Showing 240001 words to 243000 words out of 253142 words

Chapter 81 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18386

zancen ba"

"Ni da har na yi zaton wata kila yana jin tsoron ko kar Rito yake ki bitto? Ya cutar da ita ne da shi shiyasa Turhan din ya dauke ta suka koma can, sai yace aa ba wannan matsalar ba ce, ai Vito ya dade da mutuwa"

Wani rudududun Emily ta ji kamar saukar cida, ko a mafarki bata taba mafarkin Vito ya mutu ba, bata ma taba mafarkinsa tun da ta bar gidan?

"Ya mutu yaushe? Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un"

Ta kai tsaye numfashinta na rawa, jikinta ma haka nan da nan hawaye suka taru a idonta sai kuka.

"Miye abun innalillahi a mutuwar kafiri kuma mutumen da ya addabeki? Yake neman rayuwarki data yarki da ta mijinki? Daman baki san ya mutu ba?"

"Wallahi ban sani ba, Aliyu be fada min ba, babu wanda ya fada min, yaushe ne?"

"Zuwansa na karshe da yayi muke wannan maganar da shi"

"Miyasa suka kashe shi? Why not su kama shi su hukunta shi, be cancanci kisa ba"

"Mutumen dake kashe mutane? Kuma idan yana raye ke kanki ai rayuwarki na cikin hatsari"

"Kawai ya fada ne, amman ba zai iya komai ba, ba mamaki lokacin da ya turo min sakon baya cikin hayyacinsa ma, Vito ne mutumen da ya fara taimakon rayuwata, ya maida ni mutum na zama yadda nake a yau, miyasa za su saka masa ta wannan hayyar? Ban kyauta masa ba, ni ce sanadi be kamata ba"

Kuka take sosai kai kace Aliyun ne ya mutu ma, daker ta iya janyo wayarta ta kira Aliyu. Jin muryarta da kuka yayi mugun daga masa hankali.

"Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un, me ya faru Qalbina?"

"Me... Me... Me... Yasa kuka kashe Vi.. Vito?"

"Kun yi magana da Mama ne?"

"Mutumen da ya taimaki rayuwata ya so ni shi zaku kashe, ya zama kamar na ci amanar sa kuma sanadina ya rasa ransa, bayan ka yi min alkawarin ba zaka kashe shi ba"

Tana kuka tana maganar. Kashe wayar yayi sai ta kara fashewa da kuka sosai tana jin silarta komai ya faru, bata kyautawa Vito ba, be cancanci irin wannan sakamakon daga bangarenta ba. Babu jimawa Aliyu ya faka harabar gidan domin yana jin kamar ba zai iya jure rarrashinta ta waya ba, ba lallai ta fahimce shi ba.

Ya shigo falon babu ko sallama a lokacin Emily ta ci kuka sosai har idonta ya kumbura, Aliyu ya zauna kan kujera ita kuma tana zaune kasa rike da dankwali a hannu sai sharbar kuka take.

"Na yi rarrashinta har na gaji ta ki ta yi shiru"

Mama Baraka ta fada cikin yanayin damuwa. Aliyu ya kai hannu ya karbi dankwali ya rike kanta ya shafe mata hawayen.

"Wallahi Wallahi ba mu muka kashe shi ba, ba ta sanadinmu aka kashe shi ba, ko da aka aje an samu police har sun dauke garwarsa da ta matar da yake tare da ita, Chidimma sun kaita gurin aje gawa, lokacin da na nunawa Daddy sakon da ya turo miki, sai Daddy yace na sanar da Turhan saboda kar wani abu ya faru tun da har ya dauka Turhan kika aura ba ni ba, kuma Fatima tana gurinsu saboda kar ayi sake ya cutar da ita, na san Turhan ba zai saurare ni ba, ko ya dauki abun da muhimmanci shiyasa na aikawa Ammy da sakon, kuma na tabbatar mata ana kan nemansa, da sakon da ya turo miki aka yi amfani da Location din sim din aka gano inda yake a Lagos, amman ko da aka tafi sai aka samu gidan a rufe da shairdar police saboda an yi musayar wuta a gidan makota suka kira police amman ko da suka zo aikin gama ya gama sai gawa suka dauka, sun turo mana komai sun mana bayani, kuma da suka zurfafa binciken sai aka gano abokan sana'arsa ne suka masa wannan aikin, ba daga mu ba ne, Ki yarda da ni Aisha Wallahi tallahi a haka muka samu shi, sun turo mana hotuna, ban fada miki ba ne saboda ina jin tsoron kar hankalinki ya tashi"

Yana maganar yana share mata hawayenta da dankwalin. Mama Baraka ta ce.

