Showing 102001 words to 105000 words out of 144591 words

Chapter 35 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2366

lafiya komai ina iya yi dan a samu sau?in fitina, ina dalili sati nawa ana dauki ba dadi, to ki bi diyarki ku yi yaji ku je gidan kannin mijinta ku ce kun yi me?, in yi zaku yi ku bar kasar kawai kowama ya san da gaske kuke, Ni kam yanzu bari in je in ga likitar dake kwana su zo su gani idan da halin barinki mu je gida mu tafi, saboda ina so gobe da safe in sha Allah a yi a gama da rikicin yarinyar nan da aka kawo aka rufe, ko ba komai tana da hakin sanin dalilin da ya sa aka rufeta, kuma iyayenta ke bani tausayi dan Dazu mahaifiyarta na kofa tsugunne tana ganin motata ta taso tana kuka da magiya, lokuta da yawa yayanmu ke janyo mana masifar da ta fi karfin mu, in sha Allah a yi a san abinda ake ciki ko sa samu nutsuwa . Son taso ka fara yin gaba da jama'arka tunda ba cin abincin zaka yi ba"

Sultan ya dubi Abiey, ya rasa me zai ce, gashe Abiey din ya tsaya jira yake yi ya sa komai a muhallin sa

A dole ya mike, ya sake kallon bayanta ya sauke ajiyar zuciya a tausashe ya furta" Allah ya kara lafiya Anmy, Allah ya huci zuciyar ki "

ANMY ta yi murmushi a hankali ta furta" Allah ya kai ka gida lafiya, Allah ya albarkace ka"

Idannuwansa ya lumshe mata saman lebensa tana amsawa still idannuwansa a kan Najeeba kafin ya juya a nutse ya amshi alkyabarsa , yaya Dayabu ya aniya kakabe masa bayan ya saka, suka juya suka fito tare, Abiey ya nufi ofishin likitocin , su kuwa suka nufi waje yaya Dayabu sai sake kabe masa rigar yake yi yana karawa har suka karaso wajen mota, Sultan ya juyo yana tabe baki hadi da yi masa kallo mai kama da harara ya ce"
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




35




Ya yi masa kallo mai kama da harara ya ce" Kai, wai meye?"

Yaya Dayabu ya sada kai ya ce" Kar ka bari magauta su shiga tsakaninka da kanninta ranka ya dade, kar ka yarda da kaidin mata ka ji?"

Sultan ya gyada kai yana dubansa ya ce" kar ka haWa matata da kaidi, bata iya shi ba, kuma ai ba ita ta boye kanta ba, maimakun ka rarasheta kace ta dubeni a'a, sai ka boyeta ko? Zaka fada dan sai na rama!"

Daga haka Sultan ya shige bayan mota ya zauna, Sarkin bulala dake kusa kadan kansa a kasa yana MURMUSHIN uban gidansa da d'an uwansa, domin tunda suka ga Gimbiya ce aka gani hankalinsa ya kwanta sosai, ya san yanzu uban gidansa zai fara gane hanya da kyau, sai kuma diramarsa da d'an uwan nasa wace basa taba dainawa, domin wani lokacin idan yaya Dayabu yayi niya kawai sai yace da Sultan da gaskiya za'a bi shi yayansa ne, shi kuwa sai yayi MURMUSHI kawai yace gwara a bi karyar........
Motocin suka ja suka dauki hanya yaya Dayabu na kallonsu har suka bacewa ganinsa kafin ya sauke ajiyar zuciya hadi da jin wani sanyi na ratsa zuciyarsa,

Tunda suka fara wannan hawa da saukan yake cikin tashin hankali

Idan ya tuna tana cikin damuwa da fushin nan da yake yi da ita sai ya rasa yaya zai yi ya kwatantawa Wan uwansa cewar bafa zata zubar da ciki ba, ta yi komai banda taba rai ko na mikiyinta ne bale gudan jininta, sai dai kamar yadda yake sarki a waje, a cikin gidan ma shine ga a da su, dole zasu yi shayin tunkararsa idan yana cikin fushi............, a yanzu da ya ga haka kuwa sai ya ji wani sanyi na ratsa zuciyarsa, Duda yana fargaban fushin nata ita din ma, saboda maganganun da suka tattauna da kuma irin yadda ta yi kamar ba Sultan din ta ba ta juyar da kai , Ama ya san dukan tsanani yana tare da sauki, kuma yana fatan ganin sau?in kwana kusa.

