Showing 39001 words to 42000 words out of 144591 words

Chapter 14 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2344

13



"BEEBAH" ya fada cen karkashin makoshinsa......, rashin dagowar kanta ta Dube shi ya saka shi Wan yin gyaran murya ya sake furta


"NAJEEBA"

Shiru ne ya wanzu a wajen tamkar bata nan

A tausashe ya sake fuskantarta ya furta" BEEBAH"

NAJEEBA ta lumshe idannuwanta, hawayen dake faman sai sun zubo ta shanye su da dukkan kokarinta sannan ta fuskance shi, dubansa ta yi tsai cikin ido har na second biyar da duban da ya saka shi cire nasa idannuwan daga cikin nata kafin ya sake saka dubansa a cikin nata.

A tausashe ta furta" Allah ya bada zaman lafiya, ina maraba da haka, kuma ina farin ciki" daga haka ta lumshe idannuwanta ta ringa mayar da numfashi a hankali a hankali har ta samu yadda take so

Mikewa ta yi daga zaunen da take cikin shiga ta alfarma, ta dauki wanka ne cikin riga doguwa budadiya wace ta sha uban adon dinki irin na manyan mata, jikinta sanye da alkyaba ruwan azurfa sai dan kyalin fari dake daukan ido, shigar ta na haskaka duk inda ta bi, duda dare ne hakan bai Hanna ake hango walwalinta tamkar dawisu ba.

Juyawa ta yi zata fice ya gaza hakurin hakan, ya dubi nadiya da ido yayi mata alamun kar ta bari ta tafi.....yana iya yinsa dan Hanna kansa nuna gazawarsa

Nadia dake cike da tsoron yannayin da suka samu kansu a ciki kwana biyun nan, da kuma wannan tashin hankalin ta mike da sauri ta bi bayan NAJEEBA dake tafiya cike da kasaita tamkar zata kifa domin juwa je janta kamar zata bugata da kassss

Muryarta a raunane ta ce" Gimbiya, dan Allah ki tsaya, kin san hankalinsa ba a kwonce ba, kina gani tun daga kan fadan nan na magani da ransa ya kiya har yanzu bai samu nutsuwa ba, kin ga yau ko fada bai leka ba, ko yara da suka zo yi masa firar yama basu samu ganninsa ba, ba kin ga Nayla ta koma bangaren ki da wuri ba? Na tabbata dan ya hukunta mu ne zai karra aure, Ama idan yana so ya auri biyu rana daya mana ai ba a kanmu zasu zauna ba tunda mun san mijinmu mai adalci ne zai ba kowace hakinta ne"

NAJEEBA ta lumshe idannuwanta, a hankali ta saki dan murmushi ta juyo ta zuba mata ido.....

