Showing 192001 words to 195000 words out of 253142 words

Chapter 65 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18396

fita yaja mata kofar, sai ta lumshe ido murmushi kadan ya bayyana a fuskarta dake dauke da hawaye. Nemanta kawai da ya bata lokaci yayi abun farinciki ne a gurinta, gashi kuma a yanzu ya daureta da kalaman da wani be taba mata ba, ko da karya Aliyu yayi mata a yau ta jidadi domin ya nuna mata tana da muhimmanci, da ace zata iya da ta zauna Aliyu yayi ta zuwa yana dawowa ba dan komai ba sai dan waken da daya rare mata mai dadi a yau ya karanta mata shi a kullum ya zo neman Alfarma. Ta mike tsaye ta share hawayenta ta nufi kofar dakin ta bude ta fita tana tana takawa a hankali kamar mai tsoron bayyana sautin takun kafarta haka ta haura sama ta shiga falon Momy, sai kuma ta yi tsaye bata karasa kusa da kowa ba.

"Emily kin yi magana da wannan"

Dr A-B ya nuna mata Aliyu ta kalli Aliyu da be kalli inda take ba tun da ta shigo, ta daga kai.

"Ya fada miki sun zo man ne saboda su tafi da ke?"

Ta daga kai.

"Za ki bisu?"

Ta dubi Aliyu har lokacin be kalleta ba idonsa yana kan wayarsa. Ta daga kai

"Kin tabbatar kin shirya komawa?"

Ta yi shiru na lokaci kamin ta daga kai. Dr A-B ya mike tsaye daman tun dazun yake da shirin tashi ya nufi kofar fita ya raba gefen Emily ya fice ba tare da yace komai ba. Aliyu na ganin haka ya san Emily ta amincewa bukatar da ya zo da ita sai ya hade yawun farinciki ya gyara zamansa ya daga ido kadan ya kalli Emily.
Emily ta ji babu dadi ficewar da Dr A-B yayi domin haka ya nuna be yi maraba da tafiyar tata ba. Ta juya ta bi bayansa ko da ta shiga dakinsa Already ya zauna akan kujera and to her wannan ne karo na farko data taba shigowa dakinsa. Ta karasa inda yake zaune ta risina kasa ta dafa hannun kujera.

"Ka yi fushi da ni?"

Ta tambaya da wata murya gwanin tausayi.

"No bani da hujjar yin fushi dake akan abun da ke kika yanka da kanki, kawai dai abun da nake tsoro ya zamana cilasta miki yayi ko kuma yayi miki barazana"

"Ba ko daya, kawai ya yi rubutu a kwakwalwata ne, ya karanta min da halshen da da zan fahimta"

"Kuma bana fatar ki koma ki sake fuskantar wata matsala"

"Ni ma bana fatan haka"

"Ko ma dai miya faru ki sani you're always welcome here"

Ya mike tsaye ya nufi gurin da yake aje kayansa ya dauko card din ya nufota ya kama hannunta ya mikar da ita tsaye ya danka mata.

"In case of.., kuma ba lallai sai kina cikin matsala ba ya kamata ace ko da yaushe ina jin duriyarki domin sanin halin da kike ciki"

"Na gode na jidadin haduwa da kai, ka taimaka min gashi ba ni da wani abu da zan biyaka"

"Zaki biya idan lokacin biya yayi"

Ta yi murmushi tana hawaye sai ya rumgumeta yana jin babu dadi domin zaman da ta yi a gidan ya saba da ita.

"Idan kin tafi karki fasa shan maganinki, kuma ki guje duk wani abu da zai saka miki bacin rai ko damuwa"

Ta amsa masa da kai tana kallon katon hoton dake tsaye gefen mirror sa kamar na cikin hoton zai yi magana. Ta dago daga jikinsa tana cigaba da kallon hoton.

"Mahaifina ne"

Ya amsa mata tun gabanin ta yi masa tambayar. Sai ta juyo ta kalleshi da mamaki ta sake kallon hoton amman bata ce komai ba.

