Showing 48001 words to 51000 words out of 144591 words

Chapter 17 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2343

yin aure a boye idan ya so ya sanar da matar daga baya dan kar ta daga hankalinta saboda maganar auren, kamar yadda fiyayen halitta yayi , wanda du wani abu da ake yi shi ake koyi dan samun rabauta mai kyau, Ama shine za'a tirke shi Wan kawai ya fito da maganar aure Ita Y'ar neman ta nuna bata amince ba?????, ai na zai taba yiwuwa ba, yayi aurensa tunda ya yi niya ba mai Hanna shi.

Wannan rigimar suke cikin yi yan matan suka fito suka zauna kusa da yayansu suma suka sada kawunansu

Rai bace ANMY ta ce" Maryam, na rantse maki ki kiyayeni, a kan yarinyar nan tabasss sai na batawa kowa a gidan nan, ok kenan ba zaku Dube Ni ku saurareni ku gane me nake nufi ba? An taba yanke hukunci cikin fushi ne? Wai shi da yake fushin cikin nan ya dan da shi ne? Kunna gani fa na tura yaron nan dan ya amso min takardun asibitin akace basa asibitin, kuma ita likitar wai bata nan sai dai ya koma gobe ita zata sanar inda ta saka gwaje gwajen da ta yiwa yarinyata? To bari ku ji, koda ace da gangan yarinyar nan ta zubar da cikin nan iya abinda za'a yi mata kenan dan ta gane kurenta ta yi tuba a wajen wanda ya bata, bale in ba son kai da neman fitina irin taku gaba dayanku ba ai kun san cewa yarinyata ba muguwa bace, yarinyar nan ta fi shi son haihuwar nan, shi har haihuwa yake so? Nace kai wannan yaron har ka san kana son haihuwa? In fada maka Ni na san irin halin da take ciki a gidan nan, kuma babu wanda zai kai zuciyar uwa son ya'yanta ! , ka san halin da ta shiga da aka sanar mata jinin da take zubar wa na abinda ke cikinta ne????, a irin wannan halin da na yi tunanin kaine maganin damuwarta zaka sakata a gaba? Ok dama jira ake yi in yi magana a nuna na bi bayanta ko????, ba damuwa na je na bin a yi abinda za'a yi, aure ko? Ai sai ka yi, Ama sai an bi min bayan abinda yake faruwa da yarinyar nan!"

Kansa a kasa yake, tunda take fadan nan zuciyarsa ke bugawa....., a hankali a hankali yakan dan dago ya dubi Aba ya ji kamar ya ce dan Allah ka yi hakuri ka barta ta yi fadan ko zata huce......, a hankali kuma sai ya lumshe idannuwansa yana sauraro har ANMY ta dasa aya tana dubansa rai bace

A hankali ya jinginar da sandar hannunsa, ya gyara alkyabar jikinsa sannan ya sassauta , ba tare da kowa ya gane abinda zai yi ba ya duko kasa gaba dayansa ya duka

Da sauri Dayabu ya zabura zai mike, sai kuma ya kai duken shima ya sada kai jikinsa na neman daukan rawa......

Aba ya taho da sauri inda yake duke ya furta " Tashi, tashi ka zauna"

A hankali ya sake sada kai, a tausashe sosai ya ce" Ka yi hakuri Aba, ka bari in ba ANMY hakuri ka ji????"

Aba ya sauke kansa kasa, a hankali ya koma gefe

Sai da ya sauke ajiyar zuciya, a tausashe ya ce" Ki yi hakuri Anmy, na bata maki rai ki yi hakuri, in sha Allah ba zan kuma ba....., kuma zan kiyaye dukan abinda kika ce"

Yayi shiru na dan lokaci, sai kuma ya dora da fadin" In sha Allah koda auren kika ce kar a yi, ba za'a yi ba, haka kuma idan kika ce In bata hakuri ma sai in bata"

Da sauri ummi ta ce" Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, ba zaka bata hakurin ba....."

