Showing 18001 words to 21000 words out of 144591 words

Chapter 7 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2332

yi fada a Hanna shi, kuma a zo a Wora masa da wani fadan

Da ido suka raka shi, kafin Najeeba ta tabe baki

Aunty A'isha ta ce" Anmy fa tace ki je, tace a dauki kayan ki ko kala biyu ne sai kin yi wankan ruwan zafi koda na kwana biyu ne, tace kuma ki je gabanta ki ci abinci"

A dole Najeeba ta nufi coridor bangaren Anmy ta bude da ky din cen, ai kuwa ya budu ta shigewarta zuciyarta cinkushe cike da tunanin ina baban su junior ne??? Me ya samu wajen bude ky din bangarenta to bangarensa ne?????????????

Wannan abin ya Hanna mata walwala, duda irin yadda ta samu su ummulkhair da su ummukulsum da sauran kaf dinsu a cal Wanda yaya Dayabu ya haWa suka dan taba fira da yi mata addu'ar samun sauki sannan ya yi jimula ya ja musu warning din du wace ta yarda ta zo saboda wannan sai ya sasaba mata, kafin ya katse kiran yana yiwa Anmy dariya dan ita ta ce ya Hanna su, dan sun ga damar harda wace ke Lagos din ta kamo hanya, bayan jikin Najeebar da sauki abinda aka rasa kuwa ai ba dawo da shi zuwansu zai yi ba, idan suka riga suka zo din kuwa kafin su koma sai an fara kai ruwa rana , shi yasa aka katse hanzarin su harda wa'inda suke cikin garin DAMAGARAN.


Wanka ta shige bayan Anmy ta ja mata kunnen ruwan nan zata shiga ta zauna, ruwa mai zafin gaske, da kyar ta daure ta iya zaunawa har ya huce sannan ta juye shi a salga ta yi wanka da wani mai zafin da Aunty A'isha ta juye ta mika mata da tawul karami kafin ta iya fitowa ta shige tsohon dakinsu ta kimtsa jikinta ta shafa turare sannan ta zauna ta Wan tutura abincin sama sama tana yi tana duba wayarta, ta sha magungunanta sannan ta nufi dakin Anmy ta kwonta tana janyo filo cike da jin matsananciyar kewa ta sake lalubar wayarta ta danna kira dan ta kasa jurewa......sai dai tana ji tana gani sai da wayar ta fara RINGIN aka katse kiran, ta dake turawa aka sake katsewa, hakan ya sa ta mike zaune da sauri tana dubawa da kyau, ta sauka ta je ta dauki wayar Anmy ta aika kiran a wayar, ga mamakinta tana yin RINGIN na biyu aka daga, ba dan bai gane cewar itace ta dauki wayar Anmy ba, a'a, sai dan ya tabbatar mata cewa kiran nata ne baya so ya daga yayi salama cen kasa sannan yayi shiru

Shiru ta yi zuciyarta na bugawa, a hankali ta ce" Papah junio, kana gida????? Mun dawo fa, nd ina ta kiranka bana samu ko lafi......."

Kitttt ya kashe kiran ya ajiye wayar ya sake duban Muhammad dake kawo masa harda bayan ya gama rarashinsa da ya shigo masa da kukan momynsa ce ta dake shi, wani takaicin ya sake sha?ar masa wuya, wato ba zata karra haihuwa da shi ba, kuma ba zata bar masa ya'ya su numfasa ba ko......lalle Najeeba zata fuskanci hukunci mai tsanani a wajensa , ba zata ganshi Bama da idannuwanta bale har muradin kasancewa da ita ya kama zuciyarsa.......


Jin shigowar sakwani kamar a jere ya saka shi daukan wayar a nutse ya shiga dubawa.............

