Showing 96001 words to 99000 words out of 253142 words

Chapter 33 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18375

zuciya na shiga tsakaninki da mijinki"

Cewar Mama Barakat tana kokarin zama, ba dan ta ji tattaunawarsu ba sai dan ta ga alamar komai ya wuce a fuskar Kameela da Kuma muryarta.

"Ke yanzu ko kishiya za a miki ai be kamata ki tada hankalinki ba Kameela kina da kyaunki daidai gwargado, mace bata gwada miki komai"

Ta tabe baki.

"Mama Barakat baki ganta bane, kyakkyawa ce kuma yarinya, ina tunanin ma duk yadda aka yi baturiya ce tun a gidan marayu ta tashi wata kila jefar da ita aka yi ko tsintarka, domin gashin kanta ja ne irin na turawa idanuwanta blue ga farinta ma ba fari ne irin na mu ba fari ne irin na turawa"

Mama Barakat ta natsu sai kuma ta yi jimmm kamin ta ce.

"A a ina take?"

"Lagos wai"

"Miye sunanta?"

"Aisha amman Emily ake ce mata"

"Tana da yara? Kina da hotonta?"

"Ni mi zan yi da hotonta? Ko kishiyata ce ai ba zan aje hotonta ba balle wata banzar alaka can gamon tsintsiya da ragga, tana da yara, baban yarinyar ma nemanta yake ruwa a jallo wannan matar criminal ce, kin san daman yan Lagos da wadanda ba hausawa ba ba su da tarbiya ita kanta nemanta yake amman kin ga ta mallakewa mijina, ai Wallahi ina komawa ko dai Aliyu ya zare hannunsa daga gareta ko kuma duk yadda za'ayi ayi, haka kawai wata katuwar banza ta lakewa mijina"

Tana sane take fadar yan Lagos ba su da tarbiya da kuma yare saboda Step Mom din ta ji haushi, ta jefi tsuntsu biyu ne da dutse daya domin ta ciki na ciki ba son Mama Barakat take ba ko da kuwa zata bata duniyar nan, ta mike tsaye ta fice rike da wayar zuciyata cike fal da kiyayyar Emily.


_______________________

Sannu  yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe Winki da kaya masu kyau, masu ?ima daga Khadeeja Candy Store

Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sau?in sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing.

Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taSawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet Winmu sun dace da ke

Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sau?i ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko ina!


Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1

da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0


Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame.

Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ?ayatarwa duk a farashi mai sau?i.

Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu!

Baki da lokaci? Muna da sau?in oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina!

To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08


Ba kawai kaya ba ne salo ne, ?ima ce. A Khadeeja Candy Store.
Ki zo yau, ki WanWani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haWuwa.
[5/25, 9:50/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: *

*? Khadeeja Candy*


SARAC STARS. C - Pen...
'?



FOLLOW ME ON =?G?
FACEBOOK
https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914

TIKTOK
https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1

INSTAGRAM
https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0

CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

KHADEEJA CANDY STORE
https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08



Page 3?? 0??


ONE WEEK LATER...


Ba zata iya musa masa ba, dan haka ta amsa bukatarta ta dora tata bukatar akai. Tun a washe garin wacan ranar ta cigaba da zuwa aikin, sai dai a tsawon zuwan da take bata fada ma Tasmia cewar ta koma aikin ba duk kuwa da irin dukan ruwan cikinta da Tasmia take na son ta ji labarin Aliyu ta, tana yawan tambayarta ya kira ki? Kun yi waya? Emily ta ce mata aa saboda gudun kar Tasmia tace bata dauki shawararta ba, ba kuma dan bata gamsu da shawarar ba, sai dan Tasmia ta bata ba sai dan bata son musawa Aliyu ne.

Kusan tun da ta koma aikin bata hadu da Aliyu ba, ko a hanyar shiga Office dinta ko nashi, hakan kuma sai ya kara mata kwarin guiwa da natsuwa, da fari ta yi tunanin ko zai takura mata ne ko dan neman jin karashen labarinta da Turhan, ko kuma ya nemi wani abu a gurinta ko da yake Tasmia ta fada mata bata gama karantarta namiji ba ne, wata kila haka ne wata kila kuma ita din wawuyace shiyasa ta kasa son mai sonta tsakani da Allah, amman kuma idan bata so Vito ba wa zata so? Ai bata isa ta bude zuciyarta ga wani ba.
Ta gama saka dankunnenta ta dauki jakarta ta fito tana tafiya a hankali, tun da ta fito Chidimma ta hade rai saboda yadda Vito yake kallonta har ta iso gurin dinning din ta dora jakarta ta fara zubawa kanta abinci.

"Good Morning Beautiful"

Ta juya ta kalli Chidimma dake kujera biyu kamin tata. Hakan kuma ba karamin bakantawa Vito rai yayi.

