Showing 75001 words to 78000 words out of 144591 words

Chapter 26 - MAGE MAI KWANCIYAR DAUKAR RAI BOOK 2 COMPLT BY SAJIDAH NIJAR.doc

26 Feb 2026

2357

tace ba zai yiwu ya ringa shiryawa bata ganni da kyau ba...........

Wani irin zafi yake ji a cikin zuciyarsa na irin yadda ta fito, da irin yadda ta iya budar baki ta hana a hora masa wanda ya aikata laifi mai muni......

Rawaninsa ya cire ya cire Babar rigar ya karasa saman kujera ya zauna yana cije lebensa.....
Yau da ace wannan dan duniyan bai samu yafiya daga wace ta isa ba, da shine zai zane masa jiki har sai ya fasa masa fata ta yadda gobe ko an tube matar wani a gabansa akace yayi furucin zumunci da ita ba zai yi ba......, shi Najeeba zata wulakanta kuma ta nuna ita aka cuta? Me yayi mata? Shine ya dace ace ta nema ta rarasa, Ama kawai dan yace zai yi aure har ta iya budar baki tace ba zata yi kishin mijin Nadiya ba? Why ake so lalle lalle sai an kai shi inda baya son zuwa???????

Mikewa yayi ya cire wandon nan ya dauko na sport ya saka, ya ciro takalman gudu da rigar gudu duka ya saka ya dauki airpc dinsa ya makala ya dora hular samari ya boye gaban goshinsa ya zamo sajensa kawai ake gani......sannan ya fice a falonsa baba ya nufi karamin falon kafin ya bude kicin ya bi ta nan ya fice ta baya inda dawakansa suke ya dauki motarsa ta sports ya fice a gidan gaba daya ya nufi filin buga kwallo wanda ake biya kafin a shiga a buga kwallon dan ya tabbata idan ya ci gaba da zama a gidan nan komai na iya faruwa...........


Nadiya

Tunda ta shigo falonta ta zube a falon tana saka na makokin da ya sa auntynta sakin kwalbar jus din da ta dibo ta nufota da gudu hannaye saman kai ta ce" Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, Nadiya, Nadiya.........lafiya ?"

Nadiya na kukan nan ta rike hannun AUNTYNta ta ce" Aunty, ashe wannan anobar ce ta kai karar mu? Aunty ashe itace ta haWa zaman? Shikenan mun shiga uku, ita Najeeba baiwar Allah batama yi laifin ba ta sakata a ciki, Ni kuma wai wayar nan da na yi mata ne ta kai karana? Aunty hankalina ba ?aramin tashi yayi ba, na zata Shikenan sakina zai yi ya huta da iskancina "

Auntynta ta bige mata baki tana fadin" Kisa kika yi ko kwartanci? Ke dan Allah tashi mu je, wuce mu je dakinki "

Kamata ta yi ta cicibata suka mike suka nufi dakin ta

Sunna shiga ta dubeta ta ce" wai me ya faru ne? Yanzu haka kika fito rigija rigija kamar zaki zube da katon kai ana kallon ki? Baki san wadinnan hadiman naki sunna iya kaiwa kishiyarki labarin ki na? Ke me yasa Bakya tunani ne? Haba dan Allah nadiya fada min abinda ya faru "


Nadiya ta girgiza kai tana duban ta ta ce" Aunty, ai yanzu masifa ta tunkaro mu Ni da najeeba sai yadda Allah yayi da mu, wannan lokitar tsinaniya ce sak, saboda har NAJEEBAN bata bari ba da Shari, dan dai Ni ba Shari ta min ba, kiran nan da nace muku na mata na zazageta ne ta fadawa mama ma? To saboda shi, kawai saboda wannan dan laifin ne ta kawo iyayenta aka titsiyemu, baki ga Najeeba ba baiwar Allah harda ita, Duda ta wulakantani ta ki saka baki ta nuna ba zata yi zagi ba Ama ta mata Shari babu ita a laifin nan"

Auntynta da takaici ta katse ta ta ce" Ita me akace ta yi??"

