Showing 141001 words to 144000 words out of 253142 words

Chapter 48 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18417

amsawa abokinsa sai ya ce

"Ita ma fa yarinyar ta jefa ni a matsala, miyasa ta amince da auren nan tun farko fisabilillahi"

"Allah ya kawo sauki, ni zan wuce abun da zan fada maka shi ne ka yi hakuri da mahaifiyarka kuma ka yi ta addu'a"

"In Shaa Allahu, ma gode Aliyu, bari na yi ma direban magana sai ya kaika gida"

Aliyu ya shiga motar Direban yaja shi zuwa gidansa, a mota Aliyu ya gwada kiran Number Emily ya jita a kashe sai ya aika mata sako.

"Are you okay?"

Domin ya san ya kamata ace ta kira shi bayan riskar sakonsa, and maganar Ammy ta taba shi na cewa bata da wanda zai damu ya san halin da take ciki tun da bata da kowa. Bayan direban ya aje shi ya juya shi kuma ya shiga gidan da yayi datti yana mamakin taya haka ta faru domin yana da mai gyara masa gidan every week. A falo ya samu Fatima na ta bachi har lokaci akan kujera hannu ya kai ya taba jikinta yana mamakin wane irin bachi ne take haka, sai ya ji shi da dan zafi kadan. Mai kula da harabar gidan ya shigo yana masa sannu da zuwa Aliyu ya amsa yana tambayar ina mai gyara gidan.

"Tun da ta tafi bata dawo ba, bata fada maka komai ba tace dai zata je ganin gida ta bada keys a aje maka"

Ya saka hannunsa aljihu ya ciro keys din ya bawa Aliyu da hannu biyu. Aliyu ya mika masa Atm dinsa ya fada masa code sannan ya fada masa inda zai tafi ya samo musu abinci mai kyau...




Sorry ku yi hak'uri gobe zan yi long page in Shaa Allahu.
[7/2, 6:50/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??:

*? Khadeeja Candy*



Page 4?? 5??


Kamin yaron daya aika ya dawo Aliyu ya shiga ciki yayi wanka ya canja tufafi sannan ya dauki wayarsa ya kira Mama Barakat ya tambaya ko tana gida.

"Eh ina gida Aliyu ko ka shigo garin ne?"

"Eh na shigo kuma yau nake son na shigo gurinki saboda ina son komawa gobe kin san aikin na mu babu daga kafa"

"Haka ne to sai ka shigo"

Ya sauke kiran sannan ya fito falo yayi sallah yana sallamewa aka yi knocking, knocking din da ya tashi Fatima ta farka idonta har sun yi ja tsabar bachi, Aliyu ya karba ya rufe kofar.

"Yaushe muka zo nan?"

"Kina bachi little princess"

Ta yi mika

"Kai ka dauko ni?"

Ya risina inda take zaune yana kallonta da murmushi a fuskarsa.

"Eh kin tashi lafiya?"

Ta kalli falon.

"Nan gidanka ne?"

Ya daga mata kai.

"Ashe kana da wani gida Vito ma gida biyu yake da shi"

"Good taso ki wanke baki ki yi wanka sai ki ci abinci ki yi sallah"

Ta kalli shaddar dake jikinsa.

"Kai ka yi?"

"Eh"

Ya kama hannunta suka sauka tana fada masa kanta na ciwo, ya shiga da ita dakinsa ya nuna mata bandaki da yadda zata yi komai sannan ya fito ya dawo falon ya zauna yana taba wayarsa, har a lokacin sai da ya gwada kiran Number Emily ya ji ta a kashe. Yana ta nazarin abun da zai saka ta kashe wayarta kuma ta dauki lokaci har haka bata kira ba bayan sakon da ya tura mata, duniyar tunani ta dauko shi daga can bangaren Emily zuwa na Turhan idan ya ce be ji tausayin abokinsa ba yayi karya, ya san da zarar Emily ta bayyana a rayuwarsa komai zai zame masa daidai, sai dai kalamansa na dazun cewar da laifin Emily na amincewa ta aure shi ya sanyaya masa guiwa, jikinsa kuma yana ba shi cewar Emily ta yi gaskiya ko Ammy ta san da Fatima a matsayin jikarta abu ne mai wahala ta bar mata ita balle kuma Turhan, hakan ya saka shi ya ji lallai ya kamata ya bar garin Kaduna gobe gudun kar makamancin abun da ya faru a Airport ya sake faruwa, gashi kuma yana son ya san halin da Emily take ciki domin rashin samun wayarta da kuma maido masa da amsar sakonta ya saka shi a damuwa.

