Showing 33001 words to 36000 words out of 253142 words

Chapter 12 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18442

wayarta. Amman ta kasa magana.

 My bad

Ya furta sannan ya kashe wayar, hotunan da Fatima ta tura masa ta duba a lokacin ne ta sake kallon Fatima cikin tsawa ta ce.

 Me ma'anar hakan? Ina kika san shi? Ina kika samu number shi?

A nan kuma ta kwashe labarin komai ta fadawa mahaifiyarta, babu abun da ta boye ko ta manta tun daga farkon haduwarsu har zuwa yau.

 Amman na fada miki ki daina magana da mutanen da baki sani ba, miye amfanin abun da kika yi, baki san manufarsa akanmu ba, bayan ganinsa da nake a kamfanin nan ban san waye shi ba, ban san halinsa ba

 Cewa yayi ya sanki

 Meyasa baki bari na gabatar miki da shi ba? Kin taba ganin na nuna miki shi ko na masa magana? Kin taba ganina tare da shi...

Ta sake daka mata tsawa har tana mikewa tsaye kamar zata dake ta, Fatima ta razana sosai ta matsa baya tana fashewa da kuka.

 Sorry Momy

Ta dafa kanta ya juya ta juyo gaba daya ta tsoro kamar wata marar gaskiya, can kuma ta koma ta zauna ta dauki wayarta ta aika masa da sako.

 Me kake nufi da abun da ka saka yata ta aikata? Me kake nema a yanzu? Bayan korar da kuka min yanzu kuma wani sherin kuke neman bina da shi?

Ya duba sakon amman be bata amsa ba, kuma da alama be shirya yin hakan ba.

 Kana wasa da rayuwarka ne yaro, baka san waye ni ba, kuma bari na fada maka idan wani abu ya same ni ko ya samu yata sai ka yi nadamar zuwanka duniya

 Boy? Huh? Hmm

Ya rubuto mata as reply. Kana ya rubuto mata.

 Mutumen da ya fada min halinki ya fada min babu ruwanki da fitina, amman naga akasin haka, bana nufinki cutar da ke, mu musulmai bama cutar da kowa, kawai ina nemi yarinyarki ta turo min hotunanki ne saboda tantance Aisha da Emily, ina son na san banbancin wacan mai kibar da ke, ina son na gane banbancin wacan marar masifa da kuma ke

 Waye kai?

Ta mike tsaye tana kallon wayar gabanta na bugawa da mugun karfi. Hoton Turhan ya turo mata.

 Kin san waye wannan?

 Aa

Ta amsa da sauri gumi na karyo mata, sai ta kashe data ta goge chat din ta jefar da wayar akan gado, ta fara safa da marwa cikin dakin kamin hawaye su samu matsugunni a fuskarta. A nan ta fara tambayar kanta? Waye wannan mutumen tun farko? Meyasa yake bibiyar yarta da ita kanta? Yanzu kuma da ya turo mata hoton Turhan me yake nema a gareta? A kokarin samun amsoshinta ta sake daukar wayar ta bude data sai kuwa ta ci karo da sakonsa.

 Meyasa kike boya? Meyasa kika boyewa yarki gaskiyar cewar tana da uba? Why?

Ta kasa bashi amsa jikinta rawa yake kamar yadda zuciyarta ma take rawa.

 Baki san yarki ta yi farincikin ganin mahaifinta? Baki taba tunanin samarwa yarki iyali ba? Kiran sunanta da ake da Fatima Aisha Emily be taba damunki ba? Idan yarki ta girma ta mallaki hankalin kanta wane irin amsa zaki bata?

Nan ma bata amsa masa ba.

