Showing 117001 words to 120000 words out of 144591 words

Chapter 40 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2362

adalci, kishi daban, son zuciya daban"

Daga haka ya dan jimke hannayenta sannan ya mike ya karasa wajen drowernsa ya ciro ky din kofar wajen dawakai ya dawo ya bata ya furta" Idan sun zo, a bude musu sai a rufe, Ama su wuce karfe bakwai."

Daga haka kuma sai ya kashe fitilar mai hasken nan ya cire rigar dake jikinsa ya bar iya dogon wandon mai santsi ya haye gadon sa..


Jiki a mace Nadiya ta mike ta furta" Thank you, good night"

Bai amsa ba, sai idannuwansa da ya lumshe kawai yana hange har ta fice sannan yayi aiki da comand ya kashe duk wani abin a kashe kafin ya kara sanyin ac ya lumshe idannuwansa.......


Ya Salam
Mace mai gyara duniya ce
Macen da ta san kanta duniya ce
Yaya za'a yi ya iya hada Beebahhhhhhhhhhh da kowace irin mace ne a duniya?
Anya kuwa zata gundure shi kamar yada ake fadin mata na gundurar maza????
Ko dan ta zamo ba KULUN idannuwansa ke ganinta ba, ba KULUN yake samunta a shinfidarsa ba, ba KULUN yake jin muryarta ba, bale idan sun samu sabani sai ta zame masa abin nema a cikin batatun abubuwa masu daraja, sai ya zamo yana haska fuskarta a kirjinsa du dare kafin ta bayyana a gare shi ne......? Gaba daya yarinyar nan ta gama gane hanyar da zata sa zuciyarsa ta haukace , ta gigice, ta nemi bugawa idan har bai samu yada yake so da ita ba..............

Laushin lebenta ke sosa nasa leben.......
Kanshin jikinta kuwa baya hada shi da kowani kanshi a duniya.
Dumin jikinta na bashi mamaki, koda yaushe hannunta da yar jika jika ta zufa da kuma dumi mai tafe da shi, kamar dai yadda ....yadda ....yadda......uhummmm ya Allah

A dole ya janyo filo ya matse sosai a kirjinsa har yana fitar da wani irin nishin da ace itace a wajen filo din da sai ta yi karan wahala....wanda yake tausaya mata ainun.....
Kwarai yana tausayawa du ranar da zata sake maye gurbin filo din nan
Baya ko tantama sai ta rasa gane wani dare ya fi gigitata tsakanin na farkon ta da wannan............

Beebahhhhhhhhhhh, ta yi nisan kiwon da zata sake bayar da budurci a karo na biyu...................

Beebahhhhhhhhhhh ta iya horo, sai dai kuma zata amshi horon abinda ta sa ya sake taurara saboda nisan da ta masa..............



Beebah kenan.



NAJEEBA


Tunda Nadiya ta tafi sai ta kasa shiga dakin Anmy a irin halin da take ciki, karshema sai ta nufi dakin su Muhammad saboda su Auta na nasu dakin ta bude ta shiga ta rufe dakin a hankali ta silale jikin kofar ta kifa kanta da gwuiwarta ta fashe da kuka mai zafin gaske..........

Gaba daya ta rasa gane irin yada kirjinta ke azalzalarta da kanshin bakinsa da kanshin jikinsa uwa uba da maganarsa dake fita kasa kasa a daidai kunnenta wace idan tana sauraro sai ta ji kamar zata sume dan shauki..........

A kan me zata tsaya ta yi ta bege a cen cikin zuciyarta bayan ta sosa inda ya fi saka shi fita hayacinsa har ya daga maka hankali daidai yada ka daga masa , maimakun ya biye mata har a raba su saima ya barta da halinta bayan ya dan dandana mata abu kadan?
Me yasa Za'a ringa wulakantata dan abin da ake iya badawa da yawa ma ita sai a dan lasa mata?????