"Why would I called Chidimma Beautiful?"

Chidimma ta ji kamar an tsomata a ruwa tsabar muzantata da yayi agaban Emily, ba kuma dan bata da kyaun ba, sai dan a gurinshi babu wata mace mai kyau sai Emily.
Emily ta kalleshi.

"Because she is pretty, isn't she?"

Ta fada tana kai abinci a bakinta, da ido Vito yayi ma Chidimma magana sai ta tashi ta dauke abincinta ta bar dinning din. Ya dora hannayensa kan dinning din

"Miyasa kike tunanin zan ga kyaun wata mace idan kina nan?"

"Da bata da kyau ai ba zaka sakata a matsayina har ka ci abinci a teburi daya da ita ba, har ka nemi ta dafa maka abinci, ko ba haka ba VITO"

Ta ambaci sunansa da babban baki, madadin yaji haushi sai yayi murmushi, bukatarsa ta biya daman makasudin yin hakan saboda ya gani idan zata ji kishi ne, idan har ta ji kishin hakan ya nuna tana son shi kenan. Ya jimgina da kujerar dinning din yana cigaba da kallonta, kamin ya ciro wayarwa dake vibration ya duba sannan ya amsa kiran. Yayi shiru na dakiku yanayin fuskarsa ya sauya zuwa bacin rai.

"Ganin nan zuwa"

Ya mike tsaye sai ta kalleshi tana kai lemu a bakinta.

"An sake kama kayanka ne?"

Har yayi gaba sai kuma ya juya ya kalleta.

"Nope wani ne yake wasa da rayuwarsa, someone set me up"

Ta aje glass cup din.

"Me kake nufi?"

"NDLEA aka turo su bincike gidana daga Abuja"

Ta mike tsaya da sauri ta karasa inda yake tsaye.

"Kuma zaka tafi"

"Yes ina bukatar na tafi"

"Aa karka je dan Allah bamu san manufarsu ba, gashi kana da saurin fushi ba mu san abun da zai faru ba"

Ya shafa fuskarta.

"Babu abun da zai faru"

Ta rike hannunsa tana girgiza masa kai idonta har ya fara tara hawaye.

"Ya kamata na tafi ko dan na nunawa wanda ya turo su wanene ni"

"Be zama lallai turowasu aka yi ba, sana'ar da kake yi ba mai kyau bace kana jefa rayuwarka be kawai cikin hadari, daman dole wata rana za a iya bincike za a iya ganeka"

Tana maganar tana kuka jikinta na rawa gaba daya ta tsorata.

"Set up ne, NDLEA da suke da nan ko jami'an tsoron duk mutanenmu ne, shiyasa ba ayi amfani da su ba aka turo baki daga Abuja, amman ki kwantar da hankalinki babu abun da zai faru"

Ta girgiza kai.

"Aa karka je"

"Dole sai na tafi ai, suna bukatar ganina"

"Kace musu baka nan"

"Ina nan"

Ya amsa mata yana kai hannanyensa ya rika fuskarta.

"Toh ka aje bindigarka karka je da ita"

"Zata min amfani"

"Idan zaka je da bindiga ba zan bari ka tafi ba"

Ta rumgume shi tana kuka, sai yayi murmushi ya dago ta daga jikinsa.

"Ba zan je da ita ba"

Ta fara lalaben aljihunsa.

"No idan kika taba zata samu shatin hannunki, idan na aikata wani laifi da ita aka yi bincike za a samu shattin hannunki kai, ba ni bukatar haka"

Ya cire bindigar da kansa ya nufi Kitchen ya dauko wata madaidaiciyar cooler ya saka bindigar ciki sannan ya fito rike da wuka ya nufi gurin da Swimming pool dinta yake yayi gina a inda kasa take ya saka cooler ya rufe sannan ya janyo daya daga cikin kujerar da suke aje a gurin ya dora a sama, sannan ya kalleta ya ce.

"Ko da bincike ya biyo ta nan baki da matsala babu wanda zai san da wannan you're safe"

Ya rika hannunta ya jimke ya saki sannan ya fice daga gurin zuwa gurin motarsa. Biyo shi ta yi ta tsaya tana kallonsa cikin tsoro da tashin hankali, shikam damuwa data nuna masa a yanzu ta gusar masa da duk wani bacin rai da ya ji a lokacin da aka sanar da shi abun da yake faruwa a gidansa. Dawowa ta yi falon ta doshi gurin da jakarta take ta bude ta dauko wayarta, number Aliyu ta fara kira domin shi zuciyarta ta raya mata, wayar ta yi ringing har ta katse be daga ba, ta sake kiransa be daga ba ta sake kira be daga ba, sai da ta jera masa miss calls kusan tara sannan ta maida wayar ta dauki jakarta ta fice daga gidan zuwa gurin aikinta cause she want to see him badly...




