Showing 60001 words to 63000 words out of 253142 words

Chapter 21 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18385

cin hanci nake bata, shi kuma da zarar ya ga flashing dina zai kira mu dade muna yawa, idan yana son ganina kuma zan boya na tafi nesa da gidanmu na hadu da shi mu ga juna, a gaskiya na so Khaleepa a wacan lokacin irin son da idan ina tunaninsa bana iya bacci, idan ban yi waya da shi sai na wuni cikin wani yanayi na rashin dadi, a makaranta gurin aiki bana da komai sai tunaninsa.

Wani lokacin zai yi min siyayya sai na boya na shigo da ita ba zan fadawa kowa ba, ranar da Marry wacce take kasan gadona ta gane ina soyayya ta tsare ni da tambaya har sai da na fada mata shi ne mutumen da muka hadu kuma na fada mata shi musulmi ni, sai ta fusata kuma ta tsorata ni cewar ai su musulmai basa auren kafirai, kuma a arewa ba a son wanda ba bahaushe ba, arna suke kiranmu, a madadin na yi nazarin kalamanta sai soyayya ta rufe min ido na fara gaba da ita. Na same shi da maganar tabbas a lokacin, sai ya karyata abun da ta fada, a nan yake fada min asalinsa da gidansu da garinsu da yake kauyen Kaduna. Ya nuna min fargabarsa ta daga gurin inda nake zaune ne, yana ganin kamar ba za a yarda a aura masada ni ba, a lokacin ni ma hankalina ya tashi domin na san ba za su yarda ba.

Haka dai muka cigaba da soyayya, yana fada min idan ya aure ni, zamu yi rayuwar aure mai kyau, zai nuna min soyayya zamu rika cin abinci a tare wanka kwana komai kamar na masoya, ashe karya yake amman ni ban gane ba, kawai abun da ke daukar hankali kyaunsa da kuma yadda be taba yarda ko da wasa ya taba nuna son taba jikina ba, har ta kai yana kiran mahaifiyarsa ya ba ni mu gaisa, be min karya ba ya fada min sana'arsa kuma ya fada min shi dan kaduna ne, amman a kauye suke zaune tare da iyayensa. Soyayya da muka fara da Khaleepa kusan kamar ta budewa maza kofa ne, domin babu ranar da zan fita wani be nuna yana so na ba, amman bana sauraren kowa sai shi, idan naje church kullum addu'ata na yadda kowa zai amince na aureshi ne.

Ana haka wata rana aka shigo kirana tare da sauran yan mata sa'anin na, muka tafi sai muka samu wasu manyan mutane ne suka zo neman ya da zasu rike kamar su suka haifeta. Daman akan yi hakan wasu jarirai suke so, wasu kuma wadanda suka dan tasa, amman ita tace tana son matashiyar buduwarwa, domin ta taba daukar jaririya kuma ta reneta tana can hannunta a gurinta ta girma. Matar tana yin arba da ni, sai ta zabe ni, suka ba ni damar tafiya na shirya domin a ranar zan tafi bayan ta yi duk abun da ya kamata, a ranar na sha kuka sosai a gurin abokan zamana na gidan, domin tun muna yara muka taso tare, har na ji kamar kar na bita, sai dai kuma ina son tafiya ni na shiga family na samu wanda zata rike ni a matsayin ina son na rumgumeta na ji yadda ake ji.

Gidanta babba gida ne a lagos tana da masu kyau, ga manyan motoci da ac abinci sai wanda na zaba nake ci, tun a ranar da aka kawo ni ta fada min ita bata taba haihuwa ba, tana da jiki sosai likitoci sun ce kitse yayi mata yawa ba zai barta ta haihu ba, hakan ya saka take son rike yara kamar yaranta. Ta nuna min kauna tace zata rike ni kamar yarta, ban maida sati a gidan ba aka canja min makarantar da nake zuwa makarantar masu kudi makaranta mai kyau. Mukan zauna musha hira da ita idan na dora kaina a jikinta sai na yi ta kuka, ashe dai ni ma wata rana zan samu masu sona.
Ta tambaye ni a ina na iya duka yaruka hudu da nake ji, na fada mata yaren Igbo da yarbanci daman kowa ya iya a Lagos domin mun tashi mun ga su ake amfani da su, turanci kuma ba iya a makaranta, hausa kuma na koya a gurin Oga Shakur da yaronsa da ya kasance bahaushe.
Kwakwalwata tana da saurin fahimtar abu, kusan duk abun da na sakawa raina zan iya na kan iya cikin kankanen lokaci, haka ya saka tun ina primary har secondary school ni nake dauko ta daya aji.