Eh, ai fa, dole ne ya zamo a yanzu idan rike ta ma zai yi sai yayi na zalunci ya dan rike sama sama ya rike Nadiya da karfi!

To ai Shikenan daga shi har nadiyarr ta gama da su, ba ita ba su cen sai su nemi wanda zasu ci gaba da wulakantawa ba ita ba...........

Abdullahi dake tilawa saboda saukar dake gabansu ne ya fito daga dakin karatun su wanda ke cikin dakin barcinsu da sauri sakamakon barkewa da kukan da ta yi har tana bubuga kafa a kasa saboda ai a zaton ta ita daya ce a dakin shi yasa ta buya ta yi kukan huce haushi dan ta samu karfin sake yakar makiya sai ganin Abdallah ta yi ya fito da sauri hankalinsa tashe

A lokacin da ya ganta gaba daya jikin yaron ya dau rawa, da mugun sauri ya karaso ya dire gabanta yana ririko hannayanta shima ya fara kukan ya ce" Waye ya taba min ke Oumi? Wanene? Fada min ba zan kyale shi ba, waye ya saka ki kuka? Ko jikin anmynki ne? Da sauki fa yanzu ma na baro Muhammad a wajen ta yace shi ya gama harda shine na zo nima in iya saboda gobe malan zai amsa da dare bayan taro in sha Allah, kuma dazun ma tana tafiyarta fa, ko Abiey dina ne? Abiey ne ba lafiya? Menene Oumi....!?"


NAJEEBA ta ringa zaro ido, kafin ta ce" Kai, kuka ne kake? Baka jin kunya kake kuka baba da kai?"

Yana kukan ya dubeta da mamaki ya ce" Oumi ke fa kike kuka????"
Najeeba ta turo baki kamar wace ke magana da yayanta ta ce" Kai Ni kuma kukana ai kamawa ce, babu wanda ya tabani, kuma kowa lafiya ka share hawayenka mana"

Abdallah ya zuba mata ido da mamaki, sai kuma ya hau share nata hawayen yana tuna abinda malamar su ta islamiyya ta ce, a hankali yana duban ouminsa ya ce"
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




41



A hankali yana duban ounminsa ya ce" Oumi, ki yi hakuri kin ji? Malama tace idan ka ga hawaye abu biyu ke kawo shi, farin ciki ko kuma bakin ciki, oumina kin ga Abiey yace a duniya ku kadai muke iya zuwa mu yiwa kuka ko?"

NAJEEBA na kalonsa ba tare da ta bashi amsa ba

Ya ce" Yace idan muna cikin tashin hankali mu fara zuwa wajenki, idan Bakya nan mu neme shi, in baya nan mu nemi Anmy, idan bata nan mu nemi kaka, in bata nan sai mu nemi Iyayenmu ko?"

NAJEEBA ta gyada kai a hankali

Abdallah ya ce" To nima idan kika ji kina so ki yi kuka ki nemo Ni kin ji Oumina, saboda shi Muhammad shima kukan zai yi ta maki, Ni kuma ba zan yi ta yi ba, kadan zan yi kin ji Oumina?"

MURMUSHI ya kwacewa Najeeba ta lokaci hancinsa tana sake duban kamaninsa da mahaifinsa, dama shi ya fi ruwan Sultan, ita kuma Muhammad ya fi dauko yanayin ta

A tauyashe bayan ta mike ta ce" Du in tsallake ANMYNA, da yayuna, da kanaina in diro kanka boyboi?, tashi mu je in ji hardar taka idan ka rike da kyau"

Shima yana MURMUSHI ya mike ya bi bayanta suka nufi wajen karatun su suka zauna ta dauki litafin ya shiga biya mata


Ba ita ta leka dakin Anmy ba sai da dare yayi sosai, ta samu Anmyn na jan carbi, Muhammad kuwa yana saman gadonta yayi barci

Abdallah ya tsallaka ya je ya haye shima, ta bi su da kallo kafin ta girgiza kai, dan ta san idan tace zata sa su je dakinsu ma kakar tasu ce zata ce ina ruwanta kuma? Sai kawai ta yi zamanta tana kama hannayen Anmyn da ta miko mata tana murmushi, itama tana yi mata MURMUSHI ta ce" ANMYNA, yaya karfin jikin ki?"