Nadiya ta zayane mata komai

Auntynta ta dubeta ta ce" ba dai da aka tambayeki ko kin yi ba cewa kika yi kin yi? In jin musawa kika yi, baki yarda cewar kin yi kiran ba?"
>?????????????????????????????????
(Mai KWONCIYAR ?AUKAN RAI 2)

na
SAJIDA Nijar


Paid book ne,
Normal grup 500
Yan Nijar
Normal grup 500
Account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar biyan ta numbana kamar haka +22793811618
Yan Nijar idan ka sayi kati ka kankare sai ka turo min ta numbana kamar haka 93811618

Na gode mutanena




25





Nadiya ta dubeta da mamakin ta, ta ce" Wai in ce ban yi me ba"

Aunty ta ce" Ki ce ba ki yi kiranta ba"

Nadiya ta girgiza kai ta ce" kai, ina, ai Aunty cewa na yi eh na yi, tsabar kishi ne ya sa na yi kuma ko gobe sai na zageta ita matsayaciya"

Hannaye auntyn ta dora saman kai ta sauko kasa daga saman gadon tana hailala ta zubawa nadiya ido

Bacin rai ya tuketa ta mike tsaye tana nunata ta ce " Ke kam baki da wata hanyar kwatar kanki? Du girman ki ya tare a jiki? Sai gabonci da shirme? Zaman auren mu zamu maki ne?, innalilahi yanzu haka kika bude baki kika fada? To Ni Ko rantsewa na yi kishiyarki ta aikata aikin nan da tace ba ita ta aikata ba, ke yanzu baki ji wani iri ba da kika maimaita min maganganun nan?, to bari in tafi gida saboda in har na kwana a gidan na zuciyata zata buga, zan je in samu mamanki mu zage dantse mu miki nema na kirki wanda zai sa ki samu furkar mijinki duk rintsi, saboda a haka wallahi bana tunanin za'a wanye lafiya, na tabbata idan ta shigo hadaki zasu yi su yi watsi da ke karshema daya ta tafka laifin da zata tsunduma ki ciki tsundum ki amsa da karfin Muryar ke kika yi tunda shashasha ce ke, an gaya maki haka ake zama da kishiya ne? Tir da wannan halin naki, ke iya ruwa fida kai fa, babu wanda kika fi tsoron Allah in gaya miki gaskiya, kawai shirme kika fi su da batar da baka, sai an jima saura ki bude Muryar ki yi ta boda har kowa ya gama sannin ke din sakarya ce kawai!"

Daga haka Aunty ta fice a dakin, dan ji take yi kamar ta rufe nadiya da dukan tsiya wanda zai fidata a hayacinta , gwara ta bar mata gidan kar ta yi aikin da za'a rufeta .


.....................Lauya da Hajiya Turai

Tunda aka fitar da Lauya ya zo wucewa Sarkin bulala ya masa alamu da hannunsa mai nunin sai ya yanka shi ya sake tarewa , ya je kusan motarsa ya tsaya jikinsa bai daina rawa ba yana cin alwashi kala kala a zuciyarsa

Daga inda yake ya ga fitowar Hajiya, sai dai ta ki karasowa inda yake ta tsaya daga nan har sai da su IZRANE suka fito sannan suka karaso tare da iyayen IZRANE din

Bai tsaya wata wata ba ya sha wuyan Hajiya ya ringa tafka mata mari da kyar iyayen su IZRANE suka shiga tsakaninsu........... Suka kwace ta tana rusa kuka

Shima yana cira yana ihu yace" Ku barni in ilatata muguwa yar daba marar mutunci, yau dauke dauken maganar naki nan ya kawo Ni aka zane Ni? Na sake ki Turai na sake ki, yau baki isa ki kwan a gidana ba!"

IZRANE ta zarro ido tana Wora hannaye a saman kanta, sai dai ga mamakinta Hajiya dake rizgar kuka ta dubeshi ta ce" In ka isa Allah tsinen, Kai din banza ka sakeni? Ai in me na yi maka haka zaka zauna da Ni, barima ka ga sai na rigayeka komawa gidan!"

