Showing 24001 words to 27000 words out of 253142 words

Chapter 9 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18400

miki shiyasa ba zaki amsa ni ba idan na miki magana, amman na san ki mahaifiyarki ta nuna min hotonki a wayarta tun da dadewa shiyasa yanzu ma ina ganinki na gane ki

Ta juyo ta kalleshi.

 Da gaske

Ya daga mata kai.

 Uhm-

 To waye kai?

 Ni...

Ya nuna kansa yana tunanin me zai fada mata, sai ta ce.

 Are you her new boyfriend?

Ya wara ido.

 Boyfriend? No... Karki ji haushi ki yi kishin Babanki

 Ni ba ni da Baba ai, Momy na tace bata haife ni da Baba ba, tsaya ma ka ji sunana Fatima Aysha Emily, amman yayana yana da Baba shi sunanshi Londom Hamza, amman shi babansa ya mutu kamar yadda Momy ta fada, amman ni ba ni da Baba, amman ka ga kowa yana sa baba ko a makarantarmu kowa yana da baba ban da ni, shiyasa na matsu Momy na ta yi new boyfriend so that na samu Baba, saboda na tsani Vito bana son shi shi kuma wai yana son Momy ne, amman ni bana son shi....

Sai da ta kai ayar zancen sannan ta numfasa, mamaki da burgewa ya saka Aliyu jan numfashi.

 Hmmmmm wannan yarinyar ya a je da ke Hi-five

Ya mika mata hannu ta mika masa nata suka taba, shi kam abun nema ya samu daman bincikarta yake son yin, sai kuma yayi sa'ar ita din ku ace gurin magana, ya kama hannunta yana murmushi tunawa da yayi da matar dazun wanda tace idan ta sake masa magana ya kirata da aku and he did.

 Ciki zaki shiga?

 Eh Momy na tace na zo na same ta a nan saboda yau nannynmu tana gurin London ba shi da lafiya yana asibiti shi sickle ne kuma Autisms, baya yarda da mutane sosai daga Vito sai Nanny Chidimma sai Momy sai ni

Ya nufi elevator ya danna ta bude. Sai da suka shiga sannan ya sake tambayarta.

 Shi Victor shi ne Babanki? Ko saurayin Momy kika ce ko?

Ta tofar da yawu.

 Allah ya kiyaye bana son shi, sunan shi Vito not Victor Vito sunan yan Italian ne da aka samo daga latin word  Vita Vito yana nufin rayuwa, sunansa ke nan?

 Amman miyasa kika tsane shi? Ba shi da kyau ne

 Yana da kyau, amman baya yin dariya, and wata rana idan Momy ta bata masa rai sosai yana dukanta, i just hate him, kawai ina zama da shi ne dan dole, amman Momy tace da sabon aikin da ta samu yanzu zata siya gida zamu koma can Vito ba zai sake zuwa gurinta ba

Aliyu ya daga girarsa sama ya sauke yana tan tabe baki kadan.

 Wow, okay

 Ina son haka, and na san idan Momy ta bar gidan Vito zata samu Boyfriend sai ya zama Daddyna, ni ina son Daddy

Aliyu ya rage tsayinsa ya kama fuskarta ya rike cike da tausayi, ko bata fada masa uwarta ba ya fahimci akan waye take magana, secondly fuskar abokinsa dake shimfide a yarinyar yake kallo.

 Amman kai kana da girlfriend?

Yayi murmushi kawai ya mike tsaye ba tare da ya amsa mata ba. Ita ma bata sake cewa komai ba har suka sauka a 5floor.

 Momy na tace a 4 Floor zan sauka office na biyu hannu dama shi ne nata

 Na sani, ina son na kai ki office dina ne mu gaisa

Ya shiga office din yana rike da hannunta, ta bude ido tana ta kallon office din.

 Amman kai ya sunanka?

 Aliyu

 Okay Mr Aliyu are you Muslim or Christen?

 Muslim amman Momy na Christen ce, but her name is the Aysha

Ya bude fridge dinsa ya dauko mata lemu ya bata.

 Taya kika zama musulma mamarki ba musulma ba?

Ta nufi kujera ta zauna ba tare da ta jira ya mata izini ba.

 Okay, Momy na tace babana musulmi ne shiyasa ta saka min suna Fatima kuma na tashi ta ga ina son musulunci shi ne take barina ina yi, ta koya min sallah, ta fada min ita ma ta taba yin musulunci, amman yanzu ta daina

Ya zauna a kujerar dake facing din wanda take zaune.

 Kin fada min baki da baba? Taya kuma zaki ce babanki musulmi ne?

 Ni ma haka Momy na ta fada min, shiyasa nake son ta samu new boyfriend ya zama daddy na, amman kai kana da mata?

 huh-?