DOCTO din dake jikin sakwanin da suka shigo ya saka shi budewa kai tsaye

*Bayan gaisuwa da fatan ALKHAIRI a gare ka ya kai sarki mai adalci mai tausayi da yafiya, ina sake miko sakon n??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????eman gafara bisa laifin da na aikata ba da son raina ba, ina neman afuwa da yafiya domin a jiya ban samu rintsawa ba, tunanin fushin dake kan fuskar sarkina ya Hanna min samun nutsuwa, Allah ya huci zuciyar asarki*

Sai kuma na kasa ta rubuta sako kamar haka *Ina fata ka tashi lafiya, ina rokon Allah ya tsareka daga dukan sharin dake wannan rana, ya haWaka da dukan alkhairan dake cikinta, ya kuma sa a cikin sassaucin da zaka yi a yau in shigo ciki*

Ya dan kalli Muhammad dake karatu kasa kasa, ya sake duba dayan sakon da ya kunshi kalamai kamar haka *Da ace ina iya Hanna kaina jin haushin du wani wanda zai iya sanadiyar ciki, da ban kawo bayanin nan ba, sai dai burina da fatana na samun miji adali, jarumi, mai tsoron Allah da rikon addini ta yadda zan yi ta haihuwa a gidansa ya sa na kasa rikewa har na fada, ina neman afuwa, ina neman afuwa ya kai mai DAMAGARAN*


Sai da ya kai karshen msg din kafin ya dan dage girarakinsa da tunanin ai ba abinda ta masa da zata nemi wannan uwar yafiyar.....shi baima san me zai bata matsayin amsa ba, dan haka sai ya sauke wify din saboda irin yadda msg ke shigowa kala kala daga mutanensa kala kala

ya mayar da hankalinsa kacokam kan Muhammad da Abdallah bayan ya musu sulhu da fadin cewa ba ya Hanna su rigima da junna ba? Sai dai ya riga ya sani Muhammad AKOY rigima da fushi, shi yasa yake yawan zama da yaron dan ya koya masa iya dane fushinsa da iya kawar da kai a abubuwan yau da gobe, domin wannan halayyar mace take yiwa kyau ba namiji ba.


A bangaren Najeeba kuwa a tsaye nan da take dai da Anmy ta fito daga bayi sannan ta ajiye wayar ta fita ta nufi dakinsu na da ta zauna kanta na daukan wani irin zafi da ciwo.........

Rayuwa kenan, yau da gobe babu abinda ta bari, tunda ta wayi gari ita NAJEEBA MUTALAB ta tashi daga Najeebar da babu abinda ya dameta da fushin namiji ko waye shi, zuwa Najeebar SHAHEED, wace bata iyawa sai da SHAHEED, duniya ta dawo take bata tsoro......... Du yadda ta so cire damuwar nan a ranta gazawa ta yi, motsi kadan sai ta dubi agogo, har aka kawo mata abincin rana, aka kawo mata maganinta, yama ta yi aka sake sakata yin wankan jego na kirki ta saka riga marar nauyi ta zauna da wayarta , har Nadiya ta shigo kusan magariba yannayinta na nunin bata da nutsuwa, sai dai itama bata da nutsuwar da har zata tsaya gane rashin nutsuwar wani........, sai kawai suka yi zaman kurame, ita Nadiya ta kasa fada mata tashin hankalin da take ciki, wanda ya Hanna mata sukuni, domin a lokacin da safiya ta yi ta nufi coridor dan zuwa ta bashi abin kari kamar yadda suke yi, ta samu kofar a garkame, kofar ta ki buduwa, sai kawai ta sake firgicewa harda koke kokenta ta rasa inda zata saka ranta ta ji sanyi, tashin hankali, firgici, tsoro suka lulube mata zuciya.....ya zamo ta rasa gane hanyar da zata dosa, bale da ta yi kiran Aunty tace da ita tana wajen biki zata yi kiranta idan suka koma gida kuma har yanzu basu yi kiran nata ba dai ta wuni cikin zulumi, ko wanka sama sama ta yi ta yabo hijabi ta nufi bangaren Anmy bayan an sanar da ita NAJEEBA na nan sai gashi ta gaza fadawa NAJEEBAr ma damuwarta, sun zauna a baban falon anmy sun yi jigum jigum hankalinsu du ba a kan abinda ke wakana a falon ba, har yaya Dayabu ya biyo ya dauki Aunty A'isha suka wuce, yaran kuwa sunna dayan falon sunna buga game tare da Andiya hankali kwonce

