Showing 237001 words to 240000 words out of 253142 words

Chapter 80 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18394

mahaifinsu.

"Ni gaskiya ya min tsufa ga mata ga yara, ni ba ta siyasar ko kudinsa nake ba"

"Matsalata da ke baki iya daukar shawara ba, ga kuma rashin hangen nesa, ai ko dan ki bawa Aliyun da uwarsa haush da ma matar ya kamata ki aure shi, kullum su yi ta ganinki gaban tv komai za'ayi sai da ke, idan kika yi hakuri ma kina gidan sai ya sake su ki koma ke kadai sai yayan da za ki haifa, ke yanzu ni ban isheki ishara ba? Yau ina Baraka ina Yayanta suke? Sai dai idan ubansu yayi marmarin ganinsu ya je ya gansu ko ya aika musu da sako, ni ko ganinsu ma bana jin yana zuwa yi, domin ko jiya da na masa maganarta cewa yayi na daina tuna masa da ita, na ce ranka ya dade ai dole na tuna maka saboda akwai yaya a tsakanin sai ya ce yara idan suka so ganinsa sun san inda yake ai, shi dai hakkin dake tsakaninsa da su ya kula da cinsu shansu da kuma sauran hidindimun rayuwa, ke har cewa yayi ba dan kar dawowar nan ya zama matsala a gareni da su ba sai ya karbe yaransa sun dawo nan, ni kuwa na yi karaf na ce a'a ya bar mata yaranta ta rike, toh ina zan iya da rikon balagagun yaya?"


Tana magana tana tsire baki dadin ya isheta, yanzu Mama Baraka da yayanta basa gidan. Ta shafa kanta yarta.

" Shiyasa nake son ki fitar da miji ki yi aurenki ki manta da wani Ali, daman can ba ku dace da juna ba, balle kuma yanzu da ya auri shegiya, kuma yar Baraka, ko dan ke na san dole ta aura masa ita, kuma abun kamar ba na banza ba, kin san lamarin yarbawa fa, in ba shi ba yaushe Aliyu zai auri shegiya? Ko da tana da kyau ai Asali wani abu ne mai girma, ko dan yayan mutum"

"Daman ita ta lalata komai gurinta nake tafiya neman shawara lokacin da muna samun tsabani kuma ba ta ba ni shawarar kwarai har cewa take ba laifin yarinyar ba ne, ashe saboda ta san yarta ce"

"Eh mana, dan Allah ki bawa maraWa kunya, ki zabi mijinki ki yi aurenki ga ki tsaye da kyau zaune da kyau son kowa kin wanda ya rasa, idan ma ba ki som shi His Excellency ki zaba cikin masu son ki mana, daman Alhaji yace tun da yayi maganar be sake ba, be zama lallai sai shi ba, ki zaba wanda kike so ki ba shi dama idan vaki bada daman ba baza ki iya kawar da tunani da damuwa a ranki ba, amman fa karki dauko Wan makiyinmu kuma, karki mana na Aliyu, yanzu kam ba za mu bari ba ma"

Ta kwnatar da kanta a cinyar mahaifiyarta.

"Ki taya ni da addu'a Hajiya Allah ya sauya abun da nake ji a zuciyata kuma ya zaba min inda zan samu kwanciyar hankali da zaman lafiya, duk masu mata ne, samarin sun ki zuwa wai ko dai dan na yi aure ne?"

"Aa ina ruwan aure da samarin, ke yanzu baki san an fi son zaurawan ba? Kuma saurayin zai iya zuwa, amman dai mun fi son mai kunbar susa, kin san logi be kin dadi, ba mu ki ace surukanmu duk manyan mutane ne ba, su kuma samari nan wasu ba rikon aure ba wasu kansu babu komai ciki sai tunanin abubuwan da ba su za su gina gobensu ba, kadan kake samu na kwarai, yanzu ba ga Aliyu ba? Amman da ace wanda ya san ciwon kansa kika aura inda ba shegen zamani ba ne, babu ruwansa da wani hango wata sai hada hadar kudi, ina za su shigo ina suka fita, daman duk abun da iyaye ba so babu albarka a cikinsa, shiyasa Aliyu ya zama haka"