"Daman su irin wadannan mutane ai basa tsawon rai, saboda sana'arsu ta shadari ce suna neman rayuwar wasu ana neman ta su"

"Haka ne, amman Wallahi ba daga mu ba ne"

Ta kwantar da kanta jikin Aliyun da ya sauko kasa yana kokarin fahimtar da ita. Mutuwar Vito wani abu da ya tsaya a zuciyar Emily kuma ya zauna zaman da ba zai taba yiyuwa ta manta ba, daga lokacin da ta ji labarin mutuwarsa sai ya zama bata da walwala saboda tana ganin shi ma ya cancanci farinciki, ta bangaren da take jin sanyi da ya kasance ba Aliyu ne ko ita ba ce siyar mutuwarsa, da ba zata iya yafewa kanta ba.

Haka Aliyu yayi ta fama da ita yana nuna mata amfanin mutuwarsa, da kuma tausaya mata har ta fara kwantar da hankalinta. Ba ma kamar ranar da Mama Baraka ta kirata ta sanar mata Ammy ta aiko da Fatima gidan Mama Baraka saboda bata san gidan Emily ba. Ammy ta yi hakan ne saboda bata son aika direbanta kai tsaye gidan Emily din ne, kuma daman bata san gidan ba saboda sanin gidan da Emily take rayuwa da Aliyu baya cikin lissafinta a yanzu.
Mama Baraka ta aiko Misira ta kawo mata Fatima a ranar farinciki da far'a kamar su kashe Emily da Fatima. Sosai Emily ta jidadi da yarta bata rame ba, kuma bata labarta mata wani abu marar dadi da aka mata ba, sai ma jindadi da take fada mata da wasu abubuwa da ta iya a zuwanta garin, tana ta bata labarin yadda masarautar take da mutanen cikinta.
[9/5, 12:32/ AM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t

*

*? Khadeeja Candy*



Page 7?? 5??


Kin dade kina sha awar sayen kaya a wajen Khadeeja Candy amma ba ki samu dama ba?
Kin shirya fara tanadin kayan Sallah ko na azumi tun yanzu? Ko kuma tanadin kayan auranki ko na  yarki? To, ga sau?i ya iso!

ADASHE NE NA GATA!
Ki zuba kuWi, ki Wauki abin da kike so daga:

Sutura da zannuwan gado

Kayan kitchen

Kayan electronics (fridge, freezer, washing machine, gas cooker, da sauransu)

Talkami da jaka

Zanen gado

Frames (flowers decoration ko standing ones)

Console mirror

Boxes na Lefe ko na traveling.

Warmers iri-iri

Food flask iri daban-daban

Jugs da flask. Kai abin fa sai wanda rai ya so!


Sau?i ya zo, za ki mallaki duk abin da kike so a wajen Khadeeja Candy cikin aminci da kwanciyar hankali, babu cuta babu cutarwa.

=??? Tsarin: Zubi ne wata-wata da kuma sati-sati.
=??? Akwai sharudda da ka idoji.

Domin ?arin bayani, ki/ka
tuntube ni ta wannan lamba: 08036126660
Ko ta hanyar WhatsApp =?I? Danna nan https://wa.me/message/2Y7RIJEODZO2K1

Ko kuma ku yi join WhatsApp Group https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t

Thank you =?
? =?O?




Yana warware hannunsa da yayi alwala ya ce.

"Ki shirya ina dawowa daga Sallah za mu tafi mu kaita"

"Da gaske wai ba zata kwana nan ba? Ni ma fa ina da hakki da ita"

Ta fada a shagwabe.