A tare suka ci abincin da Fatima tana ta fada masa mafarkin da ta yi, ya rigata koshi a dole ya jira sai da ta koshi ita ma sannan ya kwashe kayan ta bishi Kitchen tana kallo komai ta gani sai ta taba ta tambaya, ko ta fadi Momy na irinsa.

"Fatima Zaki iya zama a gidan nan ke kadai naje wani guri na dawo?"

Ta lake kafada

"Aa ba zan zauna nan ba, sai dai mu tafi tare"

"Ba zan dade ba kuma zan iya bar miki wayata ki yi game ki yi kallo"

"Duka na kalli komai na cikin wayar ni bana son zama"

Ya rasa ta ina zai fara rarrashinta ta zauna domin baya son tafiya da ita gidansu Kameela, na farko dai yana ganin hakan kamar cin fuska ne ga Kameela na biyu kuma iyayenta ma ba lallai su fahimce shi ba domin ko kowa be gane yar waye ba Kameela zata gane kuma karamin aikinta ne ta fallasa shi a gabansu.
Ya mika mata dayar wayar da ita ya fi aiki da ita ya dauki wanda ya bata dazun ya saka aljihunsa.

"Wannan baki san me ke ciki ba, na kunna data zaki iya duba duk abun da kike so a YouTube ki kalli cartoon kuma ki sauke duk game da kike so, Momy ki na na san zata kira ta wannan wayar idan ta kira sai ku yi magana kamin na dawo?"

Ya karba ba dan ranta ya so ba, can ta kalli hotonsa dana Kameela dake makalle a falon.

"Waye wannan?"

"Matata ce"

Aiko take ta hade girar kasa da ta sama ya nukokoce kai.

"Ba zan zauna ba, so you have a wife"

"Yes Baby"

"I hate you"

Yayi murmushi

"I know I'm sorry, Bari na tafi na siyo miki chocolate da ice cream kinji?"

Sam ta ki yarda gaba daya mood dinta ya canja daya fada mata yana da mata, ita a tunaninta idan suka saba da shi zata iya dawowa gidansa ita da Emily su bar gidan Vito, amman tun da har yana da mata ai ba wannan damar.

"She's ugly"

"No she's not"

Ya amsa yana dariya.

"I want my momy"

"Bari na tafi na dawo sai na kaiki gurinta"

Daker ya samu ta yarda ta zauna sannan ya dauki dayan key din motarsa ya fice, daga gidan be zame ko'ina sai family house din su Kameela, a bangaren Mama Barakat ya faka ya fito yana tunanin ya kamata ace ya riko musu wani abu, gashi babu enough cash a aljihunsa, sai dai kuma babu yadda ya iya domin ya riga ya zo dama ace be zo ba ne sai ya tsaya ya nema.

Haka dai ya aje komai ya shiga bangaren da sallama, yaranta suka amsa masa suka gaishe shi sannan suka kawo masa drink da abincin, suka fice daga falon cike da tarbiya, babu jimawa Mama Barakat ta sauko sanye da wani lace mai tsada irin na su na yarbawa domin zama a cikin hausawa da kuma auren bahaushe be saka ta jefar da al'adarta ba, yaranta ma yawanci da yaren yarbanci take musu magana shiyasa duk sun iya yaren.

"Maraba maraba da Aliyu"

Ya sauka daga kan kujera ya zauna kasa saboda ta zauna akan kujerar.

"Haba zaunawarka mana"

"Aa nan ma ya wadatar, na same ku lafiya"

"Lafiya Kalau Alhamdulillah, ya hanya"

"Alhamdulillah"

"Maa Shaa Allah baka ci komai ba?"

