Showing 132001 words to 135000 words out of 253142 words

Chapter 45 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18391

suka fara yi min gizo ina ganinsu kamar mafarki.

Tun da muka tashi ba mu sauka ko'ina ba sai Abuja Nigeria. Da muka sauka jirgin ne matar tasa aka matso da ni kusa da ita ta gargade ni da halshen igbo.

"Ina fatan ba karya kike min ba, domin idan ya zama tsabanin abun da kika fada min toh zaki hadu da mummunan hukunci kuma zan saka a nemoki a ko'ina kika a kasar nan"

Na ce mata na amince, suka shiga motar alfarma mu kuma aka saka ni a wata motar, ina ta kallon gari da titunan Abuja da tunanin dan yancin da na samu har muka isa gidan mijin matar mai kama da wata babbar fadar Sarki, mutanen da suka tarbeta ita da mijinta ma abun kallo ne, a nan na kara gane kudi suna da muhimmanci sosai a rayuwar dan'adan. Da muka sauka gidan sai ta hannata ni a hannun wata mata yar Kaduna tace mata wai ina da zan je na dauko Wana tana son kar a barni na tafi ni kadai na tafi tare da rakiyar wasu saboda tana son ta gano gaskiya ta, ni dai an kira ni kawai aka nuna min matar da za mu tafi tare, ta hanyar wayar da matar take da yaren yarbanci, na fahimci kudin wacan matar da ta ceto ni wanda ko sunanta ban sani ba. Komai aka bani kasa ci na yi ina ta zumudin ganin Wana ga kuma tsoro ya cika zuciya gani nake kamar Turhan zai aiko a tafi da ni ne. Hankali be kwanta ba sai da muka bar garin Abuja tare da matar da mijinta da nake kyautata zaton dan siyasa ne.

Guri daya na zauna da matar, da alama ticket din da aka saya min na kusa da ita ne. A nan ta gabatar min da kanta ta fada min sunananta Barakat amman yaranta suna kiranta da Mama Barakat ta fada min ita bayarabiya ce, sannan ta tambayi labarina, ita kan ban boye mata komai ba na fada mata labarina tun daga tashina zuwa auren Khaleepa da kuma Turhan, gaba daya sai ta sauya ta rika kallona har sai da na tsorota, har muka isa Kaduna hawaye ke cika mata ido tana sharewa. Mun sauka Airport din idanuwa a zare kamar wata marar hankali ga rama na yi gaba daya ba ni da natsuwa. Mota daya aka zo daukarmu na shiga gaba ita da mijinta suka shiga baya, duk maganar da mijin yake bata amsawa har ya tambaya lafiya? Tace babu komai. Mun sauka gidanta ba laifi gida ne mai kyau amman ko kadan be kamo gidan wacan matar ta Abuja ba, kuma ita wannan da alama tana da abokiyar zama domin gidan bangare biyu ne, sai da muka fara shiga bangaren na farko ta shiga ita da mijin sai ta fito ita kadai ta shiga motar aka karasa da mu bangarenta.

Na sauko motar ina jin kamar na yi tsuntsuwa na gan ni gaban Wana, haka dai na daure muka shiga ciki, ta nuna min dakin da zan zauna sannan ta haura sama har lokacin hawaye take hawan ma tana yi tana waigena har ta haura stairs din. Ina ganin ta shige na juya ya saci kafa na fice daga bangaren, da kaina na gate din gidan na fice, tafiya kadan na tari abun hawa na hau na fada masa ya kai ni cocin da take kusa a nan garin Kaduna, babu wata daguwar tafiya sai gamu gaban cocin, na gaishe da mai gadin na fada masa ina tafe da matsala ne amman ina son ya bani kudi na sallami mai achaba tukuna babu musu ya biya mai babur din, sannan ya shiga da ni ciki a tunani idan na je ma Ammy kai tsaye ba zata ba ni Wana ba dan haka na zabi neman taimakon mutanen cocin bayan na fada musu ina ra'ayin komawa alnahin addinina na Christianity.

