Showing 105001 words to 108000 words out of 253142 words

Chapter 36 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18414

da tabbas, zuwan ba na yanzu take magana ba tun a wacan karon ne, shi ma kuma karya aka shirya mata domin bayan tafiyarki Aliyu be taba zuwa gidan nan nemanki ba"

"Toh yanzu me zaki yi? Reporting dinta za ki yi ma police ko kuma yaya? Ko a fadawa Aliyu"

"Aa bana son kowa ya sani, so nake ki raka ni asibiti"

"Okay tashi mu tafi"

Emily ta fada tana kallon fuskarta data dan kumbura kadan. Tasmia ta mike tsaye

"Ban san inda wayata take ba, ara min wayarki na kira na sanar da iyayena halin da nake ciki"

Ba tare da tunanin komai ba Emily ta mika mata wayar sai ta tashi ta shiga daki da sunan kiran sai dai a badini ba kiran zata yi ba, amfani ta yi da wayarta dake aje a dakin ta saka number Kameela ta aika mata sako sannan ta goge ta duba inbox din Emily ko zata ga sakon Aliyu bata gani ba, ta shiga longcalls a nan ta ci karo da kiransa da kuma wanda Emily ta yi masa ta dago ta kalle kofar cikin wani yanayi sannan ta sake maida idonta gurin wayar ta saka wata fake number ta kira ta yi canceling.

"Kin ga na kira wayar Yayana saboda na sanar masa saboda shi namiji ne, kar na fada musu hankalinsu ya tashi su yi zaton ko wani babban abu ne, bari zuwa gobe zan sake kiransa"

Ta fada bayan ta mikawa Emily wayarta.

"Okay mu tafi asibitin"

"Wace asibiti zamu je ni kin san ba wanin garin nan na yi ba"

"Muje ni na san asibitin, sun gwarai sosai a can ake duba London ni kaina can nake zuwa idan ba ni da lafiya"

"Okay"

Ta shiga ta dauko jakarta da wayarta dake boye a jakar ta fito suka shiga motar Emily, da suka isa likitan dake duty dare ya dubata sai ya rubuta mata maganin ganin kamar ciwon be kai a bata gado ba, amman ta ki yarda wai ita ko'ina ciwo take ji ita dai tafi son a bata gadon, ganin tana bukata ya saka likitan bata gado, a dole Emily ta tsaya tare da ita asibitin ganin bata da kowa kuma be kamata ta tafi ta barta ba, domin ita ma ta tsaya mata lokacin da take cikin damuwar rasa danta.





ALIYU POV.

"Daman abun da kake takama da shi kenan? Shiyasa kace ba zaka min kishiya ba? Sai ta waje? Abun be tsaya iya kan Emily ba? Har da Tasmia kawata Aliyu? Emily ta turo sako ta fada min komai ta fada min ka fi sonta akaina, shiyasa ka zabi korata, ta fada yadda kake ziryar gidan Tasmia gurin nemanta, ka nuna kafira ta yi matarka muhimmanci Aliyu, toh na bar maka gidan sai ka dauko ta ka kawo daman ai ta fada min lokacin da bana cikin gidan har cikin gidan ta kwana ka yi ma danta jana'aiza ka kyauta"

Shi ne sakon da ya fara cin karo da shi kenan a wayewar safiyar yau, ya dafe goshinsa yana kallon Number Emily da Kameela ta yi screenshot ta turo masa ta whatsapp tare da sakon data aiko mata, da yayi coping number ya duba sai ya ga number Emily din ce.
Amman me zai saka Emily ta yi haka? Be samu amsar tambayarsa sai ga kiran Tasmia ya shigo wayarsa wannan karon be amsa ba, har wayar ta gaji da ringing be kula kiran ba. Sako ne ya biyo bayaj kiran Tasmia tana sanar da shi Kameela ta yi mata duka jiya da dare a asibiti ta kwana.

"Ahhh Ahhh"

Aliyu ya fada yana zaunawa bakin gadon dake dakin na Hotel. Da kansa ya kirata sai ta daga tana kuka.