"Kina mamaki ne? Ni ma haka nake mamakin jin cewar Madam Barakat ita ce mahaifiyarki"

Ta share hawayenta ta yi

"Shiyasa nake son tafiya, akwai tambayoyin da ita kadai zata iya amsa min su.

"Fatan alheri"

Yayi fada da murmushi sai ta saki hannunsa tana jin kewarsa tun kamin ma ta bar gidan. Ta fito dakin sai ta sake dawowa falon Momy ta samu mai aikin gidan ta hado mata kayanta a akwaiti har hudu domin Dr A-B ya wadata da tufafi a gidan daidai gwargwado. A sanyaye ta karasa kusa da Momy ta risina kasa

"Na gode da karbata da ka yi, na gode da masauki da hidima da kika yi da ni, na gode Sosai"

"You're Welcome, kina jin kina son tafiya Emily?"

Ta daga kai.

"Okay, ga kayanki an hado, ki shiga ki duba idan baki manta komai ba"

Emily ta girgiza kai domin bata son komawa dakin, ji take kamar ta yi kuka ita ma ta saba da su musamman ma DR AB dake shiga mata gaba a komai na gidan. Duk abun da ake Emily bata kalli gefen da Mama Barakat take ba ita ma kuma bata yi saka bakinta ba sai bin Emilyn take da kallo cikin yanayi marar dadi. Mai aikince ta saukar da kayan kasa aka saka a motar da suka zo da ita Aliyu yayi ma Momy godiya sannan ya mike tsaye yana kallon Emily.

"Zamu iya tafiya?"

Ta kalleshi sannan ta fara takawa ta wuce ya bi bayanta, da suka zo gurin sauka stairs sai ya cira kafa ya rigata sauka just to watching her steps kar ta fadi domin benen mai hawa biyu ne ba daya ba gashi hawaye take ba lallai tana gani da kyau ba. Da suka sauka kasa gaba daya sai ya bude mata kofar falon ta fita Mama Barakat ma ta fita sannan ya fita, sai da Emily ta sauka entrance din sannan ta juyo ta kalli kofar falo, bata sani ba ko zata dawo ko kuma tafiya ce ta har abada, domin kaddara tana hadata da mutane kala kala kuma ta rayu a gida mabanbanta, sai dai a wannan gidan ta hadu da mutane masu karamci da girmamawa.

Aliyu ya bude mata back Seat yana tsaye yana kallonta sai ga kira ya shigo wayarsa ya dayan wayarsa, yana ganin haka ya san Fatima ce domin har yanzu wayarsa dayar tana hannun Fatima, kusan kullum sai ta kira shi tace ya bata Momy zata yi magana da ita ko ta ce ya fadawa Momy ta zo, wani lokacin zai ce Momy ta yi bachi, ko kuma yace ta yi tafiya, ta ce ya turo number ya tura mata idan ta kira ta ji kashe. Shi kanshi fargabar kiranta yake domin kuka take masa sosai idan yace Momy bata nan, wani lokacin ta kan ce shi ya zo amman ba zai tafi ba, idan ta bukaci akaita gurinsa Turhan ba zai yarda ba.

"Hello"

"Bana fadi miki idan kin kira ki rika sallama ba?"

Sai ta yi sallamar cikin kuka.

"Waya taba ki?"

"Momy ce, har yanzu bata zo ba? I miss her i want to see her"

"Bari na kira ki FaceTime"

Ya yanke wayar ya kirata FaceTime yana kallon fuskarta hawaye shabe shabe sai yayi murmushi ya rage volume din ya juya camera from font to back ya nuna mata Emily dake tsaye tana kallon gidan bata san wainar da ake toyawa ba. Wani irin tsalle Fatima ta yi ta fashe da kuka.

"Hi Momy Hi Hi Hi Hi Momy Momy Momy I'm sorry"

Aliyu ya juyo da front camera yana murmushi ya kara volume din.