"Already sai da na ci abinci na fito"

"Tohm, ina godiya dai Aliyu daka saurare ni kuma ka ni umarnina a matsayina na step mother din Kameela, hakan ya nuna kai yaro ne mai jin magana mai biyayya kuma mai tarbiya, na jidadi sosai Allah ya maka albarka"

"Ameen"

"ka shiga bangaren na su ne?"

"Aa na fara zuwa nan ne tukuna"

"To yayi kyau, da har jiya nake cewa ina son na sake kiranka, domin Kameela gaba daya ta fara fita hayyacinta abincin kirki bata iya ci, yarinyar nan tana sonka kai ma kuma na san kana son matarka, ni ban san me yake shiga tsakaninku kuke ta samun matsala ba"

"Kameela ta cika kishi ne, da abun da ya kai da wanda be kai ba duk na kishi ne a gurinta, bata tsayawa ta saurara kuma bata amfani da tunani kamin ta aikata abu, amman dai In Shaa Allahu ba za a sake jin kam mu ba"

"Hakan yayi kyau domin na tabbatar ita ma kanta a yanzu ta dauki darasi kuma zata gyara"

"Allah yasa"

"Ameen"

Mama Barakat ta ji kamar ta masa maganar Emily sai kuma ta ji rashin dacewar hakan, domin be kamata ta shiga tsabgar rayuwarsa ba, bayan kuma ta fada masa Kameela bata fada musu komai ba, sai kawai ta sauke numfashi ta ce.

"Tashi ka tafi, ka yi hakuri da duk abun da zaka ji ko ka gani gurin Hajiya, kasan ita uwa dole ta nuna bacin rai idan aka taba mata ya, balle ma Kameela bata fada mana dalilin dawowarta gida ba, amman dai duk yadda zaka yi ka yi iya kokarinka ka tafi da matarka, Allah ya kawar da fitina a tsakaninku"

"Ameen na gode Mama, tafiyar ta zama ta gaggawa ban riko komai ba, sai dai idan na koma In Shaa Allahu"

"Haba ina ce ai an zama daya, idan zaka zo gida sai ace dole sai ka riko wani abu? Yanzu ai mun zama iyayenka ba surukai ba, saurarena da kai yi kawai ka bi shawarata Wallahi ya fi duk wani abu da zaka ba ni na gode"

Yayi mata sallama ya tashi ya fice ta bishi ta kallon burgewa tana jin ina ma ace daya daga cikin yayanta yake aure yadda yake da biyayya da jin magana haka. Motarsa ya shiga ya yi mata key yayi reverse ya shiga bangaren mahaifiyar Kameela yana faka motarsa tana fitowa tare da kanwar Kameela cikin shirinta da alama fita zata yi, Aliyu ya fito mota ya nufo inda suke sai Hajiya ta yi kamar bata ga Aliyu, sallamar da yayi ma kanwar ce ta amsa masa shi ma cikin rainin wayo domin basa kallonsa da daraja gaba daya, ya mika mata gaisuwa bata amsa ba sai kokarin shiga mota take.

"Hajiya Gurinki na zo"

Ya dago ta kalleshi a wulakantacce kai kace ba shi da gata ko kuma dan talakawa ne.

"Ina jinka?"

Ya danna tafarfasar da zuciyarsa ke yi.

"Na zo ne akan maganar Kameela"

"Ina jinka bani da lokacin batawa fa fita zan yi, kuma saboda kai ka san ba zan fasa fitar da zan yi ba"

Ya hade yawu zuciyarsa na bugawa da karfi.

"Ina son na dauke ta mu koma ne"

"Kam uban nan"