ALIYU POV.

Tana kallon yadda ya saka wayar da ake ta kira tun dazun a aljihu ya ki ya amsa kiran sai ma saka wayar da yayi a silent kuma ya ki ya aje a inda zata ga sunan mai kiran zuciyarta ta raya mata ba kalau ba, amman bata nuna masa ba da ya gama saka turare ta mika masa agogon da ke aje, ya karba ya fara sakawa.

"Yaushe ka siya agogon nan Honey?"

"Wannan agogon ina da shi, bata yayi sai yanzu na ganshi"

"Da alama yana da muhimmanci a gareka kusan tun da na dawo kullum shi kake sakawa idan zaka je aiki"

Ya kalleta da dan mamakinsa domin be yi zaton ta maida hankali a gurin ba.

"Toh har kin saka min ido kenan, yana da tsada ne shiyasa duk wanda zai gan ni da shi zai san babban agogo ne"

"Hmmm"

Ta furta sannan ta mike tsaye ya kama hannunta suka fito seating room, sai da ya fara ja mata kujera ta zauna sannan ya zauna ya ciro wayarsa gudun ya zaune ta domin ya sakata aljihun bayan wandonsa ne, sai ya ci karo da sakon Emily.

"Na zo baka shigo ba, ka yi sauri ka shigo akwai matsala"

A take ya mike tsaye ya fasa cin abincin Kameela ta daga kai tana kallonsa.

"Lafiya"

"Lafiya kalau, wani uzuri ne ya taso zan tafi Office yanzu"

"Abincin fa"

"Ki ci zan samu wani abu a can na ci"

Ya sumbance ya sannan ya fice da sauri tana kallonsa. Ya shiga motar sa yana karanto addu'o'i yana tukin har ya isa gurin aikin, kusan al'adarsa karanta addu'a idan ya shiga motar da safe, ya faka a inda ya saba fakawa ya fito ya nufi cikin ma'aikatar, sai da yayi kamar ya fara shiga office din Emily saboda ta fada masa akwai matsala sai kuma ya yanke shawarar fara tafiya Office dinsa albashi ita sai ta same shi a can. Ya shiga office dinsa bayan ya gaisa da sakaterinsa Nick ya shiga cikin Office din ya zauna, sannan ya kira wayar Emily bata daga ba, ya sake kira bata daga ba, sai ya aje wayar yana mamakin matsalar me aka samu? Tana office dinta ko kuma ta wuce gida? Ya sake daukar wayar ya sake kiranta bata daga ba, ya sake kira sai ya ji user busy alamar tana waya, wannan karon be aje wayar ba sai da ya tura mata sako cewar ya shigo ta same shi a office dinsa sannan ya aje wayar ya nufi fridge dinsa ya bude ya dauko gorar ruwa ya rufe, ya murda murfin ya bude ya kai gorar bakinsa, juyowar da zai yi sai aka turo kofar Office din aka shigo ya cika bakinsa da ruwa yana kallon Kameela dake sanye da green Hijab har kasa hannunta rike da bracket. Ya hade ruwan yana kallonta da mamaki.

"Me kike yi a nan?"

"Kana ta sauri ka fita baka yi breakfast, ni kuma hankalina ba zai kwanta ba idan ka wuni da yunwa shiyasa na biyoka da abun karyawa a nan"

Ta karasa kusa da shi ta dora bracket din kan teburinsa tana kallonsa da murmushi a fuskarta.

"Okay Thank You Dear, amman Baki fada min zaki zo ba, kin san bana son ana fita ba da izinina ba ko?"

"Haka ne am sorry"

"Me kike hau kika zo nan"

"Taxi"

Ya dauki wayarsa da nufin turawa Emily sako sai ga Emily ta turo kofar office din ta shigo, daga Aliyu har Kameela juyowa suka yi suna kallon Emily da ta yi tsaye ta kasa karasa inda suke tsaye, Aliyu ya dauke idonsa daga kallon Emily ya kalli Kameela, to his greatest surprise ever sai ganin yayi Kameela na murmushi kamar babu komai.

"Karaso mana Emily shigo"

Ta fada sannan ta juyo ta kalli Aliyu.

"Ashe nan take aiki? Maa Shaa Allah tana da kyau gaskiya"

Ta sake duban Emily tana danne wani turnukun fadan ibilisan dake kirjinta.

"Toh bari na tafi na barku ku yi aikinku, daman na kawo masa abun karyawa ne, idan ke ma baki karya ba sai ya sam miki ki karya"

"Kawai na zo nan ne na.... Na..."

