi motar Aida ta sa ta tsaya gefe ita kuma ta nufi inda ta bar gungun samari a farko anguwar

Tana tsayawa ta sauka bayan ta rufe fuskarta da kyau ta karasa inda suke, a yannayin yadda suke bushe bushen shisha ya ganar da ita abinda take so zata samu

Ba wani tsoro ta sanar musu bukatar ta tana duba time, ta kuma zube musu kudin da ya tsoratasu

Daya cikinsu ya ce" Ama ke baby kin ga ai cen din anguwarmu ce, yaya za'a yi mu musu wannan gajaliyancin???"

Najeeba ta Dube shi ta ce" Ba damuwa, bani kudina, ban ce ku taba lafiyar kowa ciki ba, abu ne zaku yi na minti biyar, da zarar kun hangi na ja motata kuma ku ware, Ama idan ba hali ku bani kudina zan kaima wasu"

"Kai kanwar babarka ce uwar sa'idar?, dillah malan mika jakar nan dakinka rufo, ka kwaso mana wukake, Ni idan na samu kuncin hajiyar nan sai na dala mata mari saboda irin yadda ta wulakanta min uwa aka hannamu magana dan ana tsoron mijinta, mu je mu raba shi da kaya malan idan kuwa baka ciki bamu mu mu yi aikin lada" Mansur ya fada da karfi yana mikewa hadi da jan wandonsa da kyau

Najeeba ta juya ta shige motar ta koma kusan Aida ta bar mata motar da fada mata cewar kar ta kashe motar sannan ta karasa ta tsaya dan nesa da su tana hangen kwanar kwalawan

Ko minti uku ba'a dauka ba suka shanyo kwana da makamai suka dirar musu, a lokacin basu taba tunanin gannin haka ba, saboda ba'a taba yi ba, hasalima basu taba hasashen gannin haka ba, hakan ya sa suka rude, wasu suka yi cikin gidan da gudu, wasu suka yanki hanya a guje sunna ihu su kuwa du wace ta yarda ta musu garaje sai su daki banza ba ruwansu

Tunda ta ga mikewarta ta nufeta gadan gadan ta shakota ta baya ta nufi duhu da ita ta makata da jikin bango, makawar da ta fi wace ta yi mata a falon Anmy

A rikice ta budi baki tana ihu

Sai dai Najeeba bata bata damar morewa da ihun Bama ta zabga mata mari, ta taro mata wani, ta karra mata wani, sannan ta ja rufar da ta yiwa rabin fuskar ta bayan ta matse mata wuya da baki sosai ta fido mata idannuwa tana kallon ta ido cikin ido ta ce" Na san ke kika bani maganin zubar da ciki, idan har baki kai kanki kin tona asirin haka a gabansa ba, ina mai tabbatar maki a nan zan nuna miki ke karamar yar duniya ce a duniyar yan duniya!, kar ki yi tunanin saboda zaki aure shi zan adabeki, ke kike binshi, Ni shi ya biyo NI! Kuma ai isasshen namiji ya ajiye hutu, bayanki ma sai na karo masa wata, cikina da kika zubar ne zaki biya du wani digar jini da na yi sannan ki sanarwa wanda kika yi dominsa idan ba hakanan ba IZRANE sai na gigita duniyar ki!"

Daga haka Najeeba ta ja kanta ta buga da garun nan, wanda hakan ya sa IZRANE silalewa numfashinta na daukewa ta kai duniyar suma

Da gudu Najeeba ta karasa motar ta shige , Aida ta daga birki ta dauki hanya suka bar wajen , a lokacin ne kuma yan daban summa suka shiga watsewa a haukace saboda kukan motar polisawa dake karasowa inda suke......


Aida na tuki Najeeba na cenza kayanta da wani irin sauri, lokaci daya tana dane kiran dake shigowa wayar Aida da NUMBAR ummulkhair


Da wani irin gudu suka shige likitar najeeba ta sauka da sauri tana daura nikaf din ta da komai , ta karasa wajen wata buta karama ta sura sannan ta nufi lungun da suka bi dazun tana yiwa Aida alamun su yi waya, ta nufi hanya tana tafe a hankali hadi da mayar da numfashi, har numfashinta ya daidaita sannan ta fito lungun ta dauki hanyar inda zata ga likitar, wato inda ta kwatantawa ummulkhair


A lokacin da ta shanyo kwana ta karaso ummulkhair ta mike a tsorace zata yi magana, su Sarkin bulala suka shigo wajen da mugun sauri sunna tambayar ko nan ne likita mai sunna Halima take duba mararsa lafiya??????????????