"Muna Abuja yanzu tare da Momynki, za mu dawo idan muka dawo zata zo ta ganki"

"Okay..."

Ta daga mishi kai tana dariya sosai tana daga mishi hannu alamar bye bye, sai duk ta ba shi tausayi, shi ma ya daga mata hannu ta kashe wayar ya kira sunan Emily.

"Emily"

Ta juyo sai ta kalli motar daya bude ta fara takawa ta nufi motar ta shiga tana ta kallon kofa wai ko Dr A-B zai fito ko Momy sai dai rashin jindadin tafiyarta ya hana Dr A-B fitowa because he don't want to say good bye to her, Momy kuma tana jin kanta ba kasafai take saukowa kasa ba, ba kuma dan wulakanci ba domin bata da wulakanci ko kadan sai dan isa ta naira. Ta shiga ta zauna Aliyu ya rufe motar Mama Barakat ta bude dayan gefen ta shiga ta zauna Aliyu ya shiga front seat sai da suka fice daga gidan sannan Aliyu ya tambaya ko dai su tsaya su kwana Abuja domin to him Abuja gida ce no need to rush, Ummi ma a nan take zauna ba dan abun da ya faru ba da yanzu bata je Kaduna ba.

"Aa mu tafi kawai"

Mama Barakat ta fada, a nan Emily ta kalleta.

"Da gaske ke kika haife ni?"

Mama Barakat ta kalleta jiki a sanyeye.

"Ni ce?"

"Taya? Meyasa kika jefar da ni? Me na yi?"

"Baki yi komai ba, na haife kyakkyawa cikin koshin lafiya, na aje ki a inda na bar ki ne saboda na haife ki ba da aure ba, kuma baki yi kala da ni ba, ina jin tsoron irin kallon da duniya zata min a wacan lokaci ne"

"Amman kin san ina gurin kuma a gurin na rayu? Kin taba tunanin nemana? Ko sanin halin da nake ciki?"

Mama Barakat ta girgiza kai.

"Ban taba ba, saboda ina tunanin kamar abun da na aikata shi ne mafita a gareki da ni, ban taba sha'awar na san wane kike ciki ko rayuwa kike yi ba, tun da na aje ki na rufe shafinki, ban sake ganinki ba sai wacan ranar da kika labarta min labarinki, dana kalleki kuma sai na ga siffarki da yanayinki be sauya ba daga na mahaifinki, kuma sai kika gudu saboda neman mafita, sai n aji tsoron nemanki saboda yarana da aurena da kuma ke taya zan fuskance ki?"

Emily ta yi juyar da kanta ta jinginar jikin mota tana hawaye, hawayen da ba su tsaya mata ba har suka shiga jirgi. A guri daya suka zauna da Mama Barakat a first class, Aliyu kuma ya zauna wani guri dabam ba kusa da su ba.


TURHAN POV

"Momy zata dawo na ganta"

Turhan yayi mata murmushin zahiri badini kuma wata wuce ta ce take cin ransa.

"Wow zata dawo I'm happy, to yanzu sai kije ki ci abinci kar Momy ta ga kin rame ko?"

Ammy ta fada, Fatima ta daga kai har ta fara tafiya sai kuma ta juyo.

"Idan ta dawo zata zauna a nan? Zamu zauna tare? Bana son wani ya sake tafiya kuma"

Ammy ta daga mata kai, sai ta dawo da gudu ta rumgume Turhan.

"Ina son haka"

Ta fada da hausa domin zamanta gidan ta fara tsintar wasu kalamai na hausa, Ammy ta kan gwada mata magana da hausa ta koya mata wasu abubuwa, idan kuma ta ji ana hira aka fadi wani abu sai ta tambaya me aka ce ko me ake nufi har rubutawa take idan yan kwaran suna bisa kai, idan kuma rigimar neman Momy ya tashi bata kula kowa. Sai da ta fita dakin sannan Ammy ta kalli Turhan ta ce.