Sai kuma ta ratsa da sauri ta karasa inda NAJEEBA ke zaune dishan kanta a kasa, ta riko kunnen NAJEEBA ta daga hannu zata sauke mata zazafan mari , ANMY ta yi saurin rike hannunta tana kallon ta da mamaki, shi kuwa wani irin rintse ido da yayi sai da fatar gaban goshinsa ta dau ja, ......., gaba daya kirjinsa ya cinkushe, hankalinsa ya nemi tashi

Rai bace ANMY ta ce" cika ta!, cika ta na ce!"

Sakin kunnen nata ta yi tana kallon ta

ANMY ta ce" A kan me? Me ta yi????, dan Allah bakwa gannin cewar kunna takura yarinyar nan fiye da kima?, me ta maki Maryam?, Shikenan dan itace mace, itace karama ba za'a dubeta ba? Ke in tambayeki an taba zuwa aka dora maki laifi kankani wanda kin san baki aikata ba kika yarda kika amsa? Yaya za'a yi wasa da maganar zubar da ciki kuma a ki bata damar ta wanki kanta????, tace bata zubar ba, shine zai zama baban matsalar da za'a daga mata hankali? Haba ba dan mun haife su bane zamu ringa cuta musu, Allah fa baya barci kuma a abinda muke ganin karami ne tsaf zai iya janyo mana fitinar da ta fi karfin mu, ba dan Najeeba bace nake wannan maganar, ko Nadiya ce iya abinda zan yin kenan, saboda du adalcinsa a kan wasu ya kare banda ita!"

Najeeba da idanuwanta ke lumshe hawaye ya gama cike mata ido, tana duke a kan gwuiwoyinta, sa'in sar iyayenta na nema ta gigita zaman lafiyar zuciyarta, uwa uba irin yadda sarkinta ke duke har yanzu kansa a kasa , basu bashi damar gama abinda ya fara Bama bale har su masa uzuri da abinda ya dace...........,


A hankali ta budi baki, muryarta a raunane ainun ta ce" Anmy, ummi..........PLZ...... i'm sorry"

A hankali ta fashe da kukan da ya sa zahra'u fashewa itama da kukan ta sake sada kanta sosai dan gudun batawa wani ko janyowa yan uwan ta fushin yayansu da iyayensu.......

A hankali NAJEEBA ta dubi yaya Dayabu, wanda duban da ta masa ya sa ya rarafo da sauri ya duka shi dinma ya rike hannun NAJEEBAN, a hankali ya ce" Ku yi hakuri kun ji? Dan Allah ku yafe mana, ku yafe mata, ku yafe mana baki daya, in sha Allah ba zata taba tayar da wannan maganar ba ko Najeeba? Ko???"

Najeeba ta Wora kanta a kirjinsa , muryarta na fita da amon kuka ta ce" Idan har kaima kace in bari Shikenan, na bari, na bari yaya, kowa yayi hakuri in sha Allah na bar maganar, ba zan kuma tasota ba, a yi hakuri a yafe min zubar da cikina da na yi Ni Najeeba......."

Ummukulsum ta fashe da kuka a inda take kanta a kasa ta ce" Wallahi baki zubar da ciki ba, ba zaki dauki wannan girman abin ba, idan kin dauka yaya kike so zamanki yayi ke da yaya ? Zai zauna da wace ta zubar masa da ciki fa kenan???????"

Da karfi umi karama ta ce" Wani irin zama ne zaku yi???, Najeeba akoy hakuri na laifi da ake yi na yau da gobe tsakanin mace da mijinta, Ama wannan fa wani laifi ne baba, yaya maganar maganin da likitar nan ta baki? Yaya maganar gwaje gwajen da aka maki?????"

Yaya Dayabu ya juyo yana hade rai sosai ya ce" Zaku min shiru ko sai na fatatake ku a wajen nan baku ga wanda ke wajen ya fi karfin daga muryoyinku bane????"