______________________________


Nadiya

Tunda ta dawo bangarenta ta rasa amsar tambayoyin ta, haka kuma tana duban lokaci har karfe tara ta yi ta sake komawa bangaren nasa, Ama still bai dawo ba, hakan ya sa ta zo ta sake kasawa ta tsare tana hankalce da motsin dake waje har ta ji shigowarsa karfe goma saura sannan ta Wan ?arara lokaci dan ta san yanzu sai ya shiga wanka koda zai fito dan cin abinci, ita kuma ta auna lokacin da take iya samunsa sannan ta mike ta nufi bangaren nasa a lokacin har karfe goma sha daya na dare ta gota, Danma Allah ya sa su Anmy sun shigo, su Abiey basu kai ga tafiya ba shi yasa bai kunna matakan tsaron dake bangarorin ba ai da Bama zata samu shiga ba, domin idan suka wuce irin wannan lokacin ko su basa samun shiga bangarensa,a yanzun ma da ta taSa sai da ta yi mamaki da ta ga kofar ta budu dan haka ta shiga ta nufi falonsa na biyu inda yake yin zama yayi yan karance karancensa da harkar kasuwancinsa dai da sauransu

Samunsa ta yi yana motsa jiki a saman tiles hankali kwonce domin ko da ta shigo bai dakatar da abinda yake yi ba har sai da ya kai irgen da ya sakawa zuciyarsa zai dakatar sannan ya dakata yana duban ta kamar yadda ta gaishe shi tunda ta shigo ta zauna ta yi shiru kawai tana kallonsa ba tare da ta mike ta kawo masa tawul karami da ruwa marar sanyi kamar yadda Najeeba ke yi idan ta same shi yana motsa jiki, har takan taya shi ko ta dane gadon bayansa ya rinqa dagawa yana ajiyewa da ita tana irgawa har sai ya gaji su zube tana nemansa da rigima yana ramawa sunna kyakyatawa da dariya, sai dai ita kawai ta yi zaune zugum abinta har sai da ya dan sauke ajiyar zuciya ya mike da kansa ya je ya dauko abinsa ya dawo ya zauna saman kujera yana karra gudun ac hadi da lumshe idannuwansa

Nadiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Aban Aliyu, Ni kam ina ta so in yi tambaya kuma ban san ko zan samu amsa ba yanzu?"

Idannuwansa ya bude ya zuba mata yana kallon ta, to tambaya ai tun jiya take cikin yi yada ka san zata je zana jarabawar zamowa y'ar jarida ta ketare Bama ta cikin kasa ba, in ba dan ya bata waje ba a Dazu ma da tambayoyin nata sai sun sa ransa ya bace, kuma a yanzu sai yake ganin anya tambaya ce ya dace ta yi masa a irin wannan time din, ga gajiya , ga barcin da bai rintsa ba a jiya ko dis wanda yake da bukatar yi a yanzu ko zai samu nutsuwa ya iya tunkarar rigimamiyar Anmy, kai abubuwan dai da yawa WA'INDA a ganinsa a yanzu baya bukatar yin dogon surutu, sai dai kuma Nadiya matarsa ce, tana da iko da damar yi masa tambaya a duk lokacin da ta so, shi kuwa adalcin da zai yi mata shine ya bata kyakkyawar kular da ta dace da ita, dan haka ya gyada mata kai a hankali ya ce" Yi mana tambaya kuwa"

Nadiya ta sauke ajiyar zuciya tana dubansa ta ce" Aban Aliyu, tun jiya nake ganin yannayin gidan nan ba yadda na saba ba, har rufe get aka yi baki daya, sannan aka bude Ama kuma Duda haka ba'a barin shiga da fitar sai an yi bincike, kuma na tambayeka baka bani amsa ba, wai lafiya? Ko sabuwar dokar da aka dora kenan a fadar?"

Sultan ya dubi hanyar shigowa kamar zai ga wani abin, ya dubeta ya ce" Au, wai JIYA ko? Ok, wata matsala ce aka samu, Ama yanzu alhamdulilah ba za'a kuma binciken ba"

Nadiya ta yi dan shiru, ta so ace ya sanar mata wace irin matsala ce? Sai dai ya kama bakinsa yayi shiru, daga maganar da yayi bai kara ba, sai kawai ta sauke ajiyar zuciya ta ce" To Allah ya kara tsarewa....."

A saman lebensa ya amsa yana dan murza gaban goshinsa

Nadiya ta sake cewa" To, wai ina Najeeba ne? Rabona da ita tun shekaran jiya"

Sultan ya bude idannuwansa, ya dubeta, sai kuma yayi dan MURMUSHI ya ce" Beebahhhhhhhhhhh, tana nan ai, yanzu haka tana nan"

Nadiya ta kafe shi da kallon da ita kadai ta san me take tunani a zuciyarta, sai dai wani mamakin da ya rike mata zuciya ya sa ta ce" Ikon Allah, na zata fada kuka yi kai da ita fa, fada na kirki da har ta kaurace maka, ko kuma wannan din ma wani salonta ne dan ta sa nima in kaurace maka ita ta samu ita kadai ko?, hum, har nunawa take yi bata wani damu ba dan na kwana a nan, ashe itama zuwa take yi a boye, ko meye na boye boyen????"