Sai suka ba ni shawara na fara tafiya dauko yaron har sai idan ta hana tukuna za su shigo ciki, na ba su addireshin gidanta sannan na cire takardar na rubutawa Ammy martanin karyar da ta yi min cewar danta na kirki ne ya banbanta da sauran, domin na san ba lallai na samu tsayawa na fada mata baki da baki ba, amman idan na bata wasikar zata karanta. Su suka ba ni kudin abun hawa na hau achaba na isa unguwar a lokacin ne tsoro ya yaye min saboda ina son ganin Wana ta kowane irin hadi, da Allah yayi nufin ba ni nasara ina buga gate din mai gadi ya bude sai da ya dade yana kallona sannan ya gane ni, ya bar ni na shiga ciki na samu falon babu kowa sai Wana shi kadai yana kallon Cartoon, na karasa da zafin nama na dauke Wana na aje mata takarda a gurin da na dauke shi na fito yana ihu domin shi ma be gane ni ba, mai gadin ya tsaya tambayar ina zan je da yaro na kai masa mugun halbi a gurin da ya fi komai muhimmanci a jikinsa, ba shiri yaja baya na bude gate din na fice da gudu kai kace sato yaron na yi.

Ina tafe ina waije ko za'a biya ni amman ban ga sawun kowa ba sai da na samu Achaba na hau sannan Ammy ta biyo ni da motarta tana cewa na tsaya na cewa mai Achaba kar ya tsaya, be tsaya ba sai da muka isa cocin na sauka da guduna na tsaya layin mutanen da cocin ke rabawa tallafi. Ammy ta dade tana kallona har sai da mai gadin ya bude min na shige.





TIRKASHI....!!!

A tunaninku tsakanin Auren Khaleepa da Turhan a ina Emily ta fi shan wahala? Waya ya fi gallaza mata?

Team Turhan kuna da katon aiki a gabanku=?"? indai kuna son Emily da Turhan sai kun tanadi makaman sallama >??





_______________________

Sannu  yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe Winki da kaya masu kyau, masu ?ima daga Khadeeja Candy Store

Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sau?in sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing.

Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taSawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet Winmu sun dace da ke

Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sau?i ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko ina!


Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1

da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0


Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame.

Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ?ayatarwa duk a farashi mai sau?i.

Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu!

Baki da lokaci? Muna da sau?in oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina!

To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08


Ba kawai kaya ba ne salo ne, ?ima ce. A Khadeeja Candy Store.
Ki zo yau, ki WanWani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haWuwa.
[6/26, 9:29/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL





*? Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen...
'?


Page 4?? 1??


Sai da ta bar gurin sannan na fito na sallami mai achaba na koma ciki na rika Wana dake ta ihu, gaba daya ya ki yarda da ni saboda be gane ni ba. Kansa na rike na saita shi ya fuskanci sai na koma kiransa da sunanyen da nake masa ina hadawa da Momy, a take ya tsagaita kukan da yake ya kalleni sai na yi masa dariyar dake tafe da hawaye na rungume shi ina jin kamar za a sake raba ni da shi ne.

Kwana na uku a coci, a tsawon kwanakin nan bana sallah bana saka hijab duk wani abun da ya danganci musulunci bana yinsa, saboda na fada musu zan koma addinin Christianity, sai dai a can kasa zuciyata na ni na san ban shirya barin addinin musulunci ba, ba dan mutanen cikinsa sun yi min gata ba sai dan ina jin natsuwa da addinin a cikin zuciyata, domin addinin musulunci addinin mai tsari da tsabta da dokoki, ni kuma mace ce mai son zaman lafiya mai son natsuwa. Sun mutunta ni sosai a cocin domin gidan wani pastor aka kai ni, abinci sai na ture gurin kwanciya mai kyau, matarsa tana ta nanata min halayyen musulmai basa da kyau kuma daman su basa son kafirai, har take cewa na yi kuskure da na bar addinin da ace ban gane gaskiya na dawo ba da Yesu yayi fushi da ni kuma ya kona ni.

Kusan duk wa'azinta jinsa kawai nake, amman a zuciya ina kyamar abun, ana gobe Lahadi wanda ta kama ranar coci a ranar za a min wanka da ruwa mai tsarki kuma a maida ni addinin kirista a ba ni bibles kamar yadda na sani yake a hukunce kuma matar ta jaddda min, sai na dauki London na goya ma sanya hijab dina cikin giyon na fito da sunan zagayawa harabar cocin, na nufi gate da yi ma mai gadin karya cewar zan fita naje na dawo kuma sun san da fita ta, domin an fada masa duk wanda ya zo nemana kar ya bar mutum ya shiga sai an sanar saboda ni da su muna tunanin Ammy zata dawo nemana.

