Showing 36001 words to 39000 words out of 253142 words

Chapter 13 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18436

ta yi magana ba.

"I have to take care of something, ba zan iya zuwa ba, amman na yi magana da wani abokina yace akwai wani abokinsa kwararen likitan kwakwalwa, kuma ya shigo garin nan yin wani abu, zai shigo ya duba London kamin ya wuce"

 Dana ba mahaukaci ba ne Vito, ciwo ne kawai yake damunsa

Ta rufe da fada zuciyarta na bugawa da karfi tsabar bacin rai, ya san yadda zai tafi da ita dan haka yayi shiru be ce komai ba sai na tsawon lokaci.

"Zan aje wayar"

Ta fada jin be ce komai ba har na tsawon minti biyar.

"Na sani, kawai zai duba shi ne ya bashi ya bamu shawarwari wata kila za su taimaka mana"

Tare da ta sake cewa komai ba ta kashe wayar, daga inda take zaune take kallon danta har bachi ya fara daukarta tana angaje har ta kai ta kwanta a gurin, bachi mai nauyi yayi gaba da ita, bata farka ba sai kusan asuba, ta bude idon tana hamma ba tare da ta rufe baki ba, dagowa ta yi kadan ta leki London, ganin yana bachi ya bata karfin guiwar mikewa tsaye ta karasa kusa da gadon da yake kwance ta zauna, ta mika hannunta a hankali ta shafa fuskarsa zuwa kansa, tausayi yake bata sosai saboda lalurar da yake dauke da ita, ba zabin mutun bane ya kasance a yadda yake so, ko kuma waninsa ya kasance a wani hali na dabam marar dadi, abu ne sa yake tsare tun gabanin halittar rayuwa, an rubuta yadda dan'adam da rayuwarsa zata kasance.

Knocking aka yi sau biyu da two fingers, da sauri ta dago ta kalli kofar dakin hakan yayi daidai ta turo kofar dakin da aka yi aka shigo. Cak ta tsaya tana kallon mutumen da ya kasance bakuwar fuska a gurinta, kamar yadda shi ma yake tsaye yana kallonta.

 Lafiya?

Ta tambaya ganin ya gagara karaso, haka kuma ya gagara cewa komai. Takawa yayi baya ya ja mata kofar ya rufe, bata gama mamakin waye shi da kuma dalilinsa na aikata hakan ba, ya sake turo kofar dakin ya shigo with full confidence...
Kallonsa take har ya karaso kusa da ita idonsa cikin na ta.

"Sunana Doctor Adam Bello amman an fi sanina da Dr A-B kwararen likitan kwakwalwa, ina aiki a asibitin Special Care Hospital dake Abuja, abokina ya fada min akwai wani yaro da zan duba a dakin nan, wanda nake kyautata zaton kanenki ne..."

Ya karasa yana kallon London dake bachi, zuciyarsa na raya masa kanenta, a yanayin halittar jikinta da kuma kurciyar dake fuskarta ba su bar masa alamar da zai aje London a matsayin danta ba.

"London ba mahaukaci ba ne"

Ya daga girarsa biyu kadan ba tare da ya kalleta ba.

 Ni ma ban ce ni likitan mahaukata ba ne, mutane ne suke kuskuren fahimtar ciwon sai suke ganin kamar hauka ce

Ya kai hannu ya kama hannun London yana taba tsatsunsa a hankali.

 Fada min idan kanenki ya farka yana farkawa a firgice? Idan babu kowa a kusa da shi?

Ta daga masa kai alamar eh.

 Wane kalar turare ya fi so?"

Har lokacin be kalleta ba.

"Ban taba lura da wannan ba"

"Uhm, da wa yake yarda? Bayan mahaifiyarsa da Babansa da kuma ke?

 Dana ne ni na haife shi

Sai a lokacin ya sake kallonta, ya dauke shi tsawon dakika biyar kamin ya iya dauke idonsa daga kyakyawar fuskarta mai matukar daukar hankali.