"Me ya faru?"

"Baka ga sakona ba"

"Na gani, garin ya ta miki duka?"

"Ban san waya fada mata kana zuwa neman Emily a gidana ba, ban san hawa ba ban san sauka ba, sai ganinta na yi a falona babu bayanin komai ta hauni da duka"

"Amman jiya ke kika kira ni kika ce kin je gidan nemanta bata nan, ina kika samu number na"

"Mai gadinka ne ya bani da na kira ban same ta ba, sai yace ba ri ya ba ni number ka na kira kace baka dawo gida ba, sai na dawo gidana ina zuwa babu jimawa sai gata ta shigo kawai ta hauni da duka har tana fadar sai ta kasheni, ban san hawa ba ban san sauka ba, Aliyu ba ni da kowa garin nan sai Allah, bana son wani tashin hankali duk abun da za ku yi ya tsaya tsakaninku da Emily da Kameela ka jawa Emily kunne dan Allah ta daina saka ki cikin rigimarku, babu ruwana sa soyayyar dake tsakaninku da ni dai ina zaune da kowa da zuciya daya"

Bata jira abun da zai fada ba ta kashe wayar tana kuka. Ya mike tsaye yana tunanin damuwar Kameela shi ta saka masa guba ta duki Tasmia bayan ta gama haukata akan Emily.
Number Emily ya kira domin ya ji dalilinta na turawa matarsa sakon da yayi sanadin da aka duki Tasmia kuma aka kara kunno masa wata sabuwar wutar. Emily ta amsa wayar ba yabo ba fallasa.

"Hello"

"Emily"

"Na'am"

"Kina ina? Me kike yi a yanzu"

Ta kalli kitchen din da take zubawa Tasmia abun karyawar da Chidimma ta shirya domin ita ta kwana a asibiti ne sai washe gari ta dawo.

"Ina gidana"

"Wata magana ta shiga tsakaninki da Kameela?"

"Aa"

"Tasmia fa?"

"Meyasa ka tambaya?"

"Meyasa kika turawa Matata sako cewar ina zuwa nemanki a gurin Tasmia?"

A take ran Emily ya bace

"Matarka bata da hankali, wane irin magana ne wannan? Sai kace akanta aka fara aure? Kwanan baya ta yi min cin mutunci yanzu kuma taje ta daki Kameela hakan be mata ba sai ta hada karyar cewar na aika mata sako?"

"Karki sake kiran matata mahaukaciya karki sake fadin wata magana marar dadi akan matata, ban kira ki dan ki zageta ta ba, sai dan tabbatar da abun da na ji ko na gani"

"Kasan matarka ai zata iya shirya komai saboda da kanta"

"Cikin abun da zata shirya har da tura ma kanta sako da Numberki? Emily karki maida ni dan iska mana, na san matata tana da kishi amman idan an ciza dole za a hura ai"

Emily ta yanke wayar ba tare da ta sake cewa komai ba, hakan kuma ba karamin fusata Aliyu yayi ba. Keys dinsa ya dauka da wallet ya fito daga hotel din ya shiga motarsa a hanyarsa ta tafiya gida Nura ya kira shi ya sanar masa Dr A-B yana cikin PH.

"Ka je ka ganshi misalin karfe tara, na yi magana da Dr Osman zai hada ku sai ku yi magana ya baka ranar da ya kamata ku hadu, idan a Abuja zaka same shi sai kaje idan kuma a zai iya dubata idan ya shigo PH duk daya domin yana yawan shigowa nan aka ce"

"Okay na gode Nura zan shirya zuwa 9 na tafi gurin ka turo min address da number Dr Osman din"

"Okay"

Daga haka suka yi sallama, Aliyu ya koma gidan sai ya samu Kameela ta yi masa gyara, wato ta hargitsa gidan gaba daya ta fashe abubuwan da zata iya fasawa ta watse wasu. Zaunawa yayi kan stairs din ya dafe kansa yana ta ambaton Allah, daya daga cikin dalilin daya saka yayi ma kansa kuma yayi ma Kameela alkawarin ba zai kara aure ba har da gudun tashin hankali da kannan maganganun ashe dai ko a yanzu bw tsira ba.





