Showing 15001 words to 18000 words out of 253142 words

Chapter 6 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18406

ne ita din ai musulmace, ta duka ta dauki Atm din tana amsa mata.

 Yana office dina

 Idan kin ga dama ki kawo nan

Kallonta kawai Emily ta yi ta juya ta fice daga office din, nata office ta koma ta dauko file din ta sake knock ta tsaya har sai da ta yi mata izinin shiga sannan ta shiga ta aje mata ta fito. A nan kuma ta fara tunanin ina zata samo mata snacks da bubble tea a yanzu, ita ba sanin kamfanin ko unguwar ta yi sosai ba.

Haka dai ta nufi elevator ta danna botton din dake jiki ta bude mata, ta shiga sannan ta taba number 1, a take ta fara yin kasa har ta isa first floor ta fita, wata zuciyar na fada mata ta tambaye mutane wata zuciyar kuma na hana ta, ita wa ta sani ma balle ta tambaya. Haka ta mike ta fita daga roof din kamfanin ta mike doguwar hanyar har ta isa gate. Ta kalli dama ta kalli hagu kaminnta yanke shawarar nufar left side tana tafiya tana dubawa ko zata samu mai siyar da wani abu amman bata samu ba sai da ta bar unguwar gaba daya ta shiga wata karamar unguwa dake kusa da su, sannan ta fara ganin masu siyar da abubuwa wasu ma yanzu suke fitowa domin goma ta dan gota.
Abubuwan da ta fada su ta siya mota ta biya da Atm din sannan ta sake juyowa tana takowa a kafa, tun tana tafiyar tana jurewa har ta fara gajiya ranta ya fara baci, tana daf da isa kamfanin ta ji an yi mata magana da shigar da Vito ne kadai yake mata haka.

 My Beautiful Babe

Ta kalli gefen da titi yake sai a lokacin ta lura da motar dake binta, yadda fuskarsa take hade kai kace ba shi ne yayi mata furucin mai dadin sauraro ba, dan murmushi ta yi ta tsaya har ta bude motar ya fito, tana mamakin ganinsa. Ko da yake ba abun mamaki ba ne domin ya san kamfanin take aiki kuma kamfanin ba boyayyen kamfani ba ne.

 Waya aike ki siyen abu?

Ta kalli robobin dake hannunta da bubble tea.

 Uhmm...

Ta yi shiru kamar mai tunanin abun da zata fada.

 Ba ki sha Bubble tea na sani, kuma na shirya miki breakfast kamin ki fito, so don't lie to me

 My Boss

Ya gyara tsayuwarsa yana jin ba dadi.

 Are you a maid hare? A aike ki ki siyo abinci shi ne aikin nan Babe?

 No ita kadai ce ta aike ni, saboda a karkashinta nake aiki, kuma ta zo bata karya ba

Ya kalli kayan dake hannunta da kyau sannan ya sake kallon fuskarta.

 Ba ki rasa komai a gida ba, ban san miyasa kika zabi wannan rayuwar ba

A kokarinta na kawar da zancen ta ce.

 Me ya kawo ka nan?

Ya sauke numfashi a hankali ya matsa kusa da ita sosai.

 Na zo ne na yi miki bankwana zan tafi Lagos yanzu, akwai kayana da aka rike dole sai na tafi za a sake su

 Drugs...?

Ta tambaya kai tsaye, be amsa mata ba sai kawai ya kai middle finger dinsa yana shafa soft kuncinta na dama up and down, idanuwanta cikin nasa ita tana jira amsar tambayarta shi kuma kaunarta kawai ke kara zafafa daga idonta zuwa nasa idon then straight to his heart. Dauke yatsansa yayi ganin tana kokarin kawar da fuskarta ya juyo ba tare da yace da ita komai ba ya bude bakar motarsa mai bakin gilashi ya shiga ya ja ya barta tsaye a gurinta yana kallon sawunsa.
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta juya ta karasa cikin kamfani, a nan ma sai da ranta ya kara baci saboda tafiya ce mai tsayi daga gate din zuwa cikin kamfanin, haka dai ta daure saboda tana son aikin, daman hausawa sun ce daukarwa ya fi bauta ciwo.





ALIYU POV.

Yana daura necktie dinsa ta aje masa littafi a gaban madubin da yake shiryawa ta zauna gefen gado tana kallonsa. Kallon littafin yayi sannan ya kalleta

 List din yaudara za a fara min? So kike duk sai kin karar da abun da na tara kin maida ni talaka ko?

Ta saka dariya tana kai apple din dake hannunta a baki.