Ya bude baki not knowing what to say. Ta yatsina fuska.

 Kana da ita?

 Uhhhh No

Ya amsa mata saboda ta saki jiki da shi ya samu abun da yake so.

 Okay Good

Ta masa thumb up ta fara shan lemun da ya karba ya bude mata ya bata, ya ciro wayarsa ya dauketa hoto.

 Hoto kake daukata?

Ya juyar da wayarsa ya kalli wayar ya manta flashlight din wayarsa a kunne yake.

 Kin min kyau ne shiyasa nake daukarki hoto, kina da kyau, zan so haihuwar kyakkyawar yarinya irinki, so ina son na dauko hotonki ne na aje ina kallo a wayana, saboda mamanki tana min rowarki ba zata tura min hotonki ba

Ya fada mata haka ne saboda ya wanke kansa.

 Why? Ko zaka sace ni ne?

 Nooooo ta fada min akwai hotunanki masu yawa a wayarta, nace ta tura min tace aa ba zata tura ba

 Idan kana so zan tura maka

 Taya?

 Zan karbo wayar Momy na tura maka

 Aa ai ba zata yarda ba, amman ina son ki yi a boye, zan rubuta miki number na sai ki saka a wayar Momynki ki duba whatsapp dinta ki tura min hotunan ta can idan kika tura sai ki goge karki bari ta sani, kin iya turawa ai ko?

Ta daga mishi kai.

 Na iya, amman ban iya gogewa ba

Ya bude whatsapp din wayarsa ya nuna mata yadda zata goge.

 Kin gane?

 Yes

Ya tashi ya bude karamar durowa ya dauko katinsa ya bata.

 Idan kika gama sai ki jefar da katin a inda ba za a gani ba

 Okay

Samun hotonta da hoton mahaifiyarta zai taimaka masa sosai gurin samawa abokinsa mafita cikin sauki.

Ya matsa kusa da ita ya rumgume ya sumbanci kanta, sai ta lafe a jikinsa ta yi shiruuuuu kamin ta dago ta kalleshi ta yi murmushi.

 Muje gurin Momy ki kar ta nemi ki bata ganki ba, amman wannan sirrinmu ne ba zaki fadawa kowa ba haka ne

 Yes

 Yanzu na san dalilin Mamankin na cewa kar ki yi magana da wanda baki sani ba, you're talkative

Ya fada a ransa domin samu abun da yake so cikin sauki, ya kama hannunta.

 Mu tafi

Ya rike hannunta suka fita office tana kara masa wasu labarunka da be sani ba, amman hankali ya tafi wani guri he just can't wait ya nunawa abokinsa hoton yarinyar nan da kuma mahaifiyarta, ya san ba karamin dadi Turhan zai ji ba na samun Aysha kawai balle kuma ace ya ga yar nan mai kama da shi.




EMILY POV.

Ta kalli wayarta dake ringing ganin sunan driver Fatima ya saka ta mika hannunta da yayi tsami saboda typing din da take tun safe ta dauki wayar cike da gajiya.

 Hello

 Ranki ya dade gani na iso gurin tare da Fatima

 Bata wayar

Ya mika mata kamar yadda ta umarce shi.

 Hi Momy

 Hi Baby ki shigo ciki zaki ga Elevator irin wanda muke hawa a New York da Abuja kin tuna? Sai ki taba number 4 idan ya iso office na biyu hannun dama shi ne nawa

 Okay Momy

Ya aje wayar yana mika ji take kamar ta gudu saboda wahalar typing din da take amman babu saboda muradun dake zuciyarta. Kamin ta kalli kofar office din wata matashiyar yarinya ta turo ta shigo.

 Hi

 Hi how can i help you?

Matashiyar ta karaso kusa da ita.

 Sunana Raheenatu, ni ce sabuwar Assistant ta Miss Amal da aka dauka

Emily ta gyara zama tana kallonta with little bit of confused.

 O... Ka..y.... Congratulations

 Thank you, am an fada min nan ne office dina, na yi tafiya ne yau na dawo shiyasa ban samu shigowa da wuri ba sai yanzu

 No wata kila sun yi kuskure ko kuma ke din baki gane???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? wane office ba, domin ni ce a wannan office din kuma ni ma Assistant din Amal ce

 I don't think so, but bari na tambaya

 Okay

Ta juya ta fice, Emily ta bita da kallo har lokacin mamaki take, ana daukar masu taimakar har biyu ne ko kuma dai kuskuren ta yi kamar yadda take zargi? Can kuma wani tunanin ya zo mata, kar dai ace mutumen da ta yi ma magana dazun babba ne a gurin ya saka aka koreta, bata gama raba dayan biyu ba Amal ta turo kofar ta shigo.

 Emily kika ce ba a nan office din ba ne?

Emily ta mike tsaye da sauri domin girmamawa ga Amal.