Da sauri ta fice ta dauki hanya dan kuwa adaidaita sahu zata shiga ta je gidan..

Gaba daya da ido suka bita, kafin lauya ya juyo yana duban baban IZRANE ya ce" Elhaji saki uku ai ya raba komai ko?"

Baban izrane ya gaza cewa komai, saboda abin ya girmami tunaninsa, yanzu a wannan halin izrane ta saka su? Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une

Ya dubi IZRANE ya ce" Ke kuma tunda alkhairi ya nufo ki kika hada kayan ki da mutanen nan kin shiga uku, dan kuwa ita da kanta bata san kanta bale ke ta koya maki sanin kanki, Wada kuke neman yin fada da ita kuwa ta fi karfinku dan kuwa ko Ni sai na tsaya mata bale tana da masu tsaya mata!"

Daga haka ya shige motarsa ya fice yana yiwa kansa alkawarin yau sai ya gigita hajiya Turai


Mahaifin IZRANE ya sake duban ta, a lokacin da ta bude musu mota dan su shiga su tafi gida

Kai ya girgiza ya ce" Allah ya shirye ki, ban taba sanin cewa lamarinki ya kai haka ba sai yau, tabas IZRANE a yanzu a tsorace nake da ke, kuma dukan wani abin da ake fada a kanki ina mai tabbatar maki a yanzu na yarda dari bisa dari, Allah ya baki sa'ar abinda kika sa a gaba ya shiryeki "

Daga haka ya dubi abokinsa makocinsa ya ce" Elhaji ka ga inda haihuwa ta kawo mu yau ko?, dan Allah ka yi hakuri da irin abinda yarinyar nan ta janyo mana, ka ga yau haihuwa zata sa a yi tunanin mutanen banza ne mu, da darajar mu da komai yarinya ta zubar mana? Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une"

Elhaji ya kama hannunsa saboda irin yadda yake huci na abin rashin lafiya ya ce" Ka ga, ka yi hakuri ka ji? Kar ka saka abin nan a ranka, komai yayi zafi maganinsa Allah, ina fatan daga wannan zata kiyaye, ke IZRANE shige mu je, daga yau Nine da kaina zan saka ido a kanki in sha Allah, ke da ya dace ace zuwa yanzu kina tausayin mahaifinki? Haba IZRANE "

Izrane dai kanta a kasa har suka shige ta shiga ta tayar da motar itama ta dauki hanya

Du ba zasu gane ba, ita fa a halin da take ciki ta fi kowa firgici da tashin hankali saboda irin tashin hankalin da ta gani a yau

Zata iya rantsewa cewar wannan matar ce ta tardata ko dan kalaman da ta fada da maganar ciki, innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, bayan tabbatar mata da ta yi ta san ita ta zubar mata da cikinta kuma ta nada mata duka ta yi tafiyarta yanzu kuma ta yi kamar ba ita ba? Anya kuwa zata iya wannan fitinar? Tabas NAJEEBA *MAGE CE, MAI KWONCIYAR ?AUKAN RAI*

A lokacin da Hajiya Turai ta karaso gidanta ta shigo rai bace ta samu ?a?anta baje sun kunna kida sunna shan rawa , dakin kuwa kaca kaca harda breziya a saman kujerar a yade ga warin abincin da suka ci, ga abincin nan zube komai dai a hargitse kamar mahaukata ne aka bari a gidan ba masu hankali ba, ko kuma kamar dabbobi ne suka zauna a wajen ba mutane ba

Rai bace ta shiga zage zage tana tambayar abinda suke yi a gidan haka????? Kasancewar tana so idan babansu ya zo ta samu kansa tana fadan tana tatarewa sannan ta kwala kiran sunnan kurma tana fadin" Kina gidan uban wa wai da ba zaki fito ki gyara gidan nan ba tunda sun ci abinci sun gama?, ke kurma?"