Shekara takwas kennan da kadarar auren miji daya ta haWa su, an yi gwagwarmaya an yi sama an yi kasa, sai dai cikin hukuncin Ubangiji har yanzu da take da shekara talatin da daya a duniya idan abin ya murdo mata tana jin zafin nadia da kuma wanda ya hadata kishi da watanta ......ta yayama za'a yi ta kasa jin zafin nadia ne a rayuwa? yaya za'a yi ta manta abinda MAI DAMAGARAM ya aikata mata a lokacin baya? a ranar da ya amshi budurcin Nadia ya kaita ciki ya Kwontar, a haka aka tilastata ta sake waiwayarsa har ta yi masa biyaya....., eh ba zata ce bata yafe ba, ta yafe fa , sosai da sosai ama ba zata taba mantawa ba..... Sai ga wani mikin ana son caka mata a lokacin da take cikin jin ciwon mara na rashin gudan jinninta???...., yaya za'a yi a yi kiransa da mai adalci bayan shi din ya kasance mai zalunci? Yaya za'a yi a ce da ita ta san cewa mijinta zai yi aure dan haka karma ta yi haka matsayin matsala kawai ta amsa ta rayu da haka?????, ana nufin fa cewa matarsa ta da zai dawo da ita wato zinariya ko wacece zai aura? Dama du wannan wahalar da ta ba kanta har ta yarda ita Najeeba ta zubar da dukan makaman yakinta ta Dube shi ta fada a makauniyar soyayarsa ashe shi ba haka bane a wajensa.....? Uhummmmmm koda yake dama sarki ne shi fa, ko dan ya nuna mazakuntarsa ai sai ya cike hudun nan rerassssss....., yaya za'a yi ta yi tunanin ita din nan ta isa ta isarwa mai DAMAGARAN ciki da bai? Ita da kanta ta san ko a yanzu da shekarunsa suka haura arba'in idan ya rike ta a gadonta sai ta nemi agaji....., ita da kanta ta san kula da yake ba jikinsa da lafiyarsa kadai sun isa a so shi, ita da kanta ta san dukiyar rike hudu ai ya gama tarawa sai dai a yi fatan habaka da bakin ci su ci, ita da kanta ta san garke ta shigo tare da uban garken mai kwadayin tara abin kiwo du kuwa da irin yadda ya tara garake zafafa a gabansa...., ita da kanta ta san wannan fadan da ya dage, ya nace, ya kuke ya rike ya jajirce sai yayi da ita da dalili mai karfin gaske wanda yanzu ya bayyana kanta....., ita da kanta ta san irin yadda ya rike ta ya ki ya tayata ya ki ya saurareta ai da dalilinsa ne! Sai dai Babar tambayar itace......shin ita ta shiryawa wannan cakwakiyar.......???? Shin an san yadda aka yi ta aminta da Nadiya a duniyarta tsakaninsa da ita???? Ba zata yarda ba! Ba zata taba yarda ba! Ita me yake ganin ya tanada yayi , Ama ba da ita ba!

Cike da iza ta yi taku daya har zuwa daf da Nadia, ta rage muryarta sosai sannan ta saka kakausan idannuwanta a cikin nata ta ce" kina nufin kamar yadda aka kawo mana shi Ni da ke rana daya yanzun ma yana iya kara biyu kowace ta zauna da kugunta mijinta ta aura ba na wata yar kutumar ........"

Ta dantse lebenta da karfi dan Hanna kanta durawa nadiya ashar, sannan ta Wora da fadin" Ki je ki sanar da mijinki cewa hakan baya gabana Nadiya, ki fada masa na fi shi farin cikin hakan! ki tambaye shi dama na isa na hanna shi yi ne ni? Ai da na isa da ban raba mijina da ke aminiyata ba Nadiya!, ki fada masa zaurancenki ya kawo biyu....kowace da gindin zamanta zata zauna....., kina iya kara masa da cewa ai dama matar cushe bata daraja.......na dauki hakan matsayin aiki ne ya biyo ta kaina!"

Tana gama fada ta juya da sauri.......
Har ta fara tafiya ta juyo da karfin da ya saka alkyabarta watsuwa sosai a kasa ta bude kamar gashin dawisu ta dan dago hannunta mai dauke da jan lallen da Andiya ta yi mata cikin daren jiya ya yi mata dassssssss a yan yatsunta, da yan faratunanta masu dan tsayi da fararan zobunnan azurfarta ta nuna mata yatsar ta ce" Ki fadawa SHAHEED! Sarki ne shi ai, anyway talakama ya tara mata bale mijinki? yana da lafiya ai, ya tara ya'yan banki, ya dauko biyu a rana daya idan yana so daga shi har matan basa gabana.........., kema ya zama na karshe da zamu yi irin maganar nan da ke Nadiya, idan kuma kin kiya zan tabbatar maki kura nake lulube da fatar akuya idan na riki wuyan ki....., barci na yi mai tsayi ba mutuwa ba ki gane haka!"

Daga haka ta hade yan yatsunta biyu ta dana a kusan fuskar Nadia sannan ta juya da sauri ta fita daga sabon bangaren da aka gina wanda iya su kadai matansa suke kai ziyara wajen idan zasu yi zaman nan domin ko ya'yansa sunna zuwa ne dayan bangaren nasa na cen cikin fada dan su gana da shi, wato su Muhammad, Abdallah, nayla da Saima'u,.