Sai da na yi wata biyu a gidan sannan na samu damar aron wayar mai aikin Momy kamar yadda muke kiranta na kira number Khaleepa da tuni na haddaceta, da na kira shi kamar zai yi karamar hauka saboda yadda nake ta jiran kirana a koda yaushe, ni kaina sai da na yi kuka, daman dauriya kawai nake amman duk tsawon kwananki da na yi a gidan da jindadin da nake samu bana jin farinciki saboda bana jin muryar Khaleefa.
A ranar be iya bachi ba sai da na fita na tambayi mai gadin gidan ya fada min yadda zan masa kwatance ya zo ya same ni a gidan muka gaisa, a nan kam ban da fargaba duk kuwa da kasancewar ban gama sanin halin matar ba, amman dai da alama tana da fahimta kuma tana da kirki ina ganin kamar da alama zata bar ni na auri Khaleepa, ya kawo min waya a ranar keypad da sabon layi saboda ba zai iya jure rashin jina ba, ba tare da fargabar komai ba na karba na shiga da ita gida, ban boye mata ba na nuna mata wayar na fada manta wanda ya kawo min.

"Saurayinki ne"

Na daga mata kai ina murmushi ita ma ta yi murmushi.

"Ashe na kai ga buduwar, bari na fara shirin aure"

Na rufe ido ina dariya, ta tambaye ni sunansa da kuma inda muka hadu na fada mata komai, a take yanayinta ya sauya, sai ta karbi wayar hannuna tace zata aje sai idan mai gidanta ya dawo kasancewarsa matafiyi, idan sun tattauna abun da ya dace zata ba ni wayar, ban jidadi ba amman haka na daure na cigaba da waya da Khaleepa da wayar mai aikinta. Wata rana sai ta kira ni tare da mijinta suka zauna da ni suka fada min ilolin da suke cikin auren musulmi, ta yi ta fada min kalamai marasa dadi akan musulmai da kuma yan arewa, ita da mijinta burinta su cusa min kyamar musulmi kamar yadda ake yi sauran yara, ta fada min na yi kankanta da fara soyayya a yanzu, kuma Khaleepa ba ajina ba ne domin shi achaba yake yi, ni kuma a yanzu na kalli irin gidan da nake rayuwa.

Soyayya bata da hankali bata ji bata gani, duk ban ji abun da suka fada min ba, a haka na nuna musu ni dai ina son Khaleepa ba zan rabu da shi ba, sai suka saka min dokar ba zai sake zuwa na fita ba, kuma ba zan sake waya da shi ba, haka kuma ba zan ma taba aurensa ba, idan ma ina wannan tunanin na aje. Suka saka min kulli mai tsanani bana zuwa koma'ina daga gida sai makaranta sai kuma idan mun fita siyaya, ko kuma ranar Sunday muna fita zuwa church. Sun min gata sun nuna min soyayya suna kashe min kudi amman duk bana gani saboda Khaleefa ne a rayuwata, kullum cikin kuka da damuwar rashinsa nake, ban sani ba a lokacin ashe hawaye ba su cancanci zuba saboda shi ba.
Wata rana mun je Church, na sulale na ari wayar wata mata na kira shi na fada masa dokokin da Momy ta saka min ita da mijinta kuma sun ce ba zan aure shi ba, a wayar ya rika kuka yana fadin Innalillahi idan na rabu da shi zai halaka zai mutu, ni ma na rika kuka ina jin kamar ma na kashe kaina domin ban taba soyayya da kowa ba sai da shi.

"Emily zaki iya aurena a kowane hali?"

Na rasa taya zan amsa masa.

"Amman ba addininmu daya ba Khaleepa"

"Karki damu da wannan addinin musulunci ya yarda mu auri wanda ba addininmu daya ba, kuma na san idan kina so na zaki musulunta domin ki aure ni"

"Zan iya ina kaunarka sosai Khaleepa"

"Emily zaki iya bina mu gudu? Idan ba haka ba ban san wata mafita da nake da ita ba, daga wannan wayar ma ban san ta ina zan sake jin muryarki ba, kuma muna nan ba za su bari mu kasance da juna ba"

"Idan mun guda ina zamu je"

"zan gudu dake mu koma kaduna gurin iyayena, zaki zauna a can a daura mana aure mu zauna a can"

"Ina tsoro ba zan iya ba Khaleepa"

Duk wata kalma da zata raunata ni ta sanyaya min guiwa da zuciya sai da ya nemo ta ya fada, amman ban yarda be shi ba. Na koma gida ina ta tunanin mafita amman ban samu ba sai wanda ya kawo, gashi kaunarsa sai kara ruruwa take a zuciyata, da kaina na samu Momy a dakinta ina kuka na fada mata ina son Khaleepa ta bar ni na aureshi, madadin ta tausaya min sai tace idan na sake mata maganarsa sai ta min duka kuma ko zan mutu ba zata taba bari na auri musulmi ba. Ranar mutuwa ce kawai ban yi ba tsabar bakinciki da nadamar kin bin shawarar Khaleepa na bishi mu gudu. Da sati ya zagayo muka je church Momy ta saka pastor ya dafa kaina ya rufe ido yayi min addu'a, bayan an zauna zaman church ana tsaka da wakar church na saci kafa na fice daga cikin church din daman Momy tana zama a gaba ne mu muna zama baya. Na fito na ari wayar mai gadin church din na kira Khaleefa na fada masa yanzu na amince zan bishi mu gudu.