Babar yarta dake chating ta tabe baki ta ce" Mama wai meye haka dan Allah daga dawowarki kin fada kowa da tashin hankali? Kurma fa tana daki kwonce bata da lafiya Jiya fa an mareta cikin abin nan, kuma da IZRANE ta farka ta sake kwada mata kwano dan kawai tace bata san inda wayarta take ba, yau fa ko girki bata yi ba oder na mana"

Uwar ta yi turus tana kallon ta , da haushi haushi ta nufi dakin da kurma take ta bude ta shige, bata tsaya wata wata ba ta shiga jibgawa kurma dundu tana fadin" Dan ubanki dan ki kwonta ki sha panka na dauke ki aiki? , uban waye ba'a daka ba a gidan nan? Nace uban waye bai samu nasa dukan ba da zaki langwabe min a daki har saman katifa ki wani rufa? Tashi tashi idan har ba zaki iya yin aikin ba ko wuce gidanku a daren nan sai kin bar min gidana!"

Gaba daya kurma maganar take ji har cikin kwonyarta, jikinta kuwa banda rawa babu abinda yake yi, zafin da ya dauka kuwa har ya nemi wuce misali domin daf take da fadawa duniyar zabura saboda zafin masasara.

Tana ihu tana neman inda zata gudu Hajiya na dukanta har filin gidan

A lokacin da ta bude gidan zata hankada kurma lauya ya dano kai , domin a kofa ma ya bar motarsa saboda gudun kar ta fashe masa madubi, domin idan sunna fada in ya daki fatar jikinta motarsa take duka, shi yasa ya bar motar nesa da gida ya karaso kar abin ya masa yawa

Gefe ya koma tana tura kurma ya shakota shima ya hau jibga.....

Wannan abu da kurma ta gani ya idasa fitar da ita a hayacinta ta yanki hanya ta ringa gudu kamar zata tashi sama ta dauki hanyar gidan su, gidan nasu da yake da nisan gaske da gidan su Hajiyar, shi yasa ma take kwana a gidan hajiyar sai weekend take lekawa gidansu saboda Hajiya bata bata kudin abin hawa, idan tace a kafa zata ringa jigilar zuwa da dawowa gidan aikinta da gidansu wahala zata sha sosai dan aikin gidan Hajiya ya fi karfin ta gama shan shi, kuma ta dau doguwar hanyar nan.

Gudu take yi har ta shanyo kwanar gidansu, tana saka kafa a gidan tana haki ta yanke jiki ta fadi tamkar numfashinta zai tsaya

Hankalin mutanen gidansu kaf sai da ya tashi, mahaifiyarta ce kawai ta iya kamata hankali tashe ta jata kasan rumfa inda mahaifinta ke kwonce ba lafiya ta jinginar da ita, irin yadda jikinta ke rawa kuwa kamar ta ga abinda ya girmami idanuwanta ne

Mahaifiyarta hankali tashe ta shiga tambayarta lafiya? Hakama kanwarta da kanninta saboda itace baba a gidansu dama, mahaifinta accident yayi , dalilin kwonciyarsa kenan, kusan shekara biyar kenan wannan dalilin ne yasa karatunta ya ragaice harma aka sama mata aikin aikatau dan ta taimakawa mahaifiyarta da wahalhalun yau da gobe na rayuwa

Fita uwar ta yi ta duba ko ina ta dawo tana janyo kyauran gidan ta sarkafe da kyar ta dawo ta zauna tana ganin irin yadda kurma ta kafa ruwa a baki tana sha kamar ta samu zuma

A hankali ta zauna cike da tausayinta ta ce" Daga ina kike? Me ya sameki? Wa ya biyo ki da daren nan?"