Tunda ta bayyana a baban filin gidan masu rakiyarta suka mara mata baya saboda dare ne dole a take mata baya, ta bar Nadiya sangame a tsaye cike da tsoron irin abinda ta gani a idannuwan NAJEEBAr....., wato sak Najeebar da ta sani a da, wace ta yi sanyi sosai ta zubar da fitintinun da take yi, ashe bata daina ba ajiyewa ta yi? Sun shiga uku.

Da lafiya kalau take da sai ta kai fira bangaren Ummu Duda dare ya yi, domin yau bata leka ba sam, sai dai a yadda take jin duniyarta baki daya ba zata iya zuwa cen ba a yau, dan ko da wasa ba zata so a ga wani abin a tare da ita da ya shafe shi ba wani irin zafinsa take ji, wani irin haushinsa take ji!

Du irin kirarin da suke yi bata ji saboda kunnayenta sun gama donewa, har suka iso bangarenta aka bude baban get ta dan dakata da ido ta yiwa babar jakadiyarta alamun su tsaya iya nan sannan ta shige ta sake ja ta tsaya har jakadiyar ta gama magangannunta na kirari aka rufo kofar falon nata sannan ta yi wurna wurna ta rasa inda zata tsoma kanta sai kawai ta cire alkyabar ta yar a nan, ta nufi sama da gudu gudu ta rarumi wayarta dake saman bed dinta kirar iphone 16, ta lalubo numbar yaya Dayabu ba tare da ta yi la'akari da dare ya yi ba, yana dagawa ta danna sauran numbobin kiran ya zama na conferense, da gaba daya yan uwanta, wa'inda a yanzu auta kadai ce bata dakin miji , wannan bai shafe ta ba dan tana tare da su Nayla a bangaren da andiya a bangaren Anmy

Yaya Dayabu a gajiye da abin barci yace" NAJEEBA, dan kina auren yaya ba shi zai sa ki yi kirana Ni magidanci a irin wannan lokacin ba, auren yaya ba zai hanna ni in ci ubanki ba!"

zahrah dake fama da yar nakudarta tunda yama tana nishi ta ce" NAJEEBA, yanzu fisabililahi lokacin kiranki baya aunuwa ne ? iyeah? in dai ba ranar aikinki bane ke sai kin ishi mutane?"

Umma khulsum da shirun NAJEEBA ya dameta domin ta saba idan ta yi kiran nan sai ta fashe da dariya akan yanzu tunda suka dauka babu wanda ya ji muryarta ta ce" NAJEEBA lafiya? shirunki yayi yawa"

NAJEEBA dake langwui , juwa na neman makata a saman gadonta ta budi baki a hankali ta ce" Walahi, walahi, idan har ya yarda, idan har ya kuskura ya sake aikata min irin abinda ya min a kan Nadia a lokacin da nake gudun haduwa da shi a lokacin da hakan bai dame Ni ba, a lokacin da shi da tsuman rayuwarsa basa gabana na shanye na aminta na kyale na kawar da kai na dauki duk wani tsarinsa na zubar da nawa.....na gama aminta da shi, hakan yake damuna...a yanzu ba zan dauka ba, na rantse da rabul arshi sai na gigita duniyarsa, Ni NAJEEBA in dai jinnin Umi ce da Mutalab sai na gigita rayuwar SHAHEED, ku zama shaida!"....... Sai kuma ta ja wani irin numfashi , ta ja da karfi ta karra ja sai kawai ta fashe da kuka lokaci daya numfashinta na wani irin karra mai nuni da hukarta ta tashi.........ta saki wayar ta zube saman gadon tana numfarfashi tana neman daidaita numfashinta


Wata irin mikewa Dayabu yayi, da karfi ya ce" NAJEEBA!, ke Najeeba!, Najeeba!"