NAJEEBA ta yi saurin yiwa ummulkhair signa da ido, sannan ta juyo inda Sarkin bulala yake tsaye, ta dage nikaf din fuskarta a tausashe ta ce" Sarki lafiya????"

Da sauri Sarkin bulala ya dukar da kansa hadi da dire gwuiwarsa guda, hakama direba ya duka shima kawunansu a kasa, Sarkin bulala ya ce" Allah ya taimake ki, kira ne daga Mai DAMAGARAN"

NAJEEBA ta Dube shi a tausashen nan ta ce" Lafiya dai ko???"

Sarkin bulala ya miko mata wayar yana fadin" Allah ya karra maki lafiya, an yi tunanin Bakya nan ne"

Najeeba ta yi abun mamakin nan, ta dubi ummulkhair da ta karra suma a tsaye ta ce" UMMU, ina na je???"

Ummulkhair ta bude baki da kyar tana share zufa ta ce" Bayi ne kika shiga yanzu yanzu, ai yanzu ma likitar ta karaso ita muke jira....."

Najeeba ta sakar mata murmushi, bata amshi wayar Sarkin bulala ba ta juya inda aka dakatar da mutane kar su shigo ta ce" Zan yi kira a wayata, ka sanar da Mai MARTABA ina cikin aminci, magani kawai zan amsa mu juya gida"

Daga haka ta amshi jakarta dake hannun ummulkhair ta yi gaba, ummulkhair ta bi bayanta da sauri suka bude ofice din Docter Halima suka shige....


Sarkin bulala ya mike suka fita, ya mayar da kiran , cikin girmamawa ya ce" Allah ya taimake ka, tabasss giwarka babu inda ta je, tana asibiti, "

SHAHEED dake tsaye da waya a hannunsa yayi dan shiru da mamakin abinda aka fada, ya kai dubansa kan shamaki dake duke da malami da Majidadi da mai rike da wayar cikin gida , a tausashe ya ce"
A tausashe ya ce" Giwatah....., tana asibiti ai"

Shamaki ya dan dago idannuwansa, a hankali ya mayar a tausashe ya ce" Ikon Allah, to kai daracin waya yaya aka yi da maganar nan?, wanene zai yarda yayi kika ya sako Giwa a shirmensa?, a sanar da mahaifin yarinyar su zo gobe, girma da darajar GIWAR Mai WUKAR YANKA ta fi karfin a zo ana kawo sukar ta yi abinda bata yi ba"

Malami ya sake sada kai, saboda a lokacin da wayar ta shigo aka kawo maganar hankalinsa ya tashi, dan shi dai shi kadai ba zai zo da maganar nan ba, shine ya nemi shamaki suka zo suka samu mai DAMAGARAN da maganar

Sultan SHAHEED ya dan gyara zama saboda irin yadda suka dau zafi, a nutse ya ce" Uhum, su dai zo da ita yarinyar, ama su zo gobe da magariba falon Anmy, ko me yake faruwa zan sani, kuma za'aiwa tufkar hanci"

Ya dan dakatar ya Dube su ya ce" Ina aka sameta da fadan?"

Shamaki ya ce" Allah ya taimake ka ban sani ba, Ama mahaifin nata yace ne an sameta har an sumar da ita sunna asibiti"

Sultan ya mike tsaye yana fadin" A yi du abinda ya dace na kula, Allah ya bata lafiya"

Daga haka ya yi shigewarsa ya barsu a falon farkon sunna tattaunawa

Malami ya ce" Ba zamu yarda a ringa kawo mana irin abun nan ba fa, shamaki a tura maga takarda da jakadiya su kai sakon kula da dubiya sannan a jiyo inda yan daban suka sameta, gaba daya bi abin ya daure min kai, yaya za'a yi ace yan daba ne suka kai hari, kuma a kawo maganar Gimbiya a ciki????"

Shamaki ya sauke ajiyar zuciya ya ce" In sha Allah, yanzu zamu je saboda mu sanar da sakon su zo gobe bangaren mai baban daki, dan mu gano in zata iya zuwa din itama, Ama abin nan gwara a katse shi tun lokaci bai kure ba, GIWAR uban dakin mu ba abar wasa bace!"

