Showing 18001 words to 21000 words out of 253142 words

Chapter 7 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18428

lokacin kuka yake ta rumgume shi.

 Ya isa haka ya isa haka gani a nan

Jikinsa yayi zafi sosai alamar fever, rage tsayi ta yi ta dago shi daga jikinta ta kalleshi.

 London saurareni, kukan ya isa haka kaga jikinka ya fara zafi, Fatima London yayi wasa da ruwa?

Fatima ta juyar da kai ta rumgume hannayenta ta turo baki gaba tana cigaba da kallon tv ta ba tare da ta amsa mata ba, ita ala dole fushi take.

 Fatima I'm talking to you...!

Emily ta daka mata tsawa har sai da London din ya zabura ya kara fashewa da kuka.

 Yayi wasa da ruwa

Ta amsa mata a dikile sannan ta mike tsaye ta haura sama tana wani halba kafa kamar wata babba. Emily ta rumgume London tana jin kamar ta fashe da kuka, domin babu abun da yake firgitata a yanzu kamar rashin danta, He's not just an autisms yana fama da sickle tana yawan tashin masa lokaci zuwa lokaci, abu kadan yana iya saka ciwon nasa tashi, kusan ta fi wahalar da shi fiye da Autisms domin yana a cikin jikinsa ya zama rayuwarsa da hallintarsa ce a haka, wannan kuma a cikin jininsa take.

Daukarsa ta yi ta koma saman cushion ta zauna tana rumgume da shi tana juyawa a hankali, kamin ta aje shi ta tashi ta haura sama ta shiga dakinsa, maganin ta dauko ta sauko ta bude ta bashi sannan ta tallaba shi daker ta haura sama, suna shiga dakinta ya fara kwara amai a jikin sai ta sauke shi da sauri ta rike shi. A nan fa hankalinta ya tashi da sauri ta sake shi ta nufi gurin da ta adana keys din motarta ta dauka da nufo shi ta dauke shi saman duk wani nauyinsa sai ta daina jinsa a lokacin. Kamar ba ita ba haka ta saukowa downstairs din da sauri ta nufi kofar falon ta bude ta shimfidashi a balcony ta nufi gurin da jerin motocin uku na gidan suke ta matsa remote din hannunta domin gane keys din wace motar ce ta dauko.
Sai da ta fito da motar sannan ta nufo shi ta dauke shi har lokacin amai yake ta saka shi motar, gaba daya ta gama fita hayyacinta, ko kadan bata son wani abu ya sami yaranta sai take ganin zata ragu ne, domin a halin yanzu bata da wasu family bayan Fatima sa London, kuma ta tabbatar ba zata sami wasu ba, domin alkawarin da ta daukarwa kanta abu ne da take jin babu wani abu da ya isa ya saka zuciyarta kusantar kofar da zata karyashi.

Yadda ta ja motar ta fice daga gidan kai kace koyon tuki take bata kware ba, domin jikinta rawa yake ta ko'ina irin rawar nan na wanda ke tsoron faruwar wani abu, each and every second sai ta juya ta kalli danta dake gidan baya tana kiran sunansa, kamin ta isa asibitin gaba daya ta fita hayyacinta, domin bata taba ganin danta yayi amai mai yawa haka kamar yau ba. Babbar asibitin kudi ce da aka saba kwantar da London a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, ba London kadai ba har Fatima da ita kanta Vito ya dauki nauyin a duba su asibitin ta kudi.

Ta karbi kati shiga asibitin suka duba bayan motarta sannan ta tuka da karfi ta isa Emergency ta fito a firgice ta tare da ta kashe motar ba haka kuma tashin hankali be barta ta rufe motar ba, ta bude back seat da sauri ta fara janyo danta sai ta ji karfinta ya kare ta gagara fitowa da shi, sai kawai ta fashe da kuka ta saka ihu, securities din da suke tsaye a emergency din suka nufota da sauri suka fito da London da har lokacin amai yake ta shekawa. Nurse suka fito da gado aka dora shi.

 Dan Allah ku taimaka min kar ya mutu, ku taimaka kar ya mutu

Shi ne abun da take ta fada da halshe Ibo tana kuka ta bi bayansu, daya daga cikin security ne ya shiga motarsa ya faka a gurin da aka tana domin aje motoci, ya shiga mata da key din. Tana ta zarya ta kasa tsaye ta kasa zaune, kafarta babu talkami kanta a yamutsa fajamas din dake jikinta ma kadan wandon ya wuce mazaunanta be gama sauka a cinyarta ba, rigar kuma bata da kauri sosai. Kusan kowace fatar jikinta a bude take, ban da kirjinta zuwa kasan cibiyarta.