Sai ya fada min inda zan je na jira shi, haka kuwa aka yi ba bawa mutumen wayarsa na fice daga church din na tari okada na fada masa inda zai kai ni, ko da na isa na samu Khaleepa a gurin tsabtsab da shi kamar kullum, yana jirana. Ya sallami mai okadan ya goya ni ya tafi da ni wani kangon gidan ya aje ni a nan, be dawo ba sai dare ya dawo da kudi mai yawa ya fada min ya siyar da babur dinsa kudin ne zamu hada da wanda ke gareshi mu tafi garinsu. A gurin ya bar na kauna ni kadai shi kuma ya kwana a inda ya saba washe gari da asuba dai gashi tare da kayansa, ba bishi muka isa tasha ni da shi muka kama hanyar Kaduna.
Shi a tsorace ni, a tsoroce hankali be kwanta ba sai da muka isa cikin garin kaduna. Garin da ban taba zuwa ba kuma ban taba saka ran zuwa ba ko a mafarki sai ranar. A cikin tashar ya saka ni saka hijabi, kusan ko'ina muka bi kallona ake saboda farin fatana ba fari ba ne na sauran mutane, fari ne mai haske sosai da ya fi kama da na turawa ga kuma idanuwa blue. Tashar muka bari muka isa wata dabam muka hau motar garinsu Khaleepa, garin da basa son tubaben, basa marasa ba ni, bana tausayin kaddara da kuma kuskure da na aikata, garin da suka koya min hankali da sabon karatu, suka maida ni wulakantacciya.






_________________________


A jiya na yi mistake a page 17, na yi page din ne kamin na canja akalar labarin, bayan na canja kuma sai ya zama na manta ban yi editing ba, wadanda suka karanta wanda na yi ba edited one ba, za su ga Nace Emily baka ce, ku manta wannan kuskuren ku shafe shi a Kwakwalwarku, ni yar adamce ina kuskure dole na.
Emily fara ce kamar yadda aka fada tun a farkon labarin.


Shin zaku iya fada min abu daya zuwa biyu da kuka fahimta a page din yau kawai?

Kuna son a karo? Zo na gani a kasa, ance da kare ana biki a gidanku yace mu gani a kasa=??

Ma'ana ku suburbudo comments na suburbudo muku pages>??


Don't forget to follow my channel https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01


*Karku manta ku yi Sharing*
[5/1, 8:59/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy




*? Khadeeja Candy*


SARAC STARS. C - Pen...
'?


Page 2?? 0??


Mun sauka garin Rizaga (Sunan garin kirkiren ne)
Da dare sosai kusan sawun mutane da yawa ya dauke. Daga tashar garin ya dora ni a babur shi ma ya hau daya muka kama hanyar gidansu, tafiya muka yi mai nisa sannan muka isa.
Da duk inda muka bi muna ganin mazan garin kwance wasu a bakin kofafin gidajensu wasu kuma a fili.
Bayan mun sauka ya biya mai achaban su biyu sannan ya nufi kofar gidan data kasance katuwa da aka yi da gambun kwano.

"Su waye a nan?"

Na ji an tambaya, sai Khaleefa ya nufi daya daga cikin maxan da suke kwance a wajen yace ni ne baba, mutumen ya dauko fitilarsa ya haska fuskar Khaleefa duk kuwa da kasancewar akwai hasken wutar nepa.

"Lafiya? Hamza kai ne a dare haka?"

"Lafiya kalau Kawu, bari na shiga ciki"

Sauran mazan duk suka tashi zaune suna gaisawa da shi suna tambayar lafiya ya ce musu lafiya kalau.

"Da muka a kuke tare?"

Ya tamabaya bayan ya haska fuskarta.

"Zuwa da safe za ku ji komai ba Kawu"

Ya nufo ni muka doshi cikin gidan, Tun kamin mu shiga gidan na gama fahimtar gidansu family house ne, ashe kuwa na canka daidai da muka shiga ciki sai na bangare bangare na gidan, yana gaba ina biya har muka isa bangare da mahaifiyarsa take, tana cikin bachi ya tasheta ta zabura tana daura dankwali.