Gaba daya yan uwan suka shiga kiran sunnanta da karfi , ya zamo a cikinsu babu wanda bai yi waje da gudu yana kiran sunnanta ba, harda zahrau da ummulkhair ......su duka a rikice suke kiran sunnanta, sai wace mijinta ke kusa ne ya rike ta ya amshi wayar yana faman tambayar abinda yake faruwa, bale ummi dake cikin nakuda nan ta durkushe ta fasa kuka tana kiran sunnan NAJEEBAN


Dayabu da ya fada motarsa tuni nmya tayar ne ya ce" Kai ku min shiru dan ubanku!, gani nan zan je, ku barni hakanan ku kwontar da hankalinku, auta tana gidanta dazu ta tafi , bari in yi kiran layinta ta fara je min dakin nata kafin in isa, kuma Andiya tana nan, kar wace ta yi kiran Anmy, ku bari in fara zuwa in ga abinda yake faruwa, kar ku manta fitinar yar uwarku ta yiwu yar rigima ce ta haWa su , idan abin baba ne du zaku ji"

Daga haka ya kashe ya shiga falfala gudu a makekiyar hanyar damagaran ya dauki hanyar fada kirjinsa sai bugawa yake yana tafe yana neman layin andiya domin ta auta ta yi RINGIN har ta katse bata daga ba

RINGIN na biyu Andiya ta daga a lokacin sunna kokarin bude bangarensu su shiga sun fito daga Sangaren Anmy, dan ita Anmy tuni ta yi barci, sunne suke karatu tare da yan biyu da su nayla

Irin yadda ta ji Muryarsa sai da gabanta ya fadi, a gagauce ya ce" Andiya, yi maza dakin auntynki athsmanta ya tashi ki kafa mata bantoline dinta "

Da wani irin gudu ta yi ciki , auta ta mara mata baya tana tambayar ko lafiya, suka yi dakin Najeeba wace take daf da rasa numfashinta, dan gaba daya ta gaza janyo abin gadonta bale har ta iya ciro pampon nata

Da gudu ta ciro shi, auta ta talabota ita kuma ta kafa mata ta danna mata shi da karfi ta karra danna mata a danawa ta uku ta iya daga hannunta ta rike tana matsawa tana jan numfashin da karfi har ta fara daidaituwa a hankali a hankali sannan ta yi lataf a jikin auta, gashin kanta ya watsu ko'ina, jikinta ya saki sai tari da take yi da kuma numfashin da kyar , da kyar..............

Tafiyar dake iya daukan masa awa guda ce yayi a minti ashirin da biyu, a lokacin da ya zo Babar kofa ta fada ta baya dan ya san bai isa ya bi ta gaba ba a irin wannan lokacin, Sarkin bulala ya dakatar da shi ya nemi layin uban gidansa saboda ba'a ce masu zai zo ba, dogaran dake nan ba zasu barshi ya shiga ba du kusancinsa da sarki

A lokacin da Sarkin bulala ya sanar masa wanda ke son shigowa, SHAHEED ya nemi a bashi wayar, dan haka ya amsa da girmamawa ya ce" Barka da warhaka excellency"

SHAHEED ya mike zaune daga ringeshen da yake ya ce" Ina fata lafiya? Baka sanar da Ni zaka zo yau ba"

Dayabu ya sauke ajiyar zuciya, a tausashe ya ce" Eh, dama Najeeba ce muna waya da ita sai ciwonta ya tashi, shine na kasa hakuri na taho"

Da sauri SHAHEED ya jimke wayar idannuwansa na budewa tarrrrrrrrrrrrrrrr, sannan ya furta" Beeban?????'"
Sai kuma ya mike tsaye da wayar a hannunsa ya ce" Su Barka ka shigo"

Daga haka ya kashe kiran dan Sarkin bulala ya ji abinda ya fada domin wayar tasu mai karfin amsa amo ce, kuma a irin yadda suka horu da jin Muryarsa koda a hankali yayi magana abu mai sauki ne su jiyo shi a yanzun ma, dan haka suka bude masa.....