Hausawa suka ce wanda ya cika da ya?i ya mallakeka har ?a?anka, babu yadda Kameela iya bayan bin shawarar mahaifiyarta da yan'uwanta matukar tana son zama lafiya da su, kuma ta shirya samawa zuciyarta salama. Abun babu dadi kam amman dole ta daure a haka ta budewa masu kwankwaso kofarta dama, ko labarin zai sauya. Tun da wadanda take dakon zuwa sun manta hanya, wato marar mata da yaya ko kuma saurayi, har yau bata samu ko daya ba, masu matan ne dai suke ta kawo mata hari, daga mai daya, sai biyu har da mai uku yana nema ta hudu da ita tsabar sun raina mata wayo.
[8/31, 11:54/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: *

*? Khadeeja Candy*



Page 7?? 4??


>?X?  Abinci na gargajiya, WanWano na musamman, jin daWin iyali! >?X?

Idan kina/kanason abinci mai WanWano na musamman wanda zai tunatar da kai daWin gargajiya, to babu kamar Taliyar Hausa  Yar Murji!
Wannan taliya ba wai kawai abinci bace, al ada ce mai haWa iyali, ?auna da jin daWi a teburin gida.

(' Me yasa za ka zaSi Taliyar Hausa  Yar Murji?
" ' An yi ta da tsafta da inganci
" ' Ta dace da kowanne irin miya: miya mai ?wai, miya taushe, ko miya mai ?yau?yau
" ' Sau?in dafawa  cikin mintuna ka samu abinci mai gamsarwa
" ' Lafiyayye, mai sau?in narkewa, kuma ya dace ga kowa cikin gida
" ' Za ka iya amfani da ita wajen girki na yau da kullum ko kuma na musamman

=??? Muna a Kaduna  amma WanWanonmu ya zarce iyaka!
=??? Ana kawo muku duk inda kuke a Najeriya (delivery guaranteed).

=??? Idan kana son jin daWin abinci na gida wanda ke haWa zuciya da iyali, to ka gwada Taliyar Hausa  Yar Murji yau!

=??? wa.me/+2347071821482 tuntube mu yanzu domin yin odar ku.
=?I? Ka more WanWanon gargajiya mai tsafta, mai daWi, mai Worewa!



"Okay bari idan na duba zan miki magana"

Ya amsa sannan ya kashe wayar ya aje sannan ya dauki comb din yana gyara mata gashi, suna zaune a falo, shi kan kujera ita kuma tana kan kasa.

"Daga gurin aiki ne"

Ta dago ta kanta ta kalleshi.

"Ban tambaya ba ai, Aliyu i trust you, kullum aka kira idan agabana sai ka ce min ga wanda ya kira, ina son ka san kai ka aje ni ba ni na aje ka, kuma kana aiki dole mu'amala zata hadaka da wasu wani lokacin, dole na yi hakuri, kuma kana da yancin haka, matukar be tsabawa addini ba kamar yadda kake yawan fada, kuma be tsabawa zamantakewarmu ba, ba zai kawo matsala ba, ni na yarda da kai, na san wa na aura"

Ya ja hancinsa yana murmushi kadan.

"Kin ance hadarin da ya baka kashi, gobe idan ka gan shi gudu kake, na dan shiga damuwa ne, saboda irin haka, kuma ya haifar da matsala kala kala a zamantakewata ta baya, na yi iya yadda zan iya wajen ganin ba a samu matsala ba amman hakan be samu ba, kuma ba a raba mata da kishi dole za ku yi kishi ai, kawai dai ba a son ya wuce gona da iri ne saboda yana haifar da matsala, ko ga matar ko ga miji ko kuma duka"

"But don't get mad at me idan na yi kishi"

Ta fada a shagwabe tana turo baki. Yayi murmushi ya saka hannayensa ya dagota

"Come here"

Ta daga ta koma saman jikinsa ya rumgumeta irin yadda ake ma yara har ya dan girgiza ta a hankali.