"Ya kamata ki san kalar turaren da yake so, his favorite color, wane kalar cartoon yake so, wane kalar wasa yake so, wane yanayi yake shiga idan yana kuka, su waye mutanen da yake so, ki fahimci idan yayi bachi wane kalar mafarki yake? Ya yanayin sakewarsa da mutane yake?"

"Na san wasu daga ciki, amman dai shi ba mahaukaci ba ne

Yayi murmushi ya kalleta.

 Da alama zaki sha wahalar rayuwa kamin ki fahimci duniya da mutanen cikinta, ni dai ina baki shawara ne kawai na yadda abubuwa za su miki da sauki tsakanin ke da... Danki...

Ya fada tare da jan zaren furta kalmar danta kamar mai jin nauyin alakantata da jininta. Sannan ya ciro katinsa a aljihunsa ya mika mata.

"Bana kallon marar lafiya a free ma, balle kuma magana da shi, sai an yi min biya mai kyau, amman da yake ke tafe kike da sa'a, sai ga shi an lallaba ni na zo har asibitin da kike na duba danki kuma na baki shawarwari a free, so hare is my card idan kina son wanin hakikanin waye danki, taya zaki zauna da shi, wane mataki zaki bi har ki yi nasarar sauya rayuwarsa, da kuma yadda zai samu lafiya, sai ki bi matakin da yake kan card din

Ya aje mata card din ya juya ya fara tafiya.

 Bama bukata daman ka zo nan ne dan ka ci kudinmu ko? Toh ni na san waye ana kuma shi ba mahaukaci ba ne

Juyowa yayi yana murmushi.

 Halinku daya sak da matar direban direban Babanmu, amman kuma da ta bi shawarwarin da na dora ta a kai da magani, sai ga shi ta dawo tana min godiya

A kokarinsa na fahimtar da ita kudi ba matsalarsa ba ce kamar yadda take zato ya ambato mata direban direban babansu.

Da farko she was confused kamar ya Direban direban babansu kamin ta sake kallonsa cike da mamaki.

 Direban Babanku?"

"Nope Direban Direban Babanmu"

Ya furta yana hade lips dinsa.

"Direban Babanku yana da Direba kenan.?"

 Uhm

'Wane irin kudi babanku yake da shi haka ne? Da har direbansa yake da direba?'

Kamar ya san tambayar da ta yi ma kanta a zuciyarta sai ya taka ya matsa kusa da ita, yana kallon kwayar idonta.

 Babanmu na da kudin sosai, kwatankwacin yadda kike da kyau sosai mai jan hankali

Ya fada cikin wata murya na irin mutumen da kuzari ya bar jikinsa, gaba daya kyauta ya gama rudashi. Ta hade yawu da karfi tana kallonsa.

 Akwai wata tambayar ne?

Ta kasa cewa komai, ya kalli agogon hannunsa.

 Lokacin sallah yayi, duk lokacin da kika shirya bata kudinki, zaki iya nema till then good bye

Ta matsa baya ya fara tafiya.

"To miye amfanin zuwanka? Baka duba yaron ba baka fada min komai ba taya zan tabbatar da kwarewarka ko akasin haka?

Tana maganar tana daga kafadunta.

 Ko ba komai ai na auna nauyin kyaunki na fada miki matakinsa, yanzu kin san darajarsa

Ya fada sannan ya juya ya cigaba da tafiyarsa, ta bi bayansa da kallo har ya fice, sannan ta sauke numfashi ta kalli card din da ya bar mata, ta kalli danta, sai kuma ta dago wayarta ta shiga camera tana kallon fuskarta.
Ita kan bata ga wani banbanci a tsakanin kyauta na jiya, shekaran jiya da kuma yau ba. Mai da wayar ta yi ta aje, tana nan tsare da danta har ya farka misalin bakwai da yan mintuna.