 Turhan yana ta nemanki babu dare babu rana, yana ta neman hanyar haduwa dake, wata kila baki san da hakan ba, amman yana da kyau ki hadu da shi ko dan yarki

 Ba kasan komai akan rayuwata ba, baka rayu a cikin duhun da na rayu ba, har yanzu ban gama warkewa daga ciwon da zan bukaci kowane namiji a kusa da ni ba, balle kuma Turhan, ba ni da alaka da shi, alakarsa da yata kuma na yanketa, daman be san da ita, idan ya saka shiga rayuwata da rayuwar yata ne saboda ya san halin da nake ciki, to ka fada masa Aisha da ya sani a da ba ita ce a yanzu ba, kuma kar ya kuskura ya tunkaro gurin da nake

 Ban riga na sanar masa ba, amman zan sanar masa a yau?

 Sanar da shi zai jefa rayuwarka da tawa da tasa a matsala ne kawai, karka aikata hakan, karka jefa ni a matsala, ina da yara har biyu yanzu, kokarin gina rayuwa nake, karka maida ni a kangin da na fito, ina da kudi enough zan biyaka ko nawa kake so, zan nika maka abun da ya baka dan Allah karka sanar masa, ina son yata ina son rayuwata, farincikina kankane karka barar da shi

Tana rubuta masa sakon tana hawaye.

 Na miki kama da mutumen da za a biya kudi a aikata wani abu? Ke kina ganina kin na girmi talauci, duk abun da kike takamar kina da shi, ina takama da ninsa sau dari

 Amman kace kai musulmi ne?

 Yes haka ne, babu shakka

 Ina hada da Ubangijinka Ubangijin gaskiya, da Manzon Allah ( S A W) yace ranar tashin alkiyama Allah baya magana da mutum uku har da wanda aka hada shi da Allah be aikata ba, na roke ka dan Allah dan Allah karka fadawa Turhan komai akaina, idan kuma har ka fada masa to ka canja, dan darajar Manzon Allah S A W na san indai kai musulmin kwarai ne ba zaka aikata ba!!!

Bayan wannan sakon bata sake aika masa wani ba, shi ma be sake cewa komai ba, ta aje wayar ta mike tsaye hawaye na cika mata ido har suna zuba ta fice daga dakin ta nufi dakin Fatima da tunin ta fice daga dakin na mahaifiyarta bayan ta fahimci nufinsa abun da ta aikata babban laifi ne.
Emily ta tura kofar dakin sai ta tsaya daga bakin kofa tana kallon Fatima dake kwance akan gadonta tana kuka, ta fara takawa tana tafiya jiki babu karfi, wayen da suke zubo mata a yanzu sun sha banban da na farkon. Jinjirar yarta take jangowa tana tuna lokacin da farinciki da kuma kishiyarsa suka lullube a rana daya, ranar da ta haifi Fatima, ta dauki cikin yarta ta yi rainon cikin ba tare da sanin Turhan ko danginsa ba, ta raini yarta irin rainon da bata fatan ko makiyinta ya fuskanci rayuwar data fuskanta, ta tuna lokacin da Nurses suke fadar a kawo kayan jaririya, kuma aka rasa abun da za a lulluba mata sai da wata ta taimaka mata da zane daya, ta tuna tsawon kwanakin da Fatima ta dauka a hannunta tana lullubeta da zane saboda babu tufafi.

Ta tuna yadda ruwan nononta yake kafewa saboda yunwa har sai da ta saci nonon akuya ta shayar da yarta, ta tuna yadda ruwa yake dukanta a rumfar wani bakanike da take fakewa idan dare yayi, ta tuna yadda take bin gidajen masu hali tana neman abun da zata kai a ciki, taya rana tsaka a yanzu Turhan zai bayyana yace nemanta yake me yake nema a gareta? Ya rabata da yarta kamar yadda ya rabata da sauran farincikin da ya rage mata a wacan lokacin? Ya sake dawowa rayuwarta ya haifar mata da matsala? A yanzu ta samu mai bata komai yayi mata ginshiki shi ne yake neman rusawa?
Ta kai hannu ta dago yarta, wani mummunan furuci da yayi mata a wani lokaci da farinciki ya juya mata baya ya dawo mata.

