Showing 153001 words to 156000 words out of 253142 words

Chapter 52 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18392

karantar da shi ko ma minene abu ne mai muhimmancin sosai a gurinta, karfin hali yayi ya tashi daga inda yake ya taka cikin takunsa na kasaita kamar wanda baya son taka kasa ya karasa inda take zaune tana kukan ya tsaya daga gefenta ya kalli mutanen da suke gurin yana kirga mutane nawa ne, domin ya san Emily zata iya disgashi ya lura gaba daya an hure mata kunne, har ya kalli inda take zaune kamar ya zauna amman ba dama ya san zata iya tashi ta bar shi a gurin.

Ya tsaya a gabanta kamar wani hoto ya kalleta ya kalli harabar ya kasaita ta hana shi bude baki ya tambayi me ya saka ta kuka, baya son ta zubar masa da kimarsa just because yana nemanta kuma yana neman gyara abun da ya bata, sai dai kuma tunawa da Fatima ya saka shi kawar da komai, domin samun Fatima a yanzu yana jin Emily ta gama masa komai, ya hade yawu zauna a gurin, jin alamar mutum ya zauna a kusa da ita ya saka ta mike dago kanta daman tun da ya iso gurin ta ji alamar mutum amman bata dago ba sai da ya zauna kusa da ita.
Ganin Turhan ne ya saka ta mike tsaye da sauri sai yayi hanzarin mikewa tsaye ya riko hannunta.
Juyowar da zata yi sai ta juyo da shirinta na sauke mata yatsunsa biyar na dayan hannun a fuska, yayi hanzarin saka dayan hannun ma ya rike dayan hannun.

"Zaki iya marina ki ci mutuncina yadda kike so idan muna daga ni sai ke a guri a gurin da jama'a suke kai da kawo ba, Aisha kin fa san waye ni na san kina jin haushina amman..."

Be kai aya ba ta buga masa kanta a hanci ba shiri ya saki hannayenta.

"Ya Rabbi ya Allah..."

Ya furta yana jin wani gishirin bala'i a hancinsa yana ratsashi har cikin kai, ya kai hannu ya taba hancin nasa har yana huro iska ya ji ko hancin yayi jini, bata tsaya a gurin ba ta kara gaba, bata wani san asibitin ba da tambaya ta isa gurin da ruwa suke ta tara hannunta ta wanke da kasa sannan ta tara hannunta ta dauraye. Turhan na can daga nesa yana kallonta ganin ta wanke hannun ya saka jin wani iri ya kalli hannayensa even though ya san hannunsa are clean. Karfin hali yayi ya karasa gurin da take duke ya tsaya daga bayanta.

Duke take a gurin tana ta kuka, abubuwa sun chabe mata a yanzu, Vito yayi fushi har ya cutar da Aliyu, ga Fatima bata hannunta ga shi ta hadu da daya daga cikin manyan makiyinta wato Turhan, Aliyu yana raye ko ya mutu bata sani ba, but no matter what bata so wani abu marar kyau ya samu Aliyu ba, balle kuma ace sanadinta ne.

"Ina son na san dalilin kukan ne wata kila zan iya taimaka miki, ki fada min me ya kawo ki nan kuma me ya faru ba dan ni ba sai dan Fatima"

Ta runtse ido cike da bacin rai, yanzu kuma ta rasa dalilin wannan mutumen na bibiyarta, da ace tana da iko da ta toshe kunnuwanta daga sauraren muryarsa. Mikewa ta yi tsaye ta juyo ta kalleshi.