Su kuwa sun kasa motsawa, ita Nadiya ta gaza tafiya, duda tsoron da take kar ya sameta a nan ya fadi abinda ta yi gaban mutane......, ita kuwa NAJEEBA burinta ya zo ta ga abinda yake faruwa, domin bai saba horata ta haka ba, bai saba yi mata wannan horon ba, sukan zauna ne su fahimci juna, in ta yi wani laifi ne ta amsa laifinta ya yafe mata, in shima laifin ya mata ta sanar su fahimci junna, bata san wannan tashin hankalin na kin amsa wayarta da kin yi mata magana ba sai yau, shi yasa take jiransa ta san duk rintsi baya zuwa wajen kowa sai ya fara leko Anmy, idan ya zo zata ji laifin da ta yi a kwance a saman gadon asibiti.

Bayan sallar isha'i a lokacin har Aliyu ya fara yan rigingimunsa na dare, Anmy na bashi maganinsa sannan ta yi ciki da shi tana fadin" Bari in gwada saka shi barci kafin ki tashi Nadiya"

Nadiya ta amsa da to Anmy, duda wata zuciyar na umartarta da ta tashi ta gudu wallahi kar ya sameta a nan, wata zuciyar kuwa tace gwara ta zauna ta yiwu ya yafe mata in ya zo nan din.

Anmy bata jima da shiga ba su Muhammad suka dawo daga masallaci suka wuce wajen Andiya, hakan na nunin mahaifinsu na kusa domin tare suke shigowa daga sallar isha'i

Shelar karasowarsa ya saka Najeeba lumshe idannuwanta sannan ta bude ta sauke a kan farar alkyabarsa dake walwali da mugun daukan ido, uwa uba rawanin dake saman kansa fari tassssssss, da sandar dake hannunsa mai ratsin zeba da fari, tufafin dake jikinsa kuwa rantsatsiyar shada ce mai aiki sasauka sai ni'imtacen kanshin da yake yi ya idasa shigowa ba tare da ya wani dakata ba , sai masu biye da shi da ya dakatar dan wani lokacin sukan shigo su kwashi gaisuwa wajen mai baban daki

Idannuwansa ya dauke a kan fuskarta........., zuciyarsa cike da tunanin yaya jikinta ne?, sai dai ya ki ya tambayeta ya juyar da kansa a nutse da nufin ratsewa ya ki amsa gaisuwar da suke yi masa, bale Nadiya da ta sauko kasa Muryarta na rawa rawa.......

Kasa hakura Najeeba ta yi, ta mike Muryarta a sanyaye ainun ta ce" Papah............."

Har ya kama kofar dakin Anmy ya dakata ya juyo ya sauke dubansa a kanta a tsayen da take

NAJEEBA ta langwabar da kanta a hankali ta furta" Papah, me yake faruwa ne????"

Nadiya ta dubeta da tunanin to, ko dai abin ba ita kadai ya shafa ba????

Najeeba da gaba daya ta manta Principe dinta cewar bata maganar da ta shafeta ita da shi a gaban kowa sai ita fa shi din ta kasa rikewa ta zagaya a hankali ta je tana dubansa a sanyaye ta kai hannunta zata rike nasa ta ce" Me yake faruwa ne?, ina ta kiran wayarka baka dagawa......, ina ta neman layinka bana samu....., na yi jiran kiranka da safe baka yi ba....., na zo zan bi ta coridor na ga kofar a lalace....ko aiki ne ya maka yawa har ka manta da matarka marar lafiya?????"