Dubanta yake yi har ta dire aya, ya dan dubi agogon bango Ya sake duban ta........
Eh , da gaske dai lamarin Nadiya sai ita, saboda ita bata iya wani kwane kwane ba, idan ta tashi magana kamar fitar kashi kuma haka take fadin abinta , sai dai idan kai zaka gyara dan kar ranka ya Saci ka gyara, Bama wannan ba, ai shi ya jima da kafa musu dokar idan yana tare da wata kar wata ta kawo zancen Y'ar uwarta in ba yabonta zata yi ba ko sakon da ta bata ta sanar zata sanar ba, Ama shine take ta sakin zamcecekun nan kamar an kunata? Fira kuma ba mai dadi ba

Bai ce komai ba ya dauke kai yana fitar da dan hucin zuciya ya nisa yana dauke kansa

Nadiya ta hade hannayen ta , sannan ta saki ta ce" Kuma Ni abinda ya baki mamaki, to in wani cikin ta samu ai bai ci ace ta fara zuwa awonsa ba, tunda an ce wancen ya zube, to inma ba wata fitinar ba wancen din na ga ai bai jima da zubewa ba, kuma ta nuna fushi take da kai din , to yaushe ta yi wani cikin Ni ban sani ba?"

SULTAN ya Dube ta yana dan fitar da idannuwansa na mamaki haka kuma haka kawai sai maganarta ta so saka shi dariya da tarin mamakinta.....

Kai, ikon Allah
Aya, yanzu da wani ya ji abin nan ba shi ba ai da ya gama raina mata wayo
Anya Nadiya idan ta samu kishiyar da zata zauna da ita da fitintinu irin na wasu matan da kisa da munafurci zata kai labari kuwa? To ko shi namiji ai ya ga wautarta a fili

Da farkon maganarta so yayi ya fatataketa sosai, sai dai yadda ta karashe maganar ya saka shi Wora kafa daya kan daya a hankali ya ce " To yanzu idan zan mata ciki sai kin ji?"

Nadiya ta kale shi a zabure, a kuma tsorace, Astagfrullah, kai innalilahi dama mutumen nan ya iya kalaman da zaka ji kamar ashariya ne?????, to ai ita bata ce sai an fada mata za'a yi ciki ba, ita munafuntarta da aka yi ne kawai bai yi mata ba

Ta gyara zama zata janyo wata doguwar maganar ya kafeta da idannuwana a hankali ya ce " Wr 's my son?"

Nadiya ta Wan sosa kai ta ce" Aliyu, yana wajen nani dinsa, su nayla sunna wajen su zahra'u ne su"

Idannuwansa ya mayar ya lumshe cen cikin makoshinsa ya furta" Idan a nan zaki kwana, ki dauko min yarona.....if not, ki je, ina son hutawa"

Nadiya ta zuba masa ido, magana gareta a bakinta, magana gareta a zuciyarta, amsa take so tsayayya daga bakinsa, amsa take so gamsashiya daga wajensa, sai dai kamar yadda ya saba ba wata doguwar magana ake yi da shi ba, har ya gimtse abinsa...... Gashi ita da ta zo da nufin kwana ta zo ta bar Aliyu a cen, tana ganin lokaci yayi da zata dage ta dauki wani cikin, dan ba zai yiwu ba ace tana zaune tana fama da yaron da ya wuce shekara uku shiru bata kara haihuwar ba, abinda ke Tsoratar da ita , ita ba komai take sha na hana haihuwa ba Ama kuma shiru tunda ta haifi Aliyu, kar dai maganar Aunty ta tabbata? Kar dai aiki ake yi mata tukuru dan kar ta tara ya'ya a gidan nan?????,


Kai ta girgiza cikin tunanin da take a ranta ta ayyana ' Shikenan, idan baka sanar min ba zan je ta sanar min ita ai, kuma zan yi kiran Aunty, lalle lokaci yayi da za'a sama min ciki, a tashi tsaye sosai da sosai, tun farko laifina ne, sai da Aunty ta nuna mayarwa da kura aniyarta, malamin dake mana taimakon Aliyu yace aiki ne ake yi a kaina na mugun abin da ya shafi haihuwa, Aliyu ma da kyar cikinsa ya zauna, gayanan kuma an salwantar min da shi an hada shi da iska, idan ina so ana iya mayarwa wace ke min din, Ama nace a'a a bari haihuwa ce na san zan yi sai dai maki gani ya mutu, ashe dai sai an sa na rama ko? Ba laifi zan sa a rama itama ta kawo irin Aliyun in ga tsiya!'