"Har abada, har kasa ta rufe idona, har duniya ta nade ba zan taba karbar taimako daga gareka ba, balle kuma har na nema, da zaka iya da ka taimakawa kanka ka nisanta kanka daga ni da duk wani abu da ya shafe ni, idan ka aikata hakan rayuwarka zata tsawaita ka cigaba da zalunci da ka sakawa gaba, kuma saka ceto kanka daga wulakanci, idan akwai muryar da na tsani ji kamar mutuwata to taka ce, idan akwai fuskar da zan iya kwakwale idanuwana na zubar da su saboda kyamar kallonta to taka ce, idan kana kallon Fatima a wani tsanin hawa to ka yi kuskure domin Fatima bata da uba, ko a tsintuwa ta zo ba zata taba zabarka a matsayin uba ba, mutumen da ya kalli uwarta ya aibanta surarta, ya kaskantar da ita a matsayin baiwa a fadar da ya kamata ace an girmamata, ya kira ranar auren uwarta da bakar rana, ya kira ranar da ya kebe da uwarta har aka samu cikinta da bakar rana, ya fadi cewar ba zai taba son abun da ta haifa ba, ya watsa mata yawu a fuska, wai duk saboda kawai ta aure shi dan ta farantawa uwarsa rai, ya kira uwarta da tubabbiya, ya kira dan'uwanta da shege yana musa cewar ta sunna aka same shi, ya bar uwarta ta wahala a titi ta haife ta a titi ta raine ta a titi kuma yana raye yana da hali da Ikon da zai iya kula da yarsa, ya juya mata baya sai a yanzu da yarinya ta yi wayo zai dawo yace shi ne ubanta? Yarinyar da na gina rayuwarta da tsanarka? Yarinyar da bata taba yarda ta zo duniya da uba ba? Kai kan wane irin mahaukaci ne? Har kana da idon da zaka kalli Fatima ka fada mata kai ubanta ne? Allah ya waddaran namiji irinka, Allah ya kwashewa rayuwarka Albarka, ka yi hasara"

Kallonta yake kallon da ya hango tsanarsa a cikin idanuwanta ya karantar da shi kiyayyarsa a cikin kalamanta da muryarta, ta tuna masa da abubuwan da ya manta kuma yake ganin kamar ba komai ba ne, ta yi gaskiya shi din be cancani ya kalli Fatima ya fada mata shi din ubanta ne ba, amman hakan ba zai karya guiwarsa ba domin komai ya faru ne saboda rashin sanin inda take da kuma cikin da take dauke shi. Ya bi bayanta da kallo ganin rashin dacewar tufafin dake jikinta. A sanyaye ya juya ya nufi gurin da ya aje motarsa ya shiga ya zauna kalamanta na ta yi masa yawo a cikin kai.

Be kyauta ba ya sani, kuma ya zafafa da yawa a yanzu ya gane hakan, kuma ya fahimci kirjinta ya cika da tsanarsa da kiyayyarsa tana ina ma zai fara gyara abun da ya bata, tun da bata ba shi hadin kai, kamata yayi ace Aliyu yayi masa wannan yakin tun kamin ranar yau wata kila da abubuwa sun zo masa da sauki, tun da gashi ya san har da ya a tsakanin su amman be masa ba sai ma kokarin boye masa yake yana munafurtarsa, a yanzu ya kara gane Aliyu ba abokin kwarai ba ne, ta ina ma ya gane ta? Ina ya hadu da ita taya suka kulla alaka abu ne da yake bukatar ya sani..
Ya dauki wayarsa ya kira layi Ammy ta amsa kiran ya gaisheta ta amsa, kasancewarta uwa sai ta fahimcin canjin muryar danta ta yanayin yadda yake amsa mata magana alamar akwai abu a kasan halshensa.

"Ammy ina Fatima?"

"Tana can falo tana cin abinci, daker ma na samu take cin abincin, babu wanda take kira sai Aliyu da Aisha, gaba daya ta ki yarda da mu, na fada mata ni ina matsayin kakarta ne amman ta ki karbar hakan tace mahaifiyarta bata da kowa, ita kuma bata da uba, ban san yadda zan yi na fada mata kai ubanta ba ne, Turhan ka lalata abubuwa da yawa"

Ya sauke ajiyar zuciya yana taba hancinsa da har yanzu yake masa ciwo.