Anmy ta ce" Alhamdulilah autana, da sauki sosai , daga ina kike haka?"

Najeeba ta ce" ina dakin yaran cen ne, wai harda zai yi shi ne na rike masa"

Anmy ta gyada kai, a tausashe ta ce" Masha Allah, ai Ni na zata ko mutumen nan ya tare ki, saboda har sai da na sa aka leka min, bana son fitina sakinmi muke so ya bamu kawai......"

Zuciyar Najeeba ta yi dan dummmmmm, domin har sai da yannayin rikon da ta yiwa Anmy na farko ya ragu , sai da Anmyn ta Wora da fadin" jira nake yi a gama taron nan, idan kowace ta koma gidanta in matse musu wuta a bamu yancinmu, babu wanda zai takura ki tunda ai ba'a dole, haka kawai a zo ana daga min hankalinki......, ta shi ki je ki huta saboda wunin nan na gobe za'a yi ta kai kawo, dazu ma mahaifiyar zinariya wai take cewa zata turo yara wajen taron sunan, kin san tunda akace sunan wannan yaron babyn ya ci Masha Allah ake ta samun mutane, inaga su zinariya ne zasu zo wajen taron sunan kin ga kuwa za'a wuni ana hidima, je ki huta kar abin ya miki yawa ga condition din ki"

A yanzu kam ba wai iya zuciyarta ce ta buga ba, harda kwakwalwarta.......

Kai ka ga wata sabuwar jarabar, wace? Zinawuya dai ba zinariya ba, o ta shiga uku ita Najeeba me kuma ya haWa taron sunan nan da zuwan ya'yan Sultan din agadez? Ba an ce shima zai zo ba? Shi zuwansa ai da biyu ne dan ya cewa matarsa yana nan tafe su juya abinsu....., Ama ya'yansa fa?????? Kai ina

Bata san cewar ta mike daga zaunan da take har ta kama hanyar tafiya ba sai da Anmy ta ce" A'a, Najeeba, lafiya kuwa???"


Turus ta yi, ta juyo da sauri, sai kuma ta kakaro MURMUSHI tana susar kai a hankali ta ce" Anmy wanka nake so in yi, good night ANMYNA"

ANMY ta gyada kai ta ce" ALLAH ya tashe mu lafiya yar albarka"

Tana kallon yadda take ta faman murda ky, da kyar ta iya murdawa ta bude ta fice , har ta manta kofar a bude ta dawo ta ja sannan ta wuce da sauri

ANMY ta mayar da kanta kan tazbaharta ta ci gaba da ja bayan ta saki MURMUSHI a ranta ta ayyana ' zaku yi bayani ne '


Najeeba ta ga kanta ne kawai a dakinsu, haka kuma tun kafin ta karasa ta cire hijabin jikinta ta rike ya rage mata doguwar rigar dake kasa

Hijabin nan a matse a hamatarta ta haye gado ko Safar kafafuwanta bata iya cirewa ba ta kwanta tana fuskantar bango saboda wani haushin ummulkhair da ya rike mata wuya ta ishi mutane da fira da miji ita mai miji dan kaniya, .....sai kawai ta shiga tunanin rayuwa

Idan da ace zata iya fitar da abinda take tunani a zuciyarta a ji, ana iya yi mata gurguwar fasara, bayan ita Bama abinda take nufi ba kenan, abinda take nufin daban da wanda wani zai ce tana nufi, shi yasa ta fi ganewa yin shiru ba tare da kowa ya ji abinda take tunani ba