 Karki sake nuna kin san ni, akwai banbanci tsakanina dake

Ta lumshe ido tana tuna wata rana da matarsa ta saka bayinta suka yi mata bulala yana kallo be yi kokarin hanawa ba har sai da suka bar mata tabo a jiki. Ta rumgume Fatima, wani kalar ruwan hawaye ne yake mata zuba mai zafi da dacin zuciya, ashe duk bayan wannan zai dawo nemanta?

 Momy me yasa kike kuka? I'm sorry

Tambayar Fatima ta dawo da ita hanyacinta, sai ta bude idon ta share hawayen tana murmushi.

 Ina sonki Fatima, no matter what happen, daga ke sai London ne Iyalina, na wahala na yi sadaukarwa kamin ku kawo inda kuke a yanzu, a yanzu ma ban gama ba dan Allah kar wata rana ta zo ki fifita wani akaina

Ta rumgumeta, sun dade a haka sannan ta sake ta tashi ta fice daga dakin, kasa ta sauka ta zauna a falo zuciyarta cike fal da tunani. Vito be dawo gidan ba sai after 8pm, ya shigo falon tare da Chidimma dake rike da leda tana biye da shi a baya. Emily ta kalleshi ta kalleta.

 Ina London?

 Bachi yake, na zo na dauki wasu abubuwan ne na yi wanka

Ta maida dubanta gurin Vito, ya san abun da take bukatar ji tun kamin ta gabatar masa da tambayar ya bata amsa.

 Ya sauko ya daina fushi, na yi magana da shi

 Thank you

Ta gyada mata kai kawai, sannan ya kalli Chidimma.

 Ki shirya da wuri direba zai maida ke asibitin kar a barshi shi kadai

 Okay Sir

Ta amsa tana wani karairaya daman idan shi ya bada umarni ba ta bata lokaci take aikatawa. Sai da ta fice Emily ta maida dubanta gurin Vito da idanuwansa suka dade a fuskarta.

 Zan tafi na kwana can

Ya amsa mata kawai da ido sannan ya nufi kujera ya zauna, ita kuma ta haura sama ta shirya ta fito ta shiga dakin Fatima ta yi mata sallama sannan ta sauko suka fice a tare, ya rigata isa gurin motar ya bude mata ta shiga ya rufe sannan ya nufi bangaren da Chidimma take ya fada mata an samu sauyi zata kwana da Fatima saboda Emily zata kwana da London a asibiti, ya dawo motar ya ke kunne tun a lokacin da ya faka a harabar, daman a ka'ida baya kashe mota sai idan ya gama fita gaba daya a wunin ranar. Yana tukin yana karantar yanayinta har suka isa asibitin.

 Aikin fa?

 Na aje

Ya kalli irin kallon mai cike da tambaya, sai ta sauke kanta kasa tana taba yatsun hannunta.

 Saboda na bawa yarana lokacina

 Ko dai sun koreki?

Ya tambaya ne kawai ba dan hana da tabbacin haka din ba, domin ya san yadda ta kwalla fa rai da son aikin kuma har ta fara zuwa ba karamin abu zai saka ta aje aikin ba. Ta bude motar ta fice ba tare da tace masa komai ba, yana daga cikin motar yana kallonta har ta shige ciki sannan ya ciro wayarsa ya duba time, sai kuma yaja motar ya fice daga asibitin.




ALIYU POV.