"Na sani Ammy zan yi kokarin gyarawa kamar yadda kika ce, ba za su karbe ni da sauki ba amman zan... Zan jure wajen ganin komai ya tafi daidai, wata kila shiyasa Allah ya kawo ciwon nan naki yasa na zo abubuwan nan suke ta faruwa"

"Kana ina? Ina Aisha take?"

"Ina asibiti, na kwana a gidan Aliyu jiya saboda ina tsoron kar na tafi tayi tafiyarta ban san inda zan same ta ba, kuma yanzu ta zo asibiti ban san wa take nema ba, amman dai kuka kawai take"

"Ka tambaye ta mana"

"Ba zata min magana ba, na gwada yin hakan ban dace ba, amman dai ko minene yana da muhimmancin sosai a gurinta domin kuka take sosai kuma hankali a tashe ta zo nan"

"Duk yadda zaka iya idan ka gano matsalar ka taimaka mata, kuma ka fada min ta hakan za mu yi ta yakin har mu yi nasara In Shaa Allahu"

"Okay"

Ya sauke wayar, ya sake fita motar jiki a sanyaye ya fara zagayawa ta asibitin har ya samu inda take zaune ya zauna nesa da inda ba zata ganshi ba yana ta kallonta, ta ya ta canja haka? Ina wacan yaron? Yaushe da bar addinin Musulunci ya yi ma kansa tambayoyin a take, tun yana tsayuwa da dadi har kafafuwansa suka yi tsayi domin yayi awa daya da rabi tsaye a gurin yana ganin Emily, a tsawon awa daya da rabin babu abin da Emily take sai kuka domin jikinta na raya mata ko dai Aliyu ya mutu ko kuma yana cikin mummunan hali bata san me zata yi a yanzu ba.
Sau goma sha daya yana yunkurin tafiya ya sameta ya sake tambayarta damuwarta sai kalamanta na dazun su rike masa kafa, sai dai kuka yana jin wani iri kamar dai babu dadi tana kukan ko ba komai kukanta na yanzu yana tuna masa da kukanta da ta yi a wacan lokacin har take rokon ya dawo da ita gida ya ki.

Ya shafa kansa yana jin babu dadi, lokuta da dama mutum ya kanki abu kuma ya zama shi ne alheri a gurinsa, ko kuma ya so abu ya zama abun sheri ne a gurinsa, a yanzu ya fahimci hakan domin gashi tsananin rabo ya saka ya samu haihuwa da matar da ya tsana yake ganin kamar bata dace da shi ba, ashe uwarsa ta iya zabe kuma ta hango masa abin da shi be hango ba be fahimta ba, kibar ma ashe da ta samu kulawa mai kyau jikinta zai canja ne yayi kyau ita ma ta yi kyau kamar yadda take yanzu, wato sai a yanzu ya fahimci ba karamin aika aika yayi ba, gaba daya ya rasa ta ina zai kama zaren lamarin ma balle ya dinke.

Hango waya a kunnenta ya saka shi maida hankali sosai gurin kallonta na son fahimtar abun da yake faruwa, bata ji ma da sauke wayar ba ya hango Ummi ta iso gurin da take zaune sai Emily ta mike tsaye Ummi ta yi mata magana sannan ta rumgumeta, can kuma ta kama hannunta suka shiga cikin asibitin. A nan ne kansa ya kara daurewa zuciyarsa ta hararo masa ko danta din nan ne ba shi da lafiya Aliyu ya turo Ummi ta taimaka mata? Waya sani ko Aliyun ma yana ciki? Amman kuma Ummi ai ba anan take ba Abuja take zama. Motarsa ya koma yana ta tunanin me ya faru me zai faru, be san a inda zai samu labarin komai ba sai da Kameela ta fado masa a rai sai dai kuma ba shi da Number ta.