EMILY POV.

Cikin bacin rai ta fito Kitchen din, Vito dake zaune a dinning yana karyawa ya bita da kallo.

"Jiya baki kwana a gida ba"

Emily ta kalli Chidimma, domin ta san Vito baya kwana a gidan balle ya san ta kwana ko akasin haka.

"Ni ba karamar yarinya bace, ina da damar na kwana a duk inda nake so"

"You're just 25yrs old kuma kina karkashin ikona dole ne na san a duk halin da kike ciki"

Ta juyo a fusace

"Wai duk wannan gatan da wannan kulawar da ka ba ni ka bani ne saboda ka yi iko da ni? Ka juya ni yadda kake so? Da zarar na yi abu sai kace ina karkashin ikonka bauwa ce ni? Nawa ka biya ka siye ni?"

"Babu kudin da zai siye ki a duniyar nan Emily, ina kulawa da shiga da fitarki ne saboda ke Matata ce"

"I'm not your wife, ni ba matarka bace ba matar kowa ba ce, and i need another maid bana son Chidimma"

Chidimma ta kalli Vito tana girgiza masa kai idonta na cika da hawaye.

"Dan Allah karku koreni aikin nan da shi kadai na dogara da shi nake komai na rayuwata"

Emily ta dauke kai ta fice rike da abincin, motarta ta koma ta shiga ta dauki hanyar asibitin domin kaiwa Tasmia abun karyawa, bayan bacin ran Aliyu na zarfinta da abun da bata aikata ba, yanzu kuma Vito ya kara mata da shi. Ta faka motar a harabar da aka tanada domin aje ababen hawa sannan ta fito rike abincin ta nufi cikin asibitin, tana tafe ranta da fuskarta a bace kamar zata yi kuka.

"Da alama kin fini tsada, shiyasa baki nemi ni ba"

Ta karkato kadan ta kalli gefenta sai ta yi arba da fuskar likita daya taba bata katinsa saboda rashin lafiyar London, tare da wani likita a gefensa.

"Hi"

"Hi, ashe kin gane ni"

Ta yi murmushi.

"Wacan karon na manta ban tambaye ki ba, are you married? Kar mijinki ya fasa min kai"

"No"

"Cool, ya mai jikin?"

"Ai ya rasu"

Ta fada cikin wani yanayi marar dadi idonta na son tara hawaye.

"Ayyah... I'm sorry"

Ya fada cike da tausayawa. Ta sauke kanta kasa ta cigaba da tafiya har suka isa gurin da zai shiga.

"This Way Ma'am"

Ta kalli hanyar da zai bi.

"No ni nan zan bi, akwai wata kawata da bata da lafiya ita na kawoma abinci"

"Toh kuma ba zaki so mu gaisa ba"

"Mun gaisa a nan ai?"

"Asibitin tana da mutane da yawa, ba zai yayu na siyar da ke ba, ni ma akan hanya nake nan da minti arba'in zan bar garinku"

Ya fada yana kallon agogo hannunsa.

"Da alama baki san waye Dr A-B ba ki zo kawai ku gaisa"

Likitan dake tare da shi ya fada, a yanzu kuma Emily bata da wani zabi daya wuce ta yi abun da ya kamata even though bata san makasudinsa na son hakan ba. Da suka jera suna tafiya yake fadar.

"Daman alamu sun nuna min baki da aure, amman na yi tunanin mutumen da ya saka aka nemo ni na duba yaronki shi zaki aura"

"Aa"

"Kin yaudare shi k?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? enan"

"Aa ni bana soyayya da kowa, babu zancen aure a gabana ba zan sake yin aure ba balle na yaudari wani"

Ya dan tabe baki kadan.