"Thank you for trusting me, i love you Qalbin, ba zan ji haushi ba idan kin yi kishi, ke ma ina hango kishi a idonki, amman ki iya rike shi ki yi controlling dinsa kar ya cutar da ke"

Ta lafe a jikinsa tana ta zuba shagwaba. Ya cigaba da shata mata kan a haka ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?tana masa raki har da kuka wai da zafi.

"Shiyasa ai nake miki a gida, ba zan yarda kina tafiya shagon gyaran gashi ana kalle min kaya kuma jansa da karfi ana wahalar min da mata ba"

Ta kai hannunta tana taba chin dinsa zuwa wuya.

"Babe..."

"Mhn"

"Ina son na yi ma Dr A-B maganar tafiya gurin baban shi ina son na gan shi na ji yayi shiru be sake min maganar ba"

"Lallai kuma ya kamata ya hadaku ko a waya, kuma ina son idan kin samu time ki tafi ki gurin Ammy ki bincika Fatima ko lafiya"

Ta kara daga kai ta kalleshi.

"Ba matsala?"

"Bana jin wata matsala to matsalar me? Ni da na rike na mallake ki na malleke zuciyarki, na san kin damu ki san halin da take ciki ai, kina da aurena yanzu idan ma Turhan yana gidan dole ya daga miki kafa, balle na san ba ya nan, kuma ba ni da hujjar hana ki ziyarta su tun da Fatima ta shiga tsakani, kawai dai abun da ba zan yarda ba shi ne ki shiga ki dade ko ki wuni, ni zan kaiki na jira ki gama abun da za ki yi na dawo da ke"

"Na damu sosai na san halin da take ciki"

"Na sani, ina karantar damuwarki ko ba ki fada min ba, ya kamata ace ko sau daya ne ta zo gidan nan ai"

"Za mu iya tafiya gobe?"

"Mu tafi anjima da dare"

"Da gaske?"

Ya kai mata rankwashi a kai.

"Ina miki karya ne?"

Ta dafe kan

"Da zafi fa"

Ya kara mata wani, da ta ga zai kara mata na uku sai ta sauka jikinsa da sauri ta dauki fillon kujera ta jefeshi da shi.

"Zan kama ki ne ai"

Ta masa gwalo ta gudu. Bayan Sallah isha'i ta shirya, Aliyu ya sakata mota suka dauki hanyar gidan Ammy. A waje ya faka ta bude zata fita sai ya sumbanci hannunta dake cikin nasa.

"Ko da Ammy ta fada miki wata magana marar dadi karki ce za ki yi fada da ita a gaban Fatima"

"Okay"

Ya sake mata hannun ta fita ta rufe motar, sannan ta kwankwasa gate din gidan aka bude mata.

"Ammy na ciki?"

"Eh tana nan"

Emily ta shiga tana sayen da hijabinta na islamiya da ya kai mata har kasa, cike da zumudin son ganin Fatima ta kwankwasa kofar falon, aka bude mata ta shiga. Da sallama yan matan da suke nan suka amsa mata bata zauna ba sai da ta tambaya ko Ammy na nan aka ce mata eh tana nan, sannan ta zauna zaman jiran fitowarta. Ammy ta dade sosai kamin ta fito falon ta zauna fuska ba yabo ba fallasa ta zauna tana kallon Emily dake gaisheta.

"Lafiya kalau"

Emily ta dan yi shiru na lokaci kamin ta ce

"Daman kwana biyu ban ga Fatima ba, shi ne na zo na dubata"

"Fatima kuma? Ba Turhan ya fada miki zai tafi da ita ba? Ai Fatima bata gidan nan tana gurin Babanta"

"Gurin Babanta kuma? Ya fada min amman ban ce masa na amince ba, kuma ko bankwana bata zo yi min ba"

"Bankwana me ko? Ba an kai miki ita kun yi biki ba?"