Da wannan tattaunawar suka mike suka rabu dan aiwatar da abinda yake gabansu

A asibiti kuwa Najeeba ta ga likita , kuma ko dan a lokacin ta hada ciwon da gudu , sai da aka yi mata allura ma sannan aka rubuta mata magani sabo da yakinin in sha Allah in dai tana kula da dukkan abinda akace zata rinka jimawa ciwon bai tashi ba

Takim takim suka fito suka nufi hanyar mota, sunna zuwa Sarkin bulala ya bude musu suka shiga sannan direba ya ja motar suka dauki hanyar fada

Sai da suka ajiye su har bangaren anmy sannan suka wuce

Ai kuwa sunna sauka zasu fara tafiya ummulkhair ta ce" Najeeba dakatawa zaki yi mu yi magana"

Najeeba ta dubeta, kafin ta langwabar da kai ta ce" Ummu, mu je ciki mana, Bakya ganin mutane?"

Ummulkhair a dole ta yi shiru suka shige cikin, suka kaiwa Anmy result da abinda likita tace, Anmy kuwa ta duba sosai sannan ta yi ta fatan samun lafiya kafin ta mike tana fadin" Kin ga abinda na sa a girka maki fa,"

Anmy ta bude kular da abincin ke ciki

Najeeba ta dubi abincin, ta kalli Anmy da mamaki ta ce" Anmy, taliya ce da man ja fa,...................me zan y". Ai kuwa bata gama magana ba ta wuce bayi da sauri saboda irin yadda amai ya tukota

Ummulkhair ta kama kai ta ce" Anmy, yarinyar nan ta raina mutane, bata son abincin ne harda su amai?"

Anmy ta yi dan shatakai kafin ta ce" Kin san me likita tace? Ta yiwu Akoy abin cikin nan, ta yiwu bai fita ba, shine wai na yi mata abin nan da ta ringa so a cikin su Muhammad, kuma kin ga ya sakata amai"

Ummulkhair ta dan zarro ido, kafin ta ce" Anmy, ta yiwu shi din ne fa, saboda kin ga amai take shekawa daga ganin abinda ranta baya so, Allah ya sa shi din ne, tunda ba lallai abinda ta so da wancen cikin yanzun ma ta so shi ba"

Amy ta saki murmushi tana fadin" Hakane bari in fitar da shi kafin ta fito, kin ga zo ki gani......., taho mu je"

Najeeba kam sai da ta yi amai sosai sannan ta wanke fuskar ta tana fitar da numfashi ta fito tana toshe hanci zata yi magana ta samu basa nan, dan haka ta wuce dakinsu wajen yan uwan ta Wan umi karama ma bata nan tana cikin dakinsu

Bayan ta shiga ta samu sunna kwonce sunna kallo a computa, sai kawai ta wuce bayi direct dan ta yi wanka sai tuna yadda zasu kwashe da ummulkhair take yi

Bata jima sosai ba ta fito, ta same su su duka sunna ta fira , ga dukkan alamu sun samu wani tsegumin ne

Zaunawa ta yi tsakiyarsu ta sa hannu cikin abinda suke ci, a nutse itama ta shiga ci tana son gane abinda suke tattaunawa, kuma abin mamaki ummulkhair bata dago zancen ba har ita dai ta gama barci yaya awon gaba da ita saboda nauyin barcin da ya kwashe ta


Sai bayan ta yi barci ummulkhair ta ce" Ina fada muku Aida zamu samu ita zata fada mana inda suka je, wallahi da gaske na fara tsoron kar aje Akoy abinda suke aikatawa ita da uwar gidan nata, yau da an kama mu ban san yadda zamu yi ba, kun san fa halin yaya, Duda yana aurenta sai ya mana hukunci wallahi, ban san yaya aka yi sam bata tsoron kowa Najeeba"

Zahra'u ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Kin san ko, tsorona kar aje a dauki hoton ta idan ta fita, Ama ba komai zamu bita a hankali kar mu daga mata hankali saboda maganar cikin nan, dan ba zan so ko da wasa ta ringa yin crise da cikin nan ba"

Haka suka bar maganar suma du suka nemi wajen kwonciya , sai wace mijinta yayi kiranta ne kawai ta raba dare tana amsa call, umi kuwa dake jego ta koma dakin Anmy dole ta KWONTA.