Hannunsa ya janye yana hade girar sama da ta kasa ya ce" dont touch me!, kofa kuwa ba lalacewa ta yi ba, Ni na rufeta......nd babu aikin da ya min yawa, addu'a na maki daga inda nake Allah ya baki lafiyar ciwon da kika ja ma kanki!"

Kan Najeeba ya kule, duda kasa kasa suke magana Ama yannayinsa a kausashe ne hakama furucinsa

A hankali ta Wan baya ta ce" subahanalah....me yake faruwa ne? Ciwon da na jama kaina? Dama mutun na iya janyowa kansa ciwo mai girma irin rasa d'ansa?????, laifin me na yi da zafi haka????"

Ta karashe tana saka idannuwanta cikin nasa

Dauke kansa yayi ya juya bai murda dakin na Anmy ba da nufin tafiyarsa

Da sauri ta bi bayansa yannayinta na sake neman jagulewa harma ta manta cewar gashin kanta a tufke ne yake , kuma rigar dake jikinta yaloluwa ce ta shan iska take neman binsa a lokacin da ya kama kofar Babar hanya zai fice

A birkice ta ce"SHAHEED!"

Ya juyo shima a birkicen ya damki damtsen hannunta da damkar da ta saka ta saki dan karra , ya saka kausasun idannuwansa cikin nata a kausashe ya ce"
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati na airtel ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




7




Ya juyo shima a birkicen ya damki damtsen hannunta da damkar da ta saka ta saki dan karra tanna zarro ido tana dage tana kallon fuskarsa a raunane cike da tashin hankali, ya saka kausasan idannuwansa a cikin nata a kausashe kuma sama sama kadan ya ce" Kar ki saki, kar ki yarda ki saki ki kai hakurina bango, tunda har zaki zabi kin haihuwa da ni ta hanyar shaye shayen magungunnan da Nine na hannaki yin su da kaina Ama kike yi, har suka zamo silar zubar min da ciki ai Shikenan, sai ki sha, idan kina so ki sake daure cikinki da kyau, ki sha abinda kike so, kar ki tsufa , kar fatar cikinki ta jawu, kar ki haihu da Ni.........!"

Ya Wan dakata saboda irin yadda numfashinta ke sama da kasa ........, yana kallon yannayinta, zuciyarsa na wani irin raunana, sai dai haushinta ya fi raunin nasa yawa......ya dora da fadin" Dadin abin ba ke kadai bace mace a duniya, idan baki haihu da Ni ba, wata zata haihu da Ni!"

Daga haka ya saki hannun nata , ta yi taga taga zata fadi, da sauri Nadiya ta tare ta , sannan ta duka hannayenta hade bibiyu tana sakin kuka ta ce" ka yi hakuri ka yafe mana, ka ga ita bata da lafiya, ka yi mana uzuri, maganin matan nan da muke sha dan gyaran jikinmu ne dan kuma mu birgeka ne, bayan wannan ba zamu sha dan mu yiwa wani abu ila a jikinmu ba bale abinda zamu samu da kai....., ka yi hakuri Aban su "

Najeeba ta fuzge hannunta ta sake saka idannuwanta da suka cenza launi cikin nasa tana kallonsa ta ce" magani? Wani irin magani? Waye yace maka Ni Najeeba ina shan magani??"

Rai nace ya nunota da yatsa ya ce" karyar zaki min yauma? Idan baki manta ba na taba tambayarki abinda kike sha yake sakawa in ganki yadda nake ganninki dan.....dan.......dan ki bani....kika nuna fushinki harda nuna min ke haka kike babu wani abu da kike sha......, na yarda da ke, muka sake zaunawa da ke da ita, na nuna muku an zo an yi sensibilisation kan ta'amali da magungunnan hausan da ba'a san tushen su ba, na Hanna ku aiki da su......Ama ashe du kunna yi? Ni kuka raina.....?"