Idon Emily ya cika da hawaye.

"Amman sai a dauke ta a tafi da ita ba tare da an fada min ba, kamar na ni na haife ta? Wannan wane irin abu ne haka? Yarinya karama a dauke ta a kaita gurin larabawan da basa son kowa idan ba jinsu su ba? Kun zalince ta kun zalince ni"

"Kin damu da ita kika bar ubanta kika auri makiyinsa? Ko kuma saboda ke sai ya fasa tafiya da yarsa gidansa? Ita ba jininsu bace? Yadda Turhan yake son Fatima ai ba zai bari a cutar da ita ba, ba fin shi sonta kika yi ba"

Emily ta mike tsaye tana hawaye.

"Ke ma fa uwa ce, zafin nakuda zafin haihuwa wahalar raino duk kin sani, da aka dauke Turhan daga gurinki ina ne baki shiga kin fita ba saboda ya dawo gareki? Miyasa ni zaku azabtar da ni da wannan?"

Ammy ta mike tsaye.

"Fita ki bar gidan nan, na girmi na tsaya sa'insa da ke, kuma karki kuskura dora misalinki da nawa, dan muna da banbanci, da kina son Fatima da labarin yanzu ai ba haka yake ba"

Emily ta dubeta tana hawaye ta sake dubanta sannan ta fice tana hawaye har ta fita gidan. Ko da ta iso gurin motar Aliyu na tsaye jikin motar yaja jiranta, ya ga hawaye a fuskarta amman be ce mata komai ba ya bude mata motata shiga, ya zagaya ya shiga yaja motar, sannan ya kai hannunsa ya kwanto da kanta jikinsa ya rike hannunta yana tukin da hannu daya.

Daman ya raya a ransa Fatima bata gida, ya san da tana gidan ta yanzu ta matsa an kawota gurin Emily ko dan ta ga sabon gidan da Emily take. Aliyu be tambaya me ya faru ba, hawayenta kadai sun sanar masa ba ayi da dadi a gidan ba da suka iso gida ya faka motar sai ya fito ya bude mata ya riko hannunta ta fito yana janye da ita har cikin falonsu.

Saman kujera ta zauna shi kuma ya risina gabanta yana kallonta. Kamar jira take kawai ta fashe masa da kuka tana fada masa abun da ya faru. Yanayin fuskarsa ya sauya zuwa damuwa, sai dai be ce mata komai ba ya mike tsaye ya shiga dakinsu ya dauko wayarta data bari a gidan ya dawo falon, da kansa ya saka number Turhan dake wayarsa cikin wayarta yayi dialing sannan ya mika mata. Kallo daya ta yi ma wayar ta gane number Turhan ce saboda number bata Nigeria ba ce kuma akan rigimarsu ake ta san ba zai wuce ya kira mata Turhan din kai tsaye ba.

"Are you okay with that?"

Ta tambaya cikin kuka ya daga mata kai, sannan ta karba shi kuma ya zauna gefenta ya saka hannunsa daya cikin nata domin karfafa mata guiwa.

"Hello..."

Ta fada cikin sautin dake nuna ta yi kuka. Turhan yayi shiru be ce komai ba, ba dan kuma be fahimci mai magana sai dan kiran ya zo masa ba a lokacin da yake tsammani ba.

"Turhan Aisha ce Emily"

"Me ya faru? Me yasa kike kuka?"

Ya tambaya daga dayan bangaren.

"Na tafi ganin Fatima Ammy tace ka tafi da ni? Meyasa?"

Ya lumshe ido ya shafa goshinsa a tunaninsa zata fada masa Aliyu ya mata butulci ne.

"Bata min bankwana ba, tun da na yi aure bata zo gidan nan ba, a can bata san kowa sai kai, ta yi kankanta ta fuskanci kalubalen masarautarku a yanzu, kuma ni ina son ?ata, karka raba wannan soyayyar dan Allah, idan ma ba zaka yarda ta zauna a gurina ba, ka barta ta zauna a gurin Ammy mana, idan na so ganinta sai na tafi can na ganta, ka ce ba zaka sake cutar da ni ba miyasa ka yi haka?"