Kai, ina, to wai Bama wannan ba, kawai ita mace haka zata kare?
Daga wannan sai wannan
Ba zata tana rabuwa da fargaban cin amanar namiji ba?
Cin amana mana, shi dai namiji KULUN mata na binsa?
Kai wannan shine yake bi
Ai da ganin tsagar idon mutumen nan zaka fahimci za'a so mata
Ai yannayinsa ne mace ba zata gamsar da shi ba sai sama da haka
Ai kana ganinsa ka gama ganin dan cin amana mai hange hange
To shi wai haka yake?
Kai innalilahi, zinariya kuma?
Cabdijan.........
Tarin gajiyar da ta zo da ita ce kawai ta sa ta samu barci, shima rabi da rabi saboda cen sai ta saki ajiyar zuciya ta juyar da bayanta ta sake dantse lebenta...........


A lokacin da zahra'u ta juyar da ita ta janyota da kafafuwanta har bakin gadon tana fadin" Ke wai dan ubanki ba zaki tashin bane an fada maki an yi sallah Ama kin ki tashi? Kai Najeeba Najeeba Allah ya shirye ki"

Ta tashi a firgice tana dubansu su uku da suka yi tsaye sunna kallonta suma

Sama da kasa ta bi su da hararen da suke yi mata, uwa uba ita da kanta sai yanzu ta janye hijabin dake matse a jikinta ta bi shi da kallo harda sinsinawa kafin ta ajiye ta sauko yana cire Safar kafafuwanta

Har ta fara tafiya ta juyo ta nuno ummulkhair da hannu ta ce" Ke, in kika kuma cika mana dare kina waya da kato sai mun dake ki a dakin nan, aikin banza aikin wofi, ku dai baku da aiki sai waya da maza? Mtsssssssssssssssss!"

Gaba daya baki bude suka rakata da kallo har ta mako kofar bayin ta garkama ky kafin su kalli junna

Zahra'u ta fashe da dariya tana kaiwa zaune ta ce" Kun san Allah, matar nan idan bata koma dakin ta ba mun shiga uku, ta yiwu da ya ja ta fitsara ta masa ya ja kumatun, ji yadda ta kwana da rigar nan da Safa da hijabai....tabas kowace kwarya da abokin rmnt, SULTAN ne kawai daidai da Najeeba, shi ya san lagon kayansa , shi ya fi kowa sanin wacece ita ....., shi yake da makamin yakarta ta du inda ta bi!"

Ummulkhair kanta sai da ta jinginu da garu dan dariya ta ce" Ji fa balaki, ko ita da wa zasu zane Ni dan ina waya da mijina, harda kirayar min miji kato, to da katuwa take so in yi wayar ko yayane????"

Ummukulsum na dariya tana ciro kayansu tana lodawa saman abin t????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
uraran wuta

Sai dai sunna cikin shirya kayan Andiya ta shigo da kayan mamanta da kuma turarukan wuta tare da Auta

Nan fa suka shiga koda wasu kayan saman abin turaran Najeeba sannan suka saka turaran wutar

Jim kadan najeeba ta fito daure da tawul

Da Auta da Andiya suka shiga gaisheta

Ta amsa tana duban Andiya ta ce" Wasu kaya kika dauko min??"

Andiya ta ce" Anmy wannan jar shadar taki ce da aka kawo sabuwa"

NAJEEBA ta yi dan tsam bayan ta saka rigar sallar zahra'u ta ce" Bani ky din"

Andiya ta ciro ta mikawa uwar rikon ta

Najeeba ta amsa har zata fice ya dawo ta ce" To ke me zaki saka?"

Andiya ta ce" Momy ai nima cikin sababin nawa ne na dauki guda"

Najeeba ta gyada kai ta dubi sister dinta ta ce" Ku shirya fa, Ni zan shirya a cen.........., Aunty zahra'u karfe nawa ne za'a yi zaman nan na filin gida?"