 Good Morning Sunshine"

Suna hada ido sai ya koma ya kwanta ta rufe ya bata fuska sosai kamar zai yi kuka.

 Chichi chichi

"Okay zata zo yanzu"

Ta fada ba dan ranta ya so ba sai dan Chidinma ta fi soyuwa a zuciyar danta fiye da ita a yanzu. Ta dauki wayarta ta nufi kofar dakinta ta bude fice tana jin kamar ta fasa kuka. Ta fito asibitin sai ta tsaya a harabar tana kallon mutanen dake hada hada kamar wacce ta rasa abun yi, gaba daya ta rasa me ke mata dadi. Daga inda take tsaye ta dagawa wata matar dake tunkaro inda take hannu matar ma ya dago mata tana murmushi. Emily ta fara takawa ta karasa gurin matar dake tahowa.

"Sannu kin gane ni?

Matar ta dan yi jimmm kamin ta amsa.

 Eh kamar ke ce na kusan kade yarinyar ki ko?

 Haka ne, kina aiki a nan ne?

 No na shigo kawo ma wata abincin ne, ke fa?

 Yarona ne ba shi da lafiya

"Da sauki amman?

"Eh

 Allah ya ba shi lafiya

Tana fadar hakan ta wuce abun ta ta bar Emily tsaye a gurin da mamaki kuma da takaicin yi mata magana da yi.

 Okay& 

Ta fada sannan ta juya tana kallonta kamin ta tsuke baki ta cigaba ta tafiyarta, tana fita wajen asibitin ta dauki drop zuwa unguwarsu. Har ta isa gida haushin kanta take ji meyasa ta yi ma Matar nan magana gashi ta wulakantata.

 Chere m, a ga m ala n'ulo nweta ego gi ugbua"

Ta fada masa da yaren Igbo cewar ya dan jira zata shiga gida ta dauko masa kudinsa.

"Okay"

Ya amsa mata ta nufi gate din ta buga, mai gadinta ya fara lekowa ya ga ganta madadin ya bude mata sai ya bude ya fito ya nufi motar da ta shigo ya leka mai motar, hakan kuma ba karamin mamaki ya bata ba domin be taba yi mata haka ba.

 Me ya faru?

 Babu komai ranki ya dade

Ya amsa sannan ya bude mata ta shiga, kamar zata yi masa magana sai kuma wata zuciyar ta hanata, dan haka ta maida hankalinta gurin manyan bakaken karnukan da suka fara kuka saboda shigowarta, ba karamin tsorata ta yi ba ganin manyan karnukan har biyar daure da sarka a harabar gidanta. Tsayawa ta yi cak tana kallonsu daya bayan daya kamin ta kalli Vito da ya fito daga cikin gidan.

 Baka na son kare ka sani

 Na sani ba saboda ke na kawo ba

 Saboda wa?

Ya saka hannu aljihunsa ya ciro kudin da shi kansa be san nawa ba ne ya mika mata.

 Je ki sallami mai mota, me yasa kika dawo yanzu? Ina London?

Ta kalli kudin kawai ta dauke kai sannan ta kalli karnukan.

 A daure suke ba za su taba ki ba

Tana matukar tsoron kare, amman a haka ta jure ta shiga cikin falonta, Fatima ta zo da gudu ta tarbeta tana sanye da uniform din makaranta.

 Momy good morning

Ta rage tsawo tana shafa kan London

 Morning My love

Ta amsa da murmushi kadan a fuskarta sannan ta daga kai ta kalli Chidimma dake jera cups a dinning.

 Me yake faruwa a gidan nan

 Kamar na me ranki ya dade?