 Ga keys din motarki

Ta kalli key din sannan ta karba ta rike ta cigaba da zirya kafarta babu talkami, kana kallonta kasan a firgice take, hankalinta kuma be kwanta ba sai da London ya samu saukin aman da yake yayi bachi a dakin da aka sauke shi, Likitan da ya karbe shi ya kalleta yana murmushi.

 Da sauki ma fa sosai kawai ke ce kika daga hankalinki

 Be saka yin amai irin wannan mai yawa ba, kuma zafin jikinsa ya wuce kima

Ta fada hawaye na sauko mata.

 Eh amman da sauki sosai, kuma ina son na baki shawara ya kamata ace kuna da likitan dake zuwa yana duba shi akai akai, kin ga kamar irin yanzu, da ace akwai likitan dake duba shi ba sai kin yi wahalar zuwa ba, sai idan abun ya gagara, yana da ki samu likitan da zai duba shi koda yaushe, yadda kike daga hankalinki wata rana ba zaki iya kawoshi asibiti ba

Ta daga masa kai, sai ya daga kafadarta alamar karfafa guiwa ya wuce, ita kanta zata so ace akwai likitan dake duba danta duk lokaci, sai dai tasan Vito ba zai yarda ba, domin baya yarda da kowa ya shiga gidanta balle kuma rayuwarta ko ta yaranta, ta yi ta kokarin yin haka yin haka ba sau daya ba amman be amince mata ba. Ta shiga dakin ta rufe kofar a hankali ta karasa kusa da shi tana kallon fuskarsa.
Rayuwarta take tunawa a wani dare makamancin wannan da rashin lafiya ta kamata, ita kan ta fishi ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????wahala kwananta uku tana ciwon ciki kamin akaita asibitin, sai kuma aka rasa mai jinyarta domin bata da kowa sai gamon tsintsiya da ragga wato mutanen da aka raine ta a tare da su a gidan marayu.

Ta zauna a kujerar dake kusa da gadonta ta kama hannunsa ta rike, jininta ne wannan shi ne kadai zata iya shaidawa duniya cewar ita din daga gareta yake, kuma shi din nata ne, bayan wannan da kanwarsa bata da wani abun tunkaho, da ace ta rasa shi a yau da daren yau ya fi kowane dare muni a gareta. Hannu ta saka ta share hawayen idonta tana tunanin Fatima ta san zata ji tsoron zama ita kadai a gidan gashi bata fito da waya ba balle ta kira Chidimma tace ta shiga ta kwana tare da ita, haka kuma ba zata iya barin anta shi kadai a irin wannan lokacin da bata san karfe nawa ba ta tafi gida.

Bachi rabi da rabi ta yi saboda tunanin Fatima, da kuma danta dake tsare da shi, sanyin asuba na fara saukowa ta mike tsaye daga kan kujerar yana mika, kamin ta sirina ta sumbanci danta dake bachi ta shafa kansa zuwa fuskarsa, tana matukar tausayin rayuwarsa saboda yadda tasa kaddarar ta zo, shi din ba kamar sauran yara ba ne, gashi kuma ciwon sickle be barshi yayi walwala ba. Ta dago ta nufi kofar ta bude a hankali ta fice ta rufe, haka ta taka har gurin motarta babu talkamin domin bata zo da su ba, sai da ta yi ta dubawa sannan ta gane gurin da aka aje mata motar.
Ta tuka motar cikin natsuwa ta isa gida, sai dai ta yi horn ya kai goma kamin mai gadin ya taso ya bude mata, ta faka a gurin da ta dauki motar ta bude ta fito tana amsa tambayar jikin London da mai gadin yake domin ya ga yadda aka fita da shi.

 Ya ji sauki

Ta amsa a gajiye sannan ta nufi cikin gidan ta bude ta shiga, sama ta haura da sauri ta shiga dakin Fatima, ba karamin dadi ta ji ba ganin Chidimma na rumgume da ita suna bachi, ta yi murmushi kadan sannan ta juya ta fice daga dakin ta shiga nata dakin, tufafin jikinta ta cire ta shiga bandaki ta yi wanka ta fito daure da bathrobe ta daure kanta da tawul.
Kitchen ta nufa tana hamma ta kunna gas ta shirya abun karyawa, sannan ta fito a daidai lokacin da Chidimma ta sauko kasa.