SHAHEED gaba daya ya manta cewa Anmy ta saka ky din bangarensa daga wajen Najeeba sai da yayi yayi ya murda ky din ya kasa budewa sannan ya juya da sauri ya nufi falo ya kashe wutar lantarki dake jikin kofofin su sannan yayi waje ko alkyabarsa bai rufa ba bale rawaninsa, domin a lokacin da ya fito ko Sarkin gida sai da ya tsorata, sai dai yana yi masa alamun karma ya nuna ya ganshi sai suka yi shiru da sauri ya mara masa baya a lokacin da Dayabu ya shigo da gudu gudu suka yi bangaren Najeeba

A kofa Sarkin gida ya tsaya, shi ya fara shiga sannan Dayabu na biye da shi a baya

Tunda suka tunkaro dakinta gabansa ya sake faduwa....., da sauri ya ja ya tsaya ya kasa karasawa

Dayabu ya Dube shi, a hankali ya ce" In shiga???"

SHAHEED ya gyada masa kai, sannan yayi baya ya zauna saman kujera ya zubawa waje daya ido yana ta kama sunnan Allah


Dayabu na shiga auta dake hawaye ta kamo hannunsa ta ce" Yaya kalli fa, har yanzu bai daidaita ba kuma kuka ne take yi da ta yi shiru ma da ta samu lafiya"

Dayabu ya dubi andiya ya ce" To ke ina aikin likitancin naki? Ba sai ki mata allura ba???"

Sai yanzu andiya hankalinta ya kawo, da sauri ta sauka ta bude wajen magungunnan najeeba ta ciro dexa da seringue ta zuki ruwan sannan ta karasa inda Dayabu ya jirga NAJEEBAN suka ciro damtsen hannunta ta tsira mata allurar sannan ta mayar da kanta saman cinyarsa a hankali yana rike da hannunta yana kallon ta har numfashinta ya ringa daidaita kafin a hankali barci ya dauketa

Wata irin ajiyar zuciya ya dinga saukewa a boye ya dauke kwalar idannuwansa........
Sun jima rabon su da su ga ta yi crise........., a duniya yana tausayinta fiye da sauran yan uwansa saboda wannan lalurar Tata, kai gana dayansu sunna matukar tausaya mata da nan nan da ita saboda lakurar nan Tata......., shi yasa suke yawan son gannin sun sakata a farin ciki, domin ita idan hankalinta yayi kololuwar tashi ne hukar ke tashi........

Gannin karfe daya zata yi a dole ya barsu da ita ya sanar musu idan dai suka ga ta kuma tashi to maza su sanar masa sannan su sanar da bangaren mai Martaba

Fitowa yayi ya samu SHAHEED a zaunen nan hannayensa hade cikin junna.......

Murmushi ya saki, a zuciyarsa yana tabbatarwa kansa fada suka yi , shine ita yar rigimar zata daga hankalinta har ta daga masa, gayanan sai jimke hannu yake yi ya kasa mikewa bale ya shiga inda take tsabar tsoron gannin yannayin da take.


A nutse ya ce" tashi mu je dan uwa, alhamdulilah ta kwonta"

SHAHEED ya zuba masa ido, na dan lokaci kafin ya ce" A nan zan kwana,.....idan ma na je cen din....da wahala in iya yin barci"

Tausayinsa ya kama Dayabu ...., tabasss zai zauna da yar kanwarsa su yi magana, dan Allah kar ta kashe masa Dan uwa....., kai ta yi dan Allah ko ta yi dan wahalar da zai iya bata...........

A tausashe ya ce" Ko me yake faruwa....in dai aka yi hakuri zai wuce in sha Allah......kar ka saka damuwa a ranka fa"

SHAHEED ya sauke ajiyar zuciya, yayi murmushi mai ciwo, a hankali ya ce" ka je kani, na gode Allah ya saka da ALKHAIRI"

Tausayin SHAHEED ya kara kama shi, harma ya ji inama lafiyarta kalau ya ci kaniyarta? Kennan bata daina ba mutumen nan wahala ba????, Najeeba? Allah ya kyauta mata......, salama ya masa yayi tafiyarsa.........

Tunda ya je sallar asubahi ya dawo bangaren nata ya dake shiga, wannan karron bai tsaya jira ba ya wuce direct dakinta

A lokacin Auta ce kadai ke zaune kusa da ita tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login