Zahra'u ta ce" An ce karfe goma da safe, zuwa lokacin ne ai SULTAN zai fito, kuma zuwa lokacin ne baki ma zasu samu halarta, na ga an gyara wajen sosai an saka runfuna, Anmy fa tace da an gama wannan zaman za'a salami mutane sai su yi wunin hawan dawakansu cen wajen maza"

Najeeba ta gyada kai sannan ta ce" Ok, to mijinki yaushe zai zo? Ko shima zai zo da wuri?"

Zahra'u ta ce" Ni ban sani ba, Ama inaga ai du zasu zo da wuri ne bakin"

NAJEEBA ta gyada kai ta kai dubanta kan ummulkhulsum ta maka mata harara ta ce" Ko uban wa ya sa ta zo nan ta haihu? Kak, yau daidai nake da kowa a gidan nan, na rantse idan ban figewa zabuwar nan gashin kai ba ku ce ubana goma, kai du Wanda ma yace zai shiga hancina sai na fyato shi yau kak, mu hadu a cen kar wanda ya neme Ni!"

Tana gamawa ta fice fuuuuuuuuuu a dakin

Suka sake kalon junna, ummulkhulsum ta ce" Yau banda yan bakin halin harda yan iskan a kusa da matar nan, to wai wacece zata fige din??"


Auta ta ce" Kai, Aunty Akoy rigima wai figewa kamar ta samu kaza"

Andiya ta harareta ta ce" Kin ga dai bana son wasa da uwata, na tabbata an tabo min uwata, zan shirya kuwa dan tana figewa ina gasawa......"

Gaba daya suka kwashe da dariya har basu ji salamar A'isha ba , wace ta zo da akwatin ta dauke da tufafin da zata saka saboda sai an yi mata ma'uk zata sa sutura......, nan suka ci gaba da firarsu sunna jajen du Wanda ya tabota ya ki yin hakurin sai ta musu kwalliya sannan ya tabo ta????????, ganin har karfe takwassss ta yi ya sa suka shiga SHIRYAWA a hanzarce saboda dole zasu fita da wuri ko kula da baki da marabatansu, Danma Umi tuni ya zo, hakama Anmy tuni ya fito sunna cen sunna kula da wasu abubuwan, domin baby an shirya shi an mika shi wajen kaka jakadiya da pidansa da duk wani abin bukatarsa da kuma yara biyu da zasu kula da shi, biki ne ba za'a fito da shi ba sai an watse, sai ko mamansa da zata rinka lekawa lokaci zuwa lokaci dan ta shayar da shi




NAJEEBA



Tunda ta karasa dakin ta sai ta samu kanta da zuwa wajen tufafinta na garari ta bude ta ja ta tsaya tana kallo.........

Ita fa bata son fasarawa, kawai dai a tunaninta a yanzu ta fi karfin ace an zo har filinta an cita da yaki..........

Ta jima tana kallon kayan nan kafin ta yarda da wanda zuciyarta ta fi karkata a kai, sai dai abin takaicin ta ji zuciyarta ne kawai ta fi kwonta mata da shi, Ama bashi da wani adon a zo a gani , Ama shada ce, danyar shada ce , wace aka yi mata odanta a SAJIDA SHOP, shada ce ta garari, shada ce ta manyan mata, shadar kanta na dauke da adonta ne, shi yasa mai dinkinta ya dora duwatsu masu hasken gaske a iya wuyan da hannayen da kuma karshen Winkin

A lokacin da ta bude wajen alkyaba ne ta zuba ido sosai kafin ta yarda ta dauko fara kar din alkyaba mai dauke da mahaukacin dsgn,

A lokacin ta mayar da su saman abin turarawa sannan ta je wajen kayan kwaliyarta ta zauna tana duba lokaci ta ga lokaci na saurin gudu domin har karfe goma ce zata yi

Wayarta ta dauka ta turawa andiya msg cewar idan mai martaba ya fito ta sanar mata, sannan ta ci gaba da shiryawarta


Ba cika fuskarta ta yi da dige fige ba, a wajen turare ne ta yi anfani da wanda ko ka ki, ko ka so sai ka shaki kanshi, bale zaka shaki kanshin ne dan ya yi maka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login