"Toh haka Mama Ta fada min, za su aiko a dauke ta da karfe 9pm"

"Kai ba zaka saka baki ba? Yaushe rabon da na ga yarinyar nan ta zo kuma sai ace ko kwana ba zata yi ba?"

"Yanzu indai ba son kike Turhan ya zo gidan nan da wukarsa ya kwantar da kaina ya yanka ni ba, ina ni ina saka baki a lamarin yarsa? Hakuri za ki yi idan suka ga kamar ba ki damu ba za su daina, damuwar suke so daman ai, ni na tafi masallaci"

"Allah ya dawo min da kai lafiya"

"Ameen I love you"

"I love you"

Fadawa junansu kalmar suna son junansu wata sara ce da Aliyu ya koya mata, ba ya fita be ji kamar daga bakin matarsa ba, ita ma bata yarda ya fice be fada mata ba, furta kalmar i love you yana kara danko kauna da soyayya a tsakanin masoya ko da yaushe musamman wadanda suke son junansu. Kamin da dawo ta zubawa Fatima abinci ta kara ci ta shirya ita ma ta shirya. Key ya dauka da wallet ya rike mata kofar falon ta fita sannan ya fita ya rufe, mota ma shi ya bude mata ta shiga ta rumgume Fatima a jikinta.

"Ba zaki barta ta zauna baya?"

"Aa na fi son ta zauna a jikina"

Ya kalli yadda ta lankwashe kai tana ta zuba masa shagwaba. Ba zai iya hanata ba, duk yana ganin kamar zaman zai taba ta, sai kawai ya kai hannunsa ya gyara zaman Fatima daga jikin Emily zuwa kafafuwanta. Sannan ya zagaye ya shiga dayan bangaren ya tashi motar yana tukin yana kai hannunsa ya daga Fatima idan ya ga ta kwanta jikin matarsa. Gaban wani katon shagon kayan alatu ya faka ya shiga yayi manyan ledodi uku ya dawo da su bayan mota ya zuba sannan yaja suka cigaba da tafiya.

Harabar gidan Mama Baraka suka faka Aliyu ya fara fita ya zagaya ya bude mata ya riko Fatima ta fito sannan ya riko hannun Emily ta fito ya bude back seat din ya dauko ledodin biyu ya rike.

"Ba uku na gani ba?"

Ya ja hancinta sannan ya rufe motar.

"Daya ta ki ce"

Ya dafa kafadarta kamar wata kawarsa.

"Uhm Qalbina, dazun Mama ta kira ta ce muna da bako tace na kawo ki bayan na dauki Fatima, sai na ce mata ta mana hakuri har sai idan zan kawo Fatima"

"Waye?"

"Sai kin shiga zaki gani"

"Turha?"

"Maybe..."

"Ba zan shiga ba, idan ya fada maka wata magana marar dadi fa? Kasan ba zan kyale ba"

"Ke yanzu kin shirya fada da kowa akaina kenan?"

"Har da kai kanka ba zan bari ba"

Ya bude ido.

"Eyyyy"

"Uhm"

"Ba za ayi komai ba, muje ciki dai"

Ya sauke hannunsa daga kan kafadarta suka jera suna tafiya, zuciyarta bata hararo mata kowa ba sai Turhan, wata kila zai fada mata wasu dokoki ne ko kuma yace zai sake dauke Fatima gaba daya. Shi ya fara rike mata kofar ta shiga sannan ya shiga, daman Fatima ta dade da shiga ta bar su a waje. Ta shiga da sallama tana ta rabon ido bata ga kowa a falon ba sai Mama Baraka da Fatima ke jingine da ita suna gaisawa. Emily ta kalli Aliyu yayi mata murmushi ta yi zaton karya yake dan kawai ya daga mata hankali ya fada mata haka, saboda haka ta taka masa kafa da kafarta sannan ta wuce kusa da Mama Baraka ta zauna suna gaisawa.

"Ya ce mim wai ina da baki, ashe ba gaske ba ne"

Mama Baraka ta kalli Aliyu.