Salin salin na fice daga gidan, ba kuma dan na san inda zan je ba sai dan ban shirya komawa addinin ba, na hau achaba na tambaye shi dan Allah wace umguwa ce nesa sosai da cikin gari, unguwar da san yi tafiya sosai sannan a isa gurin, ya fada min sai na ce ya kai ni can, mun yi tafiya sosao kamin muka isa unguwar dake kama da sabuwar unguwa ma sauka na ba shi kudinsa na nisa cikin unguwar ina ta kallon yadda tsare tsarenta yake, har na hango wani gida dake da fanfo da kwararo a ciki, na dauki leda na tara ruwan na fara sha sannan na shayar da Wana na yi alwala sallah na fara yi na rama duka wandada aka biyo ni har na ji na gaji, a lokacin kuma wata zuciyar take ta fadan min na koma dai domin wannan addinin be karbe ni ba, amman dayar data ci karfina ta hana ni komawa na zauna a gurin har dare, a nan yunwa ta fara tunkaro ni ga yarona be san babu ba. Kukansa ya saka mai gadin lekowa ya tambayi tafiya na fada masa yunwa yake ji sai ya shiga ya dauko ragowar abinci ya bani na bawa yaron da muka gama yace dan Allah mu kara gaba kar mai gidansa ya dawo ya same mu a nan zai masa fada.

Na yi masa godiya na tashi na kara gaba, haka na yi ta rayuwa a unguwar daga wannan kwararo sai wannan wani gurin a hantare ni wani gurin a bani abinci ko sutura wani gurin kuma a ba ni hakuri, gaba daya na koma wata kazama saboda babu gurin da zan raba na yi wanka, bahaya ma sai na shiga daji, rayuwa ta yi tsanani gareni a lokacin, ga ciki ga yaron da ba lafiyayye ba, idan ciwonsa ya tashi sai dai na yi ta kuka domin ban san wani abu da zan yi ba bayan wannan, ni da shi muka rame muka lalace, nakan shiga gida gida neman aiki ko wanki, idan na samu mai son wanki na yi ta murna na wanke a biyani na ciyar da kaina da Wana, na samu wani tsohon shagon kwano na laba ciki nake kwana ciki nake wuni idan ina cikin unguwar.

Tun mutane ana jin tsorona a unguwar har aka fara sabo da ni wasu ma idan sun raga abinci da kansu suke kawo min saboda suna min kallon mahaukaciya, wani lokacin ba ni sadakar kudi ko abawa Wana da haka nake ta fadi tashi har cikina ya tsufa, wani sa'in sai na yi tafiya mai nisa zuwa wata unguwa nake samun abun da zan ci, kuma ban sake bawa kowa labarina ba, idan naje gida sai dai na yi bara ko kuma na tambaya idan suna bukatar a musu wanki ko wani aiki. Wasu suka kam tambaye ni waye uban yarona ko kuma cikin da nake dauke da shi sai nace musu ban sani ba ni ma, hakan ya saka suka kara daukata mahaukaciya suna tunanin kamar fyade aka min na samu cikin ko kuma wani ya yaudare ni.

Akwai masu fadar wai ko dai kishiya ta yi min asiri saboda ina kyau ta raba ni da mijina? Su tambaya daga ina nake sai na ce Lagos, idan aka ce Lagos a ina? Sai na ce ban sani ba, to gurin wa zan ce daman? Har lokacin ina jin da kamar akwai sauran kurciya a tare da ni, wata kila kuma shiga mawuyacin hali ne yasa ban taba kula da watan cikina nawa ba, ban taba kirgawa na gane ba, ciki dai yana ta girma kuma yana motsi, idan na ji motsin cikin sai na ji zuciyata ta yi fari tas kamar ba ni da damuwa, ni dai burina na haihu lafiya na samu karin wasu iyalin...