Ya hade yawu a hankali yana mamakin yadda aka yi ta san hadisin da ta kafa masa hujja da shi, ta san addinin musulunci ne har haka? Ta yi nisa a ciki? Me yasa ma ta bar addinin tun farkon fari. Ya sake karanta sakon ta dayan bangaren yana nisa tunanin a wani bangare na labarin da ta gutsura masa, gashi kuma ta daure shi da kalamanta, be rabi Turhan a zamanin da suka yi rayuwa a Emily ne, dan haka ba zai iya shaidar kyautata ko kishiyarsa a tsakaninsu ba, amman a neman da Turhan yake mata a yanzu da kuma gudunsa da take zai iya fahimta daga rayuwarsu.
Sama yayi kadan ya sake kallon hotunan da Fatima ta turo masa, Emily ta kai mace har ta wuce, and ya yaba da yadda hotunan duka basu bayyana tsiraicinta ba duk kuwa da kasancewar ba musulma ba.
Ya fita daga chat dinsa da ita ya shiga na Turhan, ya sake karanta sakon da ya aiko masa a dazun.

 Na aureta ne a bisa cilastawar Ammy ba dan ina sonta ba, she's not my type at all, kuma adadin na ji ina sonta sai ma kiyayya ce ta ginu a tsakaninmu, har dai shedan yafi karfina na rabu da ita, amman ban cutar da ita ba

Kana ta karanta dayan sakon dake biye da shi, a take jikinsa yayi sanyi zuciyarta ta karaya, ya san abokinsa yana neman Emily, and yes ya samu Emily da kuma tabbacin ita din ce, amman yana tsoron kar haifar mata da matsala, ka ya sakata a wani hali kamar yadda ta fada, ta dayan bangaren kuma yana tunanin ya zai yi da abokinsa, idan yayi shiru anya ya kyauta masa kuwa? Ya sani idan Turhan ko mahaifiyarsa suka san da Fatima ba za su bar mata ita ba.

 Lafiya kuwa?

Aisha ta tambaya tana aje Bowl ta kunna tap ta wanke hannunta tana kallonsa irin kallon nan na jiransa.

 Tun da ka amsa wayar dazun na ga yanayinka gaba daya ya canja

 Ba komai

 Ko dai akan yarinyar da aka kora ne?

Yayi murmushi ya dago daga jikin fridge.

 Ba ita ba ne

Ya saka wayar aljihu ya nufeta ta rikata suka fice daga kitchen din tana masa zancen business din da take son ta fara.

 Watan cin kudin nawa ya tsaya kenan?

Ta kyalkyale da dariya.

 Kasan ai kana cewa na rika sana'a

 Ke da baki san kowa a nan ba, taya zaki fara sana'a, kuma kin san ina binki kudi fa

 Namiji idan namiji ya rantawa matarsa kudi daman ai bata biya, amman shi idan ya ranta sai ya biya

 Saboda shi namiji be san zafin kudinsa ba ko?

Ta saka dariya a tare suka zauna ta kwanta jikinsa tana taba jira kadan bachi yayi gaba da ita, a hankali ya zaro wayarsa wani abun na cizon zuciyarsa ya sake bude sakonta ya karanta a karo na biyar, abu ne da yake bayyana a gurin kowa, zuciyar kowace mace kyakkyawa ce, sai dai wanda ta bar shaidan ya rinjayeta, ko kuma wanda wasu gurbatatun mazan suka yi ma illa.
Akwai tambayoyin da yake bukatar amsarsu a gurin Emily, yana son ya ji kadan daga dalilinta na hana yarta da ita kanwata zuwa ga abokinsa dake nemanta kamar zai salwantar da rayuwarsa wata kila hakan ya taimaka masa gurin karfafa rokon da ta yi masa.

Sai dai kuma ba lallai ta saurare shi ba, ba lallai ta yarda ta maida shi duniyarta ta baya ba, yana bukatar ganinta face to face domin amsa masa tambayoyin da ita kadai take da amsarsu. Amman kuma? Anya zata yarda su hadu? Zata yarda ta fada masa a inda zai same ta ko ta same shi? Ya shiga contact list dinsa ya tabo William ya aika masa da sako.

 Please kana da wani information na gurin da Emily Aisha take zama

William ya masa reply Immediately.