Ya kira Ammy ya bukaci ta kira layin Kameela ta bincika masa abun da yake faruwa, sai Ammy ta fada mata da number Kameela kuma ta labarta masa Aliyu yana asibiti, ta gane hakan ne a lokacin data kunna wayarsa dake hannun Fatima saboda Fatima nata yi mata kuka sai aka yi ta kira ana tambayar abun da sauki.

"Ina tunanin ko dai ya samu hatsari ko kuma wani abun ne ya faru da shi"

Turhan ya sauke wayar a kunnensa yana wani kashe ido.

"Kam uban nan, wato Aliyu take yi ma kukan nan? Lallai ko a cikin munafukai wutarka ta dabam ce Aliyu, har ya aka yi irin wannan shakuwar da ita? "

Ta ji kamar ya tafi ya bi bayanta sai kuma wata zuciyar ta hana shi, ya yi ma motarsa key ya dauki hanyar gidan Ammynsa, sai da ya kusa isa ya ji kamar ba zai iya barin abun ya wuce ba yayi reverse ya juya sai kuma wata zuciyar ta tuna masa shi da yake neman mafita a yanzu ai be kamata yayi rigima ma be kamata yayi abun da zai saka Emily ta tsane shi ba, ya sake reverse ya juyo sai kuma zafin abun ya doki zuciyarsa taya wai zata zauna tana kuka hehehe akan wani katon banza munafiki? Alhalin tana matarsa? Da ama ace Aliyun yayi masa abun arziki da sauki ko shi ya bata aurensa ai kukan da take yayi yawa balle kuma yanzu a duk duniya ba shi da makiya kamar Aliyu.

Ya juya ya sake daukar hanyar asibitin sai kuma ya sake juyowa haka zuciya ta yi ta juya shi kamin yayi nasara cin galaba akanta ya kawo kansa gida gurin Ammy, ya shigo cikin falon ya zauna takaici ya hana shi magana. Ammy ta dube shi daman ta fahimci damuwa tun a dazun da suka yi waya.

"Me ya faru? Ko yunwa kake ji ne? Ko dai minene ka saita kanka be kamata Fatima ta kanka a cikin wannan yanayin ba"

Ya kalli Ammy sai a lokacin ya tuna da wani zancen abinci daman rabonsa da abinci tun wanda ya ci a jirgi.

"Wato Aliyu munafiki ne Ammy, Wallahi ban tana tsammanin haka daga gareshi ba, wai kin ga yadda yarinyar nan take kuka? Ashe duk shi take yi ma kuka kamar wani ubanta? Shiyasa aka ce makiyinka yana tare da kai Allah kadai ya san abun da ya shuka mata? Shi ko kunya baya ji ma? Ai na yi zaton ko mutuwa na yi Aliyu ba zai min haka ba, har da Ummi ta zo ta rumgume ta yadda kika san wani shirin film wata kila gidansa ko gidan Ummi take zaune, haka yake ta kallonta yana rayuwa da ita kuma ya san ina nemanta, ya boye min komai, ba wai ina kishi ba ne, sam amman dai ni ko dolo ne ai dole na nuna takaici ko?"

Yana maganar yana jin abun da be saba ba, daman babu wanda ya kai balarabe mugun kishi na bala'i, Balaraben mutum da muryar matarsa be son aji, ko da yake shi a yanzu ba kishi ba ne haushin Aliyun ne yake ji na abun da yayi masa.

"Zaka iya kwantar da hankalinka ka yi min bayani? Ni duk ban gane wannan kewaye kewayen ba"

Ammy ta tambaya yana kallonsa domin bata fahimci inda ya dosa ba, sai ya mike tsaye yana huci.

"Idan ma na yi kishi ai ina da hujja ko dan Fatima? Emily ko mutuwa ta yi dole na kare martabarta saboda wannan yarinyar, ai ba zan jidadi ace uwar yata ce take wannan shigar ba? Har tana hulda da abokina, lallai Aliyu ya hadiye kashin da zai zame masa masifa a wuya, ba fita ba wucewa, kuma har abada ni da shi Wallahi Tallahi babu wani uzuri, abun da yayi min ya fi ka dauki wuka ka chakawa mutum"

Ya koma ya zauna yana cizon hakora.