Najeeba ta dago idannuwanta ta zuba masa ido, a hankali ta ce" Ka yafe min yaya....."

Sai kuma ta kai dubanta kan SHAHEED, a hankali ta furta" Ka yi hakuri, ka yafe min"

SHAHEED ya zuba mata ido, wani irin tausayinta na kuno masa, a hankali ya dauke dubansa daga fuskarta a lokacin da Aba ya ce" kunna ji, kowa ya zauna a yi maganar da ta dace , bana son irin wannan abin, me yasa ba zaku daina dagawa junna hankali bane???"

Su anmy suka fara zama, sai kuma su yaya Dayabu, Ama shi SHAHEED a yadda yake bai iya dagawa ba saboda har yanzu bai ji abinda yake son ji daga bakin anmy ba

A hankali Aba ya ce" Haba, ya za'a yi karamin abu ku mayar da shi baba?, du fa abin nan mai sauki ne, Najeeba tana da damar yin musun cewa bata aikata abinda ake tuhumarta da shi ba, idan aka zaunar da ita aka fada mata komai ta yarda cewar eh abinda take sha din ne ya hadasa ba Shikenan ba?????, duka kaf abin nan a bayyane yake da an bi hanyar da ta dace da rayuka basu bace ba"

Umi baba ta ce" Yanzu Abansu sultan SHAHEED Sa'anta ne da zata yi masa musu? Ko me ya zo da shi ai sai ta yi hakuri kawai ta bashi hakuri a wuce wajen ko? Koda abinda aka fada ba haka bane ai Allah zai nuna masa gaskiyar ko??? Ama dan ita mai gardama ce sai tace zata ja magana da shi????"

Anmy ta girgiza kai ta ce" Son kai sak, in an yi magana an iya cewa nice mai son kai, to shi wannan yaron din kenan itama Sarkin yake a gabanta ko????? Ki ja abinda zai sa in mike in tsinke fuskarsa da mari in tuna maki mu haihuwarsa muka yi, hakan na nufin sarautarsa ba dai a cikin gida ba, matarsa ce, in har ya zo mata da abinda bai yi mata ba tana da damar nemawa kanta haske da kuma ganar da shi abokan rayuwa suke ba haihuwar ta yayi ba, haba dan Allah!"

Aba ya girgiza kai ya ce" Ai sai ku yi, son, kana ji????, du a bar wannan rikicin, ita ba ta Musa mana cewar abinda take sha din ba zai yi mata ila ba? Ai ilimi ta gama zaga duniya yanzu, zan je da kaina asibitin gobe in sha Allah in ga likitar, idan ta fada min komai da gwaje gwajen Ni in na fada mata ta Musa min!, ka tashi ka zauna, Y'ar gidan waye zaka aura? Itama a yi a gama dan Ni bana son daukan hankali, bana son rigima a wajen da bai dace ba!"

Sultan SHAHEED ya yi shiru kansa a kasa....., gaba daya ya rasa me ma zai ce, gaba daya so yake yi su basu dama ya dauki Beebah da kansa yanzu su je asibitin nan da gwaje gwajen nata a yi mata bayani ko zata daina rigimar nan, kwarai yana so ta bashi hakuri a kan batun nan Ama da ta yi yanzu sai da ya ji ya shiga hakinta......, tana da damar ji da kanta daga bakin likitar mana, yaya aka yi ya kasa saurarawa ne idan ya so sai yayi fushin da huja?????