Kurma ta fashe da kuka ta bude baki itama sama sama ta ce" Ina, kasheni Hajiya zata yi dan ban yi aiki ba, bani da lafiya shine ta kama dukana tace sai ta kasheni ko in bar mata gidanta, ina kasheni zata yi idan na koma, wayo kunena"

Inar ta kama gefen kunnen, wajen ya sundume sosai inda IZRANE ta tafka mata kwano ne, saboda dukan da ta sha mari ne kawai a wajen yan daban nan, kwanon da IZRANE ta maka mata ne ya da gefen kuncin har cikin kunnen durar ruwa da Waukan ciwo.

A tsorace inarta ta ce" Innalilahi, duka dukan nan itace ta maki dan baki yi aikin ba?"

Kurma ta girgiza kai ta daga Muryar itama ta ce" Ba ita bace, likita ce, likitar nan ce da take zuwa wajen ta, likitar nan ce da ta zubar da cikin matar Sarki itace, itace ina itace"

Mahaifinta dake kallonsu daga kwonce ya zaro ido gabansa na faduwa,

Innarta ta kaleta a tsorace ta Wan daga murya saboda yanzu ta fara tsoron daga Muryar sosai dan kar aje a ji abinda suke fadi su shiga uku, ta ce" Ke, kin san me kike fadi kuwa? Ko dukan ya taba maki hankalinki ne ? Subhanalahi"

Kurma ta girgiza kai
Ta ce" Ban haukace na, ina sane da ranar da tace yanzu ta zubar da cikin Gimbiya mai baban daki , itace ta fada itace da bakinta "

Da hannunsa ya yafito kurma yana zaro ido, ta duko yadda suke yi idan zai musu magana saboda shi baya iya yin ihun nan

A hankali ya ce" waye ya zubar da cikin na Gimbiya ? Ke yaushe kika ji? Kuma waye ya ji miki raunin nan? Me kika masa?"

Kurma ta koma zaune tana tare gefen kanta da ciwo ke yi mata mugun radadi ta shiga ratafo musu abinda ya faru har zuwa Yanzu korotan da Hajiya Turai ta yi

Mahaifinta ya rintse idannuwansa hawaye na zubowa ta gefen idannuwan nasa, da hannu ya yafito mahaifiyarsu

Cen kurya ya ce" Kina da goma a amso mata maganin zafin ciwo ta sha?

Kai ta gyada ta mike ta shige dakin ta ta dauko gomar ta fito ta ba kanin kurma ta aika shi wajen mai tebur

Mahaifinsu yayi umarnin kurma ta je daki ta kwonta cikin sangen mamansu da su
Bayan ta shige da kanwarta sun shige kanwar Tata sai sanu take yi mata ya dubi mamansu hankalinsa a kan lamarin nan ya ce" Allah ya saka mata"

Maman su ta amsa da amen, suka yi shiru na dan lokaci ya sake budar bakinsa ya ce" Ta zubar da cikin mai baban daki?, me ya haWa su?"

Mahaifiyar kurma ta girgiza kai ta ce " Abin da mamaki sosai, anya kuwa ta gane? Ka ga fa bata ji da kyau yaya za'a yi ace ta jiyo maganar nan?"

Mahaifin kurma ya ce" Dan ji kam tana ji, tunda har take jin maganata, abinda ya fi damuna kar aje su biyo bayanta, kin ga idan sun san tana da wannan sirin ba zasu bar mana ita ba, mu da kanmu a hatsari muke dan mutanen nan babu abinda ba zasu iya yi ba, "

Hankalin maman kurma ya tashi, tana dubansa ta ce" Yanzu yaya zamu yi? Guduwa zamu yi ko me?"

"Ku gudu ku je ina?, waye zai amshe ki da ya'ya? Da ace su Gogo da rai ne sai ku nausa daji , Ama a haka ina kike ganin zaku iya shiga ba'a kama ku ba?" Ya fada shima hankalinsa na kara tashi

Jikin ina ya dauki rawa har lokacin da yaronta ya shigo sai da ta ji kamar zata suma dan tsoro saboda sai da ta firgita , gannin shine kuwa sai da ta sauke wata wawuyar ajiyar zuciya

Nan da nan ta fara hawaye tana fadin" Yaya zamu yi? Na shiga uku yaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login