 Aa Wallahi kasan jiya ka yi min alkawari, to ni dai ban gamsu ba so nake ka rubuta, domin a doka ya fi ka'ida

Ya zauna kusa da ita yana murmushi mai sauti.

 Rantsuwa fa na yi miki jiya baki yarda ba?

 Na yarda amman dai kara ayi a rubuce ko da ka manta na rika tuna maka, ni fa a rayuwata babu abun da na tsana irin kishiya, ni bana sonta ko kadan, ko wata macen ka kalla a tv bakinciki nake ji, kuma mata a yanzu sun yi yawa da kansu ma suke kawowa mazan mutane hari, idan na mutu dai sai ka yi aure amman idan ina raye ban yarda ka yi aure gaskiya

Ya girgiza kai, ya dauki littafin yayi rubutu a kai.

 Ni Aliyu Mudallab na yi alkawari ba zan yi ma Matata Aisha kishiya ba, har abada zata zauna ita kadai a gidana sai yayanta

Yana rubutawa yana fadar alkawarin har ya gama yayi saka hannu, ba tare da tunanin komai ba, domin har ga Allah ba shi da ra'ayin kara aure.

 Hakan yayi miki?

Ta daga mishi kai tana murmushi sonsa na karuwa a ranta. Bakinta ya sumbanta kadan sannan ya mike tsaye

 Sarkin kishi, anya zaki bar ni a aljanna na more hurul'aini kuwa?

 Wallahi ba zan bari ba

Ta fada da karfinta, kyalkyalewa yayi da dariya sosai ya dauki abubuwansa ya fice tana masa addu'a tare da rakiya har kofar falo. Sai da yayi addu'ar fita daga gida sannan ya fice ya shiga motarsa yana dago mata hannu da blowing mata kiss sannan ya fice. Karatun Qur'ane ya kunna a motar kamar yadda ya saba, domin baya sauraren waka idan ma yana son rage kadaice ne sai dai ya saurari karatun ko ya karanta ko ya rera kirar da kansa.

Kamar kullum baya shigowa sai 11am ko fiye da hakan ma, idan yayi sakammako shi ne zai shigo 10am, kasancewar CEO na kamfanin, sai dai kuma baya barin kamfanin sai 3pm ko 4 sometimes har 5pm ya kan kai idan aiki yayi yawa, ko wani Meeting. Ya faka motarsa a gurin da aka tanadar masa sannan ya bude motar ya fito, iPod dinsa ya saka a kunne ya cigaba da sauraren karatun Qur'ane a kunnensa na hagu, ta ko'ina ya wuce gaishe shi ake har nufi elevator, matar dake cikin yake kallon irin kallon nan da ya kasa kyabta ido ma balle ya dauki, kallonta yake da kyau yana tantancewa, tunaninsa kuma yana tafiya wani gefen.

Yana shiga ciki sai ya taba 5, a take Emily ta taba 4 ba tare da ta kalleshi ba.

 Ni na fara zuwa

Be ce mata komai ba bayan karkatowa da yayi ya kalleta ya kalli ID din dake kirjinsa, ita kuma sai ta yi zaton kirjin nata yake kallo, hakan ya saka ta kokarin gyara rigarta da maballi sama yake bude ya bayyana wani bangare na kirjinta sai dai be fito da dukiyar fulaninta ba. A kokarinta na yin hakan Bubble tea din dake hannunta ya fadi ya zube. Bakinciki ya saka bata san lokacin da ta fara yi masa ihu ba.

 Kallo har na bala'i har na masifa, ka kura min ido har na zubar da abun da na yi wahalar tafiya can wata unguwa nesa na siyo

Nan din ma dai be jin magana ta zame masa dole dan haka ya adana kalamansa ya kalli gurin da ya bace kawai ya dauke kansa, his mind is somewhere else shi dai jin yake kamar ya taba ganinta, and he won't lie tana da masifar kyau, ta ko'ina ta kai mace, shiyasa William ya rikice jiya yana ta masa santinta. Suna isa four floor ta Elevator ya bude sai ta fita suna hada ido ta watsa masa masa wani kallo na jin haushi wanda ya fi kama da harara. Ya dauke idonsa da sauri ta har Elevator ya rufe, number 5 ya taba, ya ciro wayarsa ya kira Turhan.

 Hello Aleeyou

Turhan ya fada da dan sautin labarancinsa kadan.

 Turhan, yarinyar nan da kake nema fara ce sosai?

 Eh fara ce, tana da jan gashi, da blue eyes and tana kiba

Kibar da Turhan ya fada ya saka Aliyu kwankwanto, domin ita dai wannan da ya hadu da ita daga jiya zuwa yau siririya ce.

 Tana da masifa?