Emily ta makale a maganar ta ki ta fita, Kameela ta karasa kusa da ita tana murmushi ta dafata.

"Karki damu, ba sai kin min bayanin komai ba, ki gaishe min da yarki Fatima"

Ta nufi kofar fita ta bude office din ta fice, Aliyu yayi saurin bin bayanta, sai suka sauka kasa tare.

"Muje na sauke ki gida"

Ya fada yana kallon yanayinta har lokacin bata nuna masa komai ba.

"Okay"

Ta bi bayansa suka isa gurin motar ya bude mata ta shiga ya zagaya ya shiga yaja motar, bata ce masa komai ba har suka isa gida shi kuma sai sake saken yadda zai bullo mata yake ba dan yana tsoron ta ba sai dan yana gudun bacin ranta, kuma ya san ko da ace bata da wannan zafin kishin idan ta ganshi da wata dole zata yi kishi balle tana da shi. Sai da ya faka harabar gidan sannan ya ce.

"Da zaka min uzuri ki fahimce ni Kameela..."

Bata bari ya karasa ba ta tari numfashi.

"Dan Allah kar mu yi wannan maganar da kai, ka kaddara ban ga komai ni fa yanzu na yarda da kai, ba ni da matsala ko cikin mata dubu zaka shiga na san zaka fita, hakan be daga min hankali ba ko kadan"

Ta bude motar ta fita tana murmushi.

"Allah ya tsare me zan dafa maka?"

"Anything"

"Okay I Love you"

Shi dai mamaki ya hana shi amsa mata da I love you too sai kallonta yake kamin yaja motar ya fice. Ya faka a inda ya gurin da aka tanadarsa domin aje motarsa sannan ya fito ya shiga cikin ma'aikatar ya shiga Elevator ya sauka hawa na biyar ya shiga office side dinsa, fada Sosai yayima Nick.

"This isn t professional behavior, why would you allow anyone into my office without notifying me first?"

"Apologies, sir. I allowed her in because I recognized her as your wife. As for Emily, she's one of our staff, and you had previously instructed that any staff member who needs to see you should be allowed in. That s why I let her through"

"That policy is now revoked"

Aliyu ya fada a fusace. Nick ya amsa masa cikin ladabi da girmamawa.

"Understood, sir. I apologize and will be more careful going forward"

Ya wuce ya shiga office dinsa. Zaune ya samu Emily ta hade kanta da guiwa.

"Miya faru minene matsalar?"

Kamar jiransa take ta dago.

"Miye ma be faru ba? A wane dalili zaka aikawa Vito da jami'an bincike masu tu'ammali da miyagun kwayoyi? Me ya maka"

Aliyu ya dan yin kamar mai tunanin waye kuma Vito.

"Vito.. Vito... Oh Vito? Me zai saka na yi haka toh? Miye alaka ta da shi?"

"Ni dai na fada maka, idan wani abu ya same shi kamar ni ya sama, domin shi yake dauke da ni, kuma shi ne mutumen da ya taimake ni a lokacin da babu mai taimakona, shi ya maida ni a yadda nake a yau, ko farcensa bana son wani abu ya sama"

"Ahh ahhh ni kika gani kofar gidansa ne? In banda dai kina son ki dora min laifi?"

"Indai kana son na cigaba da aiki a nan na cigaba da mu'alama da kai, to ka cire Vito a idonka"

Ta fada masa har tana nuna shi da yatsa. Ya kalli yatsanta ya kalleta be ce komai ba ya nufi kujerarsa ya zauna ita kuma ta juya ta fice daga office din. Sai da ta koma office dinta sai ya fara jin haushin abun da ta yi ma Aliyu bata san lokacin data fashe da kuka ba, ya wuce makadi da rawa amman bata da zabin da ya wuce haka, saboda gudun jefa Aliyu a matsala, ta san watan wata rana Vito zai iya ganowa kuma komai zai iya faruwa idan ya sani, haka kuma ba ta so wani abu ya samu mutumen da ya tallafawa rayuwarta ta sanadinta ba, ko da yake bata da tabbacin Aliyun ne, wata kila Vito ba zai rasa makiya ta wani bangaren ba tunanin haka ya kara jefa ta a damuwa. Kasa aikin komai ta yi duk kuwa da kasancewar ta yi waya da Vito ya fada mata babu wata matsala har sun tafi, amman kunya da nauyin abun da ta yi ma Aliyu be bari ta iya komai ba a ranar.


ALIYU POV.

Sai da lokacin tashi aikinsa yayi sannan ya sauko compound din ma'aikatar ya nufi motarsa ya shiga ya saka basket din da Kameela ta kawo masa dazun be taba komai ba, yana shiga motar ya amsa wayar mahaifinsa, ya fara tukin da hannu daya dayan hannun kuma manna da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login