Kanwar ta fada Hajiya kuma sai ta fito motar

"Ka dauke ta ku koma saboda a titi ka aureta? Ko kuma an fada maka bata da kowa? Ai ko baranta muka yi aka ba mu ita sadaka ba zaka shigo haka nan kawai ka dauke ta ku tafi ba, kuma ta inda aka hau ice ai ta nan ake sauka, kai karan kanka baka isa ka zo na tsaya tattaunawa da kai akan matsalarku ba, idan ma bikonta za zo toh ba kai ya kamata na gani ba, domin kai ka maida auren kamar wasan yara, haka kawai dan ta maka dadi zaka turo yarinya gidansu, yanzu kuma da ta yi maka dadi ka shigo kana fada min zaka dauke ta ku tafi, ai ba ni na baka aurenta ba ubanta ya baka aurenta kuma shi kansa yanzu yadda ransa ya bace ba lallai ne ya yarda yarsa ta koma inda ba a san darajarta ba, daman can abu ne da Allah ya riga ya tsara babu yadda za'ayi, amman da na san idan ka aureta haka zaka wulakantata kai da iyayenka ba zan yarda Kameela ta aureka ba ko zata mutu"

"Iyakar abun da zamu tattauna tsakanina da Kameela ne Hajiya ban da iyayena, domin iyayena babu abun da suka mata sai alheri, kuma ina tunanin da ace baki ga alamar za a rike Kameela da daraja ba, da ba za ku ba ni aurenta ba"

A take Hajiya ta zaburo masa da fada.

"Alherin me suka mata? Me suka kulla mata tun da aka yi auren? Duk tsabanin da kuke samu ummi ta taba tako kafarta gidan nan da sunan danta yayi ba daidai ba zata bada hakuri? Mahaifinka ma harkokin siyasarshi kawai ya saka a agaba, yanzu din ma ai ba kai ya kamata ka zo ba iyayenka tun da ba daga mu sai kai muka baka aure ba, kuma Kameela ba daga sama ta fado ba tana da gata, kar na sake ganin kafarka gidan nan da sunan biko wannan iskanci da tsageranci na surukan zamani ni ba zan dauke shi ba, kana neman bata min lokaci ina da abu mai muhimmamci a gabana"

Ya koma cikin motar ta shige direbanta ya rufe sannan ya shiga motar yaja suka bar Aliyu tsaye kunshe da bakinciki kamar ya kashe shi, meya ma ya zo tun farko meyasa ya kawo kansa? Sai a yanzu yake bakincikin neman auren kameela tun farko, domin auren macen da iyayenta ba su dattijai ba ne abu ne mai illa sosai ko da kuwa ita yarinyar tana da tarbiya. Shi aka yi ma laifi ya daure a haka ya zo bikon matarsa amman mahaifiyarta take fada masa magana son ranta.
Juyawa yayi ya shiga motarsa ya kama hanya yana yi ma kansa alkawari na damuwa ba ko cewa aka yi Kameela zata mutu akansa ba zai dawo bikonta ba. Yana hawa titin unguwar kiran Emily ya shigo wayarsa. Fakin yayi gefen hanya yana maida numfashi a hankali wani irin tafarfasa zuciyarsa take be san lokacin da ya daki sitiyarin motar da karfi ba tsabar bacin rai. Ya sauke ajiyar zuciya ya fi a kirga sannan ya bi kiran Emily da already ya yanke bayan ta yi ringing be daga ba.




KAMEELA POV.

Tana can kwance dakinta bata san wainar da ake soyawa ba har sai da Hajiya ta kirata tana mata gargadi wai karta kuskura Aliyu yace ta zo suke ta bishi daga ita sai shi ko saukowa ma kar ta yi ya ganta ko da ya kirata.

"Aliyu ya zo ne?"

"Eh wai wani ya zo bikonki a nan na bar shi na tafi gurin sabgogina"

Kameela ta bude baki kamar ta yi magana babu hali, domin ita kadai ta san yadda suka tsara da Mama Barakat har aka samu kansa ya zo, kuma ta san ita ce mai laifi amman be fada a gidansu ba kuma be fadawa iyayenta ba haka kuma ya danne komai ya zo bikonta meyasa Hajiya zata mata?

"Hajiya kuma kika ki saurarensa"

"Ke dalla can rufewa mutane baki, shiyasa yake wulakantaki ai, saboda baki san daraja kanki ba kina nuna masa rawar jiki da shegen so shiyasa yake gallaza miki yadda ya ga dama har da wani turo ki gida tsabar rainin wayo da wulakanci, kar na ga kafarki waje dan na san halinki shiyasa na kira na gargade ki"

Ka kashe ta tashi ta sauri ta leka windows dakinta bata ganshi ba balle motarsa, saukowa tayi kasa ta shiga bangaren Mama Barakat ta tambaye ta ko Aliyu ya shigo bangarenta.