"Hamza lafiya? Saukar dare? Kuma baka fada mana zaka zo ba?"

"Lafiya kalau Inna, ga dai bakuwa na zo da ita a bata gurin ta kwanta, kuma idan akwai abinci a bata ta ci zuwa sa safe za mu yi magana"

Ta kalleta daga sama har kasa a lokacin ina sanye da jean sai hijab din da Khaleepa ya siya min

"Sannu da zuwa zo nan ki zauna"

Na gaisheta ta amsa min, na karasa na zauna a inda ta nuna min zuciyata cike da tsoron abun da na aikata da kuma wanda zan tarar. Tuwon gero aka kawo min da miyar kuka, luma daya na yi na gagara ci domin ban san miye tuwon gero ba a lokacin, miyar kukar ma ban taba jin sunanta ba sai a ranar. Haka na kwana da yunwa, washe gari tun da asuba na ji garin ya karade da kiran sallah, Wallahi idan na ce ban jidadin sautin da na ji ba na yi karya, natsuwa ta sauko min, sai na ji kamar ina cikin wata duniyar ta dabam...

A daki aka maida min shimfidar su kuma suka yi sallah a ciki, tun da na shiga bachi mai nauyi yayi gaba da ni, ban farka ba sai karfe tara na safe, ban sani ba ashe Khaleefa yana nan yana rigima da iyayensa akan cewar ba zai maida ni domin shi a yanzu tsoron komawa garin Lagos yake, kuma ni na yarda na biyo shi ba cilasta ni yayi ba. Suka kira ni aka tsare ni a gaban manyansa suka tambaye ni, da amincewata ya taho da ni na fada musu cewar eh ni na mince masa na ce masa mu gudu domin iyayen dake rikona ba za su bar ni na aure shi ba, kasancewar shi musulmi ne, suka sake tambayata shin zaki musulunta ki auri danmu? Na amsa musu a take cewar eh zan musulunta.

Sai suka yi farinciki suka nuna jindadinsu musamman mazan, amman mahaifiyarsa kamar bata yaba da hakan ba. Da yamma aka aiko mai gari yana neman yarinyar da aka zo da ita da kuma Khaleefa. Muka tafi har da iyayensa irin bayani na yi a nan shi na yi a can shi kuma haka, mai garin ya gamsu yace gobe idan Allah ya kaimu za a kai ni gurin limamin garin na musulunta kuma a daura mana aure, suna tambaye ni wane suna kike so nace musu Aisha Muhammad, haka nake son sunana ya zama.

A lokacin farinciki ne kamar ragagge ne, sai ya zama ban ji wani dauki na auren ba sosai ba, wata kila kuma ishara ake min cewar babu alheri a ciki. Yadda mai garin ya fada haka aka aiwatar washe gari aka kai ni gurin wani limani na musulunta kuma suka daura mana aure, kusan kowa zuwa yake kallona har sai an boye ni, abubuwa biyu ke kawo su, jin cewar ni ba musulma bace da kuma yanayin hallitata.

A dakin mahaifiyarsa na fara zama kamin ya gina mana karamin dakin da zamu zauna a tare a bangaren mahaifiyarsa, ya siya mana katifa da zanen gado da dan abubuwan bukata na aikin gida domin ni ba ni da kowa kuma bani da kudin siya. Sannnu sannu ya fara koya min sallah karatun sallah da wasu gajerun addu'o'i kasancewata mai saurin gane abu sai na fara fahimtar yadda zan yi ibada ta.

Kusan a lokacin bani da wata matsala kamar yadda idan na gaishe da mahaifiyarsa take amsa min kamar dole, ga kuma rashin iya girki, ya siya min gawayi da murhun gawayi ina girki da shi, akan girka shimkafa ko taliya, ko indomie na girka chabewa take saboda ban taba girki ba, shi kuma yana da saurin fushi, ko kirana yayi na dade ban amsa ba ko ban zo ba sai ya fusata, ya fara fushi da ni, ko gaba, idan ya fara gaba da ni sai ga na zama kamar marainiya yake kula ni, domin ba ni da kowa a garin, gashi mutanen gidan sun ki su saba da ni, ni ma naki sakewa da su, kullum ina ciki daki.

Abun da na fahimta bayan aurenmu shi ne Khaleefa yana da farin jinin yan matan garin, shi ka kansa ya fada min kuma kanwarsa da ke dan leko ni muna taba hira wani sa'in ta fada min. Ban kuma yi mamaki ba domin yana da kyau ni kaina kyaun ne ya dauki hankalina a lokacin, gashi ya iya wanka idan ya shirya ba zaka taba yarda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login