"Abuja Ummi take zaune, amman a yanzu ance tana gidanta na Kaduna yanzu kuma Aliyu yace suna Abuja za su dawo Kaduna yau, jikina sai yake ba ni kamar aje yarinyar nan suka yi a can na tsawon lokacin nan"

"Ni ma jikina ya ba ni haka, wata kila kuma daman ya san inda take ko da shi ya boye ta ba, ko kuma ya nemota ne, tun da ya fi ni sanin mutane a Kasar nan, yanzu kuma ita sai ta yu tunanin ko ban yi kokarin nemanta ba ne, Aliyu be kyauta min ba, na rasa gane me na yi masa, babu yadda za'ayi ta fahimce ni"

Ya dafe kanta kansa idonsa na cika da kwalla damuwa ta matsa tsaye a rai.

"Ban san dalilin Aliyu na yi min haka ba, amman ni ba zan iya yi ma Aliyu abun da yayi min ba, abota bata ce haka ba, aminci be cancani wannan sakamako ba"

Ammy ta tashi ta dawo kusa da shi ta zauna ta dafa kafadarsa.

"Haka butulci yake da ciwo, amman ka yi hakuri kuma ka yi addu'a idan kuma ta nuna bata son kasancewa da kai, dan Allah ka saka musu ido, mutum be taba cin amana ya ga daidai ba a rayuwarsa"

"Ko ba zata dawo gareni ba, na aminta amman kar ta auri Aliyu, gayen nan ya gama da rayuwata, kuma idan ya sameta hakan ya nuna ya ci ribar abun da ya aikata kenan"

"Idan bera da sata daddawa ma tana da wari ai, idan da can kamin ka bayyana a rayuwarta tana kula Aliyu a yanzu be kamata Aisha ta yi haka ba ko dan yarinyar nan, matukar tana da hankali da tunani yadda dai ka dawo mata ka nuna mata kau??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????na be kamata ka saurari kowa ba sai kai, ita uwa koda yaushe tana son abun da danta yake so ne ko dan farincikinsa"

"Ammy Aisha bata da laifi, Aliyun nan dai shi ne shege, ita ai daman fansa take son dauka shi ne be dace yayi min haka ba, Ammy ko dai naje na taro ta?"

"Ai baka san yaushe zata sauka ba, kuma karamin aikin yarinyar nan ne ta disgaka a gaban mutane, kuma kasan har Aliyu yana gurin sai ya ji dadi ai"

Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi.

"Turhan idan Aisha ta zabi Aliyu ko wani ba kai ba, ka yi hakuri dan Allah ka bi a hankali, kai fa namiji ne kuma kai ka fara wulakanta ta, na san ka yi nadama amman ka kara da hakuri idan ka yi hakuri ita kanta zata dawo maka, ko kuma ja ga Allah ya musanya maka da wanda ta fita alheri, ko kuma Allah ya baka zuri'a da matar da kake aure yanzu, tun da ba cewa aka yi ba zaka haihu ko kuma ita ba zata haihu ba"

Ya mike tsaye cikin rashin jindadin maganar. Ammy ta bishi da kallon tausayi har ya fice, saukowa yayi kasa ya nufi dan karamin dinning din daya siyawa yarsa take zama ta ci abinci ya durkusa a gurin ya dauki spoon din da take cin abinci ya cigaba da bata abincin tana ci data gama ya bata ruwa ta sha sannan ya rumgumeta.

"Fatima ina sonki, kuma ina son mahaifiyarki Allah shi ne shaidata, yanzu ku ne farincikina"

Ta yi murmushi domin ta san ina sonki da hausa Ammy ta koya mata.

"Daddy ina sonki"

Ta yi kwance jikinsa tana jindadi ga babanta kusa kuma ga mamanta zata dawo.
[8/1, 6:32/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL?mode=ac_t



*

*? Khadeeja Candy*



Page 6?? 1??