Ana haka wata rana nakuda ta fara taso min tana kwantawa na kwashe kusan kwana biyu sai ta motsa min sai ta koma, idan ta laba min sai na cigaba da harkokina, wata rana na fita neman abun da zan ci ban karasa inda zan je ba aka sako ruwan sama na kuda ta taso min mai karfi kamar zan fita hayyacina gashi kuma na yi nisa da gida ba zan iya komawa ba, Wana kuma ya firgice saboda tsoron ruwan da iska sai ihu yake min ni ma kuma ihun nake a gefen hanya babu wanda ya kula ni sai kai Aliyu, shi ne farkon haduwata da kai, na zan iya manta wannan alherin ba, na gode na gode Aliyu, a lokacin ne na rike hannunka har agogon ya cire ya dawo hannu sai na matse shi ina ihu na yi tunanin mutuwa zan yi ma gaba daya, ka taimake ni ka dauke ni ka kai ni Asibiti, duk wani taimako daya kamata likitocin nan sun ba ni na wahala sosai kamin na samu na haihu da kaina, ada har ina tunanin ko dai sai an fasa ni za a iya cire abun da ke cikina saboda na kasa nishi.

Da na haihu sai suka bukac a kawo kayan jaririya ba ni da su, zanen da aka hadeta a ciki ma tsohon zanen wata mata ta bada a gurin aka lulkube Fatima, suka ce ina audugar da zan saka ina kaza ina kaza, na ce duk ba ni da, sai suka tambaya wanda ya kawo ni waye shi? Nace ban san shi ba taimakona yayi, a nan wata nurse ta fita ta shigo min da pad ta pant ta kuma ba ni zane na daura sannan suka canja min daki suka kawo ni wani dakin na dabam suna tambayar ina yan'uwana ya kamata na ci abinci na ce musu ba ni da kowa, daya daga cikin wadanda suka karbi haihuwa ta ta kawo min agogonka ta ce ga wannan kin saki a kasa dazun na karba na rike ga. Daker na iya awa hudu a asibitin na kamin na saci kafa na gudu da Wana da kuma jaririya dana haifa, zanena mai jini da uwar da ke fadowa bayan haihuwa a asibitin na bar musu na gudu. Ban nisa sosai da unguwar da asibitin take ba jiri ya debe ni na fadi ban sake sanin inda kaina yake ba.

Sai da na farko naga ana min fifita ga jaririya a kusa da ni ga kuma London yana ta kuka, mutane nata min sannu aka ba ni abinci na ci sannan aka dauke ni zuwa gidan wata mata dake kusa ana tambayar a ina nake daga ina na fito na fada musu a gidan na kwana sai washe gari bayan na karya matar ta siya min wani pad ta bani tsohon wandonta na saka bayan ta dora min ruwan zafi na yi wanka, ta bani wani tufafin na saka da hijab, makota kuma suka kawo min tsofin kayan jarirai na sakawa Fatima, ta kawo min abinci na ci na sha kunu sannan mai gidanta da wasu mutum biyu yan unguwar da kuma ita matar kanta, suka dora ni a napep muka tafi unguwar da nake rayuwa na nuna musu inda nake kwana sai suka fara tambayar wadanda suka san ni a unguwar, kowa sai yace da rana tsaka ya gan ni a gurin kuma ba ni da cikakiyar lafiya, cikin ma suna zargin yi min aka yi ta karfi, wasu kuma su nanata wai asiri aka min.

Ni dai jinsu kawai nake idan aka tambaya daga ina nake sai na ce Lagos wane guri a Lagos nace ban sani ba, sai suka yanke shawarar za a kai ni police station ayi report, ina jin haka nace ba zan je ba da suka matsa na saka musu kuka a dole suka koma can gefe suka yi maganarsu sai aka dawo aka fada min wai zan bi matar zuwa gidanta na koma can da zama a nan ma na tirje domin na san akwai abun da suka shirya, ni kuma ina tsoron a yadani Cocin da na gudu su gani ko kuma Ammy. Na dake akan nan gurin zan zauna da kowa ya watse na goya jaririyata na kama hannun dana na bi ta cikin gidanen dan kar ma wani ya gan ni na gudu na bar unguwar.

Tafiyar kuma wani sabon labari ne, domin ba san kowa a inda na tafi ba, haka na kwana a jikin wata tsohuwar gina sauro ya cije ni ya cije yarana musamman Fatima dake ta jaririya a lokacin, a daren ne na rana mata suna Fatima sunan da ba a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login