 Good Morning Maa

 Morning Chi

 I'm sorry na kwana a nan ne saboda Fatima ta same ni tana ta kuka wai ba zata iya kwana ita kadai ba

 Kin kyauta na jidadin haka, ga abun karyawa nan na shirya ki shirya yanzu ki tafi asibiti gurin London, saboda zan tafi gurin aiki yanzu, ki fadawa direban Fatima idan ya daukota daga school ya kirani zan fada masa inda nake aiki sai ya kaita saboda kar dawainiyar ta miki yawa, idan na tashi zan biyo asibitin idan sun ba mu sallama sai mu dawo tare

 Okay Maa

Emily ta ratsa gafenta ta haura sama, cikin kankanen lokaci ta shirya ta fito dakinta ta leka dakin Fatima sai ta same ta a bandaki tana wanke bakinta

 Good Morning My Love

Fatima ta juyar da fuska, cikin rashin jindadin abun da ta yi Emily tace

 Idan kin tashi daga School ki fadawa direbanki ya kira ni, zai kawo ki gurin da nake aiki idan ban tashi ba a lokacin, saboda Chidimma zata tafi asibiti gurin London, ni kuma zan tafi aiki

Tana fadar hakan ta ja mata kofar bandakin ta rufe ta fito daga dakin ta sauko kasa tana jin zuciyarta na mata babu dadi, ta karasa dinning wayarta na ringing a karo na uku, tea ta zuba ta daga cup din ta sha rabi sannan ta nufi kofar falon ta bude ta fice.
?? A road din unguwarsu ta amsa kiran Vito dake ta shigowa wayarta, ta sani ba dan baya garin ba da yanzu ya karaso gidanta, domin a ka'ida idan yayi mata kira uku bata daga ba to ba zai yi na hudu ba, zata ganshi gidan ne.

 Hello

 Are you okay? Lafiya kike?

Ta ji kamar ta ce masa aa ina cikin damuwa kuma ta fada masa London yana asibiti amman bata son daga masa hankali, haka kuma bata son yana shiga al'amurranta kokarin jenye shi take daga jikinta.

 Yeah I'm fine

Dakikun da ta dauka bata ba shi amsa ba ya saka shi fahimtar tana cikin damuwa, daman kuma ya karanci muryarta.

 Don't lie to me, me ya faru bayan bana nan?

 Fatima ce kawai bata jin magana

Yayi shiru ba tare da ya ce komai ba, sannan ya kashe wayar, ita kuma ta sauke ajiyar zuciya ta tari okada ta hau ta, be sauketa ko'ina ba sai gurin aikinta.





ALIYU POV.

8:36pm...
Gaba daya yanayinsa ya canja zuciyarta ta sosu kuma ransa ya bace sosai saboda abun da yayi arba da shi a wayar matarsa. Sai dai a cikin sharudansa akwai kokarin kwantar da hankali da kuma yin uzuri a duk lokacin da wani abun bacin rai ko tashin hankali ya same shi, ya sani ya dara matarsa Aisha Ilmi da goge, kamar yadda ya fita shekaru haka ya fita hankali da zurfin tunani domin hankalin namiji ba daya yake da na mace ba. Ba da'asar bace bincikar wayar matarsa domin ya yarda da ita 100% ko da yake ita bata yi masa irin wannan yarda ba saboda kishi, a duk lokacin da ta samu dama sai ta bincike wayarsa, sai dai tana daga masa kafa domin bata taba daukar wayarsa ta bincika ta same shi yana chatting da mata ba, ko wani abu makamancin wannan, abu ne da ya daukarwa kanta nisanta wayarsa da duk wani abu da zai dauki hankalinsa daga matarsa a lokacin da tafi bukatarsa a kusa da ita. Ya haddace password din wayarta, ita ma ta haddace masa saboda yarda da suka yi da junansu.
Ya aje wayar yana kokarin saita kansa, domin be kamata ya nuna mata bacin ransa a yanzu ba, ko ba komai tana dauke da juna biyu zata iya damuwa, haka kuma ba zama lallai abun da yayi arba da shi a wayarta ya zama wata illa ko laifi a idonta ba. Ta kalleshi bayan ta sallame sallar Isha'i tana murmushi.

 Ki yi min addu'a

 Ai kullum ina maka addu'a amman cewa nake Allah yasa daga ni babu kari

Ya daga kafadunsa yana murmushi mai sauti.

 Daman ai daga ke babu kari, wai baki yarda da alkawarin da na yi miki ba?

 Na yarda mana, amman matan yanzu fa shaidanu ne, kai dai Allah dai ya tsare kawai kuma ya kawar da idonka

 Ameen

Ya girgiza kai ya kai hannu ya dauki dabinon ajwa ya kai bakinsa, sai da ta kammala addu'ar sannan ta dawo kusa da shi ta zauna ta cire hijab din. Janta yayi a hankali ya kwantar jikinsa.

 My one and only ina bukatar tuna miki wani abu, kuma ina son ki dauke shi serious

Ta dago kadan ta kalleshi.

 Minene?