"SON?" ABA ya fada a tausashe

A hankali ya dago idannuwansa ya sauke a fuskar Aba

Aba ya ce" ka tashi ka zauna"

Mikewar yayi a hankali ya zauna saman kujerar

A tausashe Aba ya ce" Sai fa kunna hakuri ku duka, in sha Allah wannan rigimar Nine nan zan kawo karshen ta, in banda abinku ku duka ai ba wani matsala a nan sai rashin fahimtar junna, ke kuwa Najeeba in banda rigima ai kin san babu wanda zai zubar maki da ciki, haka Allah ya hukunta kennan sai ku na junna lafiya ku yi hakuri ......., "

NAJEEBA dai a ranta ayanawa take yi kamar haka' Na rantse da wanda raina yake hannunsa sai na san abinda yake faruwa...., kuma ba zan taba kyale mai hannu a cikin wannan abin ba, aure kuwa ko? Idan yana so ya dauko biyu shi ta shafa!"

Aba yayi murmushi ya ce" Wacece zaka aura Son???"

SHAHEED ya Dube shi, sai kuma ya dan dubi Anmy da ta tabe baki

A hankali ya ce" DOCTER IZRANE din ce!"

Yadda ka san an gaurawa mutanen???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? falon mari haka du suka Dube shi du irin yadda suke kiyaye idannuwansu da yi masa kallon tsaf

NAJEEBA ta Dube shi har sau biyu ta gane eh abinda ya fada kenan.

Anmy da matsanancin mamaki zata yi magana NAJEEBA ta mike tana dubansa ta ce" SHAHEED!, kana nufin wace nake tunanin ta min kagen zubar da ciki ce zaka aura? Kana nufin matar da take kula da prvt prt dinmu har ta amshi haihuwar Nadiya ce zaka aura?, SHAHEED kana nufin likitar nan dama itace zaka aura??????"

SHAHEED ya zuba mata ido, na dan lokaci kafin ya dauke idannuwansa

Bayan ya dauke kansa ya ki bata amsa hakan ya sa ta sake zuba masa ido kafin ta juya da nufin tafiya

Yaya Dayabu ya mike da sauri ya bi bayanta ya ce" Ke Najeeba, me yasa ba zaki iya kawar da kai ki yi hakuri ki bari a daidaita komai bane?????"

NAJEEBA ta juyo, idanuwanta sun dau ja ta nuno masa hannu ta ce" A daidaita komai? Wallahi babu abinda zai daidaitu a lamarin nan!, ok....shine maganar da yayi cewar zan sa a dauko ta saboda kishina? .........daga wajen ta maganar zubewar cikina ta fito?????,.... Yaya Dayabu sai na ja Shari'a da IZRANE, sannan duk wanda ya yarda ya shiga tsakani sai na ja da shi, ciki kuwa koda SHAHEED ne......... , aure kuwa idan akoy igiya dubu a kula masa ita........ Ita take mararin hakan, Ni kam , Ni Najeeba MUTALAB na yafe SHAHEED wa Nadiya da IZRANE!"


daga haka ta yi ciki da mugun gudu ta fada dakinsu ta datse da ky ta karasa wajen wayarta ta zauna bakin gado ta dauko ta dana kira........





Alhamdulilah, mun rufe Free page.....zamu shiga labari gadan gadan, Allah ya bamu ikon gama shi lafiya


Domin samun naki hajiyata ki tuntubeni saman layina kamar haka 93811618............ Mage return
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati na airtel ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




16




Ana daga kiran NAJEEBA ta ce" Ki duba min abinda gareni a banki, ki aiko min da msg din a whatsup!"

Daga haka ta katse kiran ta mike tsaye ta je wajen madubi ta tsaya........

Lokaci daya ta shiga kallon kanta tun daga kan gashin kanta har zuwa faratunan kafarta

A hankali ta juya ta cire hijabin kanta ta cire doguwar rigar jikinta ta nufi bayi ba tare da ta iya cewa komai ba......hasalima tana shiga ta riga darzar fatar jikinta da sabulu ta kunnawa jikinta ruwa na dukan gashin kanta da jikinta.......