 Me yasa Vito ya kawo karnuka a gidan nan? Kuma mai gadina ya leki motar da ta sauke ni yanzu, be saba min haka ba, kuma a yanayin yadda na ga Vito da alama gidan nan ya kwana

 Haka ne, Sir Vito ya kwana a nan a falon nan ma, sauran amsoshinki kuma sai dai ki bincike shi, ban san amsar ko daya ba

Emily ta kalleta daga sama har kasa tana kallon yadda ta saka riga da wando da suka dame mata jiki sosai suka fitar mata da halittar jiki, bata sake furta komai ba ta mike tsaye ta nufi hanyar dakinta, babu jimawa ta sauko rike da kudi a hannunta ta fice daga falon. Har lokacin Vito na tsaye Balcony din yana kallon gate din gidan kamar mai jiran shigowar wani, shi ma kallonsa ta yi daga sama zuwa kasa ta dauke kai ta nufi gate din. Ta bude da kanta, ga mamaki sai ta samu direban ya tafi sai wata farar sabuwar mota ce fake a baya kadan da inda mai taxi din ya faka.

Ganin yadda ta tsaya kallon motar ya saka Aliyu ya bude motar ya fito ba tare da ya rufe ba ya doso inda take tsaye tana kallon motarsa, da sauri ta sauke idonta kasa wani irin fargaba da faduwar gaba suka tunkarota da bata san na miye ba, a ka'idar rayuwarta, tana iya kallon kowane kalar namiji ido cikin ido ba tare da tsoro ko jin wani abu ba, sai dai a yau ta samu kanta da kasa motsa ta balle kuma har ta ido da mutumen da yake cikin jerin mutanen da ta tsana.

"Ki yi hakuri na sallami mai taxi din da kika hau ba tare da izininki ba

"Me ka zo yi nan?

Ya daga kai yana kallon gidan.

 Na zo na bada hakurin abubuwa da suka faru ne, kamar hotunan da Fatima ta tura min ba tare da saninki ba, kokarin shiga rayuwarki son sani wasu abubuwan, aje aikin da kika yi saboda abun da Amal ta yi miki...

 Ka daina kokarin shiga rayuwata, karka janyowa kanka matsalar da ba zaka iya hadewa ba, sanin abubuwan da suka faru ba za su kara maka komai ba face su jefaka a ramen da ba zaka iya cire kanka ba, biya kudin taxi da ka yi kuma ban yafe ba

Ta juya ta fara tafiya.

 Ban yi da gode ba, ba jarumi ba ne ni, balle a ba ni kambu ko ayi min jinjina, na zo nan saboda wani dalili, idan ba haka ba ba zaki gan ni kofar gidanki???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? ba

Ta juyo ta tana son ta kalleshi sai kwarjininsa a yau ba zai bar ta ta aikata hakan ba.

 Taya aka yi ka san gidan nan

Yayi shiru kamar mai tunanin irin amsar da zai bata.

 Baka yi kama da mai boye gaskiya ba, magana biyu bata dace da namiji irinka ba, kuma addininku ya hana karya ko ba haka ba?

"Kokarin sanin gaskiya ko gyara kuskura bai isa ya saka na dora tubalin ginin da karya ba, saboda na faranta miki ko na burge ki ba zai saka na sabawa Ubangiji na ba

Ta yi wani murmushin shedanci tana kallon wani gafe.

 Ku dai musulman nan idan kuna magana kamar ace zuciyarku ma haka take, aikinku dabam addininku dabam

 Kar ki yi la'akari da aikinmu ko kalamai, ke dai ki maida hankalinki gurin addini kawai, Williams ne ya bani addreshinki

Ya amsa mata tambayarta bayan ya shimfida mata matashiya akan addininsa.

Ta juyo da kyau ta fuskance shi, sai dai har lokacin ta kasa kallon wayar idonta, tana dan mamaki waye ma Williams. Aliyu ya saka hannunsa aljihu ya dauko wayarsa ta kamo hoton Williams ya nuna mata.

 Idan ma ya taba fadin sunansa tohm na manta, amman dai shi Williams din be san gidana ba, be san komai a kaina ba

Wani tunanin ne ya zo mata.