 Yes saboda Ni nake nan, sai dan za a kara wata ne, amman na fi tunanin ko ta yi kuskure ne shiyasa nace ba a nan ba ne, maybe office din gaba ne

Amal ta yi murmushin rainon wayo.

 Nan ne, ita sabuwar Assistant dinta

Emily ta wara ido irin na mai mamaki

 Ni kuma fa?

 Ke ai da ke da babu duk daya, kamfanin nan be san da zamanki ba?

 Kamar?

 Kamar yadda na fada miki, tun da aka dauke ki aiki baki sign idan zaki fita ko kuma idan kika shigo, saboda haka ke da babu duk daya a kamfanin nan, shiyasa aka daukar min sabuwar ma'aikaciya, dan haka ki hannata mata komai ki bata office

Wani abu da bata yi tsammani ba ne ya zo mata a zuciya ya raunatata yayi nasarar saka ta tara ruwan gishi idonta wato hawaye. Emily ta bude baki ta fara magana a daidai lokacin da Aliyu ya shigo office din da Amal ta bari bude yana rike da hannun Fatima.

 Ban san ana sign in and out idan za a fita ba?

 Ni zan fada miki? Ban baki dokokin kamfani kika karanta ba?

Kamin Emily ta amsa Amal ta kalli Aliyu cikin girmamawa ta gaisheshi.

 Good Afternoon Sir?

Ya kalleta ya kalli Emily dake hawaye ya kalli matashiyar yarinyar sannan ya kalli Amal with seriousness.

 Me ke faruwa a nan?

 Ranka ya dade tana cikin sabin ma'aikatan da aka dauka ne, amman bata zuwa tun da aka dauke ta yau kwana uku, shiyasa kamfani ya dauki wata

 What-... Wallahi ba gaskiya ba ne, ina zuwa tun da aka dauke ni, kawai bana sign in and out ne shi ma ban sani ba, bata fada min ba

 Ba a baki file mai dauki da dokokin kamfanin nan ba? Baki karanta ba?

 An bani amman Wallahi babu gurin a ciki, ban ganshi ba ban sani ba, kuma bata fada min ba, abun da kawai ta fada min idan na shigo na goge mata office dinta na gyara, kuma na rika shigowa karfe 6:30am na safe, jiya ma na yi typing har na 4pm sai da na gama na tafi, gashi a Systems dita, and yau ma gashi ka ga ina yi

Cikin kuka Emily take maganar ta juyar masa da system din. Aliyu ya kalli Amal.

 Cire takardar kika yi a dokokin kamfani?

 Aa Sir karya take min sheri ne kawai

 Amman a dokarmu babu aikin saka ma'aikanmu aiki, idan za'ayi gyara ko wani abun akwai masu yi, har sai idan mutum yafi sha'awar aikatawa da kansa zai aikata, muna da masu aika da zasu siya muna abu, muna da clearness masu gyara guri kullum da safe, and time din shigowa kamfanin nan ga ma'aikanta mu is 8am, masu shara ne suke shigowa 6:30am haka ne?

Jikinta ya fara rawa.

 Haka amman karya take min, daman tun da aka dauke ta na lura haushina take ji so take kawai ta kulla min sheri

Emily ta share hawayenta.

 Na kulla miki sheri? Saboda me? Ina da wata alaka da ke ni bayan ta aikin da ya hada mu kwana biyu zuwa uku? Aikin ne baki son na yi shiyasa kika ce na rika shigowa karfe 6 na safe? Kika sakawa ina goge miki office alhalin ba haka dokar take ba? Kika sakawa ina tafiya mai nisa na siyo miki abun da zaki ci? Kuma baki taba fada min ana sign ba? Aikin ne baki son na yi? To na bari daga yau, ni ban shirya tarwatsa rayuwar kowa ba, daman tun da na ganki na san ba za mu jitu da juna ba, saboda ke musulma ce, musulmai ba su da halin kirki sai karya alkawari sai wulakanci sai kyama da nuna banbanci, daman ai ba zaki taba abun kirki ba saboda ke musulma ce, musulmi be taba min abun kirki ba, sai zalinci shiyasa na tsane ku na tsani addininku

Ta karasa cikin kuka da tsawa sannan ta cire id din da yake wuyanta ta jefar kasa ta dauki jakarta ta nufi yarta da Aliyu ke rike da hannunta ta fisge ta fice daga office din. Aliyu ya kalli Amal a tsanake ya fara mata magana.