 No bata da fada ko kadan, tana da tsoro idan ma aka mata fada sai dai ta yi kuka ba zata iya maida magana ba

 Okay, sunanta Aisha ko?

 Eh bata da wani suna bayan wannan?

 Ba zata rasa ba, amman na manta sai na bincika Ammy ko zata fada min

 Ta yi dogon boko ne?

 No bana jin ma ta gama Secondary School, ba wai na san komai ne akanta ba, amman dai zan bincika, me ya faru?

Aliyu ya amsa masa yana ficewa daga Elevator.

 No na tambaya ne kawai saboda na taya ka nema

 Na gode sosai Aleeyou, yau zan tafi Lagos din In Shaa Allahu, ka taya ni addu'ar Allah yasa na dace, ga matsalar masarautarmu, ga matsalar Matata ga matsalar neman yarinyar nan

 Karka damu komai zai wuce, ita haihuwa ai lokaci ne, ita kuma za a same ta In Sha Allahu

 Ina fatan haka

 Okay bye Allah bada sa'a

Ya sauke wayar yayinda yake tura office din farko ya shiga.

 Good Morning Sir

 Morning Nick. Please inform Michael to notify our new staff members that buying food during working hours within the company premises is not allowed. They can only do so either before work begins or after closing hours, as it seems they are not familiar with our rules.
Also, remind them to sign in when they arrive and sign out when they leave

 Okay Sir

Ya amsa yana dan sirinawa alamar girmamawa, sai da Aliyu ya shiga office dinsa sannan Nick ya zauna ya fara cika umarnin boss dinsa da System kamar yadda aka saba, duk wani abu da za'ayi a cikin kamfanin sai dai a tura ta email, sai idan uzuri ne ko kuma wani abu ne da ya shafi mutum personally sannan ake amfani da Telphone din da aka tanadar a kowane Office.






_______

Allah yasa Aliyu ya cika alkawarin da ya dauka, domin maza sai Allah.

Anya idan Vito ya san kudurin Emily na guje duk wani abu nasa zai barta kuwa?

Kuna ganin Emily zata iya jure aiki a karkashin Amal kuwa?

Shin Turhan zai yi nasara idan ya tafi Lagos neman Aisha?
[4/20, 9:58/ AM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: *

*? Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen...
'?

Page 6??

Sai da ta sauke numfashi sannan ta tura kofar office din ta shiga, ta manta da dokar Amal na neman izini kamin shiga.
A gaban teburinta ta dora mata abun da ta siyo sannan taja ta tsaya tana jiran Amal ta gama wayar da ta shigo ta same tana yi.
?? Sai da Amal ta gama wayar sannan ta kalleta a fusace.

 Wai ke kam baki da tunani ne ko kuma dai rainin wayo ne yayi miki yawa? Zuwanki na farko na miki gargadin shigo min office ba tare da neman izini ba amman baki ji ba ko? Ke ba yarinya ba balle ace za'ayi ta maimaita magana

Emily ta kalleta da kyau tana jin babu dadi domin matar dake zaune a gabanta tana mata fada bata wuce sa'arta ba, amman take kokarin wulakantata saboda kawai tana aiki a karkashinta.

 I'm sorry na manta ne, zan kiyaye next time

 Better

Cewar Amal tana daga bubble tea din da ya zube.

 Shayewa kika yi?

 No zubewa yayi by mistake

 To zan fada a cire min a cikin albashinki, yanzu kuma je ki siyo min wani

 Okay

Emily ta amsa mata sannan ta juya ta fice jiki a sanyaye, cikin rashin jindadi da kasala ta sauka kasa ta sake komawa gurin dazun ta siyo mata wani bubble tea din ta dawo ta hauro sama ta yi knocking ta jira har sai da ta yi mata izini sannan ta tura ta shiga.
Saman teburinta ta dora mata tare da atm dinta sannan ta juyo ba tare da tace mata komai ba zata fice sai Amal ta kirata.

 Hey

Emily ta juyo ba tare da tace komai ba, Amal ta nuna mata tulun takardun da suke zube kasa a gafen teburin.

 Ki dauki wannan ki je ki yi typing dinsu, a yadda kika gansu a papers idan kin gama ki turo min ta email dina

 Okay

In short sannan ta nufi tulun takardun ta dauka ta fice daga office din zuwa nata Office din, Widows din office din ta bude tana kallon titi da kasan building din, hutun minti goma ta yi sannan ta juyo ta zauna a kujerarta ta bude system din ta fara typing tana murmushi kamar ba ita ce ta gama bacin rai a dazun ba.
Sai dai abun da baka saba ba, yana da wuyar aiwatarwa musamman a karon farko, bata jima tana yi ba ta fara gajiya, haka dai ta daure ta cigaba da typing har azahar.