"Ihhh da Alama yan'uwa rijalu sun dandana miki gubar soyayya, kin huta ai, ni ma dai ba a dandana min gubar ba amman soyayya bata burge ni, shiyasa mutane har mamaki suke wai ina da shekara 37 na doshi arba'in kuma ban yi aure ba"

Ya bude mata kofar Office din da za su shiga sannan ya tsaya.

"Ladies First"

Sai da ta fara shiga sannan ya shigo, kana ganin Office din ka san ba na shi ba ne, amman a haka yayi mata gurin zama.
[6/3, 8:23/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: *

*? Khadeeja Candy*


SARAC STARS. C - Pen...
'?



FOLLOW ME ON =?G?
FACEBOOK
https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914

TIKTOK
https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1

INSTAGRAM
https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0

CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

KHADEEJA CANDY STORE
https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08



Page 3?? 3??


Ya duba agogon hannunsa.

"Wani kake jira ne?"

Ta tambaya tana jin sakewa da shi kamar yadda ta ji a farkon haduwarsa. Sai yayi murmushi

"Abun dariya ne, ni bana jiran wani sai dai a jirani, amman ban sani ba ko abubuwa za su canja wata rana na zo ina jiranki"

"Miyasa baka jira?"

"Wani mataki ne Allah ya kaini, bana jira sai dai a jira ni saboda kullum na tashi aiko aiki har sai na ture idan ina son hutu, saboda haka ya zama mutane sai dai su jira idan na gama wani aikin sai na fara na su"

"Toh amman me yasa kake duba agogo"

Ya wara ido.

"Hmmmmm ashe dai ke ma kin iya sa'ido"

Ta rufe idon tana murmushi, likitan dake tare da shi yayi murmushi ya mike tsaye ya fice daga office din.

"Ya kamata ki saka min number wayarki, saboda mu rika gaisawa ko? Domin na lura kin fini tsada shiyasa da na baki number wayana baki kira ni ba"

Yana maganar yana kallonta har ta bude ido.

"Gashi ko sunanki ban sani ba"

"Emily, sometimes akan ce min Aisha"

"Ehhhh nice name, Allah yasa baki kyamar musulmi"

"Kai baka kyamar Cristian?"

Ya girgiza kai.

"No... Ko kadan Mahaifiyata ahlul-kitab ce ita christen ce kin ga ba ni da hujjar kyamar ki"

Ta nuna shi

"amman kai..."

"Aa ni Musulmi ne mahaifina Musulmi ne, aljanar data aure ni ma ta hana ni aure musulma ce"

Emily ta kyalkyale da dariya...

"Interesting"

Ya fada yana kallonta da murmushinsa mai kyau.

"Wa yace aljana ta aureka?"

"Haka suke cewa wai saboda kullum cewa nake na ban ga wanda ta yi min ba, amman ina tunanin ta fara gajiya da ni ta kusa sakina"

Ta sake kyalkyalewa da dariya.

"you're so funny"

"Yeah my second job is to make you laugh"

Tana kokarin saka hannunta ta rufe bakin daga dariyar da take, Dr da ya fita dazun ya kwankwaso ya turo kofar ya shigo Aliyu na bayansa. A lokacin ne Dr A-B ya mike tsaye

"Bakonka ya zo a late jirgina ya kusa tashi"

"Hakuri zaka yi Dr ka saurare shi kuma ka ba mu lokaci ba sai mun yi ta daku ba"

Cewar Likitan dake tare da Aliyu, Dr A-B ya girgiza kai zai yi magana Emily ta kalli Aliyu da tun da ya shigo ita yake kallo tace.

"Da dai ka saurare shi, ba zan jidadi ba idan ka tafi baka ji uzurinsa ba"

"Emily ai ba zan ce miki aa ba"

Ya koma ya zauna sannan ya nunawa Aliyu kujera.

"Malam Bismillahi"

Aliyu be zauna ba domin baya son yayi maganar cewar yana son a duba matarsa ne a gaban Emily and the way da ya samu Dr A-B jikinsa ya ba shi kamar ba za su jitu ba saboda alama sun nuna masa Dr A-B is arrogant.