 Ba iya suturarmu ce take walkiltar addininmu ba, har da mu'alama da kalamai da dabi'u, kasancewarmu musulmai kawai ta hanyar shigarmu ko sunanmu ba zai wadatar ba, har sai dabi'unmu da mu'amalarmu ta banbanta da ta kowa, ta hanyar kyautata, tausayawa, adalci da kuma bawa kowa hakkinsa, ni musulmi ne ke ma haka, addini ya koyar da mu yadda zamu zauna da wanda ba musulmai ba mu ba su hakkinsu, idan musulmi yayi mummunan aiki, to yana wakiltar duka musulman duniya ne a idon wanda ba musulmai ba, su basa banbance akwai na gari akwai bata gari a cikin addininmu, haka kuma idan musulmi daya yayi abun kirki to a idonsu duk musulmi na gari ne, sai su ji suna sha'awar koyarwar addininmu da dabi'unmu, ban jidadin abun da kika yi ba, ya kamata mu zama jekadu na gari ko'ina

 I'm sorry Sir, amman sheri take min ba gaskiya ta fada ba

Be sake ce mata komai ba ya fice daga office din, office dinsa ya nufa kalaman Emily na masa yawo, ya tsinci na tsinta ya watsar da wasu, abun da ya fi tsaya masa a rai kuma ya sosa masa zuciya furucinta na cewar musulmi ba su taba yi mata abun kirki ba, musulmi ba su da tausayi, kuma ta tsani musulunci. Ya yarda da kalamanta ne sama da na Amal saboda ya ganta sau biyu a kamfani ta siyo abu kuma ya ga shigowarta a yau da sassafen nan kamar yadda ta fada.
Ya zauna a kujerarsa yana mamakin wani abu.

 Anya wanda ya tsani musulunci zai iya bari yarsa ta yi addinin musuluncin har ta koya mata sallah? Kuma ta sakawa yarta sunan Fatima? Ita ya aka yi ta samu suna Aysha? Ta tsani musulunci ta tsani musulmai ko kuma dai mu'alamar wasu daga cikin batan garin musulman ne ya saka ta tsani musuluncin?

Yana ta sake sake a zuciyarsa, for the first time ya ji yana sha'awar jin full dalilin rabuwar Turhan da matar da yake ta nema yanzu, domin ya tabbatar ita ce wannan duk kan wata alama ta bayyana hakan, dole akwai wani babban dalilin da ya saka ta boyewa yarinyar cewar tana da uba, and dole akwai dalilin da ya saka ta tsani musulunci. Har yanzu dai ba zai karyata ba tana da masifar kyau fuskarta ta tsaya masa a ido, and when ever idanuwansa suka sauka a fuskarta sai ya ji kamar ya santa, wadannan blue eyes din nata suna raya masa saninsu but be san a ina ba, maybe kyaunta ne yake rudarsa. Har ya daga wayarsa zai kira Sahibar tasa sai kuma ya tuna horo yake mata saboda ta gane girman laifinta, kuma ya ladaftarta ita da abun da bata saba ba saboda ta kiyaye a gaba.





________________

Masu karatu ya kuke ganin Turhan zai yi idan ya samu Aysha? Kamar dai Aliyu Ni ma ina son sanin dalilin Emily na tsanar musulmai kuma ina son sanin a ina sunan Aishar nan ya samu asali?
[4/20, 9:59/ AM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: https://chat.whatsapp.com/FdvabUKwybz6ogMKtgx02w

*

*? Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen...
'?

Page 9??


EMILY POV.

Suna isa gate Fatima ta fisge hannunta daga na Emily.

 Bana son tafiya gida yanzu

 An koreni a kamfanin ko baki gani ba? Asibiti zamu tafi yanzu

Emily ta sake kama hannunta da karfi ta jata. Sai ta fisge tana daka mata tsawa.

 Bana son zuwa

Ta nufi titi da gudu zata tsallaka ba tare da ta tsaya dubawa ba, Emily ta yi hanzarin bin bayanta, motar dake dafe da gudu ta taka burge domin kadan ya rage ta buge Fatima. Emily ta kamo Fatima ta riketa da karfi gabanta na dubawa, gilashin motar aka sauke wata matashiyar yarinya ta leko tana kallon Emily.

 Allah yasa ban taba ta ba

 No

Emily ta girgiza mata kai, ta matsa gefe, hakan be gamsar da matar? ba har sai da ta faka motarta kusa da gurin da Emily take tsaye tare da Fatima ta bude motar ta fito.

 Kin tabbata bata ji ciwo ba? Ban kula ba ne, ina amsa waya

Cewar matashiyar budurwar dake sanye da gown din atamfa sai fashion cap a kanta, tana jin babu dadi a tunanin kokarin amsa wayar da take a lokacin da take tukin motar ne ya haddasa matsalar.

 Ba laifinki ba ne, karki damu ita ta fisge hannunta a nawa zata gudu

Matashiyar ta kalli Fatima dake ta huci kamar wani karamin zaki ta sake kallon Emily.

 Amman lafiya

 Haka take min, bata jin magana

Emily na rufe baki Fatima da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login