ALIYU POV.

Ya bude ido yana jin jikinsa yayi masa nauyi sosai kamar ba na shi ba, kuma yayi matsa tsami, amman karfin hali irin na namiji da juriya yana hada ido da mahaifiyarsa sai ya saka matar murmushi. Yayi yunkurin bude baki yayi mata magana sai ya ji bakin yayi masa nauyi kansa kuma ya fara ciwo daman shi ma kan na shi yayi masa nauyi. Ummi ta yi ma wata yar'uwarta magana ta fita ta kira likita ya shigo da sauri ya duba shi ya cire masa ruwan dake jikinsa ya taimaka masa ya tashi zaune aka kawo roba ya wanka bakinsa Ummi ta hada masa tea ya sha aka ba shi magani ya sha.
Ummi na kusa da shi zaune sai matsar kwalla take tana kallonsa.

"Ummi da sauki fa kina gani to kuka na me kuma?"

Cikin kuka Ummi ta ce.

"Allah kadai ya san zafin da kake ji amman ba zaka nuna ba dan kar na damu, kalli yadda suka maka rauni a kafa, jiki ko'ina duka"

"Saukin abun ma babu karaya, amman ko suwa gaskiya kashe ka suka so yi"

"Ni ban san ko suwaye ba, ni dai ina tsaye ina waya da Ummi kawai na ji duka ta ko'ina da itace da hannu, Allah yasa inda na tsaya kusa da mutane ne kuma ana hada hadar shiga Sallah Magariba domin an yi kira ne lokacin sai mutane suka hankalta da wuri suka kawo dauki, mutanen suka gudu, na ji dai ana ta Innalillahi ni ma kuma ina ta tun da suka hau ni da dukan, a nan jama'a suka taimaka aka dauke ni aka dora ni a babur din wani aka yo asibiti da ni, suka ce ba za su karba ba, saboda kaina da kafata suna zubar da jini lokacin ga hannayenta sun duka bana ma iya daga su, to daga nan dai hankalina ya bace ban san ya aka yi ba sai yanzu da na farko nan"

Ummi ta ce.

"Muna wayar nan da kai na ji kana ambaton innalillahi sai ina jin karar duka na san ba lafiya ba, ko dai ita yarinyar ko kuma Kameela tun da su ma ba hankali da su ba ko kuma shi Turhan din cikinsu akwai wanda ya saka aka yi maka haka, kiran yankewa yayi na fito na shiga bangaren Daddynka na fada mishi da ya gwada kira sai ta shiga, Allah yasa yana gida a lokacin shi yayi magana da su ya fadi asibitin da za a kaika kuma ya kira CP ya sanar masa maka, yanzu haka kofar nan police ne awaje ba abarin kowa ya shigo, sun ce sai ka farka za su shigo su dauki bayanai"

"Ummi ya aka yi kika zo?"

"A dare nan ban iya kwana a Abuja ba ai, mota muka biyo da rakiyar jami'an soji sha biyu na dare na sauka garin nan, kowaye ya maka wannan abun ba zai tsira ba In Shaa Allahu"

"Allah y sauwake, idan kun dan gana sai a bar shi ya samu hutawa saboda ya ji ciwo a kai yawan magana zai iya haifar masa da matsala"

Likitan ya fada sannan ya fice.

"Emilyn ma tun dazun take kira ta zo nan ba su barta ta shigo ba"

Aliyu ya kalli Ummi.

"Taya aka yi ta sani?"

"Ban sani ba, amman dazun wayar tana hannun mubarak ya fada min ta kira ya fada mata kana asibiti"

Ummi na rufe baki sai ga kiran Emily ya shigowa a wayar Aliyu dake hannun Ummi.

"Gata nan ta sake kira"

"Ummi abarta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login