"Ya shigo baki gan shi ba?"

"Kai..."

Ta juya ta fita da sauri tana kiran layinsa bugu daya aka daga sai ta yi shiru tana jiran ya fara magana.

"Hello."

Ta ji muryar karamar yarinya.

"Wacece wannan?"

"Hello can you hear me"

Fatima ta sake fada domin bata fahimci yaren Kameela da kyau ba.

"Yes who are you?"

"Sunana Fatima Aisha Emily"

Kameela ta sauke wayar daga kunnenta ta duba layi ta ga na Aliyu ne sannan ta sake maida wayar.

"Ina mai wayar?"

"Ya fita ya siyo min ice cream"

"Ke kina ina?"

Ta dayan bangaren Fatima ta kalli inda take.

"Ina falo"

"Falon wa? A ina?"

"A gidan Uncle Aliyu"

Da turanci Fatima take amsa mata. Kameela ta kashe wayar tana jin wani jiri yana debanta zuciyarta ma tafasa numfashinta har sama yake yana dawowa. Ta nufo bangarensu tana mamakim abun da ya kai wayar Aliyu hannun yar Emily domin ta san suna da ya kuma gashi yarinyar ma ta ambaci sunan mamanta.

"Wato Aliyu ba zai rabu da matar nan ba, kuma be shirya rabuwa da ita ba, wai da ita ya zo ne ko kuma yaya? Ni ban gane ba?"

Ta haura sama tana magana da kanta kamar wata mahaukaciya. Sai kuma ta sake kiran Number Fatima ta dauka kamar zata yi kuka.

"Kina damuna ina kallon Cartoon ne"

"Ke fada min a wane falon? PH ko Kaduna?"

"Kaduna jirgi muka shigo muka zo Kaduna ko da muka zo ina bachi ma"

Kameela ta kashe wayar tana jin kamar ta haukace tsabar bakinciki wato har Kaduna ya zo dayar Emily saboda ya raina aurenta kuma ya raina mata hankali, hijab dinta ta dauka ta saka ta fita dakin ta shiga dakin Hajiya ta dauki makullin mota ta sauko kasa ta fice falon babu wanda ya sani ta shiga motar Hajiya ta dauki hanyar gidan Aliyu, yau kam ta shirya ayi ta kare domin ba zata juye wannan wulakanci da Aliyu yake mata ba akan wata kafirar banza da ba matarsa ba.





EMILY POV.

Ta sauka Airport around 5:02 tana fitowa ta kunna wayarta kamin ta kira Aliyu sakonsa ya shigo wayarta, bata wani tsaya duba sakon ba ta danna masa kira ringing daya aka daga.

"Aliyu ina yata take?"

"Hello"

Muryar Fatima na dira kunenta ta tsaya cak ta lumshe ido.

"Fatima my beautiful baby girl"

"Hi Momy"

"Ina kike?"

"Ina falo"

"Falon waye a ina? Ina Aliyun yake ina ya kaiki"

"Gidanshi ya fita ya siyo min ice cream"

"Momy ki daina damuna ina kallon cartoon ki kira dayan kira dayan wayarshi"

"Okay my Love, i love you okay"

Bata tsaya amsawa ta kashe wayar ta cigaba da kallonta, hawaye ya saukowa ma Emily sai kuma ta ji wani iri idan ta yi arba da Aliyu me zata fada masa bata yarda da shi ba? But she has no other choice dole ta sanar masa tana Kaduna kuma hankalinta zai fi kwanciya idan yarta na kusa da ita. Ta gwada kiran dayan layin nasa wayar ta yi ringing har ta katse be daga ba, kanta ta sauke kai ta kalli jacket din Dr A-B dake daure a jikinta sai kamshin turarensa take, kira ne ya shigo wayar ta dago da sauri a zatonta Aliyu ne sai ta ga Vito a nan ma bata daga ba har wayar ta gama ringing sai ga kiran Aliyu ya shigo.

"Hello"

"Aisha"

"Naam"

Sai kuma ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login