Yaya Dayabu a sanyaye ya dawo falon ya tarar da aba sai fada yake yi kamar ya ari baki

A hankali ya salale jikinsa na sake daukan sanyi na tashin hankalin nan kunnayensa na jiyo maganar Abansu yana fadin" An isa a hana namiji aure ne? Ko kuwa wani hali aka santa da shi da za'a Hanna shi aurenta? Babu mai Hanna shi aurenta, in dai na yi bincikena na gano bata da wata matsalar da zata sa a ki hada zuri'a da ita, sai ki maida hankali ki ci gaba da daga masa hankali kin dai san cewa abubuwan dake kansa basa son haduwa da fushin ki saboda kin san fushin ki ya fi komai daga masa hankali"

Ya juyo rai bace ya dubi yaya Dayabu ya ce" Kai, tashi ka tafi da matarka, ku kuwa ku mike mu je safiya na yi kowace zata koma dakin ta, bana son shashanci!"

Kusan kowace nema take ta fita a hayacinta cikin yan uwan, a lokacin da suke neman taimako wajen ummi sai ta dauke kai, anmy kuwa yaya MUTALAB ya Hanna ta magana

A hankali SHAHEED ya dubi yaya MUTALAB, a hankali ya furta" A yi hakuri aba, a bar su a wajen beeb........a bar su a wajen ta....., hankalinta ne a tashe...sannan a yi mata uzuri in sha Allah zata sauko"

Aba MUTALAB ya Dube shi, sai kawai ya kada kai ya fice dan kuwa shi gaba daya gani yake ai kamar ana so ne a nuna neman auren da wani laifi a ciki, bayan ba wani laifi, yanzu fa sai su ce saboda itace likitar matan ba zai aureta ba, kai mata akoy shirme

Umi da jikinta ke mace murus ta dubi anmy a sanyaye ta ce" Zan tafi y'ar uwata....., ki yi hakuri dan Allah, ko me yake faruwa zai wuce, mu bi su da addu'a Allah ya zaba musu abinda ya fi zama alkhairi, ki yi hakuri da fadan da na yiwa y'arki, bana so ta mayar da allura galma ne"

Anmy idannuwa kawai ta lumshe mata, a hankali ta ce" Ki kula da kanki, ki tabbatar mijinki ya yi abinda yace a kan lamarin yarinyata "

Ummi baba ta gyada kai sannan ta dubi SHAHEED ta karasa daf da shi ta kamo hannunsa a tausashe ta ce" ka yi hakuri da abinda ta fada , hankalinta ne a tashe...., na tabbata idan har ka bata dama docter ta yi mata bayanin komai ta fahimta Shikenan, komai zai wuce"

A hankali ya lumshe idannuwansa, kirjinsa ya gama cinkushewa, zuciyarsa ta gama lalacewa da radadi da rudani.....

Yaya za'a yi ta gane cewa yarinyar da ake maganar sai dazu aka isar musu da maganar auren nata da bada umarnin kilacewa daga fada? Yaya za'a yi ta gane ta kuma yarda cewar tun kafin ta san da maganar auren ta fada masa maganar dalilin lalacewar cikin?, wai yaya za'a yi ta yarda cewar dan ya auri yarinyar nan ba zai taba taba mutuncinta ba?????, haka kawai shi da ya dira kan zai auro mai sonsa, har yake ikirarin sai me dan ta ki yin abinda yace, sai gashi daga tambayar da ta masa ta tafi zuciyarsa na inda take??????....... Ya Allah.

A hankali umi ta ce" Ka huta lafiya"

SHAHEED ya gyada kansa yana dubanta har ta juya ta fice

Yaya Dayabu jiki ba karfi ya karaso ya duka kasa kasa ya ce" Ka yi hakuri broth"

SHAHEED yayi dan murmushi" a hankali ya furta" tk Care"

Yaya Dayabu ya gyada kai ya mike ...........ya karasa gaban Anmy, a hankali ya riko hannunta a tausashe ya ce" Anmy, zan sanarwa aba ya bari, gobe zan koma asibitin, idan na samu abinda ya dace din zan kawo DOCTER ta yi maki bayanin da kike so, dan Allah ki kwontar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login