 Wace Aisha?

 Yarinyar da ka zo kana ta santi, wata half Cast haka mai jan gashi da blue eyes

 No wani abu ne ya faru?

 Yeah sun yi fada da Amal ne, har ta bar aikin ina bukatar ganinta face to face na bata hakuri kuma na mata bayanin yadda abubuwan suke

 Meyasa ka tambaye ni? Sau daya na ganta ban sake sakata a ido ba

 Saboda baka shigowa Office ne a yanzu, na dauka ko kuna gaisawa da juna ne, na ga ta sace maka zuciya ne

 Ta sace mana zuciya dai

 Nooo sam ba abun da kake tunani ba ne, idan ma kishi kake ka daina, ni ai musulmi ne, kuma ni bata cikin tsarin matan da nake so ma?

 Bata maka kyau ba

 Bana son macen da ta cika kyau sosai, kyaun idan yayi yawa yana zama illa, kuma ni bari da burin kara aure yanzu ko nan gaba

Ya dauki William tsawon mintuna talatin kamin ya aiko masa da address din har da number gidan da take zaune.

 Thanks

Aliyu ya rubuta masa a as reply.

 Me ya hada ta da Amal?

 Idan mun hadu zaka ji

Ya amsa masa sannan ya saka wayar alijhu cikin jindadi, ya rika matarsa zuwa bedrooms dinsu bayan ya kashe komai na falon.





#TeamTurhan
#TeamVito

A ina kuke?

#KhadeejaCandy
[4/20, 10:00/ AM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: https://chat.whatsapp.com/Dfp3nf5JwbA22eFdvKklyG



*? Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen...
'?


Page 1?? 2??

Assalamu Alaikum.
Barka mu da Sallah.
Allah ya karbi ibada ya maimaita mana.



*** ***. ***.

Ta tura kofar dakin ta shiga fuskarta dauke da murmushi.

"Hello my beautiful boy"

Ya kalleta kawai ya dauke kai ba murmushi babu far'a kuma babu fushi, ta karasa kusa da shi cike da karfin guiwa ta zauna a kan gadon, hannu ta kai zata shafa shi a take ya saka mata ihu. Da sauri ta janye hannun, ta mike tsaye ta matsa gefe.

 Ka yi hakuri London I'm sorry

Ta hade yawu tana kallonsa rashin jindadin dake zuciyarta ya bayyana a fuskarta. Hannu ta saka a aljihu jean din dake jikinta ta ciro wayarsta ta yi dialing din number Vito. Ta juyawa London baya hannunta daya a kan lebenta tana cizon akaifarta idonta tab da hawaye.

 Na dauka ka yi magana da London kace min ya hakura fa

 Yeah na masa magana kuma ya hakura

 Amman na zo yanzu yana min ihu, baya son na taba shi

Vito yayi shiru for few seconds yana karantar yanayinta

"Kuka kike yi?"

"To me zan yi"

Ta fada a tsawa tana shessheka kuka kai kace shi yayi mata laifin. Daker ta iya hade yawu sannan ta kashe wayar ta juyo tana fuskantar London, rasa makamar yadda zata ba shi hakuri ya sakata ta zauna a gurin tana cigaba da kallonsa har lokacin hawaye sauko mata suke, tunanin rayuwar da ta yi kamin ta haifi London da kuma wanda ta yi bayan haihuwarsa, da yadda rayuwarsa ta zo mata, halin da ta shiga fargabar matsalar saninta da Aliyu yayi a yanzu duk suka taru suka mata tsaye a cikin kai.

Sai da ta yi da gaske sannan ta iya runtse ido tana maida numfashi a hankali, sai kuma ta kai hannu ta shafa sarkar cross din dake wuyanta. Wayarta ta fara ringing alamar kira, tana kallon kiran har sai da ya kusa yankewa sannan ta amsa ta kara a kunne ba tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login