 Sirrinmu sirrinmu ne, be kamata wani ya ji ba, musamman na auratayya, yadda muke mu'amala da duk wani abu da ya shafi gonarmu be kamata wani ya sani ba

Gabanta ya fadi, domin ta fahimci kalamansa sai dai kunya irin na wanda aka tsinkawa zane a kasuwa ba zai barta ta nuna masa ta fahimci nufinsa ba.

 Ni bana gane yarenka ka fito fili ka fada min abun da kake nufi

Ya tashi zaune da kyau ya fuskanceta.

 I'm sorry na shi whatsapp dinki na san be kamata na shiga ba wata kila akwai sirrinki da yan'uwanki da be kamata na ji ba ko na sani, akan hakan ina baki hakuri, wani sako ya shigo ta sama kuma na bude na gani, wata kila saboda na samu damar tunatarki me Allah ya nuna min sakon

 Kana ta jan sakon da tsaye please minene?

Ya aje numfashi a hankali.

 Na ga wani chat da kike da kawarki Huda, ban san iya aminci ko yardar dake tsakaninku ba, amman Aisha ban jidadin yadda kike fada mata sirrin shimfidarmu ba, ko a musulunci babu kyau, kuma maganganun ne da basu dace ba

Ta dan wara ido tana murmushin da ya kusa zame mata dariya.

 Haba dai, wannan fa duk zancenmu ne na mata, kuma ita da ba ganinka take ba ma

 Ko dai minene tun da kika ga musulunci ya hana be kamata ki aikata ba, akwai illa ciki? Fadin amfanin me zai mata? Shikenan kin bude mata cikinki ta san sirrinki ta san sirrin mijinki, yadda muke mu'alama da komai ta sani, ban jidadi ba kuma in miki daukar mace mai hankali ne mai sani ya kamata, ban yi tsammanin zan ga haka ba, kuma ban jidadi ba

Ya karasa da dan fada domin ya fahimci kamar bata dauki abun a wani abun ba, ganin haka ya saka jikinta yayi sanyi, shi kuma be sake ce mata komai ba ya tashi ya fice daga dakin. Da kallo ta bishi har ya fice sannan ta dauki wayar felling guilty ta bude chat din tana dubawa tare da mayar da amsar tambayar da Huda take mata, kamin da kara da.

 Ke yau ya duba wayata ya ga chat dinmu

Sannan ta kashe data ta gyara kwanciyarta da kyau, domin abu ne da ta sani idan suka samu tsabani shi yake bata hakuri, shi yake nemanta. Ba dabi'arsa bace bawa miji hakuri idan ta yi laifi, haka kuma ba mace ce mai saurin karbar laifinta ba, idan ma har ta aminta tana da laifin kenan.
And to her hira da kawa ko a group chat da mata yan'uwa Normal ne domun suna suna fadar yadda suke tasu mu'alamar kuma dukansu mata ne babu maza, bugu da kari tana ganin aminci da jindadi ke saka irin wannan chat din.

Bayan duk wannan ma why zai dauki wayarta ya shiga chat dinta da kawarta ko kawayenta har ya ga abun da suke tattaunawa, a ganinta a nan kam shi yake da laifi, kuma dai chat irin wannan tsakanin mata ai ba wani abu ba ne, dan haka bata shirya ba shi hakuri a yanzu ba. Yadda ta ayyana haka ne ya faru domin bayan ta yi bachi ya dawo dakin ta kwanta a kusa da ita, daman can no matter how suka samu tsabani baya taba raba gado da matarsa balle kuma har ta kai ga ya raba daki.

Yayi bachi not like usual yadda ya saba, domin yana son ya nuna mata illar abun da ta yi, dan haka be shirya abun karyawa ko ya jira ta shirya masa ba yayi wanka ya yi shirin office ya fice daga gidan at early morning.
[4/20, 9:58/ AM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: *

*? Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen...
'?

Page 7??


TURHAN POV.


 Shikenan zan jiraka a waje

Ya aje wayar ya nufi gurin da suitcase dinsa yake ya bude ya ciro wani karamin roll on ya murza a wuyan hannunsa sannan ya aje a mirror dake dakin ya sake nufar wayarsa ya dauka ya saka aljihu ya dauki key din dakin ya fice ya rufe dakin.
Stairs ya bi har ya sauko daga hawa na uku zuwa na daya, kamin ya karaso kasa ransa ya gama baci domin Turhan ba mutum ne mai son motsa jiki ba sai dole, ko kadan baya son aikin wahala balle kuma wahalar ita kanta da baya hada hanya da ita.

Harabar hotel din ya fito yana kallon yadda tsari da kawar babbar hotel din take daga kasa, domin sun sauka sa dare ne a jiya, gajiya bata bashi dama kamar yadda hutu ya bashi a yau da safe ya kalli ko'ina ba. Kusa da wata flower ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login