Tun da ta fara maganar be ce komai ba sai da ta gama.

"Kamin na dauke ta na yi magana ke, kuma alamunki be nuna min kin yarda ba, sannan na fada miki ba zan taba bari a taba ta ba, na zo da ita saboda ina sonta akusa da ni, kuma nan din ma gida ne, ya kamata ta san kowa kowa ya santa, idan tana bukatar zama a can ko nan zata zauna, amman gurin Ammy ba gurinki, Ammy ma da kanta ba zata bar ni na zauna da ita a nan ba, kuma ba zan so karatunta ya kasu guda biyu ba"

"Zaka dawo da ita kenan?"

"Zan dawo da ita, na yi nufin ta zauna na dan lokaci, amman yanzu tun da hankalinki ya tashi zan dawo da ita satin nan"

"Na gode, tana kusa da kai"

Yayi shiru na tsawon lokaci kamin ta ji muryar Fatima cikin haki tana fadin

"Momy?"

Emily ta kara matse wayar a kunnenta.

"Fatima, kina lafiya"

"Lafiya kalau, Momy i miss you"

"I miss you too baby, kina lafiya babu wani damuwa?"

"Babu, ina yin wasan doki yanzu, Momy na iya hawan doki, Momy Zaki zo?"

"Aa"

"I miss you"

"I know, babanki ya ce zai dawo da ke gurin Ammy za mu ga juna a can"

"Okay Momy i love you, ki rika kirana kinji Momy?"

"Tohm, idan wani yayi miki wani abun da baki ji dadi ba ki fadawa Babanki kinji"

"Tohm momy gidanki yana da kyau"

"Eh"

"Mu ma nan yana da kyau"

"I know, zan aje waya sai an jima"

"Okay bye i love you"

"I love you too"

Ta kashe kiran sannan ta kalli Aliyu.

"Na gode"

"Anything for you"

Ta kashe wayar. A ranar ta kwana da salama babu tunanin Fatima ko son sanin halin da take ciki. A kokarinsa na faranta mata kuma washe gari ya saka ta shirya da wuri ya sauke ta gidan Mama Baraka shi kuma ya wuce aiki bayan ya gaisa da ita cikin mutunci da girmamawa. After ya fice falon ne Mama Baraka ta kalli Emily tana murmushi ta ce.

"Kin yi dace mijin, Aliyu ya dade yana burge ni, wani lokacin har cewa nake be dace da Kameela ba, ashe an kaddara zai rabu da ita ya aure yata ne, ya zama sirikina, ina jindadin yadda yake nuna kulawa da damuwa akanki"

Emily ta yi murmushi.

"Yana da kirki, ga addini"

"Kusan fa duk wasu dabi'u da hallaya da ake so a gurin namiji Aliyu ya hada su, Allah yasa mutuwa ce zata taba, ga Ummi ma tana kaunarki baki da matsala ta ko'ina"

"Alhamdulillah"

"Allah ya datar da yan'uwanki su ma, su samu mazajen na kaurai"

"Ameen, har da ke ai Mama, ko Babansu Kameela zaki komawa?"

"Kai anya, ai aurena tsakanina da shi ya kare, kuma ni yanzu ba wani auren zan sake ba, kula da ku ya wadatar, sai idan na ga na aurar da duka yayana"

"Allah ya nuna mana"

"Ameen Ya Rabbi, kina da labarin Fatima?"

"Eh..."

Emily ta bata labarin abun da ya faru jiya..

"Daman Aliyu ya fada min yana ganin kamar bata nan"

"Ya zo nan ne?"

"Eh ya kan biyo, har alheri yake kawo min, da nake tambayarsa ya kike kuna da labarin Fatima yake fada min yana ganin kamar Turhan ya tafi da Fatima"

"Be taba min

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login