Suna sauka Airport Aliyu ya kira wayar direba ya sanar masa. Kamin ya iso Aliyu ya nuna Emily gurin zama.

"Zauna a can yanzu zai zo ya dauke mu"

Ta kalli gurin ta fara takawa ta isa ta zauna, sai ya shiga ciki ya siyo mata ruwa ya kawo mata da dan abun tabawa ba, ruwan kawai ta karba ta rike bata kallon sai Mama Barakat data kasa hada ido da Emily.

"Daure ki sha ruwa kuma ki share hawayenki"

Ta fara share hawayen sai ya karSi ruwan ya bude mata ya mika mata ta karba ta sha kadan, ta mika masa.

"Thank you"

Ya fada da murmushi sai ta dube shi, wai shi yake mata godiya saboda ta karbi ruwa ta sha kuma ta share hawayenta.

"Ina kike son tafiya? Gurin Ummi ko gurin Mama Barakat? Tana son ki zauna kusa da ita"

"Ban taba samun abun da nake so ba, duk abun da kuka zaba min yayi"

"Inda ina raye abun da kike so shi zaki samu Emily, dan haka zaki bi mu zuwa gurin Ummi hakan yayi?"

Ta daga mishi kai tana ta kallonshi kamar yau ta fara ganinsa. Ya kai goran ruwan dake hannunsa bakinsa ya sha har lokacin kallonsa Emily take bata ko motsa ido, daya sha ya sauke gorar sai ya sska yatsansa cikin ruwan ya cire ya tsarka mata dogon ruwan a fuska yana murmushi, daman shi yana daga tsaye ne tana zaune, sai ta lumshe ido tana murmushi.
Hakan ya ba shi damar kallon fuskarta ya koreta ta kallo har ya gano ramar da ta yi ta kara mata kyau ne madadin ragewa. Tana bude idon sai yayi hanzarin dauke kansa ya kawar da fuskarsa, a nan ita ma ta samu damar maida biki wato ta dasa masa nata idon tana kallonsa, sai dai ita ba kyaunsa kawai take kallo ba, duk kuwa da kasancewar yana da siffa mai kyau da kwarjini, sai dai ita a gurinta yanzu kyau bashi da value domin kyaun ta bi Khaleefa ya cutar da ita, haka kuma Turhan ma yana da kyau amman kyaun dan maciji, ita a gurin hali shi ne komai kuma zata iya fahimta a yanzu Aliyu yana da banbanci da sauran, sai dai bata san gaba ba.

"Gashi ya zo tashi mu tafi"

Ta mike tsaye tana kallonsa kamar babu wani abun kallo a gurin sai shi. Suka jera a tare suna tafiya har suka isa gurin motar ya bude mata baya ta shiga, Direban kuma ya dauki kayan ya saka a bayan mota Mama Barakat ma ta shiga baya Aliyu ya shiga gaba direban yaja motar suka fara tafiya. A harabar gidan direban ya faka Aliyu ya fara fita ta gefen daya fita Mama Barakat take sai ya bude mata kofa sannan ya zagayaya budewa Emily dake zaune tana jiran ya zo ya bude mata, ta kalleshi sannan ta fito ta ya rufe suka jera shi da ita suka shiga cikin falon da Ummi take tsaye tana jiran isowarta.

"Maraba Maraba da yata, yar dake guduwa ta bar yarta"

Ummi ta rumgume Emily cike da farinciki, sannan ta kama hannunta suka zauna Aliyu ma ya zauna haka Mama Barakat. Direban ya shigo da manyan akwatunan Emily sai Ummi ta kalli mai aikinta ta ce.

"Kulu a dauki kayan nan a shigar da su dakina, daga yau dakina Emily zata zauna"

"Dakinki kuma Ummi"

Aliyu ya tambaya da mamaki. Ummi ta ce

"Eh dakin uwa ai na yarta ne, ba zan sake yin wannan saken da na yi ba kika gudu kika barmu, kika daga mana hankali na fi son kina kusa da ni ina jin motsinki, idan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login