"Gaskiya ne, Aliyu je ka shigo da su, suna nan BQ da ka zagaya baya ta nan kadan zaka gansu"

Sai da ya mike tsaye ya fice sannan Emily ta kalli Mama Baraka ta ce.

"Su waye Mama?"

"Wai tsohon mijinki ne... Ko Hamza ko Khaleefa, Ummi ta turo su gurina, saboda sun tafi can ita kuma bata nan sai ta kirani tace wai sun zo gidanta ne suna son magana da ke, ita kuma bata ma garin yanzu kuma tana ganin duk wani abun da ya shafe ki mijinki ya kamata a tuntuba ko ni"

Fuskar Emily ta sauya sosai zuwa wani yanayi mai kama da fushi da damuwa. Sai dai bata ce komai na har aka turo kofar falon Aliyu ya fara shigo sannan mahaifiyar Khaleefa ta shigo tare da shi da wani kawonsa, duk a kasa suka zauna sai Aliyu ne ya zauna a kujera, Emily ta kalli Khaleefa da rabin fuskarsa take a kone idonta na cika da hawaye rayuwar data manta take tunawa a yanzu.

"Toh ga su nan, sun min bayanin komai kuma sun roki alfarmar a kira ki su roki yafiyarki, na yi magana da Aliyu yace yanzu kina murnar zuwan Fatima a bari sai dare idan kun zo kawowata kar a yi ruining din moment dinku"

"Ina wuni Aisha"

Cewar Mahaifiyar Khaleefa. Emily ta kasa amsawa hawaye na sauko mata, kewar Wanta ya dawo mata farko.

"Wata kila la lallai ki gane mu ba, duk dai Hajiya ta miki bayani kuma ta mana bayanin komai, ashe kin gane mahaifiyarki Aisha, muna miki murna ta fada mana kin yi aure shi ma muna miki fatan alheri, mun zo nan ne saboda neman yafiyarki, abubuwan da suka faru wadanda ba su yi dadi ba, musamman tsakaninki da Hamza, ki yi hakuri ki yafe masa dan Allah, Wallahi abubuwa masara dadi sun faru kuma mun san hakkinki ne, rayuwa ta zama babu dadi, musamman ma yanzu da ya koma gida saboda mai gidansa ya koresa saboda ke, ya fada mana ya ganki amman an hana shi magana da ke, tun da ya koma kullum cikin maganarki yake, daga karshe muka yanke shawarar zuwa kai tsaye mu nemi yafiyarki"

Cikin tsoro da fargaba Mahaifiyar Khaleefa take magana. Khaleefa ya dago idonsa da suka zare tsabar yunwa da wahalar ciwo ya kalli Emily da a yanzu ko kafarta be isa ya taba ba ya ce.

"Ki yi hakuri Aisha na san ban kyauta ba, na san na zalunce ki na cutar da ke, amman ki yafe min, Wallahi na yi nadama kuma na yi ta nemanki amman ban same ki ba, ban san inda zan ganki ba"

"Kowa ya cuceka sai kawai ya zo ya ce ka yi hakuri shikenan aikinka? Ka cutar da ni, ku biyun nan baku ragawa rayuwata ba, kara Ammy ta nuna min soyayya a baya, amman kai mahaifiyarka tana kallo ka tsake ni, na bar gari na kama hanyar da ban san kowa ba, kuka wulakanta ni kuka wofintar da ni saboda kawai ba ni da kowa, kasan ina da cikin Wanka amman baka damu da halin da zan shiga ba, idan jininku ce za ku yarda ayi mata haka? Na haihu a titi kamar na haifi shege, na dinga wahala da shi kamar ba shi da uba, har ya bar duniya be san ubansa ba, wai saboda kawai ni mushirika ce na musulunta na bar addini na bi na ku, kuka rika kirana tubabbiya kowa ya kasa tsaya min, kuka hade min kai bana jin sanyi kowa, bayan kuma kai ka rabo ni da inda nake da gata, ka yi aure baka fada min ba sai da na ji, kuma haka be maka ba, kuka bini da gori kuka koreni gidan, sanadin wahalar da ma sha na haifi Wana ba lafiyayye ba"

Tana maganar tana kuka sosai kukan dake taba zuciya, Aliyu kallonta kawai yake yana kara jin tausayinta da kaunarta suna shiga ransa. Khaleefa ya girgiza kai yana kuka.