Washe gari kusan karfe goma sha daya takarda ta zo musu daga wajen Malami na zaman da za'a yi, wanda Anmy ta tambayi Najeeba zaman menene? Ama NAJEEBA ta nuna bata sani ba gaskiya, dan haka Anmy din ta nuna ba damuwa a tura amsar sai sun zo, dan ita batama san su waye zasu zo din ba, NAJEEBAN dai ce ta girgiza kai tana ayyana abubuwa a ranta kafin ta yi murmushi kawai ta girgiza kai,

hakama takardar ta jema Nadiya bangarenta wace take tare da kanwar mamanta cewar bayan sallar magariba zasu yi zama,
Nadiya ta yi ta tunanin ko zaman menene? Sai kanwar naman nata ta nuna mata ko kayan fitar kishiya za'a basu? Da wannan tunanin ya sa itama ta yi tunanin ai haka din ne ma kawai, harma kanwar maman nata tace zata zauna yau ta kwana a fadar saboda in an basu su yi shawarar abinda zasu yi dan kece raini, domin tuni suka shiga maganar cenza komai na bangaren na Nadiya , dan kuwa sun kula wannan kishiyar itama wata yar a tashi tsaye a fitar da rainin ce, tunda ta gayawa Nadiya magana suka yanke hukuncin Bama sai sun je inda take din ba.


Tunda rana ta yi, yama na kokarin yi Najeeba ta tura andiya bangarenta ta dauko mata duk wani abu na bukatarta

Karfe shida na yi ta shige dakinsu ta rufe, ta shiga shiryawa cikin nutsuwa, harta mak'up din da ta jima bata yi ba yau sai da ta dandasa, ta caje gashin kanta baya sosai ta kafa daurin dan kwali bayan ta yi sallar isha'i, sannan ta zauna saman kujerar da take hawa ta yi turaran wuta a nutse ta zuba turaran wutar sannan ta shige wayarta a nutse duk wani abu da yake da alaka da fitar jiya ta goge, kafin ta mike saboda irin yadda ake ta bugawa ana komawa kuma a dawo a buga

Budewa ta yi tana sauke dubanta a kan fuskar Nadiya, wace fuskarta ta dau ja saboda bacin ran da ya kunota

Gaba daya Nadiya dake tsakanin falo, da coridor din dakin su Najeeba tana dakon fitowar NAJEEBAN cike da tashin hankalin wa'inda suke falo, bakinta dauke da maganar dake ranta tana son fada mata, sai komai ya bace a kwakwal??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????warta ta bi Najeeba da kallo

NAJEEBA ta dan lumshe idannuwanta masu Wauke da gashin ido kafin ta ce" Nadiya kece ke bugawar ko harda wani?"

Nadiya ta gyada kai, cike da mamakin wai Najeeba na nan daki hankalinta kwonce ana cen za'a raina musu wayo???????

A birkice ta ce" NAJEEBA, wai ke baki san zaman da akace za'a yi yau da su waye bane? Kina tune da matar nan da kuka taba hada saurayi da ita ? Wannan lauyan?"

Najeeba ta Wan tabe baki ta ce" Lauyan da na yi soyaya da su ai da yawa, wane a ciki?"

Nadiya ta dago hannu ta ce" Wace kuka yi fada da ita a kofar shagonki na cikin gari?, wannan katuwar nan wukaka din nan, wannan fa yar duniyar matar nake maki nufi"

Najeeba ta watsa hannayenta ta ce" To, Ni abin ne ya shige min, gaskiya ban ganeta ba"

Nadiya ta ce" Mu je ki ganta kya ganeta, kin kuwa san cewa itace ta zo nan ita da wannan maciyiyar amanar? Ban san ubanda suke nema ba, kafin mu shigo da su jakadiya mun wuce mijin nata da wasu datijan biyu a kofar falon Anmy, "

Najeeba ta yi dan murmushi ta ce" To ko daurin auren suka zo?"

Nadiya ta zabura tana dubanta, tace " NAJEEBA daurin aure kuma?, kuma harda ita Amaryar?"

Najeeba ta ce" To Nadiya Ni na sani ne? Kin ce harda datijai, kuma kin ga ba su zasu kawo mana akwatuna ba , mune zamu kai, bale in ce akwatunan angon Aka kawo"

Nadiya ta girgiza kai ta ce" Ke kam kamar Bakya tare da tashin hankalin kishiyar da za'a mana? Ina kyautata zaton zagin da na mata ta zo fada da iyayenta, ai kuwa bata sani bane, dan kuwa wallahi sai na hada har ubanta na kuma zagi , ke likitar nan fa kishi kishin na ji cewa mijin da suka rabu sata ta masa , barauniya ce fa, kuma yar iska ce, Najeeba karuwanci take yi fa zata aurar mana miji"

Najeeba ta zaro ido ta ce" Kar ki ce Allah nadiya, ki daina irin wannan shedar kin dai san girman laifin kaidin nan idan ba gaskiya bane ko?, kuma kin ga ki iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login