 Ka yi hanzarin barin gidan nan wata kila saboda kai Vito ya kawo dog's yau, kuma saboda kai ya kwana a nan

Rufe bakinta yayi daidai ta daga kan da Aliyun yayi ya kalli kofar gate din da aka bude gaba daya, Emily ta juya da sauri ta kalli gate din, a take hankalinta ya tashi ganin gogan ne a tsaye fuskarta kamar kullum babu annuri.

 Ka yi hanzari bari gurin nan

Ta fada ba tare da ta juyo ba, kana ta saka kai ta nufi gate din da nufin shiga cikin gidan, tana isa a daidai gurin da Vito yake tsaye zata wuce shi, sai ya fisgota da karfi ya dawo da ita. Kamin ta yi wani yunkuri ya dauke fuskarta da mari mai zafi, har sai da dafe kunci hawaye ya cika idonta, sanin karamin aikinsa ne dukanta ya saka ta auna da gudu cikin gidan tana ihu, binta yayi a baya kamin ta haura entrance din ya janyota ta fadi kasa ya fara shurinta yana kai mata duka ta ko'ina. Kan kace me ta cika gidan da ihu tana kuka shi ko dukanta yake kamar an aiko shi.
Chidimma da Fatima suka fito da gudu saboda ihun da take, sai dai babu wanda ya iya kawo mata agajiya har sai da ya duketa iya son ransa, sannan Fatima ta zo gurinta ta fada jikinta tana kuka, Chidimma kuma ta juya ta koma cikin gidan ba tare da rika Emily ko bata hakuri ba.

Duk abun da ya faru Aliyu yana tsaye yana kallo hannayensa biyu rumgume a baya, sai a lokacin Fatima ta lura da shi, da sauri ta dawo daga jikin Emily tana kuka ta nufi gurin da Aliyun yake tsaye, sai dai kamin ta karasa mai gadin ya hada gate din ya rufe. Aliyu ya sauke numfashi a hankali ya juya ya shiga motarsa dake bude har lokacin, ya dan jima a motar zaune kamar mai tunanin abun yi, kamin ya ja motar ya juya ta hanyar da ya fito.

Har ya isa gidansa ransa a jagule yake, damuwar da bata tasa ba na neman mamaye masa zuciya. Be san ya dade a cikin motar zaune ba har sai da Kameela (AISHA) ta fito daga falon ta kwankwasa motarsa sai ya sauke gilashin motar yana kallonta da murmushin da ya fi kama da damuwa a fuskarsa.

 Mai ciki?

 Lafiya ka shigo cikin gidan ka zauna a mota, kuma ga damuwa a tare da kai

Ya san daman zata ga damuwar kam domin be iya sauya kansa a duk lokacin da wani abun na damuwa ya same shi, iyakar abun da yake shi ne boye sirrin damuwar tasa har sai ya samu mafita. Sanin halinta na zafin kishi da kuma saurin juyar da abu ya saka be fada mata daga inda yake ba, da kuma dalilin damuwar tasa, haka kuma ba zai iya mata karya ba, domin karya ba dabi'arsa ba ce.

Kiran wayarsa ya yanke masa tunanin da yake na yadda zai kawar da maganar a gurin matarsa Kameela, kusan kamar an yi sara akan gaba ne, domin kiran da Turhan yayi masa yayi daidai a yanzu da yake neman amsoshin wadansu tambayoyi. Sanin ba zai iya amsa wayar a gaban matarsa ya saka shi daga gilashin motar ya rufe ruf sannan ya amsa wayar.

 Assalamu Alaikum

 Wa'alaikumussalam, Aliyu ya gida

"Alhamdulillah, har yanzu babu wani labari ne?"

Aliyu ya shiga shi tambayar ne a kokarinsa na gujewa tasa tambayar.

"Babu, na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login