Mikewa ta yi ta furta" A huta lafiya"
Sannan ta fice ta nufi bangaren ta,

Sam tunanin da take dauke da shi a kwonyarta bai wani hasko mata cewar, baligin namiji, kafiyayan namiji, namijin da ya ajiye su su biyu, namijin da yake da damar ganin wata ne ta juya ta bari cikin kadaici, da rashin kula irin ta mace......, wace ya riga ya sabarwa jikinsa da duniyarsa dadin zama da mace a kusa da shi, ta fi gane cewar gwara ta je ta gama tunanin mafitarta ta fi kwanan da zata yi a nan...
., wanda hakan ya sa ya lumshe idannuwansa bayan ta tafi a ransa ya ayyana ' Yaya ake so kular da zan basu ta zo daya? Yaya ake so soyayyar da zan iya musu ta zo daya? Magana ake yi da wace damuwata Tata ce tun kafin in bude baki in sanar da matsalata kuwa take gane yannayina, da wace ta gama gane cewar a matsala nake Ama baya hanata kawo tata matsalar wace bata da wani karfin da zai sa lalle lalle sai an kawotan ma??????......., ba za'a taba hada Macen da ta san waye mijinta, take tsaye a kan lamuransa na yau da gobe, da wace take tafe kamar tana rike da daki hudu matsayin mazan da take aure, wanda zai sa su kasa mata hankali har ta kasa ganin abinda yake gabanta........., hum Allah ya kyauta'

Daga haka ya mike ya koma dakinsa

Har ya daura tawul zai shiga bayi ya dauko wayarsa ya duba msg din dake tare gaba daya na ana sanar masa mai layin da yayi ta aikawa kira ta bude wayarta ne

Zubawa numbarta ido yayi a hankali ya shiga wajen msg ya rubuta msg kamar haka" *BEEBAH...., I'M SORRY*"

ya tura msg din ya samu kansa da zaunawa bakin bed yana murza gashin kansa.....a hankali ya lalubo wayar ya sake rubuta " *Idan na amsa laifina, harma na nemi afuwa, ya wadatar ko kuwa Akoy punichmnt din da za'a bani......?, PLZ ki amsa Ni rabona da barci tunda na karanta takardar da kika ajiye min.....* "

Ya sake tura mata sakon, sai kuma ya yi zuru ya shiga tunanin duniya

Ikon Allah

Duk abinda bai same ka ba, kar kace ba zai yiwu ba, lokacin yiwuwar tasa ne kawai bai zo ba

..............*Anya kuwa shi ne? Shi ne Sultan SHAHEED Muhammad?*



>?z?>?z?>?z?>?z?>?z?>?z?>?z?=?
?


Hello masoyana

*Sauki......duniyar sauki a gidan SAJIDA AND AMINA SHOP*

Mutanenmu, tun daga jamhuriyar Nijar har zuwa Najeriya albishirunku.......
Muna tafe da sauki mai baki/baka ikon mallakar duk wani abu da kake ganin ya fi karfin ka ko ya yi tsadar da a yanzu zaka girgiza kafin ka same shi ta hanya mai sauki , wato Zubin dashin da zaka iya har Allah ya sa ka mallaki abinka cikin ruwan sanyi da nutsuwar zuciya....
Muna da haja kamar haka:

Kaya na maza da mata, tun daga kan lesh, shada, atampa, yadi, hula, hijabai, harta pant da slip

Kayan daki

Kayan KICIN

Jakunkuna da takalma

Sarka da yan kune harda na gold.

Abin hawa kowani kala

Dukan abinda kake da bukata muna da damar sama maka shi cikin sauki da hanyar biya mai sauki in sha Allah

*A DASHIN Y'AR GATA, ZAKI IYA YIN NA KUDI WANDA ZA'A HADE MAKI DUKIYAR KI A MIKA MAKI CIKIN AMINCI*

Ba Shikenan ba

Muna da special grup mai sunna MURMUSHIN ZUCIYARKU wanda muke tura kayan siyarwa masu kyau da tabo zuciya a farkon gani.

Muna da grup wanda muke baje kolin kayan gyara tun daga kan fata har zuwa pp na mace ko namiji

Ku zo mu je tare......
KU ZO KU RAKA MU
KU NUNA MANA KAUNA
KU TAYA MU TASHI DA KARFIN IKON ALLAH......

*TAKU CE, SAJIDA NIJAR*

Domin karin bayani a tuntubemu ta layinmu kamar haka

*CEEO SAJIDA ELHAJ SA'IDU KULLEY*

+22793811618


*ADJOINTE AMINA MAIKUDI ABDULAHI*

+234 803 885 6944
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login