Bata bar office dinta ba sai 4pm domin bata yarda ta fito ba sai da ta tabbatar ta gama komai, ko da ta fito kusan wasu sun dade ta tafiya gida, few mutane ne suka rage irinta sai kuma ma'aikatan dake gyara kamfanin. Bata samu Taxi ba dan haka ta hau okada ya kaita gida, bayan ta biya shi ta kwankwasa gate din mai gadin ya bude mata ta shiga ciki cike da gajiya, jakarta kawai ta jefar ta shiga kitchen, lunch da Chidimma ta aje mata ta dauka ta fito falo ta fara ci da sauri saboda yunwa.

 Anya zan iya aikin nan? Haka aikin yake ko kuma dai...

Sai kuma ta yi shiru ba tare da ta karasa ba ta cigaba da cin abinci, a gurin da ta ci abincin a gurin ta kwanta ta fara bachin wahala da gajiya bata farka ba sai Magariba.

 Momy...

Ta bude idonta daker domin bachin be isheta ba, ta kalli yarta.

 Fatima

 Momy yau kin kwanta da wuri

Ta tashi zaune tana murmushi sai a lokacin ta tuna da yaran domin gajiya ta saka ta manta da su.

 Ina kuka tafi?

Chimdimma ta tafi da mu park daga can muka je gidansu. Emily ta kalli Chidimma dake tsaye.

 Baki fada min ba

 Yes saboda Oga ya zo bayan kin fita yace na rika fita da su, saboda baki da lokacinsu yanzu kar ya zama suna kadaici a gida, musamman Londom da yake ba lafiyayyen ba

 Okay amman daga yanzu, karki sake fita da yarana ba tare da kin fada min ba

 I'm sorry Maa

Emily ta mike tsaye ta nufi gurin da danta yake tsaye kusa da Chidimma ta risina tana shafa fuskarsa.

 My Baby how is your day

Ya mata murmushi kawai ya cire hannunta a fuskarshi. Chidimma ta saki hannunsa

 Sai da safe ranki ya dade

Emily ta fahimci Chidimma fushi ta yi dan haka ba ta dakatar da ita daga tafiya ba.

 Ba zaki karanta mana story book ba?

Fadima ta tambaya. Sai mahaifiyarta ta amsa mata.

 Zan karanta muku, ina da labari mai dadi da zan baku, and zan girka muku dinner mai dadi

Tana maganar tana rawa da kai tana murmushi, a take farinciki ya cika fuskarsu, yadda ta fada haka ta aiwatar, tana girka musu abinci tana fada musu yadda ta sha wahalar aiki yau.

 Ma'aikatar ana aiki da yawa ne Momy?

Fatima ta tambaya tana cin abinc.

 Ina tunanin haka, amman akwai wahala wata zan saba zuwa gaba

Ta busar da iskar bakinta, tana shafa kanta.

 Momy can i ask you something?

 Yes My Love

 Me yasa ake sunana ya kasance Fadima Aisha Emily, not Fadima Hamza like London

A take Emily ta ji wani kunci da bacin rai ya tunkarota da kamar fada ta ce.

 Again? Ina tunanin mun gama wannan maganar tuntuni?

 Momy kowa yana using sunan babanshi, amman ni sai dai na yi using sunanki? Why? Even London ana kiransa London Hamza, why not London Aisha Emily?

Emily ta aje spoon din dake hannunta ta mike tsaye.

 Time to bed

 I need to know Mom kullum yan makarantarmu sai sun min dariya, Yau ma da nafi gidansu Chidimma an tambaye ni sunana na ce Fadima Aisha Emily sun min dariya

 Ba na sha fada miki ba ki da Baba ba?

 London me yasa yake da Baba, Me yasa ake ce masa London Hamza?

 How many time do i have to told you Babansa ya mutu, ke kuma ban haife ki da ubana ba, haka nan na haife ki

 But-

 But, if you ask me one more Question zan doke ki da daren nan

Ta fada mata a tsawace.

 But kin taba cewa Babana musulmi ne, amman ban taba jin sunansa ba

Da sauri Emily ta bar dinning din domin ta san idan ta kara minti daya a gurin zata doki Fatima ne, gidan ya rikice mata domin tun a yanzu London ya fara rikicewa yana kuka. Dakinta ta shiga ta zauna bakin gado ta rike kanta tana shafa goshinta a hankali idonta a rufe sai numfashi take maidawa da karfi. Ta kwashe minti talatin a haka sannan ta mike tsaye ta cire rigar jikinta ta shiga bathroom ta yi wanka ta fito ta saka fajamas sannan ta sake dawowa falon ta nufi London da har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login