"No ka ba mu katinka kawai i will contact you though it"

Dr A-B ya dan tabe baki kadan.

"Okay Dr Osman zai baka Katina"

Ya mike tsaye yana kallon Emily da murmushi a fuskarsa, ita ma ta mike tsaye.

"Toh yanzu kuma sai yaushe?"

"Sai randa kaddara ta yi nufin sake hada mu sai mu hadu mu gaisa"

"Ehmmm hmmm idan kaddara ta sake hada mu, toh na san manufar hakan kuma zan baki mamaki, fatan alheri"

Ya risina mata kadan sannan ya wuce ya bude kofar ta bishi da kallo tana murmushi har ya fice Dr Osman yayi masa rakiya. Sai da suka fice sannan ya maida idonta kan Aliyu sai ya gwatsaleta.

"Ashe haka kike da arha?"

Ya fada fuska ba yabo ba fallasa.

A take ta hade rai ta turo baki.

"To miye na min magana ba mun yi fada ba"

"Na miki magana zo ki saka wuka ki yanka ni"

Ta sauke idonta kasa.

"Breakfast kika kawo masa ne?"

"Na Tasmia ne"

Ta amsa da dan fushi.

"Toh ki dauki abincin ki fice ko gadin office din ya barki ki yi?"

"Toh ka daina min fada kamar wani ni yarka ce"

"I'm your boss tarbiyarki a yanzu karkashina take dole na gyara miki zama"

Ta duka ta dauki abincin ta nufi kofa ta bude ta fita sai gashi ya fito.

"Tasmia da kika yi sanadin aka yi mata duka yanzu zaki dauki abinci ki kai mata babu ko kunya?"

A nan ta zaburo masa ta juyo a tsawace tace.

"Ni ban aikawa Matarka sakon komai ba, babu dalilin da zai saka na yi maka karya, babu dalilin da zai saka na turawa matarka wannan sakon, kai ma idan kana neman janye kanka daga jikina ba sai ka yi min shari ba, you can walkway ba tare da ka dasa min bakin ciki ba, ba sai ka zarge ni da abun da ban aikata ba"

Ta karasa maganar idonta na cika da hawaye, kallonta kawai yake har hawayen suka zubo mata ta saka hannu ta share. Ya ciro wayarsa daga aljihunsa ya kama chat din da Kameela ta aika masa daidai gurin da number wayar Emily ta fito ya nuna mata.

"To wa aika? Vito?"

Emily ta karbi wayar ta duba ganin Number wayarta ya matukar bata mamaki.

"Wallahi ban aika ba, ban tura mata wannan sakon ba, kuma Vito baya daukar wayata..."

"Toh waya aika?"

Ya tambaye sannan ya karbe wayarsa. Ta yi shiru tana nazari babu wanda ta fado mata a rai sai Chidimma da Tasmia domin Chidimma ta taba daukar wayarta, Tasmia kuma ta karbi wayarta a jiya tace zata kira ta sanar da iyayenta, sai dai bata saka ran Tasmia zata shirya mata wannan Chidimma kuma bata iya hausa kamar haka ba, a ina ma number Kameela ta fito bayan ta yi blocking dinta.

"Waya karbi wayarki jiya?"

"Tasmia tace zata kira iyayenta bayan Kameela ta mata duka, amman Tasmia ba zata yi hakan ba"

"Karfe nawa kika je gida?"

Ta yi shiru tana nazari

"Karfe tara tayi bayan mun gama waya da kai ne"

Ya duba time din sakon sai ya ga da safen nan aka turo masa shi, ya duba kiran da Tasmia ta masa jiya sai ya kalli Emily.

"Karki yarda na riga ki isa Office"

"Kamar ya kuma? Yaushe na kai mata abun karyawa har na koma gida na shirya na tafi office"

"Wannan matsalarki ce kamin ki zo nan ya kamata ki yi wannan tunanin ba yanzu ba"

Ta kalleshi tana mamakin yadda yake kokarin tsanarta.

"Why do you hate me now?"

"I didn't hate you"

"Zan aje mata abincin sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login