Ya lumshe idannuwansa saboda doguwar maganar da suke saka shi cikin bacin rai ya sake bude bakinsa ya ce" Shine kike anfani da shi, har kika saka a jikin ki....gayanan ya sa cikina ya zube.....?, me kuma kike so? Kina tunanin ke kadai ce mace a duniya ko????"

NAJEEBA ta ringa lumshe idannuwanta jikinta na daukan rawar balaki, ta dantse lebenta ya fi a irga, in ba dan sun jima da ya nuna mata in me take ji na fannin balaki ya dameta ya shanye ba da yau idan ta budewa mutumen nan wuta sai ya kade har buzunsa......, sai dai hakan ya gagara ya zamo idannuwanta a kansa kamar zasu fado tana kallonsa jikinta na daukan rawa ta ce" SHAHEED, ba zan ce maka bana kula da kaina ba, Ama ta hanyar da ta dace, ina aiki da abinda ba zai taba yi min ila ba koda cikin wata tara ne da Ni , ina aiki da abinda sai dai ya karawa cikina kwari....., ban san batun cusa magani ba...., ban san batun shan mugun maganin da zai min ilah ba, SHAHEED plz truste me......, ka yi hakuri ka daina maganganun nan.....zasu iya sakani a wani hali......"

"Ba zaki daina gardamar shan maganin da Ni ba kenan????" Ya fada a mugun kausashe yana duban yannayin tsayuwar ta

Da sauri Nadiya ta rarafo ta saka hannu zata riko NAJEEBA, ya daga yan yatsunsa biyu tare da wurga mata kallon da ya saka ta dakata da sauri kanta a kasa

A kausashe ya ce" Idan kika yarda cewa kin sha maganin da ya yi min sanadiyar cikina, kya nemi zama da Ni!"

Daga haka ya juya ya bude kofar ya mako masu ita da karfin gasken da ya saka NAJEEBA rintse idannuwanta da karfi, Nadiya kuwa ta Wora hannu a kai ta furta" Mun shiga uku, waye yace masa magani ne ya zubar maki da ciki? Ko maganin kika sha NAJEEBA? Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une"

NAJEEBA dake tsaye kamar an shukata gaba daya duniyar take ji tana daf da rufewa da ita............
Wai wani irin magani ake magana? Ita NAJEEBA, ita dake tashi sallar dare , idan ta yi sallar ta yiwa iyayenta addu'ar gamawa da duniya lafiya, ta yiwa mijinta addu'ar gamawa da mulki da kuma duniya lafiya, addu'ar dake biyo baya shine Allah ya sa tana da wani rabon a duniya kafin ta rufe itama da addu'ar gamawa da duniya lafiya.....

Tun bayan haihuwar tagwaye jinin al'ada ke yi mata wasa, ya zamo idan ya zo ta yi shi ya tafi wani lokacin sai ya dauki wata uku bai dawo ba, wannan dalilin ya sa idan tana cikin yin al'ada take shan magungunanta na mata na gyara hadi da su sasakenta da tsuminta kala kala......, tana gamawa in har ta taka kafarta inda yake ta dakatar da su kenan da fatan samun rabo, wanda ba zata kuma kulasu ba sai wani jinin ya dawo.....a cikin magungunnan nata kuwa harda baban sirrin rikaken sirri, sirin dake wanke du wani datin da ya cushe hanyar mahaifa, wanda in dai ba Allah ne yayi cewar ba zaka haihu ba a duniya to fa cikin ikon Allah idan ka yi shi yi daya, yi biyu, yi uku a na hudu ko na biyar zaka wayi gari da ciki, wasun yi daya yake karbar su, ita da kanta yinta na uku ne yanzu akace ta yi bari hakan na nufin tun wanda ta yi na karshe ta dace da cikin, domin taimako ne baba da ake hada kayan hadi kamar haka Kumba, karanfani, busashiyar cita, da jan zobo......, a tafasa su idan an wayi gari da al'ada ake sha sau daya da sasafe kafin a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login