"Wallahi hakkinki be barmu ba, bayan kin tafi rayuwa bata mana dadi ba, gidan da kika bar ni ciki ni da matar da na aura gobara yayi komai ya kone, ni kaina daker aka fitar da ni ciki, kalli yadda jikina yayi fuskar babu rabi Aisha, matata bata fita ba, sai yara biyu kawai data haifa min aka samu ceto wa, bangaren mahaifiya aka siyar a gidan aka shiga nema min magani amman har yau ban warke ba, saboda ba ayi treatment din yadda ya dace ba, yanzu haka idan yanayi ya sauya na zafi wutar tana taso min, sun ce akwai cutar har a cikin cikina, Wallahi ba mu da komai a yanzu Aisha, kuma na san hakkinki ne dan Allah ki yi hakuri ki yafe min, aiki ma ya gagara samuwa a gareni sai daker aka dauke ni a gidansu Alhaji Aliyu, ashe shi ma rabon na ganki ne, tun bayan da ya tura ni gida kuma ban sake samu komai ba, ana ba ni da albashin amman kullum gurin magani suke karewa, abun da za'a ci ma wahala yake mana, shin duk ba hakkinki ba ne? Ki yafewa min na zo neman yafiyarki ne da tambayar cikin da na barki da shi"

"Na haifi Wanka da wahala da bakinciki da ciwo, ya rayu da rashin sanin waye ubansa, ciwo ya wahalar da shi, amman abubuwa sun yi sauki da na hadu da Vito, ya taimaki rayuwarmu kamin na rasa shi, ya rasu cikin ruwa ya fada ba tare da mun sani ba, da taimakon mijina an yi masa sutura an masa sallah an kai shi makabartar musulmi. Zancen yafiya kuma ba zan yafe ba, wannan shari'ar sai an yi ta"

Hankalin Khaleefa ya tashi jin cewar Wan da aka haifa ya mutu, sai dai tashin hankalin be kai na jin furucin ba zata yafe masa ba. Shi da mahaifiyarsa da kawunsa da suka zo suka shiga bada hakuri. Aliyu ya mike tsaye

"Khaleefa, ina tunanin zai fi kyau ku kuma inda aka ba ku masauki a yanzu, gobe da safe idan kun karya sai ku koma garinku, Ummi na da numberka zan karba, duk lokacin da hankalin Matata ya kwanta ta ji zata iya yafe maka zan kiraka"

Khaleefa ya kalli Aliyu...

"Ranka ya dade ka fahimce ni, idan na koma ba tare da yafiyar Aisha ba, ban san iya abun da zai faru a gaba ba, wata kila rayuwar ba zata kai lokacin da kake zato ba"

"Amman tana cikin damuwa yanzu ba lallai ta yafe maka ba"

Mama Baraka ta fada.

"Bana cikin damuwa, na samu iyali yan'uwa da uwaye, ma samu miji ina da ya, rayuwa ta sauya na gamsu da abun da aka ba ni a yanzu, na gamsu da wannan sakamakon, kawai dai ba zan iya yafewa ba ne"

Aliyu ya nunawa Khaleefa hanya yana jin kamar ya kai masa duka.

"Please..."

Khaleefa ya kalli Emily yana mamakin yau shi ke zaune a kasa tana kan kujera, yau shi yaje neman yafiyarta tana kin yafe masa, yau ita take da mijin da yake kira da maigidansa, ga duniya ta samu tana gida mai kyau gaba daya ma ta sauya kamar ba ita ba, babu wanda zai fadawa cewar ya taba aureta ya yarda. Baya son jayayya da Aliyu saboda ta bangarensa albashi ke shigo masa duk da baya tuka musu mota a yanzu.

"Tohm na barki lafiya Aisha, ina jiran ranar da zaki yafe min, mun gode Hajiya"

Ya nufi hanyar fita yana hawaye mahaifiyarsa kuma na kuka wiwiwi kawunsa kam tun da aka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login